Showing 12001 words to 15000 words out of 40846 words
da shi, gashin nan kina da na zaman falo. Ke dai a fuska ba za ce miki mummuna ba, to don Allah me namiji yake so da ba ki da shi."
Maman Nana ta yi caraf ta ce, "Jaraba fa irin ta namiji, ki duba ki ga irin magungunan da ke ɗurawa cikina Maman Dija, ke kanki shaida ce saboda Abban Nana na fara shafe-shafen man bilicin, tun da na lura yana leƙe-leƙen fararen 'yanmata."
'Ba dai leƙe ba, sai da faɗawa. Jafar ai ya yi nisan kiwo a kan alkyabbar mata.'
Maimuna ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce.
"A toh ga shi kina ƙoƙari a turaka ma na ji kin ce ba kya sanya, to wai da ba kin ce har zauce miki yake ba?"
Maman Nana ta yi ƙwafa ta ce, "Yaushe rabo? Ni yanzu rabona ma da shi ai mun kusa sati, Abban Nana da yake da jaraba wai shi ne har yake sha mini ƙamshi jiya. Ƙiri-ƙiri mutumin nan ya ce mini ba shi da lafiya..."
"Sati fa Maman Nana? Ke kuwa kina me? A gaskiya ki dawo nutsuwarki, ni fa ba don kar na faɗa ki ji haushi ba da na ce wani abu."
A zabure Maman Nana ta dafa Maimuna ta ce, "Faɗi mana, ni da ke ai kin san ba ma haka."
"Astagafirullah ba wai zargi nake ba, sai na ga ko dai budurwar tashi ce ta ɗauke masa hankali? Kin san fa 'yan'matan yanzu wallahi idonsu a buɗe yake, ba abin da ba sa yi wa sauraye ke kina can yashe a baki suna harkarsu."
"Bantan uba! Ai kuwa sai yanzu kika kamo mini bakin zaren."
Maman Nana ta furta jikinta yana karkarwa, sannan ta cigaba.
"Ai kuwa zan saka ido a kansa, wallahi idan na gano wani abu a tsakaninsu sai an maimaita yaƙin dunuya na biyu."
Maimuna ta cigaba da zuga ta, sai ta gama yi mata famfo sannan ta yi mata sallama ta tafi. Tana fita Maimuna ta saki shewa, cike da ƙeta ta ce. "Sakarya wawiya marar lissafi, in dai ni ce wallahi baƙinciki yanzu kika fara ƙunsa. Sai na raba ki da jin daɗin, da kike hura wa 'yan unguwa hanci kina faɗar ke mowar miji ce."
Ummou Aslam Bint Adam
+2347062062624
[12/02, 23:08] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.
SHAFI NA BIYAR
UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳
Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya
Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731
***
Maman Nana ta fita babu jimawa yaran Maimuna suka dawo daga makaranta, hankalinta yana kan wayarta saboda so take Jafar ya turo mata kuɗin ta goge alert ɗin. Sai da su Asiya suka ci abinci suka wuce Islamiya sannan Maimuna ta sake lalubar wayarta. Kamar ya san wayar tana hannunta nan take ta ga alert na dubu ashirin, wani irin tsalle ta buga tana riƙe baki. Jikinta har rawa yake ta shiga ɗaki ta ɗauko ƙaramar wayarta ta saka batirin ta kunna ta, a gaggauce ta shiga kiransa sai dai bai ɗauka ba don dama ta san ba lallai ya ɗauka ba sai dai ya kira ta.
"Baby yanzu na ga kuɗin ya shigo."
Maimuna ta furta muryarta har rawa take yi, jin sautin murmushin da yake yi har cikin zuciyarta ta yi. Ta mayar masa da martanin murmushin sai ta ji ya ce, "Yanzu saboda dubu ashirin kika kira? Haba my Moon, don Allah kada ki sake yi mini haka." Maimuna ta saki murmushi, tana shirin magana ta ji ya shagwaɓe murya ya ce.
"Ni fa na gagara haƙuri gaskiya, na biya ta kasuwar waya na saya miki sabuwar babbar waya wacce za mu dinga ganin hotuna da bidiyon juna."
Maimuna ta ji daɗi sosai, amma tana tsoron kada asirinta ya tonu Nazir ya gano ta.
"To ya za a yi ta zo hannuna? Kuma ni ina jin tsoron kada Nazir..."
"Idan muna magana ba na son ki dinga ce mini kina tsoron Naziru, wai wanne irin zama yake yi da ke da kike mugun jin tsoronsa."
Jafar ya katse ta cikin sauri, shiru Maimuna ta yi sai ya cigaba da cewa.
"A gaskiya alamu sun nuna ba kya jin daɗin zama da shi, a haka ka gan shi kamar na gari yana sunkuyar da kai ƙasa. Amma ya zo a jiye kyakkyawar mace, yana azabtar da ita." Sai kuma Jafar ya ɗan kwantar da murya ya ce.
"Haba my Moon, ki duba irin kulle da takunkumin da yake yi miki? Wai a haka kika iya zama da shi har tsawon shekara goma? A gaskiya an ci amanar kyau wallahi."
Jin maganganun Jafar sai suka soso mata mikin da yake ɗamfare cikin zuciyarta, kalamansa suka yamutsa zuciyarta tana jin ɗacin yaudarar da Naziri ya yi mata a shakarun baya.
"Hmmm ai Nazir ya dasa mini mikin da zai jima a zuciyata bai goge ba, lokaci kawai nake jira my baby."
"Kada ki jira lokaci Moon, kamata ya yi lokaci ya jira ki. Saboda yara uku rak ba za su hana ki rawar gaban hantsi ba. Wai ma kina kallon kanki a mudubi kuwa?"
Tambayar da Jafar ya yi mata, ya sa Maimuna ta yi saurin matsawa gaban mudubinta tana ƙarewa kanta kallo.
"Ni fa tun ranar da na fara ganinki na san Allah Ya zuba halitta, kuma wallahi duk wanda ya ganki ba zai ce kin taɓa haihuwa ba. Ba kamar waccan sakaran da ta yi shaɓar da jiki ba, dubi ƙirjinta ba kyan gani duk ya saki ya tamushe kamar an tsoma leda a ruwa."
Dariya Maimuna ta shiga ƙyaƙyatawa har da riƙe ciki, sai da ta yi mai isarta ta ce.
"An ya ba faɗa kake ba Baby don na ji daɗi, ka san fa babu laifi ƙawar tawa tana mayar da hankali wurin gyara."
Jafar Ya saki tsaki ya ce, "Hmm ke dai a yi sha'ani kawai, yanzu dai wayarki zan ba wa Maman Nana ta kawo miki gobe..."
Tun bai gama magana ba ta katse shi, "Maman Nana fa? Ka san me kake faɗa kuwa Jafar?"
Dariya ya yi a fili ya ce, "Saboda zan ba wa Maman Nana waya ta kawo miki har shi ne ya sa kike kiran sunana gatsal? Zan ba ta ta kawo miki kamar yadda na faɗa, zan ce mata mijinki ne ya ba ni sautin waya daga kasuwa. Sai na ce ta miƙo miki, amma sai na kintaci lokacin da Naziru ba ya gida don kada a samu matsala. Idan kuma na samu wata mafitar shi kenan, ko kina da wata shawarar?"
Kamar Jafar yana ganinta ta girgiza kai ta ce, "A'a babu." Sun ɗan ɗauki lokaci suna waya sannan suka yi sallama cike da kewar juna.
Fauziya tana nan zaune a gefen gado tana hawaye ta fara jin sautin munsharinsa, wanda hakan ne yake tabbatar mata da tuni bacci ya yi awon gaba da shi. Haska shi ta yi da wayar hannunta, tana ƙare masa kallo. Ta kawar da kai gefe cikin sanyin murya ta ce.
"Ya Allah Ya Ubangiji ba don ni ba, ba don halina ba. Allah ka shirya mini mijina."
A inda yake ta bar shi, ita kuma ta haye gado ta kwanta zuciyarta a cunkushe da ɓacin rai, a haka bacci ya yi awon gaba da ita. Sai da asuba ta yi cikin bacci ta ji Kabir yana tashinta, a hankali ta yunƙura ta tashi zaune. Sai ta ga ya yi mata kalar tausayi ya zauna a gefenta, ya saka hannunsa ta bayanta ya riƙo ƙugunta.
"Don Allah ki yi haƙuri Fauzina!"
Kabir ya furzo kalamansa ƙasa-ƙasa.
"Zuwa yanzu ya ci ace na haddace waɗannan kalaman naka, ka sake ni Abban Na'ima zan je na yi sallah."
Ta ba shi amsa rai a ɓace, Kabir ya riƙo ta a jikinsa tsam ya ce.
"Wallahi ba laifina ba ne, su Abbati ne suka ingiza ni amma In Shaa Allahu wannan ne ƙarshe."
"Ashe idan su Abbati suka ce ka shiga wuta sai ka bi su ko? A yanzu babu wata magana da za ka faɗa mini na yarda da kai a kan shaye-shaye. Su Abbati sun isa su yi maka dole idan kai ma ba ka so ba?"
Kabir ya yi shiru har sai da Fauziya ta gama sannan ya shiga lallashinta. Alwala ya fita ya yi, ya wuce masallaci. Bayan ya dawo cike da daɗin baki ya ce.
"Ni kuwa ya maganar Dillaliya? Allah Ya sa ta taya kayan da mutumci."
Da yake a lokacin Fauziya ta ɗan sauko ta ce, "Ta taya shi dubu saba'in har ta bada rabin kuɗin." Fauziya ta miƙe ta buɗe drower kayanta, jakar ratayarwa ta ɗauko ta zura hannu ta zaro kuɗin ciki ta miƙa masa.
"Ragowar ta ce sai bayan kwana uku za ta bayar, an jima idan gari ya waye ta ce za ta zo da wanda zai ɗauka."
Kabir ya janye hannunsa daga jikin kuɗin ya ce, "A'a ki ajiye a wurinki ko jari sai ki ja da su" Girgiza kanta ta yi ta ce, "A'a ka cika ka sayi wani abin na aikin gidan can, ka ga an rage wani abu. Idan ta kawo cikon kuɗin, kafin nan kai ma ka samu wasu sai ka haɗa da na wurinka kafin dai ranar tashinmu an rage abin da za a rage." Fauziya ta ɗan kalli ɗakinsu da shinfiɗar su Na'ima cikin damuwa ta ce.
"Na gaji da zaman da muke yi ɗaki ɗaya Abban Na'ima. Yaranmu sun fara wayo kwana da su a ɗaki ɗaya zai iya haifarwa tarbiyyarsu matsala." Kabir ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Haka ne Fauzina, amma kuɗaɗen da kike ba ni a ginin nan ina gudun wani abu a nan gaba."
Yanayin yadda ya yi mata maganar cikin sanyin murya ya sa jikinta ya yi sanyi, ta dube shi a sanyaye ta ce.
"Me kake gudu Abban Na'ima?"
"Ina gudun kada watarana wani abu ya haɗo mu ki yi mini gori, sannan tarin kuɗaɗen da kika ba ni lissafinsu nake yi. Idan Allah Ya buɗa mana nan gaba zan biya ki kuɗinki." Maganar Kabir ba ƙaramin ɓa ta ranta ta yi ba, domin duk abin da take yi wa Kabir tana yin sa tsakani da Allah ne. Tun da a ganinta rufin asirinsa tamkar rufin asirinta ne. A irin kalubalen rayuwar da ta fuskanta a kaf faɗin duniya, gida biyu ne ya zame mata gata kuma madogararta. Daga gidan mahaifinta sai gidan mijinta, gidan mijin da take fatan sai dai mutuwa ta ɓamɓare ta daga ginin turɓayarsa. Gidan mahaifinta kuwa a yanzu ba ta fata ko burin kawo wata ƙaddarar, da za ta kwashe ta daga gidan mijinta kuma aljannar duniyarta zuwa ƙangin bautar gidan mahaifinta. Amma sai ta ji Kabir yana faɗar kamalan da take jin, tamkar bai ba ta matsayin da ta ba shi a cikin zuciyarta ba. Don haka a ɗan ƙufule ta ce.
"Shi kenan tun da kai abin da ka ɗauka kenan sai ka lissafa abin da nake bin ka, tun da ai da na ba ka cewa na yi na ba ka aro."
Murmushi ya yi don ya fahimci ta ji haushi, sai ya gyara zama ya ce.
"Tuba na ke uwargida kuma amarya a gidan Kb babban tela. Haba Fauzin Kb fushin na mene ne?"
Fauziya ta ɗan kwaɓe murya a shagwaɓe ta ce, "To ai kai ne da wata irin magana."
Hira suka ɓarke da ita har gari ya ƙarasa wayewa, gabanin Kabir zai fita ta ce masa za ta je gida ta gaida mahaifinsa. Amma sai ta fara biyawa ta wurin Inna ta gaida. Fita ya yi ya sayo mata ɗan omo, sabulu da magi ƙulli bibbiyu. Ƙulli ɗaya ya ce ta miƙa wa mahaifiyarsa, ƙulli ɗaya kuma ta kai wa mahaifinta. Godiya ta zuba masa sosai, ta sake ba wa Kabir wani matsayi a zuciyarta. Domin kusan duk ranar fa za ta je gaida mahaifinta sai ya sayo wani abin ya ce ta kai masa, har turare sayo mata yake ya ce ta kai masa. Kyautatawar da yake wa mahaifinta ya sa Kabir ya sake samun fada a zuciyarta da zuciyar mahaifinta har ma da matan babanta. Don ba ta taɓa zuwa gida haka, idan ya saya wa mahaifinta abu. Ita kuma da ɗan canjin hannunta na kuɗin kitso, ko na ɗan gyare-gyaren kayan da take yi sai da saya wa matan babanta ɗan magi ko tsintsiya. Wani lokacin kuma ƙannenta take sayawa alewa ta tafi musu da shi, haka idan za ta leƙa gidan mahaifiyarsa Inna ko bai ba ta komai ba da kuɗinta take saya mata omo da ɗan abin da ba a rasa ba.
Shirya su Na'ima ta yi tsaf cikin ankon atamfa dogayen riguna, sannan ita ma ta shirya cikin doguwar rigar abaya ta ɗora babban mayafi ta yane kanta. Lokacin da za ta fita Lawisa kawai ta yi wa sallama, saboda magana mai daɗi ba ta taɓa haɗa ta da su A'ilo. Koda ita ta yi musu mai daɗi, sai sun san yadda suka yi suka mayar mata da martanin baƙar magana.
Duk wanda ya ga Fauziya da 'yan'matanta uku sai sun birge shi, saboda kusan gabaɗaya kansu ɗaya tazararsu babu yawa. Daga gidan su Fauziya zuwa gidan Inna babu nisa sosai, don a adaidaita sahu bai fi naira ɗari ba. Idan mutun bai sa ƙyuya ba ma zai iya zuwa da ƙafa.
A lokacin da Fauziya ta yi sallama a gidan Inna, Sadiya tana tsakar gida tana wanki. Inna kuma tana zaune tana ɗaurin tsintsiya. Sadiya ce ta faɗaɗa fara'arta ta ce, "Yanzu uwar biyu ba ki rufe fita ba sai kin haife mana ɗa a titi?"
Murmushi Fauziya ta yi mata, ta ƙarasa gaban Inna ta tsugunna ta ce.
"Barka da hutawa Inna."
Inna ta ɗan taɓe baki ta ce, "Wane hutu Fauziya ana fama da rayuwa." Fauziya ta sake yin murmushi saboda idan da sabo ta saba da halin Inna, domin irin matan nan ne da ba su da godiyar Allah. Saboda bakin ƙoƙari 'ya'yanta suna kyautata mata, amma duk lokacin da suka haɗu sai ta yi jajen tana cikin wani hali. A cikin yaran Inna mijin Sadiya da Kabir ne marasa ƙarfi sosai, don haka ta fi ji da matan 'yan uwan Kabir. Kuma a haka ma tana nannan da Fauziya saboda kyautatawar da take yi mata, amma Sadiya da yaranta da suke zaune a gida ɗaya kullum cikin tsangwama da kyara suke. Su Na'ima suka zube ƙasa suka gaida Inna, Inna ta taɓe baki ta ce.
"Ai dama ku ba na ganinku sai idan uwarku za ta zo, ko ban isa a turo mini ku ba ne oho." Sadiya da Fauziya suka haɗa ido suka saki murmushi a fakaice, Inna ta sake leƙen hannun Fauziya ta ga ba ta ga komai ba sai kuwa ta sake cewa.
"Kabirun ma kusan sati guda kenan ban gan shi ba, tun ranar da ya kawo mini garin tuwo da taliya. To dai nan ɗin da ba kwa son zuwa, nan ne dai gidanku tun da ubanku ma a nan ya tashi. Kuma ni na haifi Kabiru babu yadda kuka isa ku yi da ni."
Shiru su Na'ima suka yi, saboda dama babban dalilin da ya sa ba sa son zuwa wurin Inna yawan faɗanta. Sau tari Fauziya za ta shirya su musamman ranar Juma'a ta ce su zo su gaida Inna, amma suna zuwa ko zaman minti talatain ba sa yi suke tafiya. Wani lokacin ne ma suke zama su yi wasa da yaran Sadiya.
"Kai Salim ku zo ku ɗauki tsintsiyoyin nan, ke kuma Zainabu ga mafitai ki ɗauka. Yau idan kika sake ki yar mun da kuɗi wallahi sai ubanki ya biya ni kuɗina."
Inna ta furta wa 'ya'yan Sadiya tana tura musu farantan da aka jera tsintsiya da mafici. Sadiya ko kaɗan ba ta jin daɗin tallan da Inna take ɗora musu, don dai babu yadda za ta yi ne amma ba ta son tallar musamman ga Zainab da ta kasance 'ya mace.
"Inna ga wannan a yi wanki da shi babu yawa."
Fauziya ta zaro ledar daga kan cinyarta. Ina sai da ta ɗora wa su Salim farantin tsintsiya, sannan ta waiga wurin Fauziya riƙe da baki ta ce, "Oh ke dai Fauziya ba kya gajiya, to an gode madalla. Ai kuwa kin ce na sha wanki, dama kayan sawata duka sun ƙare sai masu datti. Ai ka ga masu abin kirki, amma wasu kuwa ko ƙullin gishiri ba su san su ba ni ba. Ke dai Allah Ya yi miki albarka, wannan ciki da kike ɗauke da shi Allah ya sauke ki lafiya ya sa ki haifo wa Kabiru magaji." Fauziya ba ta