Showing 18001 words to 21000 words out of 39234 words
Chapter 7 - ZUMA DA MADACI BOOK 1 Romantic Hausa Novels by Maman Teddy .txt
guda biyu hadi da mikomun,Suhaimart ga wannan ki gaida Oumma". Tsayawa nayi na kasa amsa,wanda ganin haka yasa shi kawar dakai yana shan mur. a hankali nasaka hannu na amsa ina masa gdy sannan nayo cikin gida,Murmushi yymun kan na shige ne yakira sunana.
A sanyaye na waigo.
Buden bakin shi cewa yayi innako ma mai zan ce kince a fada ma Khaleed???.
kasa basa amsa nayi sai dai dan Murmushi danayi ina mai kutsa kaina cikin soron gidan mu.
Murmushi yy hadi da nufan moton shi wanda bai tada ba sai da ya kira Khaleed ya sanar masa da ya kawoni gida sannan yajah moton,don dama a idon shi yana kallona ta Windown sama da zan fita nice bangansa ba,ganin na fita yasa shi sanar ma Huday da yake kan Hanya akan ya maidoni gida".
Bangaren Oummu Sulaym ko batayi mmkin ganin Babu Suhaimart ba,don sarai tasan Halin ta, Murmushi tayi mawa kanta,kan daga bisani ta tarkato kayan ta hadi mawa Mhiss Caterine sallama sannan ta dau hanyar tafiya gida".
Itako wannan karuwa da shigan ta side din Sir Khaleed direct falon shi ta kutsa kai kaman dakin Uwar ta,haka sauran Ma'aikata ke gayar da ita amma bi ta kansu ba tayi ba,burun ta kawai ta ci karo da Sir Khaleed yanda ta debo fitinan ta da magungunan da tasha ma cikin ta to ta sauke jarabar ta akan shi don duk don shi tayi wannan aiki...
Tafiya kawai takeyi amma jin ta take a sama,banda tsiyaya babu abun da takeyi...sai Uwar gumi da take futarwa". Fitowan sa daga Privacy kenan daure da towel a kugun sa daya hannun sa kuma yaba dauke da karamin towel yana goge sumar kansa...
Nufo sah kawai tayi gadon gadon tana wani fixgar numfashi kaman numfashin nata zai dauke duka.......
Littafin Zuma da madaci na kudi ne,VIP da Normal #200.
Transfer #200 SPC 300.Duk ta wannan number 08081202932.09137392680.
*#SHERE TO ANOTHER GROUPS*
Mu tare a episode na gaba💃🏻.
Maman teddy🧸
*Typing...✍🏻*
🎋🎋🎋🎋🎋🎋🎋
🌹🌹🌹🌹
🌿🌿
*ZUMA DA MAD'ACI*
_*(True love never end...)*_
Na
*Maman teddy🧸*
*Episode 12*
*_________________________*
*ALHERI WRITERS ASSO.📘🖊️*
*A.W.A*
```Kungiya daya tamkar da dubu,kungiya masu aiki da nazari da ilimi,Alheri sai d'an Alheri💪🏻```
*___________________________*
*بسم الله الر حمن الر خيم*
_Dedicated to my teddy🧸Wannan pagen taki ce y'a d'aya tilo😂._
*_Domun samun Littafin Zuma da mad'aci tun daga farkon sa har karshe zaki tuntubi wannan number 09137392680/08081202932._*
_*Ma'ana zaki turo #200 idan VIP,idan kuma SPC ne #300,100 kuma NORMAL kenan....*_
_*Plz don't miss dis novel,the latest Hausa nvl in 2021.*_
_*Do not miss this Novel Hajiya ta,idan baki karanta ba an barki a baya Hajjaju....💃🏻*_
*_____________________________*
Sai a sannan ya ankare da isowan ta bedroom din nashi,don haka cikin mugun tsawa da yake firgita su ya daka mata wannan tsawa ta hanyar daga mata hannu yana mai cewa"Heee Stupid get out my Hause".
Ya fadi maganan ta hanyar yi mata nuni da kofah wato ta fice ta basa wuri".
Kallon sa tayi cike da Rashin fahimtan anyah Khaleed din ta ne,Khaleed din da ta sani ne ko wani ne dai da ban. Bin jikin ta tafara yi da kallo,ko shigarta ne batayi atracting nasa ba. ganin komai nata ya baiyana masha'allah babu wani mahalukin namji da xata gufta ta gaban sa bai ji wani iri ba yasa ta kara sauke idon sa akan na Khaleed da har ilah yau Fuskan sa take a murtike kaman bai taba sanin yanda ake dariya ba".
Bakin Zeebu har rawa yake da kyar ta iya furta masa Khaleed youuuuu???.
Mtssswwww wani dogon tsaki yajah hadi da nanata kalmar I said you should get out to my Hause,Idan kuma ba haka ba i will call my guid to fushh you away... ya fadi yana kama hanyan nufan falon sa". Saurin shan gaban shi tayi gami da furta Khaleed Da gske kk na tafi na bar ma gidan ka?" Ko dai kasha wani abu ne???, Bai bata amsa ba illah ra6ata da yy ya wuce ta gyefen ta yana mai nufan farfajiyan gidan Had'i da kwala kurar Securities maza guda biyu,wanda su ke da alhakin shigar kowa Side din sa". Cike da tsawa ya fara masu bayani akan daga yau kar su sake barin wata y'a mace ta shigo side nashi ba tare da amincewar sa ba,kuma su zo su fitar masa da wancan matan". yana fadin haka ya juyahhh fuuuuu hadi da shigea ciki,wanda a falo suka ci karo da Zeebu tana mai mmkin wannan dabi'a ta Khaleed da ya bijiro mata dashi lokaci guda,don abun jin shi take tamkar a mafarki. Kafin tayi masa mgn ne tuni Security ya daka mata tsawa ta hanyar cewa" Hajiya Outt".....
Kallon Securityn tayi wanda da kaganshi kaga yare hausa bata ganshe sa ba. da kyar cike da dacin rai tace" Heee do you know Who I'm i!!?? I think you are Nonsence,ibeg give me chance to go"..tana maganan ne cike da matsanan cin bakin ciki da tashin hankali". Shi dai security matsawa baya yayi hadi da ce mata Oyyah go Out Hjy...Out". yanda kasan yana kada karya.
Haka tasa Kafan ta ta fice daga side din tana mai nufan Farfajiyan gidan don ta shiga moton ta ta sulale babu kwarin gwiwa".
Suko sauran ma'aikatan barayin nashi kowa haka ta kama kanta,don yau sun san Sir Khaleed a zuciya yake da kowa,tunda har ya bata ran ta gaban goshin sa Wato Zeebu". kowa a zuciyan sa tambayan kansa yake mai ya kawo mawa Sir Khaleed wannan Sauyi lokaci guda ne?.
Niko Suhaimart da shigana gida na tadda Oumma na tana Zaune tsakar gidan mu tana sukola,da ganina ta hau mun murmushi yyn dana furta Oumma na Barka da gida".
Da murmushi da kuma jin dadin yanda na koma kaman bani nayi ciwon ba tace lfyl Suhaimart ya aikin naki"?
Aiki Alhmdllh Oumma na".
Ajiye kayan hannuna nayi gyefen dakin mu ina mai cire hijab din jikina da furta Oumma bari na karke Sukolan!!.
Na rabaki Suhaimart " jiya fah aka sallamomu daga asibiti,ae bar sukolan nan sai kinji sauki,maxa shiga daki yanxun zan shigo nima". Tom Oumma na ga wannan!!'.
Nan na miko mata ledojin da Huday ya bani,cike da mmki Oumma ta saka hannu ta bude ledojin da nan taga daya kaji ne cikin sa,dayan kuma kayan makulashe nd iri².
Kallona tayi wanda cike da daurewan kai Tace mun Suhaimart a'inah kika samu wa'annan kayan?.
Shiru nayi na kasa cewa kala" don sai na tsinci kaina da kasa furta mata da Huday ya bani".
Muryan ta Naji tana cewa" A wurin aikin ne aka baku?.
Saurin daga mata kai nayi da ehhh,sannan kan ta bani wata tambayan nayi saurin shigewa dakin nata...Itako Oumma sam Zuciyan ta bata bata ba,amma tarasa ta hanyar da zata fasalta mawa Ranta dangane da wannan kaya dana bata".
Don tana da 100% garanti akan Tarbiyan da tabani,tasan baxan je nayo abun da zai bata mata ba,amma kuma ranta cewa take dole takuma kula da Suhaimart, don Suhaimart tamkar amana ce Allah ya bata". Bata da kowa sai itah da Zaid,shi kuma ga yanda yake,girman ajiki yake kadai.
Bangaren Sir Khaleed kuwa sosai yakejin tsanar duk wata y'an matan sa na banza,dama wanda suke masa true love duka ya watsar da lamaran su,burin sa kawai yaga ya mallaki Suhaimart, wanda da ya rufe idon shi fuskan ta kawai yake gani tana masa gizo,tana sakar masa da wannan kayatattciyar murmushi n nata,mai sakar masa da Kasala,dajin Zuciyan shi cikin Annashiwa da jin dadi".
Rufe i don shi yy yana mai furta I Really love you Suhaimart ". Sai kuma kaman wanda aka tsikara ya mike hadi da nufan wani Daki dana gani daga gyefn bedroom din nasa,bin bayan sa nayi wanda da shiga na naga ashe Achitect Room din shi ne, Wani bord ya dauka hadi da daukan kayan colouring yafara zanata a kan bord din yana mai jin duk wani dakika son ta nakuma nikkuwa a cikin Zuciyan sa, a sarari kam Addu'a yake Allah yasa Suhaimart ta kaunace shi koda kuwa kwatan son da yake mata ne, don shi sai a yanxu dayaganta ya tabbatar da itace komance fatan shi,kwanciyar hankali,kuma tabbas ya yarda da rasa Suhaimart a rayuwan shi Babban Illah ne wanda sam baxai iyah jurema hakan ba".
Haka dai yake ta drawing nata abunka ga Archetecture tuni yayi nisa yana zanata hadi da binta da kalaman masoya masu kwantar da hankali kaman tana gaban sa".
Hmmm muje xuwa masoyan Maman teddy🧸. Don nasan Tabbas zakuyu jinjina ga wannan labari mai taba zuciyan masu karan tawa. Koya Lamarin Khaleed da Suhaimart xai kasance Allah masani,muje dai Xuwa kar ku mance nice dai taku har kullum mai maku fatan Alkhairy da nuna kauna gare ku: Wato Ayshatou Moh'd ( Mmn teddy🧸).
******************************
*JIHAR GOMBE*
Nana Aysha wai tunanin me kikeyi ne haka?". Tun da yarintan ki kar kifa dorama Zuciyan ki damuwa".
Dagowa Aysha tayi hadi da kallon Ammaie da take tsaye rashin karkashin y'an nata duk ya ishe ta.Da kyar Aysha ta iya kakalo murmushin dole ta hanyar cewa" Ammie wlh bakomai,kawai dai Rayuwar Yarima Abdoul ne yake damuna,wai ace Ammie mutum har ya isa musali ya isa munxali,anki bude masa Sirrin da aka rufe tsawon shekaru,inba a sanar masa yanxu ba tom yaushe zai sani,yaushe zai shaida ni y'ar uwar sa ce ta jini,kullum yana mun kallon bare,wlh na gaji da wannan Buye masa matsayuina da akeyi". Ta fadi tana mai cuno baki gaba".
Murmushi Ammie tayi tana mai zama gyefen Diyar ta ta, A hankali ta fara mata magana cike da taushin murya,Nanah Aysha ki fahimceni,sam bana son Karajin wannan mgn daga bakin ki,kisani idan maganan nan ta fita nice za'a kira da babban kawai,wannan sirri ne datake Rufe tsawon Shekaru 30 da dori,kuma ni na sanar dake tsakanin ki da Yarima Abdol Manan ne badon komai ba sai don Ki samu soyayya daga gareshi,ta haka ne zamu shayar da fulani mmki,kuma abun da take ganin baxai yiwu ba,xataga tayiwu". Amma idan kikayi gaggawan sanar mawa Da Abdoul Manan cewa" Fulani ba mahaifiyar sa bace,tom wazaki ce mahaifiyar tasa?
Dole ne mu cigaba da Rufe wannan sirrin Har Allah ya nuna mana lokacin da komai zai fito sarari makiya kuma suji kunyah,dan hakin dama daka raina shike tsone maka ido. Nanah Aysha kicigaba da hakuri,duk hantaran da Abdoul manan zai nuna maki kar ki damu,kisani bayan wuya sai dad'i".
Nisawa Nana Aysha tayi kan daga bisani tace" Ammie shin kinji Labarin tafiyar Hamma Abdoul kuwa??.
"Wai naji ance zai tafi Zaria ne,but bansan maiye manufar Zuwan sa can din ba".
Dariya Ammie ta sakar ma diyar ta ta,kan daga busani tace" Naji lavarin hakan Aysha,Don maimartaba oready ya sanar mun,Sannan zuwan Abdoul Manan Zaria ki sani ba wani avu bane zai kai sa illah dawowan Aminan nasa wato Huday,da Khaleed.
Ammie da wayyo dadi da gaske???, indai ko Haka ne A satin nan zan tafi Murmmyn Khaleed". Nayi mata Hutu can,cox Ammie na nasan In Hamma Abdoul bai sauka gidan ta ba,to kilah baxai wuce gidan yah Huday ba".
Dan murmushi Ammie tayi cike da jin dadin maganan Ayshan,da cewa xataje yima Yayar ta wato Hajiya Zaituna Holiday don sam Aysha bata son shiga cikin jama'a,amma yau sanadin Yarima Abdoul zata je har ta jima can Garin Zaria. kai masha Allah". Abun da Ammie tace kenan,kan ta mike tana furta Aysha Abban ki na kan Hanya,bari naje na cigaba da shirin dawowan sa!!".
Tom Ammie nima yanxu inna kammala Duba magazine din nan zan fito".
Wahhh ke din ce zaki fito,bayan kin fara duba Magazine din ki na fama"!. Hmm ae nasan fitowan ki ba yanxu ba". Dariya Aysha tayi tana mai cigaba da Gyara Medical glass din ta,tana karanta wasu news.
Ita kam Ammie Juyawa tayi tana mai rufo mata kofah,a ranta tana jajan ta hali irin na Aysha,kullum ka ganta a koke duba Jaridu,idan baka ganta anan ba,zaka ganta tana watching News...Ae wannan ko shi SENATE IBRAHIM DUTSE wato ma haifin Aysha bai wannan Resarch din irin nata lokacin yana da Kuruciya haka".
Haka Ammie tayi ta zancen Zuciya har ta isah Tanfatsetsen falon ta da yasha Ado da kayatuwa har ya gaji".
Ma'aikatan ta ne suka fara mata barka da isowa",yayin da nan ta amshe su cike da karramawa irin ta matan da suka san darajar dan Adam,don yanda take masu sai da na fada duniyar tunanin Anyah Ammie Safiya da Mum Zaituna yaya da kanwa ce???. Hmm Hakan ne tunda da bakin ta Ammie Safiyya ta fadi".
*GARIN ZARIA*
Bangare na kuwa ni Suhaimart A washe gari da sassafe na kammala shiri na na tafiya wajen Aikatau dina dana saba,don haka bayan nayi mawa Oumma na sallama ne na yo waje hadi da tare me napep gudun kar na makara na samu wata matsalan dan gane da aiki nah".
A haka muka shigo G.R.A zaria,wanda jefi² nake kallon wurare dabam².
Ido na ne ya sauka kan wani gida,wanda nan take naji kirjina ya yanke ya buga,saurin dafe kirjina na nayi,ina mai karanto Ayar Allah,har na samu natsuwa,wanda duk da hakan girman gidan har Ilah yau bamu wuce ta ba,gida ne mai mahaukacin girma da tsaruwa,wanda gaba dayan sa yake mamaye da Sojoji da jami'an tsoron lafiya.Zufah ne ta hau karyomin ta koinah,tabbas a jiki na inajin na taba Rayuwa a wannan gida". Amma kuma a yaushe a wani lokaci ni ban sani ba!!!.
Dafa kaina nayi ina mai son tunowa amma na kasa,Wage dankareren gate din da akayi yasa mai Adaidaita danake ciki dakatawa don wanda aka bude ma gate din gidan ya fito sannnan muyi gaba".
Idona ne ya sauka akan sa,wanda a sarari na furta la shakka dama nasan kaine Ya Huday ". kawai sai naji zafafan hawaye na bin koinah na fuskana. Ta jikin madubin me Adaidata na kare ma Fuskata Kallo,yanda nake a kode a kuma jeme,ga wani baki da nayi,uwa duniya baxaka taba cewa Ni Suhaimart fara ce karr ba".
Share Hawayen kan Fuska ta nayi ina mai bai Uzuri A rayuwa,don tabbas wanda yasanni abaya baxaya taba cewa nice dai Suhaimart ba'.
Tayarda da napep din da yy ne yasani ankarewa da Moton Huday ya wuce,nan naga me napep din yana wani irin gudu dani,wanda cike da sanyin murya ta nace Don Allah Bawan Allah kajah ni a sannu".
Tom Hajiya" Wannan saurin dana keyi wlh badon komai bane,saboda Nayi saurin kai ki ne,Saboda kinsan mai neman takarar mataimakin Shugaban k'asa wato Alhj. Muhammad Harun Ya dawo kasannan yau...
inkuma su kafara isowa baxamu samu hanya ba".
Gumm na masa da baki,ina mai kara maimata Sunan Mataimakin shugaban kasa Alhj. Muhammad Harun...
A haka banyi Aune ba naga ya tsaya a daga nesan gidan Hajiya Zaituna don sam mutane basa rabar kofar gidan,saboda wa'annan murda² n sojojin da suke safa da marwa hadi da bin mutane da mazurai".
Sallamar sa nayi ta hanyar basa kudin sa sannan na nufo cikin gidan,ina mai gaisar da Securitie din da sojojin sannan na nufi barayin Hajiya Zaituna,don na gaisar da itah".
Hmm sosai na wulakan ta duk da daman wannan halin tanne wulakanta talaka,mussaman mai mata aiki a karkashin ta".
A haka na nufo side din Sir Khaleed, wanda da isana na tadda mhiss caterine da mataimakin ta wato Mr. faul".
Gaishe su nayi saurin yi ina mai nufan kitchen don na kammala ma Sir Khaleed breakfast.
Cike da natsuwa na fara komai,wanda ba tare da na dauki wasu lokuta ba na kammala masa,hadi da fara jera komai a kan dirning area.
Sai da na kammala komai ne sannan na daga kaina hadi da bin Agogon falon da kallo,yyn da take nuna mun karfe 7:15am.
Shiru nayi ina mamakin rashin fitowansa har yanxu,wanda a haka ina tsaye fiye da mintoci nan na nufi,wani dan daki daga wajen falon nasa yyn da nayi saurin daukan Sweaping Stick,sannan na dawo na fara gyeran falon nasa da kitchen da sauran dakunan da suke a jere a falon. Bayan na kammala ne na dauko Mopper na fara moping din ko inah na falon,da kammala wa nane na fara bin Falon da Room freshner,ina a haka na fara jiyo takonsa hadi da shakan daddadan turaren sa,don dama tuni na fahimci Sir Khaleed ma'abocin son Kamshi ne,komai nasa ka daga sai kaji yana wani irin kamshi na dabam.
Dariyar su naji wanda sam bansan shi da waye suke wannan dariya ba". Don nasan Sam Khaleed ba wani harka ne dashi ba". Ajiye Turaren hannu na nayi a gyefen wani Table,yyn da dai² suna karakowa inda nake a tsaye". dago kai na nayi,yayin da dai² yana kallo na,saurin sidda kai kasa nayi ganin hada idanun da mukayi,shikuwa murmushi ya sakar mun mai kayatarwa".
Sai da suka taho gab da nine cike da Sanyin murya na nace masu Barkan ku da isowa,antashi lafiyahh!!!?
Babu wanda ya bani amsan gaisuwa ta,wanda hakan ya haddasa mun faduwar gaba,tom kodai yaji Duk abun da nayi mawa Sulaym jiya ne???.
Hmmm nisawa nayi sannan na kuma nufan su,yyn da dai² suna zama akan dirning. Kwallah ne ya ciko mun ido,nan nayi saurin mayarwa don kar su lura,amma abun da ban sani ba shine tuni komai nawa a kan idon shi nakeyi". Ya fito ni yayi da Hannu". Cikin sauri na karaka inda suke Wanda a hankali nake komai na nafara serving nasu, don ban kuma ce masu komai ba". Shiko Sir Khaleed tuni yayi nisa a fadawa dunuyar tunani na,don Magana Abdoul manan ke masa bai ma san yana yi ba".
Komai na Suhaimart burge sa yakeyi,sam baya gajiya da kallon ta,binta yake da kallo yana mmkin Saurin kukan ta mai kama da shagwaba!!.
Sam bai san lokacin da labban sa ya furta I love u Suhaimart ba".
Due a hankali yy maganar don ita hankalin ta sam baya tare da ita ta kosa ta basu wuri,don tuni ta lura da dukan su irin samarin nan ne yan duniya idon