Showing 3001 words to 6000 words out of 39234 words

Chapter 2 - ZUMA DA MADACI BOOK 1 Romantic Hausa Novels by Maman Teddy .txt

18 Jan 2025

4023

da ganin Hamsin Me Napep ya kashe hadi da cewa shi sam kudin ba Hamsin bane. Hakuri na soma bashi,amma sai kara butsarewa yake shi sam bai san wannan ba. Hmmm Kaman mutuniyar Arxiki Oummu Sulaym ta kalleshi hadi da cewa' tom bawan Allah nawa ne kudin naka tunda ba 50 bane.
Nan kanshi tsaye yace 100 ne kudin sa. Wani wawan Dariya Oummu Sulaym tayi cike da rainin Hankali tace " Allah ko yaya na,tom gashi kuma bama da naira 1 yanxu,sai dai kayi Hakuri. Ganin Rainin hankalin da Sulaym tayi masa yasa me Napep kara tutsewa yana bala'i har mutane masu wuce mu a bakin Hanya sun fara saka mana ido. Wurgo ma Sulaym kudin yayi yana cewa wlh baxan amsa ba,sai dai ku rike duka. kai Hannu Sulaym tayi tana mai daukan kudin da ce A'a duk haka bai taso ba,kaje mayi ma sadaka. tana fadin haka taja Hannu na muka tsallaka titi hadi da barin me Napep da sakakkiyan baki.
A hanya kuwa sai da nanu mawa Sulaym rashin kyautuwar Abun da tayi,amma sai tace ai Besty haka shine dai² gobe baxai karayi ma wata ba. kinga ko ruwa da sabulu ai masiya. nidai shiru nayi mata ina mmkin Tsiwa irin na Sulaym. wanda da muka iso gidan su A unguwan Alkali tayi mun sallama,yyn da ni kuma sai da na dan kara tfy kadan sannan na isa gida...
A bakin soron mu na tadda Abokan Zaid da shi kansa zaune suna sana'ar ta su. yyn da kaina a kasa na wuce, muryan wani Abokin Zaid da ake ce mawa Aminu naji yana cewa" Babah wannan kanwan taka fa tayi,iya wuya zan fara tara kayan Aure naxo nayi ciki da itah. Banji mai Zaid yace da suba,abu daya ne najiyo tsakanin su shine zagin da zaid ke Auna masa. don fada har cikin gida ina jiyowa,arxiki na daya oummah Rabi bata nan,niko zama nayi nai shiru ina tunanin inda ta tafi da wannan yammancin.Mikewa nayi hadi da nufan rijiyar dake ysakar gidan namu na cika bokiti da ruwa sannan na nufi bandaki....
Niko Mmn teddy nan bayan shigewa n ta ban daki ne,na samu damar kare mawa Suhaimart kallo.
A takaice dai Suhaimart Yarinya ce budurwa da baxata wuce shekaru 17/18 a duniya ba. Fara ce mai kyau,wanda wuya ya disassar da hasken takoma choculate din karfi da yaji. wanda duk da haka bashi xai hana ka fahimci cewa ita din fara ce karrr ba..... Doguwa ce bacan ba,wato matsakaiciya. tana da diri mai kyau ga shape gashi kuwa har gadon baya kaman Bafillatana,amma su cikakkun Hausa Fulani ne. tana da Ball Eyes basu girma kuma farare tasss sai tsakiya baki kirin. idan tayi murmushi ko dariya dimple din ta bayyana yake sosai ga kuma hushirya kaiiii...
komai na Suhaimart na daban ce, irin sune ake cema cikin dubu da wiya a samu daya. bin gidan nayi da kallo tabbas ko makaho ya laluba yasan suna cikin Rayuwar Wahala. Bayan Minti 15 ne na fito hadi da nufan dakina,nan na dauko wasu ko daddaun atamfa mao launin kore da fari, shafa basilin nayi don ko arxikin powder bana dashi bare na saka.
Fitowa nayi hadi da nufan madafin mu don na girka abun da ya sauwaka mana. Anan na ga ma Oummah har ta kammala tuwo miyar yauki,nan na maida miyar wuta don takara xafi.... Komawa nayi na zauna ina tunanin Rayuwa ta. Lallae a Rayuwa na na baya maiye na dandana, Hmm Zuma ne ko mad'aci. hawaye ne yafara bin kuncina a sarari nace zuma,a yanxu ne nasoma dandanan mad'aci.
A haka ina a zaune har aka fara kirar sallahn magrib sannan na tashi nayo Alwala hadi da nufan daki na don na gayar da mai sama'u....


************************


Mom"mom..." iftihal ce mai kwala kirar sunan Hajiya Huwaila dake kishijgide ta dora kan D'an nata saman cin yanta tana mai shafa sumar gashin sa wanda da'alama tana rarrashin sa ne kan abun da ta saba yi kullum. Turus taja ta tsaya tana mai aikin turo Baki da kunkuni,gami da magana cikin ranta,wai shi kullum Ya Huday baya girma ne. kullum Mom ta dinga sangar ta shi,tana Rarrashin sa kan abun da ya wuce fiye da shekaru 10 da dori, Haba wannan naci dame yy kama. Muryan Mom ne taji tana ce wa oyoyo Ifteey na,wlcm back... Daurewa tayi hadi da fad'awa jikin Mom tana rungume ta. Huday ne ya tashi daga kwancen da yake fuska tamau a daure,daka ganshi xaka fahimci miskili ne na karshe gashi koba a fada maka ba,xaka fahimci sam baya son Raini.
Hajiya Huwaila ne tace" Huday yanxu yaushe ne xaka tafi Nigeria?. Mom a satin nan inshaallh. Kan ya rufe Baki Ifteehal ta amshe da cewa" What??? Nijeria?. Mom me xamuyi a wannan k'asar da mazaunan ta ma so suke su barta. Gsky ni baxan koma can ba nafi jin dadin xaman london. zan cigaba da xama da Daddy na anan. Ta fadi tana shiru sakamakon hararan da Huday ke watso mata. Murmushi Mom tayi Hadi da shafa fuskan ifteey tana cewa" No My Daughter bamu ne xa muje ba,Huday ne keson tafiya can. Saboda kula da Companyn shi. ki kwantar da Hankalin ki,Mom ta karke maganar tana mai rungumo Ifteey Jikin ta.
Shikuwa Huday mikewa yayi ya nufi side din shi hadi da kirar Mhiss Umiey wanda take Scatery din shi ce na companyn shi a Zaria, yana mai sanar mata da isowan shi.


Wannan kenan...


*GIDA NAGERIA*
Suhaimart'...Suhaimart... Oummu Rabi ke kwala kirana,wanda cikin sauri na fito daga daki na,wanda sanye nake cikin shigar uniform dina na Aiki.
Kaman daga sama naji anshekomun Ruwan xafi a jikina. saurin jah baya nayi ina ganin Abun da Oummah Rabi ta watsomun a jiki tana mai Aunah mun uban zagi kaman yar tasha....


LABARIN ZUMA DA MADACI TA KUDI CE, XAKI TURO KATIN MTN,VIP 200 VTU,#200 SPC #300 NORMAL GRP #100 DUKA TA WANNAN NUMBER 08081202932.






*Mu tare a next episode*




*Mmn teddy🧸*
*🎋✨ZUMA DA MAD'ACI🎋✨*


Na
*Mmn teddy🧸*




*ALHERI WRITERS ASSO.*


*A.W.A*


https://www.facebook.com/100186388252056/posts/100188104918551/


```Kungiya masu aiki da nazari da ilimi,Alheri sai dan Alheri```


_________________________








*Episode 3\4*




*ABIN ALFAHARI NA*
Gare ku iyaye na,Abin Alfahari na,ina matuk'ar godiya abisa tarbiyan da ku ka bani,Allah yak'ara nisan kwana Ameeen ya Rabil Alameen.


Wannan littafin sadaukar wane ga duk wani mai kaunar labrn Mmn teddy🧸, wannan yar k'aramar kuma Babban su,wanda ta saba nishad'antar daku da dadad'an littafan ta,mai sanya ku nishad'i da faranta ranku don nasan tabbas baxaku manta da littafin ta mai suna. *YAR AIKI,BAFULLATANAN RUGA* ba, Ga kuma uwa uba *DIJAMA Y'AR FULANI* Hmmm ummmm ga kuma *BINTOTO* Hmm wannan shiru xanyi don nasan bakwa buk'atar sharhi dan gane ga wannan book d'in... To a yau ita ta taho maku da sabuwa mai dauke hankali da kuma sanyaya xukatan ku, wato *ZUMA DA MAD'ACI* Dajin sunan kunsan da badak'ala, labrn da ya xo maku da sabon salon,don Alkalamin ba irin tasu bace, ku dai keep folowing💃🏻. Don tabbas xuma da Madaci shidin ko a littafan wannan marubuciya na daban ne📘❤️.


wannan book kaman yanda kuka sani ta kudi ce labarin,Zaki turo katin MTN #200 VIP, #300 SPC,#100 NORMAL. Duk ta k'ark'ashin wannan number 08081202932/ 09137392680.


*__________________________*


*بسم الله الر حمن الر خىم*


Ganin yanda Oum na keyin Huci tana shirin cafkoni,yasa ni saurin xubewa kasa jiki na na kyarma haka baki na,Hawaye kuwa tuni yaga ma wankemun fuska. oumma na don Allah kiyi Hakuri. Na fadi ina mai bin Oumma Rabi da kallo. Yyn da itakuma cike da masifa dama kowa yasan Halin Oumma na da iya masifa sam bata da ragayya. bata bar yaranta mu ba,balle kuma makota,amma Ita oumma na irin matannan ne masu kwad'ayi da son abun duniya,bata ki taje duk inda xa'aci mata zarafi ba,indai xa'a dauko kud'i a bata.Shi kuma yaya na Wato Zaid irin yaran nan yan Allah ka shirya duk da a baiyin shaye² sai shan giya da kuma caca,don duk anan kudin shi yake karewa,amma fah shi a kwai shi da girman kai,ji da kai da isaah. Don sam har gowan shi ni yake mawa,a waje ka dauka dan wani attajiri ne,mussaman yanda inna Amsa dan kudin aikatau dina. ya kwacemun yaje ya siya ma kansa sitiru sauran kuma yayi sha'anin gaban shi da su. Itako Oumma na sam hakan da yake mun Bai da mun ta,ita dai kawai na nemo na bata,Ranan ko da ban samo masu kudi ba,a wannan rana na shiga uku na nagama,don A Ranan Zaid sai yayi mun dukan tsiya. Haka Oumma Rabi... Shiru nakeyi so dayawa ina tunanin Mahaifina da yarasu, a zuciya na nace inda ya nana nan duk ta laucin mu abun baxaiyi xafin Haka ba. Haka xan zauna nayi ta zubar da hawayen da ya xaman mun jiki don bb ranan da baxanyi kukan Maraicin Uba ba. Don na tabbata da Baba na yana nan koshi Zaid din ba zai lalace haka ba.
Muryan Oumma na ya dawo dani daga duniyan tunanin da na lula na yan seconni. don Uban ki wannan tsinkakken abun ne xaki yi ma eye".
Hawaye ne xubo mun a sanyaye kunsan ni haka dabi'a ta take,sam bana da zafin nama komai nawa salala nakeyin shi. wanda a hakan a wurin aikatau din mu wasu ke kirana da Princess Suhaimart acewan su a kwaini da kasaita. niko iya sanina haka Allah ya halicceni don tun da yarinta na ake fadamun hakan.
Oumma kiyi Hakuri bari na kunna icen na dora a wuta tayi kauri.
Bata bani amsa ba,sai dai jan dogon tsaki da Tayi ta wuce cikin soron ta. Niko tuno da masifan Hajiya Zaituna yasani saurin nufan madafi na kunna icen hadi da maida ruwan kunun a kan wuta,kafin minti 10 tuni yy nan na juya hadi da nufan soron Oumma na na ajiye mata kwanan shan dana zuba kunun. ina fadin Oumma na sai na dawo. a ciki ta amsa mun da adawo lfy.
Haka na amsa ta na nufi Zsuren gidan namu ina mai Addu'an


*بسم الله توالكر ة الله ول حول ول قوات الل بالله.*
Nan na fita ina mai kuma bin ko ina na jikina da du'ai. kunsan Addu'a makarin bawa ne, da yardan Rabbi na isa gidan Hajiya Zaituna. Nufan barayin Mu nayi wanda nan na saje da ma'aikatan gidan muka cigaba da aikin mu ni da Oum Sulaym. Bamu lafa da aikin ba sai wuraren 2pm. nan muka koma side din mu don muyi Sallah sannan muci abinci sai mukoma bakin aikin mu. Na riga Sulaym sallamewa don haka sai na mike ina mai nufan Barayin Mhiss Caterine don na gaidata. A tsaye na tadda ta kowa na tajan² wanda da'alama da wani abune dasuke riyawa suna kuma kwancewa. A sanyaye cike da zakin murya ta na gaida ta. sannan na juya zan bar wurin. cikin dan Sauri Mhiss Caterine ta dakatar dani ta hanyar cewa" Immm Suhaimart Maxa ki nufi Side din Sir Khaleed ankai masa lunching kije ki gyara masa side din nasa wato bedroom sannan kiyi serving nasa. Gabana ne ya yanke ya fadi,jin kawai sunan Sir Khaleed da Shugan namu tayi, cikin sauri na daga mata kai alamar tom,sannan na juya hadi da nufan Barayin data Umarce ni. a zuciyata ko ina Mamakin Dama ya dawo kasanne?.
A haka na kutsa kai ixuwa side din danaga an kuma kara tsara shi, kyaun ko da yy baxai fadu ba. Nufan dirning din dake can daga bayan cushines wanda akayi shi daga sama nayi. nan naga babu masaka tsinke don shake yake da abuncucuwa kala². komawa nayi na Zauna ina mai zaman jiran fitowan shi. Amma fiye da Rabin Awa babu labarin sa. Tuno da yanda muke mawa Hajiya Zaituna mu muke tasota yasa ni Saurin mikewa gudun kar nayi wani laifi yasa na nufan wani falon sa,amma nan Ma baya nan, cike da addu'a na murda kofan bedroom din nasa,ina mai kutsa kaina ciki. Ban ga mutum ba,duk zare idon dana keyi,sai da dadad'an kamshi masu saka mutum jin kasala da shakan su. Ganin yanda Komai yake a tarwatse filoli duk a kasa,ga Shi kanshi gadon duk an birkita Shi yasa ni nufan Kan bed din don na gyara duk da nasan yin hakan is part of my duty... cire bedsheet din nayi ina mai sauke sauran fillows din kan wani madaidaicin Cushine. Kaman daga sama naji karar feshe turare,wanda yasa naji kirjina ya amsa gammmm.... Saurin Dagowa nayi ina mai bin idona da kallon inda kunnuwana sukaji mun kamshin turaren. Dressing mirrow ne nagani yana passing dina,yyn da shi kuma ya juya mun Baya,sai dai ina kallon shi ta jikin Madubin. Addu'a na hauyi baki na na karkarwa don a tunanina Sir Khaleed anjani ne,yanayin yanda yasaki sajen sa yakewaye fuska. gashi fuskan sa ta mau. kuma abun da ban taba gani ba,wai ace namiji daure da towel a kugun shi. Kirjin shi kuwa wasu irin kwantattun gashi laufffff² kwance a saman kirjin shi. Yanda naga fuskan shi tamau yasa Ni kwala ihu ina fadin wa'innahu Sulaimanu,wa'innahu bismillahir rahmanur Rahim,Allahu la'ilah haillahul wayyuuuu.... ai ganin bai motsa ba yasani fara takawa sadaf² wuff na fice daga bedroom din da gudu ina Haki wanda ko gabana bana gani. shikuwa Sir Khaleed dariya ne ya kubce masa,wanda rabon da yayi kaman sa har ya manta. Sai da yy mai isar sa,sannan yacigaba da kintsa kansa,yana furta wa a ransa yaushe Mom ta fara kawo kalon type din matan da yakeso aiki gidan nan?. A sarari ya furta gata miskila amma da akwai raki ga tsoro mtssswwww....yaja wani dogon tsaki yana cigaba da kimtsa kansa.


Niko da fitana daga bedroom din bana iya kallon abun dake gabana,burina shine kawai naga na bar Side din sir Khalid. Karar Glass cup din danayi ball dashi ne yasa nayi saurin waiwayo yyn da kaman daga sama naji muryan Hajiya Zaituna da shigowan ta kenan falon tana furta mun ki gyarashi da kyau. Okay Hajiya". Amsan dana bata kenan, itako shigewan ta bedroom din Sir Khaleed tayi ta barni da tattara glass cup din. don jikina babu inda baya kaekarwa.
Suhaimart badai har kin gama ba, ya akayi kk fashe wa'annan glass din?. Oum Sulym ce mai maganan tana sunkuyowa gareni da kokarin taya ni kwashewa. Murya na har Rawa yake cike da miskilanci na,nace mata" wlh Oum bada gangar nayi ba nima ban sani ba. Ayyyah Allah ya kyauta muje mu xuba a dustbeen ko?. Daga mata kai nayi hadi da barin side din.Sai da mukayi tafiya mai dan nisa don can backyarda din gidan mukaje sannan muka zubar da kwalaben.
A hanyan mu ta dawowa ce muka ci karo da mhiss caterine cike da mmki ta kallani tana furta,Suhaimart i deducted 500 naira from ur Salary. wannan ae iskanci ne. da kijamun bala'i gomma na 6ata maki. mtssswwww shashasha kawai. nan mhiss Caterine ta fadi tana mai rabani ta wuce ta gyefena. nikuma ganin haka sam bana son wasa da aiki na yasa nayi saurin nufan Side din nashi. Yyn da Nan Oummu Sulaym ta hau bina da kallon tausayi.
Da shiga na falon dai² suna fitowa daga bedroom din. Cike da rawar murya don jiki na har d'an rawa yake,a cewana na cire rai da cigaba da aiki a gidannnan. Saboda Abun da nayi ma Sir Khaleed,tabbas yanda ake fad'an rashin Mutuncin sa da tijara to nasan baxai Barni ba. K'wallah ne ya kwanta mun a ido,ni har ga Allah ban san Sir Khaleed mutum ne ba,aiyah sanina gamo nayi da aljani😢. Ace mutum ya fito yana wani digar ruwa kaman mala'ikan zare rai. Ga kyau kaman Aljani wlh na tabbatar duk wanda yaga Sir Khaleed sai ya firgita don kyaun shi da kwarjini. Duk kyaun da ake yara mun,yau naga Wanda ya nikkani 100%.
Ganin suna karaso gareni yasani saurin sidda kai ina mai Furta Sannu da fitowa Ranka yadade. Hajiya Barka da wannan lokaci".
Kallon Izzah ta watsomun kan ta ya tsina bakin ta da yasha pink jan baki,kace ba ita ce ta Haifi Sir Khaleed ba. Take care of my son ok. Ta kalleni tana cewa". A sanyaye cike da Gamsuwa nace Angama Hajiya,inshaalllh". Bata kuma tanka ni ba,haka shima Sir Khaleed da sam Hankalin sa baya kanmu,ya tatttara ma wulakanci,don latsa wayar hannun sa ma yakeyi,ni ya barni da 6arin jiki.
Tare suka isah dirning area da Hajiya Zaituna kan daga bisani nayi saurin bin bayan su kaman munafuka inah mai jah masu kujera don su Zauna kan na fara serving nasu.
Sir Khaleed ne ya Zauna ammma Hajiya Zaituna tsayawa tayi har ya zauna,sannan ta Rungume shi banji mai tace masa ba,illah Murmushi dana ga tayi tana manna masa Kiss a saman Goshin sa. nan shima ya yy mata murmushi sannnan ta fice,nikuwa da nayi nisa inah tunanin wannan soyyaya da suke ma junan su,don ko ba'afa da maka ba zah ka fahimci hakan.nan na lula duniyar Tunanin tawa Rayuwar,wanda sam banji Tafiyar ta ba sai dana kwarari kusan 10mins. Shikuwa Sir Khaleed, bai bi ta kaina ba,don latsa wayan nasa still naga yanayi. Ganin haka yasani gigif na dago ina Furta,amin Afuwa Ranka yadade... Bai kalleni ba har nayi 6a6atu na na gama,wanda ganin haka yasani saurin fara serving nashi ina mai Du'a'i. Don sai yau na tabbatar komai nawa yin shi nake too lazy.... Shikuwa sai a sannan ya dago kai hadi da daga mun,wai a dole sai a yanxu ya bani amsa ta hanyar wannan guntuwar Alaman tasa. da ina can ma ban lura ba. Sai da naga ma yi masa komai ne,naja na tsaya ina mai kwantar da murya ta da cewa" Bismillah Yalla6ai". na fadi ina mai Kallon fuskar sa,da har ilah yau baya ta kaina. Cikin wani irin tattausan murya mai cike da Gent voice din sa na tsinkayi yana cewa " Madam" Stop calling me yalla6ai,and.....mtswww yajah tsaki wanda da'alama xaka fahimci baya son mgn ya hada dogon sentence..nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login