Showing 30001 words to 33000 words out of 39234 words
Chapter 11 - ZUMA DA MADACI BOOK 1 Romantic Hausa Novels by Maman Teddy .txt
kuma cewa" Amma Genar kar muji Haushin Khaleed, wannan yarinya ne shaidaniya,don ina tunanin Wlh bata barmun Yaro haka ba".
Jin maganar da Hajy. Zaituna take zibowa yasa Genar saurin daga mata hannu alama na ya isah!!
Sannan cike da d'an bacin rai ya fara cewa" Haba Hjy,da girman ki da hankalin ki kuma? wannan mgn taki sam batayi mun dadi ba,mene naki na shiga Hurumun yara,shifa Khaleed yace yana son ta,don haka ni sam bazan masa dole ba,kuma kema idan kinyi tunani hakan muce zamu masa dole sam ba'abu mai kyau bane,ki natsu ki sa hankalin a mizani Hajy plz.
Mikewa tayi daga kishingiden da tayi daga jikin Kujera da sauri don har zufah tafara tsatstsafo masa,a sarari ta fara cewa" Yalla6ai Genar mai nakeji daga bakin ka??. Kana nufin Zaka Aurar da Khaleed da wannan yar gidan matsayatan yar talaka?.
Kallon ta yayi cike da dattako yace hajy A gaban yara fa muke,wannan duk mgnan ki bari sai mun zauna daga ni sai ke,Amma maganar Aurar da Khaleed da Wannan yarinya babu fashi,inda yana kaunar ta,Nan ya mai da Hankalin sa ga Khaleed da ya sunkuyar da kai tunda Hjy. Zaituna tafara mgnan har ta gama bai dago ba".
Amm Khaleed Ka kwanatar da Hankalin ka zan Aura maka Suhaimart indai kana sonta,kuma baxaka cutar masu da y'a ba". Don haka kaje ku fahimci juna sosai,ni Mahaifin ka na baka go Ahead,duk randa kuka shirya zan nemi iso ga Iyayen Ta". Zaro ido waje Aysha tayi tana d'an ihu hadi da Rungume Genar tana fadin Dad mun gode,Allah yabar mana kai". Murmushi yy hadi da ce mata Bakomai mama na". ku shiga daga ciki inason mgn da Mom din ku ne".
Sai a sannan Khaleed da Farin ciki ya gama cika shi yasamu bakin cewa" Tom Dad na gode,Allah yakara girma da daukaka".
Ameen Khaleed ".
Nan Aysha ta riko Hannun Khaleed cike da Murna sukayi waje".
Shiko A wannan Rana sosai Genar yaso ganin Hjy.Zaituna ta amince da mgnar nasa,amma ina sam ta kiya,har ya gaji yace shi sam Bazaiyi ma Khaleed dole ba,Aure kam zayayi masa nan kusa,tunda Yaro ya nuna yana son yin Aure kuma yana son yarinya".
Niko nace muje dai Zuwa💃🏻 .
Kar dai kumanta free page yakare daga wannan pagen,don haka idan kina bukatar cigaban wannan littafi ki tuntubi wannan Number 08081202932.
Niko tunda na shiga daki sam na kasa fitowa sai Wuraren La'asar wanda da fitowa na natadda Oumma Zaune bakin Wuta a madafi( Kitchen ), wanda da'alama tana hidimar dora abincin dare ne".
Barka Da gida Oumma". Dagowa tayi tana kallo na kan daga bisani tace mun Yowa Suhaimart, bacci kikayi ne?.
Ehhh", Amma yanxun na tashi Alwala ma zanyi".
tom idan kingama kizo inason mgn dake". Tom Oumma na". ina fadin haka na dauki Buta don yin Alwala,bayan na gama ne na nufi da na nayo Sallah.
Fitowa nayi bayan na idda sannan nashiga dakin Oumma na".
Sosai na firgita da Maganar da Oumma na ta mun,wai acewanta Bata yarda na bar aiki gidan Hjy.Zaituna ba". Kuma tayaba da Hankali na Khaleed, bata yarda ta kuma jin wata baraka daga gareni ba". Sosai Oumma ta dinga yimun fada hadi da zagi na,wanda daga karshe ne Tafara lallami na akan nayi hakuri na so Khaleed, ni danake Marainiyya mara gata Talaka,amma irin wannan mai Arxiki yazo yace yana sona nakiya". Don haka nan tace mun na kuma tunani,amma ita tana mai son sanar mun da ajiya tayi masa Alkawarin zata Aurar dani ga Shi Khaleed din,ko naso shi kona kishi wannan duk ni nasani". Nan tace na tashi na bata Wuri,haka jiki na sarai ya mutu da mgnar Oumma na,daki na na shiga don naga Oumma na Ranta ya baci, Tabbas a raina inajin Kaunar Sir Khaleed, amma ni gani nayi ni bakowa bace,bana da Uba da Asali,anyah zai kaunace ni,amma sai naga akasin haka,don a bayanan Oumma na cemun take,wai Khaleed ne Abun tausayi tunda ya kamu da son Ice matacciya wanda batason maiye so ba".
Kuka ne ya kwacemun,tuno da tijaran Hajy.Zaituna, don wlh nasan baxata taba kauna ta naba,Wanda ni kaina a halin yanxu tausayin Sir Khaleed nakeji na kurewa" Yana neman ma kansa illah duk ta kaina,yaya zanyi ni hakanan zan kokari naga hankalin sa ya natsu kaman da". Haka zan amince da shi koda ko Hjy. Zaituna kasheni ne zatayi,tunda Oumma na na kaunar sa dole ne naso shi nima". Tabbas na yarda Sir Khaleed bason yaudara yakemun ba tundaga kan Abun da yafaru a jiya".
Shiru nayi ina a Zaune naji Muryan Sulaym tana Gaisar da Oumma na,wanda kaman ba ita ta gama zagina ba,cike da harka ta amshi Oummu Sulaym hadi da sanar mata da inda nake".
Ae da Sauri ta kutso kanta daki na,muna hada ido muka saka dariya duk da damuwan dake cin Zuciya ta".
Mun ga takanmu Suhaimart, kinga wannan mai mukayi kenan,munyi gaba mun dawo baya". Murmushi nayi mata kan daga bisani nace,tom ya zanyi Sulaym,yanxu Oumma na tace sai na koma bakin aekin gidan Hjy. Zaituna ".
Na fadi cike da nuna damuwa kan fuskata". Tom meye,ae dama komawan mu dole,wai na tambaye ki tsoron Hjy.Zaituna kk ne? Wlh Suhaimart ki natsu,shin da itah zakuyi soyayya ko da d'an ta"? don haka ki share komai,wlh jiya Sir Khaleed ya ban Tausayi yanda yake Rokona akan nasa ki Kaunace shi,Har Kwallah sai da ya kwanta akan idon sa". Haba Suhaimart a wannan Zamani ki samu mai maki Wannan zafin son!?.
Don Allah ki yarda ki amince da Sir Khaleed, a ranar biki mucashe mu jagije".
Dariya nayi mata ina mai cewa" Oummu na Amince da Sir Khaleed dama tuni,amma ni tsoron Hjy.Zaituna nakeyi Wlh ". Na fadi hawaye na sakkomun kan fuska ta". saurin sharemun hawayen Sulaym tayi kan tace" Ni ina ji ajikana babu abun da zai faru,ki natsu ki maida Hankalin ki akan Sir Khaleed, don na gaya maki wani gulma,itafah wannan Iftyhal din ashe son Sir Khaleed takeyi,da yake ita yar wahala ce".
Zaro ido nayi ina cewa" kinganki ko Sulaym wlh tsiwanki shi zai jahxamana fitina".
Taba baki Sulaym tayi kan daga bisani tace" Wlh bakomai,ni wai ina tsoro ne,abun da na fada bayan idon ka shi zan maimaita koda kuwa itace a gaba na,ai kin sanni basai nace maki komai ba".
Dariya nayi ina mai cewa" Kwarai kuwa Aminiya ta kuma".
Haka dai mukayi ta firar mu muna Dariya cike da nishadi kaman kar mu rabu da junan mu".
Bangaren Huday kuwa,a wannan dare yanda yaga rana haka ya ganta,sam ya gaxa rintsawa,wanda daga karshe mikewa yy hadi da nufan Toilet ya dauro Alwala hadi da yin nafila,yana a zaune bayan idar wansa sosai yake addu'a kan Za6in Allah kuma nagari. sannan ya mike hadi da nufan falon gidan nasu". don a gidan Momy Huwailah ya kwana".
Zaxo wuce Dairning Area ne nan take idon shi ya sauka akan fuskar ta,wanda take dauke da ,sanye kuma cikin Uniform din ta mai launin skirt Dark brown da farin riga". kafe ta yayi da ido,wanda nan take lokaci daya yafara tunanin Ta a Zuciyan shi". A sarari kam furta wa yayi I really miss u my little". Cike da jin matsanancin kyewanta ya nufi Dakin ta da yake a gyefen na Momy,kutsa kan sa yayi ciki yana mai tunano abubuwa da yawa,Zazzakan muryan ta na masa amo a kunnen sa Hamma na yau Daddy na zai dawo,kuma Daddy yace next Mounth zamu bar nageria mu koma Abroad da zama,saboda Momy zata tafi karo Couse acan". Plz Hamma Huday kar mu tafi ni bana son na Rabu da Nanny na".
Kallon ta yy hadi da rungumo ta yana kallon ta da A lokacin bata fi shekaru 4 a duniya ba". No my little zamu tafi,amma baxamu dade ba xamu dawo".kuma idan ma kinason wata Nanny ne Daddy zai dauko maki wata mai kula dake,kaman wannan".
A'ahhh...Uhmmmm....Niiiiii Uh"umm. nan tafara kuka hadi da saka masa rigima akan A'a.
Jin yayi bige wani abu kaman Glass yasa shi dawowa daga duniyar tunanin da ya lulah,saurin kallon Wurin yayi yana mai saka Hannun sa yana daukan wani Cup da yake irin na glass ne,amma gyefe guda dauke da Hoton ta da ya zana ta tun a shekarun baya". Kwallah ne ya ciko masa ido kissing din Pic din nata yafara yi yana fadin kalmar I miss u my.....
Niko maman teddy bin ko'ina na dakin nayi da kallo,wanda ta ko'ina hotunan wata diyace y'ar shekara 4\5 a jikin bango dama ko wani Wuri in idona ya sauka akai. ni kaina kyaunta sai da ya fixgeni,yarinya ce kyau har kyau ko Y'ay'an turawa Albarka,nikam mashaallah kawai nake furtawa".
Kan tarkato na fito ina mai son Kawo maku Rahoto dangane da wannan yarinya amma ina gani nake babu isashen lokaci".
Amma maji a gaba".
Tun safe na tashi nayi shiri na tsaff sannan na nufi dakin Oumma nayi mata sallama akan zan tafi aiki na. da Addu'a ta bini dashi,sannan na fice ina mai jin dadi matuka da Yanda Oumma na sam bata gajiyawa da mun Addu'a hadi da samun Albarka".
Iyaye mata plz we have to take note,idan yaran mu zasu fita zasu bar gida,mu ringa kokari muna bin su da addu'a ahaka har su dawo,inshaallh zasu da cikin yardan Allah batare da wani abu ya cutar da su ba". Musamman mun san Bakin Uwa akan y'ay'anta". Don haka mu ringa daurewa munayi,in ma bazaki iyah ba,ki kokarta kisa ko shi yaron yy Addu'a kan ya fita,kaman Ayatul kursiyu,Nasi,ihlas da falak. wa'annan ma sun wadatar.
Tun da na shiga gidan Hjy Zaituna kowa ke bina da kallon Wani iri,nikam ban fi ta kansu ba,duk da na dadaru,amma haka na daure don ko Part din Hajy. Zaituna banyi ba,da ko nazo wajen wata da'ake kira da Hanne ne ta kalle ni tana cewa" Allah kam ya kyauta sai kace wata mayya??? Mtswww turrr wlh.
Tsayawa nayi na kallesu sai na girgixa kai kurum ina mai nufan Bangaren Sir Khaleed ".
Sai da nayi kuka na na gaji dana shiga kitchen,sannan bayan na yi har na gaji ne,na wanke fuska na sannan na fara aikina".
Yana kwance tundaga bedroom nasa ya fara jiyo daddadan kamshi,wanda yasa shi lumshe ido bai shirya ba". Cikin sauri ya mike hadi da fara shiryawa don da jin kamshin ya san Suhaimart din sa ta dawo gareshi,wanda a yanxu ne yake jin zai fara tsara soyayya tsaftacciya mai kuma ban sha'awa da birge duk wani mai kallo".
Niko ina aikin kaiwa da komowa ne najiyo muryan shugaban mu Mhiss Caterine cike da Harka wanda bata ta6a yi mun shi ba ta hau cewa" Suhaimart har ki karako,shine ba k zo mun gaisa ba".
Cikin sauri kuma cike da dan jin nauyin ta na ajiye wani foodflask akan Dirning Sannan nace amun Afuwa Ranki yadade,wlh naso nayi Latti ne,kuma nasan Sir Khaleed da wuri yake fita shiyasa na bari na kammala masa sai na karako".
Ehh gsky ne my dear,hakan yy kyau,kiyi komai a natse kinji"!?.
Tom nace da itah kan na cigaba da shirya Dirning din ita kuma ta fice daga Falon.
Ina a haka ne na fara shako kamshin turaren sa dayake sani karajin wani Iri,kirjina ne lokaci daya ya buga,amma sai na dake tuno da mgnar Oummu Sulaym akan na yarda na amince ma Khaleed kodon na faranta ran Oumma na,kuma kar na ta6a kosawa dashi ko gudun masa". komai yace mun na bisa da Ehhh ne".
Wannan yasani cike da natsuwa na cigaba da aiki na ina mai jin takon sa har ya iso gareni". Cikin wata irin murya mai cike da nuna So da kulawa yace mun" Barka da Safiya Hayatee na".
Dagowa nayi na kalleshi hadi da sakar masa da wani kayataccen murmushi na da ya bayyana siririn Hyshurya ta da ya karamun kyau nan nace" Yauwa Barkan ka dai Yallabai".
Dariya yasa hadi da cemun wato yau din sokana kk jin mun,wato Yalla6ai?"
Murmushi nasa masa ina mai jah masa kujera alaman ya zauna sai da ya zauna ne nace tuba nake Ranka yaded'e Afuwan mantuwa nayi fah kace kai ba Yalla6ai bane a baya".
Hmmm Ashe kin damu dani har kin rike nace banson kalmar nan". Kallon sa nayi hadi da masa murmushi kan daga bisani nace tom ni na isah nace ban damu da Oga na ba". ae dole duk abun da ya fadi na rike,da da hali ma har rubuce shi zanyi a takarda gudun mantuwa".
Na fadi ina mai jawo wani flask hadi da dauko Mug ina fara hada masa tea".
Ae koda kin manta Ni bakya laifi a waje na,kinsan shi so hana ganin Laifi".
D'an murmushi nayi cike da jin kunyan sa kan furucin sa na sunkuyar da kaina kasa.ina mai cigaba da Hada masa break din. shiko Ganin na sunkuyar da kai yasa shi dariya wanda ya kuma bayyana mun haiban sa da kamala,nan yace" Hayateee na kince ni Ogan ki ne,bayan Oga kuma fah".Kallon sa nayi sarai na fahimci mao yake nufi amma sai na dake ta hanyar cewa" Kaman ya kenan,ban fahimta ba Sir Khaleed ".
Cips din gabansa yasa ka fork yafa ci kan daga bisani yace kinga kaman ni kina da matsayi masu yawa a tare dani,daya daga ciki kuwa shine U ar my luv. inason ki Suhaimart".
Saurin dukar da kai nayi ina murmushi ina mai wasa da yatsuna,Hanne ce ta taho hadi da sanar mun da Mhiss caterine nason gani na ina kammala".
Kauda kai yy gyefe cike da Daure fuska,kaman bashi ne yake dariya ba,nan take bani kaina ba har Hanne ta tsoron sa ya kamamu". baki na har dan rawa yake cikin Sauri nace mata tom".
Muryan sa naji yana cemun tom mene? ,sai kuma ya juya yana mai kallon wannan Hanne fuska daure yace fita ki bani wuri idan kingan mu tare ba kyaba bana son ganin kowa". jiki na rawa Hanne ta fice,niko binta da kallo nayi ina tunano zagin da tamun".
Sorry Suhaimart dina,kuma mata na". Murmushi nayi cike da kunyan sa nace" Sir Khaleed yakamata kaci abinci kar lokaci ya kure maka".
Dariya yayi kan yace bakyaso nayi late ne?"
Daga masa kai nayi ina mai ci gaba da serving nasa".
Murmushi yy break din yakeyi kaman wanda ya shekara baici abinciba,tausayin kanmu ne ya kamani,don tabbas na fahimta rabon shi da cin wani abu tun randa wannan abu ya faru". Kallo na yy gami dacewa Matan kinsan meye?
Girgixa masa kai nayi alamar A'a. ajiye Spoon din sa yy yana mai cemun" na dade banci abinci mai dadin wannan ba".
Zaro ido nayi waje,ina dariya gami dacewa" A'a Rankayadade kar ka yabeni don ka burgeni fah".
Da gaske Suhaimart kin...Lovers"masoya kenan... wlh kuna birgeni fah,Aysha ce mai wannan maganan ta fadi tana mai zama gyefen Su ta hanyar jan kujera tana zama".
murmushi yy kan yace Aysha kin tashi kenan". Ehhh Hamma Khaleed, Allah ya tashemu". tom Mashaallh.ni bari na Wuce Yafadi yana goge bakin shi da Tissue yana mikewa daga zaune.
Adawo lfy Hamma". Aysha tace tana mai murmushi. Allah yasa yace gami da kallon Na danayi shiru,kallon ke maizaki cemun yamun,nan nayi dan murmushi hadi da cewa" A dawo lfy Sir Khaleed ".
Nan ya kuma budada murmushin sa yana mai cewa" Ngd Dear". Sannan cike da tokon sa na ingarman Namiji yafara takawa har ya bar falon.
itako Aysha wani irin sanyi ne takejin yana ratsata ko ba komai ta fahimci da mun fahimci junan mu". Mikewa nayi don na fara kwashe kayan kan dirning din,amma nan tafara jana da fira,wanda sam ban san lokacin da na zauna ba,a haka muka bata fiye da Awanni,sai da nace mata inada aiki da yawa ne sannan ta barni,dana fara kwashe kayan kuwa nasha mmki,don aiyah sanina Aysha macace maiji da issah don bata yarda da Raini ba sam,wai amma a yau ita take tayani kwashe flask da su bowl da mukayi amfani dashi.
Bayan mun gama ne tace mun na shirya yau zan rakata Shopping Mall tana son tayi siyayyan biki". Da tom na bita har ta fice".
Bayan Yan mintoci ne sai gata hannun ta dauke da jaka da kuma key na moto. Matan Hamma bismillah mu tafi".
Murmushi nayi mata asannan muka fito filin farfajiyan gidan,munafukai kam ansamu abun yi,nikam bamai bin ta kan mutane bane shiyasa na shiga moton kai tsaye Abu na,duk da saida tayi mun Shakiyanci wai ita zata bude mun moto,zata fara biyayya tunda yanxu,nidai Murmushi kawai nake har muka bar harabar gidan.
Wani Malla muka shiga da yake can wuraren Kongo,wanda nasha mmkin kayan da Aysha tasiya wai duk na bikin ne". Sai dai me duk abun da tasiya biyu take siya ana tacewan nawa ne da nata, Don har wani Gown mai launin dark blue ta siya mana guda biyu wai za'asa a ranan Brider's show.
Haka dai tayi tayi har muka gama sannan muka fito. Taso bani kayan amma sai tayi tunanin mubari sai an fara shagalin bikin sannan.
A wannan rana in kaganmu da Aysha ka rantse mu irin Aminan nan ne wanda suka shekaru a tare". Sosai na saki da itah muna fira,wanda sulaym taji dadi matuka data ga hakan".
A washe gari kam haka ta faru dani da Sir Khaleed don yanda yy ta mun surutu haka yau ma yy mun,hadi da fadin kalamomin so akaina sam baya ko jin kunya a bunshi,sai dai ni naji masa". Wannan karan ma cigaba da zai tafi Companyn sa cewa yy sai munje Part din Hjy. Zaituna mun gaisa daganan shima ya gaida ta". Sosai naji tsoro kuma naso nokewa,amma sai yasamun magiya akan yanzu Mom ta amince da soyayyar su,nan yafada mun duk yanda sukayi da Dad. Da haka nasamu karfin gwiwan bin bayan sa muka nufi Part din Hjy.Zaituna.
Da shiganmu Makeken falon ta na hango ta Zaune cike da mulki kunsan ta dai,nan take tsoro ya kamani,yau ni nakawo kai na,fahimta kam da yy da hakan yasa shi girgixamun kai Alamar ba komai.
Haka dai na dake na bi bayan sa,itakam Aysha dake gyefen Hjy. Zaituna ne ta daka tsalle tana ihun murna da cewa " Mom ga surukan ki taxo gaishe ki".
Nan ta nufo ni da duk na dadara tana rungumeni hadi da jawo ni,
gyara zama Hjy.Zaituna tayi tana mai Murmushi n yake naciki na ciki,a'ahhhh sannun ku da zuwa. Khaleed kune??"
Zama nayi kusa da Aysha yyn da Naji yana cema ta" Ehhh mom kin tashi lfy"?.
Lfyl Son" How was ur night?.
kan ya bata amsa ne nace Barka da