Showing 15001 words to 18000 words out of 39234 words

Chapter 6 - ZUMA DA MADACI BOOK 1 Romantic Hausa Novels by Maman Teddy .txt

18 Jan 2025

4015

ban sani ba,kuma daxu muka gama mgn da ita tace xata taho Nageria nan da Kwana biyu 2. Wani daddaciyar yawu ya hadiye da kyarrrr....murya can kasan makoshi yace Mummy ba ita ba.


Shiru Hajiya Zaituna tayi kan daga bisani ta tsaya tana observing din yaron nata,lokaci daya ta fahimta tabbas dan nata he fall deply in love...tom amma da waye??? tambayan da ta dinga mawa kanta kenan!!!. Hmm nan ta nisa tana mai ce masa Ohk tom wace ce ita ? fada mun my son" aina take YAR WAYE a Fadin Nageria?. littafin maman teddy wanda bata karanta ba anvar ta back...💃🏻


Shiru yy kan daga bisani yace Mummy ita Hayatee na ba yar kowa bace,amma ki natsu a hankali nan da Kwana 2 xan kawota ki ganta.


Hmm dan murmushi tayi don a tunanin ta shadi fada yake mata". Shafa sumar kansa ta dinga yi hadi da sakat masa AC wanda a haka da kyar Bacci yy awon gaba dashi.


Niko bayan na kammala wanka nayi sallah ne na sha kokon da Umma na ta ajiyemun hadi da korawa da magani na. saka kayan Aikatau dina nayi,sannan na fito a daki na ina furta Oumma sai na dawo".


Suhamart ina zaki tafi kina fama da kanki??.


Oumma naji sauki don Allah kar ki damu.
Shiru Oumma tayi kan daga bisani tace Suhamart don Allah ki kula,idon baxaki iya aikin ba kai dawo gida kinji? tom Oumma na tafi". A dawo lfy.


Haka na nufi gidan Hajiya Zaituna bayan napep ya saukeni na sallame sa sannnn nayi saurin shigewa gidan,don ko sasan Hajiya Zaituna baje ba,saboda makaran da nayi.nufan sasan Ogan nawa nayi direct don nayi saurin Kaddamar da aiki na,a raina ina tunanin hukuncin da zan fuskanta daga gurun sir Khaleed. don nasan yanxu ni yake jira na hada masa breakfast.
Shi yasa nayi saurin nufan barayin sa.


Shiko gaba daya Sir Khaleed yagama cika yy fam,Haushin kowa yakeji,buri n shi kawai yaji halin da Suhamart din sa ke ciki!!.
Ga kuma yan aikin da suka zo su biyu a makofin ta wai su hidimta masa,gaba dayan su sungama wulakanta don ko sun gaishe sa baya amsawa,sai daure fuska da yakeyi,ga wani hararan raini da wulakanci da yake binsu dashi. Gaban sa Laptop ce yake Operating yyn da yake sanye cikin Farar t.shirt sai boxer iya gwiwa,ko shirib nufan Companyn sa baiyi ba. don shi yau sam bai son ganin kowa sai Hayatee n sa.


Da sallama dauke a Abaki na na shigo falon,wanda kallon inda nake baiyi ba sai ma tattara laptop din sa da yy ya nufi resting room din sa. Jiki na ne yy sanyi kalau. a raina ina cewa shikenan yau naga ta kaina,Allah yasa basun sallame ni bane. musamman yanda naga su Atika na aiki na. Daga masu Hannu nayi nan cike da iyayi suka dago mun,su adole yau sun amshi aiki na,kila nima an sallame ni ne.


Sum² nafara aiki na ta hanyar nufan kitchen don dama su goge falon da sharewa suke. Banfi mintoci 30 ba na kammala masa dan abuncuwa da zai samu yy break. Muryan su Atika naji suna gulma ta hanyar cewa" kuga Wahala Matan da Ansallemi kan mhisd Caterine ta dakatar dake kinxo kina wani wahalar banza.


Gaba na ne ya fadi Kwallah ya ciko min ido. duk da haka ban bar aikin ba sai da na kammala komau sannan na dau yar wayata baby nokia. hadi da nufan Resting room din sa,don na gaishe sa daganan na Wuce gida tinda Naji ansalle meni.


Kwance na hango shi yyn dora Hannun saman koshi idon shi na kallon POP din wurin. Daga dan nesa na bude baki ina furta Sir Khaleed bar da Safiya". Banxa yy mun, wanda sai da na mamaita sannan ya tashi daga kwancen ya zauna hadi da kallona. Kasheni yy da ido wanda hakan yasani saurin sidda kai ina ambaton Allah,kat yy mun tijara sannan ya koreni,gomma ya koreni da mutunci na!.


Cikin dakakkiyar murya fuska babu wasa yace mun Zo nan". Kallon shi nayi nayi shiru ina tunanin wani abu. don nagama tsorata da shi.


Muryan shi na kuma ji cike da maxantaka yace mun tsoro na kikejiiiii???.....










*Labarin Zuma da Mad'aci na Kudi ne,ga mai bukata zaki turo #200 VIP,#300 SPC,#100 NORMAL na MTN duka ta wannan numbern 08081202932/09137392680.*








*Maman teddy🧸*
*Typing...✍🏻*


🎋🎋🎋🎋🎋🎋🎋
🌹🌹🌹🌹
🌿🌿
*ZUMA DA MAD'ACI*
_*(True love never end...)*_




Na
*Maman teddy🧸*




*Episode 11*




*_________________________*




*ALHERI WRITERS ASSO.📘🖊️*


*A.W.A*




```Kungiya daya tamkar da dubu,kungiya masu aiki da nazari da ilimi,Alheri sai d'an Alheri💪🏻```


*___________________________*




*بسم الله الر حيم الر خيم*




"Tsoro na ne kike ji?.
Shuru na masa sai da kyar na iya girgixa kai na alamar A'a. Hmm nan ya sakar mun murmushi hadi da kai Hannun shi yana shafa sajen gyefen fuskan sa yana mai kuma cemun a karo na biyu (2), Ohk tom na gane zo inason sanar dake wani abune Suhamart". Kirgina ne ya buga mun,duba da yanda naji ya wani kira sunana!!! A raina ne nace dama Sir Khaleed ya san suna na? Tom ta yaya???. ko baxa ki xo ba?. ya fadi yana kafe ni da idon sa wanda lokaci daya naji wani irin kwarjinin sa ya Rufe ni". A hankali na fara ta kowa har Zuwa inda yake a Zaune. Shiko Murmushi yake ta bina da shi har na karako inda yake. Banyi Aune ba sai jin nayi ya kamo hannu na yana Zaunar dani gyefen sa.


Cike da tsoro da mamaki na bude ido na ina kallon sa hadi da saurin matsawa nesa dashi".


Kallo na yayi yana mai kara jin wani irin kauna na yana ratsa duk wani sassa da gaba na jinin jikin shi. Cike da gentle Voice din shi ya fara cemun Sorry Hayatee,banyi hakan dan wata manufah ba. Kawai dai so nake na fada maki wani Abu!!!.


Hmm tom Inajin ka Sir Khaleed, na fadi ciki da Rawar dari wanda daka ganni kasan a tsorace nake. Dariya yy gami da cemun Okay Rufe idon ki". Kallon sa nayi cike da mmki sai kuma ganin ya kashe ni da ido yasani Bin umarnin nasa ta hanyar Rufe ido na". Murmushi yy nan yakai Hannun sa yana riko nawa hannun wanda ya sani Saurin bude idona wanda ban shirya ba. Murmushi yymun mai kayatarwa nan yace mun Okay kar ki rufe idon naki,amma plz ki tsaya yanxu xan rubuta maki wani abu ne.
Shiru nayi ina mai kauda kai na gyefe had'i da mika masa hannnun ina mai Ware taffa na gare shi. A bangaren Zuciyata kuwa sosai nake mamakin mai Sir Khaleed Zai yi mun haka?. Tom dama wai yana magana ne haka???. jin saukar Biro a kan tafin Hannu na yasa ni saurin rintse ido ina Addu'ar Allah yasa yayi sauri yagama abun nan nashi,kan wasu kuma su shigo ayi mun mummunan Zato...
Koda ya kammala Rubutun ina jin shi ya rike Hannun nawa bai sake ba kusan minti Biyar,kana ya saki Hannun nawa yana fadin Suhaimart kar ki bude hannun naki sai ba kowa kuma sai kin samu natsuwa kin kwantar da Hankalin ki waje daya kinji?.
Daga masa kai nayi ina saurin mikewa don duk na kosa na gudu na bar dakin. Sai kuma tuno da ae ni ce Zanyi Serving nashi yasa ni saurin sidda kai ina furta Sir Khaleed Breakfast dinka fah ya Kammala.
Murmushi yayi mun Hadi da cewa" Nop kije ki huta kiyi Bacci don nasan baki da lafiya And then jikin nan ki na son kulawa da hutu,kije side din ku ki kwanta kinji?.
Cike da tsantsan mamaki nake bin sa da ido da kallo wanda sai da yayi mun murmushi yasa ni saurin daga masa kai hadi da ficewa daga Restingroom din nasa wanda yana yin yanda yake bina da kallo har tuntube da yatsuna nake yi ina furtawa a zuciya ta,Allah yasa Ba iskancin nasa bane da'ake bani labari zai dawo kai na". kee Suhaimart ke awa ne da Sir Khaleed zaiyi yunkurin lalataki?. bayan ga yan mata masu ji da aji yayan hutu yayan masu da shi da kullum suna aikin sunturi a gidannan shikuma yana aikin Wulakanta su???. Zuciya ta ce tabani amsa da hakan. A haka dai nake ta tunani tom ya akayi Sir Khaleed ya san nayi Rashin lafiya. A haka dai na nufi Side din mu ina zancen zuci don a tunani na Mhiss Caterine ta sallameni kaman yanda naji Wa'ancan suna gulman su,amma abun mmki da shiga na ta nufoni tana tana shafa gyefen fuska ta da tambaya na ya karfin jikin nawa??? Anan na bata amsa da naji sauki,Oummu ce ta taso itama tana min sannu,kan mhiss Caterine tace ta kaini Dakin mu na samu na kwanta na huta,yau baxan yi aiki ba sai zuwa gobe innaji Sauki".




Haka dai Muka shiga daga ciki ni da Oummu Sulaym yyn da nan Oummu ke ta kwadun Sannu har nagaji da amsawa". Don Oummu Sulaym Sam bata gajiya da surutu haka Allah yayi ta,dakanta ta kwantar dani hadi da gyeramun fillow ina mai tayar da kai na dashi.


"Ban wani jima ba bacci yy awon gaba dani".
_____________________________


Hutawan ka Lafiya allah yajah da kwanan yarima mai jiran gado,gaban ka da baya Mulki ne jinin sarauta,Naman giwa ta fi karfin hargogowan yara,yaro maza gaexaya je kanemo tsaranka,yarima Abdoul daya tilo, hutawan ka lafiya ranka yadede...
Duk wannan kirari da ake sheko mawa Yarima bashi yasa shi daga kai ya dube su ba,sai da ya kwarari kusan mintoci 10 sannan ya daga masa kai a hankali,wanda inba ka kuresa da ido ba,tabbas da baxaka fahimci yy wani Reaction ba.
Wani bafade ne ya baxa malilin malin sa yana zaman dirshan gaban yarima duba da ya fahimci da bayani bakin yarima,Amma mulki da isah ta hana sa bude bakin. Ni dai Labban sa kadai naga yana motsi sai kuma naga Wannan ba faden ya furta angama ranka ya dade Hutawan ka lafiya...." yana fadin haka Prince Abdoul manan ya mike yyn da Fadawa nan suka tashi suna mai mara masa baya.
Shiko wannan bafade da mikewan sa ya nufi Barayin Fulani wanda a hanyansa ta zuwa suka hadu da Jakadiyya".
Sanar mata da sakon yarima yy akan yana so afara shirye² na tafiyan sa zuwa Zaria a satin nan da yardan Allah". wanda yana sanar mata ya juya hadi da nufan barayin Yarima".
Itako Jakadiyya baki Uwar magana tuni ta juya hadi da komawa barayin Uwar dakin nata Fulani don ta sanar mata da Tafiyan Yarima zuwa zaria,wanda su sam basu san mai zai kai shi can din ba".


Niko Suhaimart ban samu farkawa ba sai can Wuraren 4pm. don lokacin tuni aikin mu ya wuce sai kuma masu aikin dare sune suka amshe mu".
Waigawa nayi gyefena nan naga babu kowa don haka sai na tashi daga Zaune baki na na dauke da addu'an tashi daga Bacci".
Kaman wanda aka mintsila na tuno da Rubutun da Sir Khaleed yy mun don haka ban tsaya wata² ba na bude Hannun tawa ina mai kura dakwa² n idona don ganin mai ya rubuta mun".
Kirjina ne ta buga nan take,kara bude ido na nayi ina mitstsuke su don tunanin ko ba sa nuna mun dai² ne,Amma still abun da nagani shine dai. Nan take Gumi ya fara karyomun,kwallah ya ciko mun ido a sarari kam furtawa nake wayyo niiii...wayoooo ni Suhaimart, Sir Khaleed mai yasa zaka cemun haka???? ko so kake dan Abincin da muke samu sanadin aiki a karkashin ka shima mu rasa!!! Bakomai ni nasan a kwanannan watan Korana daga aiki yatsaya...Ina maganan ne hadi da Zubar da kwallah,banji shigowar ta ba sai muryan Oummu Sulaym naji tana cemun Suhaimart mai naji kina cewa ne? Meye Sir Khaleed din yy maki??? Kuka na rushe mata dashi ina kwantar da kaina bisa kan kafadan ta ina furta Oummu Sir Khaleed ne,shikenan zai jah mun sallama,yanxun in ankoreni ina xan je?".


Rungumo ni Oummu Sulaym tayi tana furta haba Suhaimart wlh ajiki na nakejin Babu abun da zai faru babu wlh,meye wai Sir Khaleed din yy maki ne???.
kasa bata amsa nayi sai dai kawai ware mata taffan Hannu na nayi ina mai kawar da kai gyefe. Bin Hannun nawa tayi da kallo hadi da Karanta kalmar kamar Haka: I LOVE U SUHAIMART!!! DO U LOVE ME???.
Wani ihu mai hade da kara Oummu Sulaym tasa hadi da kankane ni tana furta wayyo Suhaimart dina,yanxu tom mai zaki ce???.


Zaro ido waje nayi ina kallon ta tabbas ban taba yarda da Oummu Sulaym bata aiki da hankalin ta ba sai yau, tom ita har tana ganin na amince masa? ina badani ba,ai Sir Khaleed sam ba aji na bane,yafini kaman sama da kasa,ai Babban goro sai magogin karfe,Ana babbakan giwa wake jiyo kaurin zomo?, Ae komai kwarya ce tabi kwarya!.
Duk maganan nan a tunani na a zuciya nakeyi but unporturnetly a sarari neke ta zubo su".


muryan Sulaym na tsinkaya tana cemun" Maganan ki haka ne Suhaimart, tabbas Kwarya tabi kwarya ne,Amma kuma kar ki mance ita Kwarya ta gari..?
Don haka ni sam ban goyi bayan ki janye kiki yarda da amincewar Soyayyar Sir Khaleed ba,Amma zan maki Uzzuri akan kija masa aji na martaban ki ta ya mace. ta fadi tana mikewa wanda da'ala Oummu fushi tayi akan maganata, sai da ta kusa ficewa ne daga dakin na tsinkayo muryan ta tana cewa" Amma kisani K'awa ta wlh amincewar ki kan soyayyar Sir Khaleed kaman taimakon sa ne zakiyi,don a halin yanxu Sir Khaleed yana bukatan taimakwan mutumiyar kirki a rayuwar sa bana banxa ba". Sir Khaleed babu wasa a furucin sa da gaske yake yana Kaunar ki,kuma so na ki zama uwar yayan sa,kisani ni ba karamar yarinya bace tuntuni na dade da fahimtan hakan,duk da sunan shi miskili ne amma ya kamata tuni ki fahimci hakan!!, Don haka ni baxan maki tilas ba,Suhaimart inkin kaunaci Sir Khaleed wlh zaki ga ribar shi gaba,kuma komai kkyi ina maki Izirin yarinta".
Tana gama fadin haka ta fice daga dakin,yyn da niko da ido nabita da kallo,a sarari na furta,Wlh sam baxan amince ba,sarai nasan Halin wannan bawan Allah mata nawa yasaka kuka akan soyayyar shi agaban ido na".
ina sam ba dani ba,wai kina wani Zanga ribar shi,wani riba xanga dai asarah,don in Hajiya Zaituna tasamu labarin nan ae wlh yanda ta tsani talakan nan sai tasa ankarar da dangin mu duka...
Mtswww wlh Sir Khaleed kayi hakuri duk da nasan kawai yimun dai kkyi,inma tunanin ka ni yar iska ce tom ba haka nake ba". haka na dingi maganganu na ni kadai ina mai mikewa don nufan Bandaki nayo Alwala. Bayan fitowa na ne nayo Sallah dako idarwa na ban tsaya ko juran Oummu Sulaym ba na biyo hanyar gida,a tunani na ma Sir Khaleed xai iyah sakawa a kamo ni ta karfin tsiya. A hanya kam da zan fice gate ne na ci karo da Wata Zukekiyar Budurwa wanda ashe karu ta haura 30 a duniya, gaba daya shigar ta babu na kwarai ta saka wasu damammun Riga jecy da wandon jean kanta da wani siririn mayafi. Sarai ta ganeni don randa da taxo har fada ya kauraye tsakanin ta da wata karuwar tasa mina wurin don har dani cikin wanda suka serving nasu, kauda kai na nayi gyefe ina kiyaye ma kaina mutunci na".


Heeeee....." abun da tace mun kenan,wanda dajin hakan nasan dani takeyi yasani waigowa ina kallon ta. Arch.Khaleed na nan kuwa???... ta fadi tana wani ya tsina mun baki hadi da wani farrr da ido sai kace nine Sir Khaleed din. Daga mata akai nayi alamar ehhh,sannan ta juta hadi da nufan cikin gidan yanda ko take karkada duwawuka sai da naji mata kunya don girgixa kai nayi na wuce ganin yanda sojojin gidan da masu aiki maza ke bin Duwawun nata da kallo.
Haka kam fa fitowa na na fara takawa a kasa don a yau bana da na abun hawa,shiyasa nake takowa tundaga gidan Hajy Zaituna har cikin Layin mu.


Jiyo Horn din moto a baya na yasani Saurin juyowa hadi da tsayawa cakkk a wurin don ganin waye ke bina da Horn".
Fuskan sa sake yanda nasaba ganin sa ya fito hadi da yi mun Murmushi yana furta Har kin tashi?
Dan murmushi nayi masa ina mai kara bin sa da kallo,hadi da ce masa ehhh Yahh Huday yanxun nafito".
Kirjin sa ne ya buga jin kirar sunan da nayi masa, a zuciya n shi yana son tuno inda ya taba jin wannan murya dakuma mai kirar sa da wannan Sunan Amma ya kasa".
Ganin haka yasa shi saurin sosa kyeya yana furta tom shigo na kai ki gida" kinga yamma tayi.
Kallon sa nayi gami da dan zaro ido na waje kan daga bisani nace a'a nagode yanzun fah zan kara ka.
Daure fuska yayi gami da ce mun" okay ni wato Suhaimart ba yayan ki bene,bana da matsayin da Zance kiyi abu kiyi,amma idan da Khaleed ne ai zaki shiga ".
Shiru nayi bance masa komai ba,sai kawai na nufi moton inajin ba dadi akan tirjiyan danaso masa,Murmushi yymun cike da miskilamcin sa da ya zaman masa jini tun fil azeem ya bude mun murfin moton nashi,yana mai rufowa....Tunda muka shiga moton bai kuma cemun komai ba,sanin hali yasa ni nima Shiru ina mamakin miskilanci irin na Huday,don narasa wayafi wani tsakanin sa da Sir Khaleed.


A dai² PZ wuraren Chiken republic ya tsaya,kallona yayi yana furta mun ina zuwa Minti buyu. yana fadin haka ya fice daga moton hadi da nufan cikin wurin Chicken Republic din. Baifi yan mintoci ba sai gashi gidan baya yafara budewa sannan ya rufo hadi da dawowa gidan gaba wurin maxaunin sa yajah moton muka tafi.


Har kofar gidan mu ya sauke ni,sannan nayi masa sallama zan tafi,anan ya daka tar dani yana fitowa hadi da bude moton yana dakko wasu manyan ledoji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login