Showing 15001 words to 18000 words out of 22403 words

Chapter 6 - SARAUNIYAR KYAU Takun Tsakiya FREE PAGE'S BY Nanah KD.txt

Nanah KD   

18 Jan 2025

2102

Kidnapping idanunta suka sauka.




Mutane ne kala kala maza da mata yara da manya. Masu kuɗi da talakawa, ɗalibai da ma'aikata.








Wurin da suka saka ƴan mata daban wurin maza daban haka ma wurin ƙana nan yara daban.










"Na shiga ukuna ni Zaynerb, wannan wacce kalar ƙaddara ce ta kawoni hannun waɗannan mutanen?....."












Zaynerb tayima kanta tambayar hannu a ka cikin tsananin tashin hankali, gani take kamar mafarki take yi bawai da gaske Kidnapping nata akayi ba.








Baya Baya motar da ta shigo dajin tayi kamar zata koma inda ta fito.




Cikin sauri da an karewa gaba ɗaya kidnapper's ɗin suka sassaita manyan bindigun su ga motar da shirin su harbe koma uban waye a ciki, muddun ya nema yi musu taurin kai.




Ƙari sawa wurin motar, wannan Gabjejan mutumin baƙin ƙirin da shi ya yi, sannan ya saka baƙin hannun sa ya buɗe motar.




Da alama halinsa ne finciko mutum daga cikin mota.


Dan kuwa duka ƙarfin sa ya saka wajen finciko mutumin dake cikin motar.


Sai dai da alama wanda yake motar shima mugun ɗan taurin kai ne.




Duba da yadda Baƙin mutumin ya dage wajen ƙoƙarin finciko shi, yayin da shi kuma na cikin motar yaƙi basa damar hakan.






"Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un. Aasief ne wallahi shi ne, na shiga ukuna ni Zaynerb inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un."






Zaynerb tayi wannan maganar cikin tsananin tashin hankali na ganin mutumin da wannan ƙaton Arnen ya sama damar fitowa waje da shi ba kowa bane fa ce Aasief.












"An kara! An kara!! kwalawa sun sama labari, kai GADDAFI ya kamata muyi gaggawar barin wurin nan kafin su ƙari so, su tarar damu fa."








Ɗaya daga cikin kidnapper's ɗin ne ya yi wannan maganar ga Ƴan uwan nasa kidnapper's a lokacin da ya mayar da wayar da aka sanar da shi abin da ke faruwa ta cikin ta cikin aljihun rigar jikin sa da take ta tare alburushi.








"Wannan munafukin ne ya faɗa musu shakka babu, domin kuwa ga waya nan a aljihun sa."




Baƙin mutumin da aka kira da GADDAFI ya faɗa hakan a daidai lokacin da yake sakarwa Aasief ɗin Alburushi a tsakiyar ƙafafuwan sa.






Wani irin ihun neman taimako Neelarh da take tare da Aasief ɗin ta saki tana mai kiran sunan sa cikin tsananin tashin hankali.












Zaynerb kuwa kusan susu cewa za'a iya cewa tayi na ganin yadda jini yake tsata ta daga ƙafafuwan Aasief da ya zube ƙasa cikin tsananin Azaba.....












Mgnr Payment duk wacce tasan bata biya 300 na littafinan ba, kuma ta karanta gaskiya ina ga ban yafe ba, fisabilillah 300 ne fa kacal. 👌👊






*Idan kina shirye da biyan ɗari uku (300) kisha karatu cikin kwanciyar hankali, to ki biya ta wannan details ɗin.* 👇👇






*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*




_____


*🔥 SARAUNIYAR KYAU 🔥*
_-_👑ƚαƙυɳ ƚʂαƙιყα👑_-_






ɯ&ʂ_-_📖🖋️📲
💓 The Nainarh Kd 💓






_-_ҽρ.11_15






*💝ƚԋҽ ҽxƚɾασԃιɳαɾყ ʅσʋҽ αɳԃ ɾσɱαɳƈҽ ιɳ Ⴆιƚɯҽҽɳ ȥαყɳҽɾႦ $ ααʂιҽϝ💝*










*Lailah Mai Kyau*




A hankali take bubbuga yatsarta akan cup of coffee dake tsakiya saman teburin da suke zaune.


Kyawawan idanunta suna saman kyakkyawar fuskar sa mai cike da haiba, tana ƙare masa kallo zuciyar ta na bugawa kaɗan kaɗan.






Tun bayan kammala yadda ya kamata su ɓullo wa al'amarin Zaynerb da Aasief da suka yi, ita da Afeefah suka shirya kai tsaye suka wuce Hospital domin ganin matar da Afeefah ta taimakawa ta haihu a Restaurant.
Koda suka je anan ne suka haɗu da Sabbir, ashe wai matar da Afeefah ta taimakawa ɗin, matar Yayar shi Sabbir ɗin ne.


A lokacin sosai Sabbir da Lailah suka sha fira abin su, dama kuma suna ɗan yin waya jefi jefi da shi.




Washe gari yau ke nan, sune rakiyar Afeefah izuwa wurin tantancewa na Miss Nigeria da za'ayi anan Abuja, kiran Sabbir ya shigo wayar ta, koda ta ɗauka cike da zumuɗi sai yace ma ta, su haɗu a Restaurant ya bata Address sannan ya ƙara da faɗin haɗuwar tasu tana da muhimmanci domin akwai wata magana da yakeso ya yi ma ta.


Ba tare da ɓata lokaci ba, cikin gaggawa da zumuɗi ta shirya, sannan ta taho Address na Restaurant da ya yi ma ta kwatance.




Tsawon mintuna da zaman su a wurin, amma bai ce da ita komai ba. Ita ma haka ba tace da shi ƙala ba.






Ƙarar da wayar ta tayi ne, yasa suka dawo hayyacinsu daga Duniyar tunani da kowannen su ya lula.


Murmushi tayi bayan tayi picking call ɗin, ganin Afeefah ce ta kira ta.


"Hello Miss Nigeria To be, toh ya ake ciki ne, ya ya tantancewar ta kasance ne, Allah yasa dai munyi Nasara?."




Lailah tayi maganar cikin son jin yadda tantancewar ta kasance.






*The Queen Afeefah*💓


Murmushi tayi mai kyau, tana zama cikin haɗaɗɗiyar motar ta sannan ta bawa Lailah amsa da faɗin






"Tantancewa ta tafi yadda ya kamata, domin na shiga cikin jerin Ƴan Mata goma sha Takwas da zasu shiga Gasar Miss Nigeria da za'a Gudanar a Lagos nan da ƴan kwanaki."










"Kai Masha Allah, gaskiya naji daɗi sosai sosai, ki ce daga Miss Nigeria sai Miss World idan Mai duka ya nufa."










Lailah tayi maganar cike da jindaɗi tana Dariya.




Dariyar ita ma Afeefah ta yi a ɓangaren ta, sha re maganar Lailah ta yi tana faɗin.




"Yanzu haka ma wata ƴar ƙwarya kwaryar Party da wannan Jiddarh take ko, wannan dai Queen Of Beauty ta Kano tohm ita ce ta shirya mana Party yanzu haka ma wurin na nufa kai tsaye."




"Iyye kaga manya harda wata ƴar ƙwarya kwaryar Party za'ayi, tohm Allah ya tsare hanya yasa ku kammala lafiya ki dawo gida Muma muyi namu acan, dan nasan zuwa yanzu ya isa ace Jirgin su Aunty Zaynerb ya sauka anan Abuja tunda da wuri ta ce miki zata taho jiya da kukayi waya ko?."








"Eh haka ne, ta ce da wuri zata taho."




Afeefah ta bawa Lailah amsa cikin Murmushi.




"Okay Tohm Allah ya sauke su lafiya, ke kuma Miss Nigeria To be, asha shagali lafiya, tunda babu gayya ta."




Dariya kawai Afeefah tayi bata ce komai ba, sannan suka yi sallama.








"Uhum Mister Sabbir Mai Naira, ka wani zubamin idanu ina waya, sai kace baka taɓa ganina ba."




Lailah tayi ma Sabbir Maganar tana mayar da wayar nata cikin haɗaɗɗiyar jakar ta.






"Uhum Miss Lailah Mai Kyau ba dole na zuba Miki idanu ba, wannan kyau haka kamar wata SARAUNIYAR KYAU gaskiya kin haɗu sosai."




Sabbir ya bata amsa cikin zabga Murmushi idanun sa akan ta.






"Okay Nagode sosai, sai dai inaga muyi maganar da ta haɗa mu anan, kace Kanada maganar da zaka faɗa min mai muhimmanci, saboda haka Go ahead ina sauraren ka."








Lailah tayi maganar tana gyara zamanta idanunta akan sa, kamar yadda nasa suke akan ta.








Shiru Sabbir ya yi da alama yana tauna maganar da zai faɗa ma ta ne, bayan ƴan sakanni yaja ajiyar zuciya still idanun sa akan ta sannan yace.






"Ina son ki, Lailah da gaske ina ƙaunar ki, please zaki Aure ni?."








Tamkar saukar aradu haka Lailah taji maganar da Sabbir yake faɗa ma ta cikin tsakiyar kanta.






Ware idanunta tayi tarr, tana masa wani irin kallo mara fassara.








"Sabbir I You Mad?. So fa kace, wai kuma da gaske Ni ce kake so?, Lallai baka da aiki."








Lailah tayi maganar ranta a mugun ɓace tana miƙe wa tsaye zata bar Restaurant ɗin.






"Yes Lailah I'm Mad akan ki, tabbas na zare akan ki."






"Sabbir wallahi bani da lokacin ka fa."






Lailah ta basa amsa tana ƙoƙarin barin wurin zuciyar ta na bugawa da sauri sauri.




"Ki dakata Lailah da gaske nake Auren ki nakeson yi, wai duk menene hakan, bakya so na ko mene?."










Dakata wa tayi da tafiyar da take yi sannan ta juyo tana kallon sa da idanunta da suka yi jajur take basa amsa da faɗin








"Yes Sabbir bana sonka, kuma ban taɓa son ka ba, kawai dai a matsayin aboki na ɗauke ka, bawai saurayi ba, please ka rabu dani, bani da niyyar sonka balle kuma Auren ka, wallahi tallahi kaji ma na rantse maka?."








Da gama faɗin hakan ta saka kai ta fice daga Restaurant ɗin, bata damu da irin kallon kinyi rashin mijin Aure da ƴan matan Restaurant ke bin ta dashi ba.










Tamkar wani sakarai ko nace zararre haka Sabbir ya koma ya zauna daɓas saman kujerar ya yi zaman ƴan bori.






This is the first time da wata ƴa mace ta kalla tsaban idanun sa ta furta bata son sa balle kuma tunanin Auren sa.




Saboda haka sosai maganar da Lailah ta buga masa ta bugi zuciyar sa.




Ya kasa koda kwakwkwaran motsi a wurin.




"Bata sona kuma bata da da niyyar sona."


Haka Kawai Sabbir yake faɗa tana maimaita wa a fili zuciyar sa na tuƙuƙi.




Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un




Shi kuwa yake furta wa cikin tashin hankali, ya ya zayyi da Dakon sonta da ya ɗauko babu gammo.😣










*The Queen Afeefah*💓


Sosai suka sha Shagalin da Jiddarh Komai Naga, ta shirya musu isu isu Ƴan Mata da aka tantance domin shiga Gasar Miss Nigeria.








Sun ƙayatu iya ƙayatuwa da shagali, sun yi lafiya sun watse lafiya ko wacce ta koma state nata harda Jiddarh, dama Afeefah ita ce kaɗai ƴar Abuja, sai dai sauran suma akwai Waɗanda suke zaune a Abujan.


















Karon da taji tayi da mutum ne, yasa ta ɗago kyawawan idanun ta domin ganin ko wanene?.










A dai dai lokacin shima kuma ya ɗago nasa Blue eye ɗin ya zuba ma ta.










"Lah ashe ma kaine, na ganeka fa, ba kaine mutumin da na haɗu da kai a Shopping Mall ba, har muka yi magana akan inaso ka bani perfect perfume, kaƙi ka bani, kuma kaine wanda na gani lokacin da muke video call da Haleesat a gidan Sunainah, ko duk ba kai bane faɗa min?."








Afeefah tayi maganar ne tamkar wacce ta yi tatul da barasa, zama tayi saman kujera dake wurin idanunta da suke lumshewa akan sa.










Da hannu ya yi ma Bodyguard na sa alama da karya ƙari so wurin, dan ya lura niyyar ƙari sowa wurin yake da shi.








Haka kawai yaji yana marmarin magana da ita, ba tare da dalili ba, don kuwa ji ya yi tamkar ya taɓa jin kalar muryarta a wani wuri bayan haɗuwar da suka taɓa yi a shopping Mall.












"I You in drink?."






Ya yi ma ta tambayar da take bakinsa bayan ya zauna a kujerar dake fuskantar wacca take kai.










Zare fararen idanunta tayi cikin sauri tana ware su akan sa jin abin da yace da ita.


Kamar wata ƙaramar Yarinya haka Afeefah ta koma cikin taɓe baki da shagwaɓa kamar mai shirin kuka take faɗin.










"Wayyo Daddyna, ga wani yana kiran Shalelen ka da ƴar basara, kazo ka taimake ni..."😆




Tayi maganar kamar dai bata hayyacinta tana zaro wayarta daga Aljihun tsadadiyar jakar ta sannan ta lalubo lambar Daddyn wai da gaske kiran sa zatayi ta faɗa masa abin da aka ma ta.🤓




Sai dai rashin sa'a domin wayar a kashe take.




Dariyar gefan fuska wacca bayyi shirin fitowarta bane ta kufce masa.




"Kaga kayimin laifi huɗu ke nan ko?. Na farko ka hanani perfect perfume. Na biyu idanunka sun kusa sakawa nayi Accident. Na uku ka kira ni Ƴar barasa. Na huɗu kana yimin dariya saboda na kira Daddy wayar sa a kashe. Saboda haka saina kira maka Saurayina yanzu yazo ya ramamin...."






(_-_Mun bani🥺 Anya kuwa Afeefah qalau take kuwa 🤔_-_)










Idanunta suna lumshewa kamar mai jin bacci, a hakan Dan bala'i take lalubo lambobi cikin tsadadiyar wayar hannun ta, gajiya tayi batasan wata lamba zata kira ba, yasa ba tare da tunanin komai ba, ta danna kira da lambar da hannun ta ya kai kai.








"Kasan menene kuwa, Saurayina yana sona sosai kuma fa sunan sa 'Rishi' sannan..."




Gajiya da surutun ta da ya yi ne yasa shi tambayarta ta hanyar faɗin




"Do you know who really i am?."






Kallon sa tayi tana lumshe ido, ita ma ta mayar masa da kalar tambayar da ya yi ma ta da cewa




"Kasan ni Wacece kuwa?."




Shiru tayi sakamakon ƙari sowa wurin da wani daga cikin securities nasa ya yi.




Miƙa masa waya Baturen security ya yi cike da girmamawa sannan ya juya ya bar wurin.




"Okay pick up."


Ya faɗa a gajarce idanun sa akan Afeefah.
Murmushi ta saki ganin an yi picking call da take yi, kara wayar tayi a kunne tana faɗin




"Hello Rishi Dear kana inaaaa..."




Tsitt Afeefah tayi tana zazzare fararen idanunta sakamakon jin muryarta da tayi raɗau tana fitowa daga cikin wannan tsadadiyar waya ta gaske dake hannun sa.




"Lah wai kaine mutttt..."


Shiru tayi tana kuma zare ido dan batasan abin faɗa ba.




"Wai kina nufin kice kece Yarinyar da take takuramin da kira muddun na shigo ƙasar nan, Ke nan kece 'RISHITA'?."




*TASHIN HANKALI*😳




Rasa abin yi ne yasa Afeefah ta miƙe tsaye sannan ta ciro Takalma masu tsini dake ƙafafunta, ta gyara jakar hannunta, sannan ta kallesa tamkar wata ƙaramar Yarinya tayi masa Grin (Gwalo) kana ta ruga a guje ta ƙari sa wurin motar ta da sauri sauri gaban ta buga wa take faɗi ga Mosses Driver.










"Mosses yi sauri ka ja motar nan mu bar wurin nan tun kafin wancan mutumin mai shuɗayen idanu ya kamani."






Tayi maganar tana jefa jakar ta cikin motar sannan ita ma ta shiga ciki, shi kuma Driver Mosses ya ja motar da gudu duk ya tsorata, ya bar Park ɗin da ita.🤣😂😘








*Three Hours To Go*






Wuntsilowar da tayi daga saman Royal Bed nata ne tare da azabar da ya ziyarci dukkan ilahirin sassan jikin ta, yasa ta saki wani marayan ihu tana gungure a tsakiyar Room ɗin jikin ta nan naɗe da Blanket gaba ɗaya gashin kanta ya barbaje ya rufe ma ta fuska.










A hankali take buɗe fararen idanunta da alama Bacci bai ishe ta ba.






Miƙa tayi tana jan wata doguwar hamma, kama sumar kanta da ya rufe ma ta fuska tayi sannan ta ɗaure a tsakiyar kanta.




Hannu takai tana laluben ta wurin da zata jiyo wayar ta, jin babu alamar wayar ne yasa ta miƙe tsaye magagin baccin da tayi bai gana sakin ta ba.








Bathroom ta shiga ta wanke fuskarta sannan ta fito kai tsaye Palo ta fita dan tanada tabbacin Deejarh ce ta ɗauka ma ta wayarta ba kowa ba.






"Deejarh! Deejarh!! Wai kina ina ne zo nan ki bani wayata kafin na nemo ki."






Afeefah tayi maganar daidai lokacin da ta ƙari sa ƙofar Bedroom na Deejarh sannan ta shiga.




Can saman Bed ta hangota ta juya baya da alama Game take bugawa.






Hawa saman ɗin tayi sannan ta karɓe wayar daga hannun Deejarh ɗin tana faɗin


"Ke Deejarh yaushe kika san password ɗin da na sakama wayata?."




Tayi ma ta tambayar tana nufar hanyar fita daga Bedroom ɗin ya yin da ta dan nawa Jiddarh kira ta wayar, ba damuwa da amsar da Deejarh zata bata tayi ba.








Palo ta fita sam bata lura da Lailah dake kwance tayi nisa a Duniyar tunane tunane ba, ta ƙari sa saman 1sieter ta zauna, Deejarh da ta biyo ta a baya tana faɗin




"Lallai ma Balarabiyar India ai ba password mai wahala kika saka ba, just 'Perfect' fa kawai kika saka abu mai sauƙin."










Deejarh tayi maganar tana zama ganin Afeefah ta fara waya ne, yasa ta mayar da kallon ta kan Lailah cike da mamaki dan ita ma bata lura akwai mutum zaune a palon ba. Sai yanzu.










"Hello! da Queen Of Beauty na Kano wato Jiddarh nake magana, ko kuwa ba ita bace, dan kuwa idan ita ce Bala'i zata sha na ƙin ƙara wa..."










Dariyar ƙeta Jiddarh tayi daga ɓangaren ta tana faɗin




"Tabbas Jiddarh ke a kan layi, wacece ke magana?, idan Queen Of Beauty ta Abuja ce wato Afeefah toh ta riƙe layi akwai labarin da nakeso na bata."






Katseta Afeefah tayi da faɗin




"Tabbas wannan muryar ta Jiddarh ce mara kirki kawai, wai ma da farko menene kika sakamin da lemon da kika bani ne?."










Dariya Jiddarh ta tuntsire da ita, tuna tsiyar da ta shuka, sai da tayi mai isarta sannan ta dakata dan kanta tana bawa Afeefah amsa da faɗin.










"Allah kuwa da gangar nayi duk abin da nayi, domin kuwa gani nayi kamar kina damuwa bakyama kowa Magana a wurin anata shagali banda ke. Shiyasa ni kuma na saka miki kwayar da zai sa ki dinga zuba taɗi ko ba'a tambaye ki ba, a lemo sannan na baki ke kuma ƴar qwalama kika kwankwaɗe lemon."🤣




Jiddarh ta ƙari sa maganar cike da shaƙiyanci tana dariya cike da nishaɗi






"Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un, Aikuwa Queen Of Beauty kin cuceni kin saka na saki baki a wurin da bai kamata ba nayi abin da bai dace ba."😑














Zaro ido Jiddarh tayi cikin Dariya tana tambayar Afeefah abin da ya faru




Cike da takaici Afeefah ta kwashe duka abin da ya faru tsakanin ta da Official ta faɗa wa Jiddarh ta ƙara da cewa




"Kuma fa yanzu nasan kallon wata Fan's ɗin sa ko kuma wata muguwar masoyiyar sa yake yimin fa."




Afeefah ta ƙari sa maganar tana kyaɓe fuska cike da takaici Jiddarh ta cuceta






Jiddarh tsaban dariya batasan lokacin da ta faɗo ƙasa daga saman kujerar da take ba, faɗi take




"Aikuwa Queen Of Beauty Wannan Drama naki ya kusa kala guda da nawa, sai dai nawa akwai takaici ciki bisa naki fa."




"Okay, ke Menene ya faru dake ɗin Afeefah ta tambaya cike da qwulewa na dariyar da Jiddarh take ma ta, ga kuma Deejarh kamar wata mahaukaciya ita ma daga ɓangaren ta tana dariya na jin labarin da Afeefah ta bawa Jiddarh, ita ma Lailah duk da bata cikin yanayi na nishaɗi sai da abin da Afeefah tayi ya bata dariya.






Sai da Jiddarh ta saita nutsuwarta sannan ta koma ta zauna sannan ta fara cewa




"Queen Of Beauty Ina baki Story mun iso nan Kano lafiya mun sauka a Jirgi ni da Humaira da tayimin Rakiya, anan Airport naga wani haɗaɗɗen Guy ina baki labari kyakkyawa da shi, ƙarshe a kyau Guy nan yake.
Kin sanni bana gani na gyale, ganin yadda gaba ɗaya Ƴan matan Airport suke binsa da wani mayen kallo ne, yasa ba tare da shawara ko tunanin komai ba, na cire facemask dake rufe da fuskata sannan na cire After Dress dake saman kayana, nan fa na bayyana cikakkiyar SARAUNIYAR KYAU na, nan hankalin mutanen Airport ya dawo kaina waɗanda suka gane ni suka ƙari so wurin da muke nida Humaira cikin tafiya na gayu, gaba ɗaya suka rufe ni daga masu roƙo akan na tsaya muyi pictures, sai masu bani Biro da takarda wai nayi musu sa hannun ƙauna.


Abin takaici wanda nayi hakan danna na burgesa ya bar wurin, amma waɗannan mutanen basu gyaleni ba sai da kyar fa nake gaya miki.."










Dariya Afeefah tayi tana tambayarta da faɗin


"Ke nan dai idan na fahimta kinyi abin da kika yi ne, saboda ki burge wannan Guy sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login