Showing 9001 words to 12000 words out of 22403 words

Chapter 4 - SARAUNIYAR KYAU Takun Tsakiya FREE PAGE'S BY Nanah KD.txt

Nanah KD   

18 Jan 2025

2105

try, sai dai fa karkayi tunanin zuciyar Zaynerb nan kusa take, um'um kaɗan hakan ya burgeni fa, ka ƙara zage damtse wata ƙila nayi tunani akan ka, Malam..."


Shiru nayi dan ban san sunan sa ba, ɗaukar handbag ɗi ta nayi, sannan na nufa ƙofa, na kama handle na ƙofar zan fita najiyo daddaɗar muryarsa yana faɗin




"Okay, babu damuwa, sannan naji daɗi da hakan ya burgeki, zan ƙara zage damtse kyakkyawata kafin nan, Aasief nake karki manta da wannan."




Murmushi nayi ba tare da na juya ba nake faɗin


"Ina maka fatan Alkhairi Malam Aasief, zan zuba idanu domin ganin naka salon a soyayya."💓








*Ten Days To Go*






Ƙara kallon agogon Apple dake hannuna nayi, yau tsawon kwanaki shida ke nan da fara zuwa ta University.


Kuma tun daga wancan Ranar bamu sake haɗu wa da shi ba.


Na ɗan shiga damuwa kaɗan, don ina tunanin wata ƙila, yaji bazai iya bane, ya kama kansa.




Tsaye nake ina jiran taxi domin Drivern Madam Joy da yake zuwa ɗaukata bai sama damar zuwa yau ba, sakamakon matar sa dake naƙuda, ita kuma Lovely bata state ɗin ma gaba ɗaya, yayin da Madam Joy aiki ya yi ma ta yawa a office saboda haka ba za ta sama damar zuwa ɗaukata ba.






Ba tare da tunanin komai ba, na shiga cikin taxi ɗin da tayi parking a gaba na, ina faɗin Address da za'a kaini tare da tambayar kuɗin




"Okay...Madam babu damuwa ae ba saikin biya komai ba, kyauta zan kai ki."


Da sauri na dakata daga ɗauko kuɗi da nakeyi a handbag ɗi na, cikin firgici na juya ina kallon sa.




Ba kaɗan ba naji daɗin ganin sa, sai dai ban nuna masa ba, saima kyaɓe fuska da nayi ina faɗin




"Har yanzu Ban san komai akan ka ba, gashi kanata bibiyata."




Nayi maganar ina kallon gefen titi dan kuwa so nake nasan wani abu a kansa, shin kuwa shiɗin Balarabe ne ko kuma Bature?.




"Firstly Sunana Mohammed Aasief Yaro wajen Hasheem Mai Waje!."


Ni da Ahalina gaba ɗaya muna zaune ne a ƙasar America. Ina karatun Injiniyanci ɓangaren gine-gine sannan ina matakin ƙarshe. Hakan ya isa ko kina son sanin wani abun?."


Ya yi min maganar yana kallona ta madubin motar.


Fuska ɗauke da murmushin dana kasa ɓoyewa nake cewa


"A'a hakan ma ya isa."




"Uhum bani labari mana?."




"Labari kuma akan ne?."


Na tambaye shi


"Akan ki mana da kuma Ahalin ki."




Ya bani amsa.


Shiru nayi dan ban san ta yadda zan fara basa labari akan kaina ba wallahi.




Wawan burki yaja da ƙarfi wanda sanadiyyar hakan sai da nayi gaba na bugu da kujera sannan na dawo baya kaina ya bugu.




Cikin zafin rai ya ɓalle murfin motar ya fita, ƙari sawa wurin Baturen da motar sa ta bugi namu muka kusa hatsari ya yi.


Cikin zafin rai da ɓacin sa ya shiga bawa wannan Baturen mari yana ƙara wa.
Faɗi yake.
"Baka da hankali ko wato kasha giya kazo kana tuki salon kaja mana hatsari."


Bugun sa yake yana ƙara wa haɗe da Ball da shi, a titin.




Cikin sauri na buɗe motar na fito sannan na ƙari sa wurin ina jansa baya cikin basa haƙuri ganin yadda yake dukan Baturen babu ji babu gani, kuma nasan duka akaina ne, sakamakon buguwar da nayi ne ransa ya ɓaci, jansa baya nake ina basa haƙuri cikin faɗin




"Ya isa Aasief ya isa haka baka ganin jini kake fitar masa ya isa mana."




Bai kulani ba sai ma ƙara kaimi wurin ball da Baturen da ya yi.




*Tashin Sence*


Zuwa lokacin fa na fara tsorata da irin zuciyar da yake da shi.
Baya nayi ina kallon ikon Allah cikin rashin abin yi.






*A Taƙaice*
Bamu muka bar titin nan ba har sai da police suka zo suka ɗauka report.




Da kyar suka barmu muka tafi wai dan ma an gwada Baturen ne an tabbatar giya yasha kuma yake tuƙi.


Fushi nayi sosai da abin da ya faru domin kuwa ko na gansa bana masa magana domin tsoron irin zuciyar sa nake.




Tsawon Sati guda muna hakan Kullum sai mun haɗu, takai har makarantar mu ya fara zuwa domin na kulasa, amma naƙi.




Daga ƙarshe da takurar sa ya isheni haƙura nayi.
Muka ci gaba da mu'amula kullum kafin ya tafi nasa makarantar sai ya fara zuwa ya kaini nawa sannan ya wuce.




Cikin Wata ɗaya da zuwa ta ƙasar Amsterdam da kuma haɗuwa dashi sosai muka shaƙu da juna abin kamar almara, sai dai muna yawan samun matsala dashi akan zafin zuciyarsa, amma daga baya komai tsananin faɗan da muka yi muna dawowa mu shirya abin mu.


Sai dai har yanzu fama yake dani akan na furta masa ina san sa amma naƙi.






Yauma zaune nake saman table a cikin wani wurin shaƙatawa da kuma buga Troupe.(Wasan Tebur).


Kallon nake cikin Murmushi ina gyara riƙon da nayiwa Jakata a kafaɗa nake faɗa masa.


"Ka iya sarrafa fushin ka Aasief, hakan ba daidai bane ka dinga ɗaukar fushi akan ƙana nun Abu."




Nayi maganar ina juya fuska ta gefe tuno abin da ya faru yau da zamu shigo wurin, duka sosai yayima wani matashi akan yayimin kallon bariki.






"Nima banason wani abu ae."


Ya bani amsa yana daka tawa da abin da yake yi.


Da mamaki na saki baki ina kallon sa.


Shi kuma ya ci gaba cewa.


"Abin da kike yi ne, har yau da baki ce ki naso ba! Ah sam bana son hakan."




Murmushi nayi ina miƙe wa tsaye cikin gyara Jakata.




"Saurayi idan ya nuna ƙaunar sa a wurin Budurwa, ta ce saita tsaya tayi tunani kafin ta yanke hukunci, hakan yana nufin tuni ta amince, sai dai mu ce mun amince ne, sam bamayi."




"Me yasa?.".


Ya tambaya cikin sauri.




Murmushi na kuma yi.




"Irin daɗin da kuke ji idan mace ta mutu akan ku, toh muma irin daɗin muke ji, idan Namiji ya dinga bibiyar mu.
Humm.
Kasan irin jin kan da muke yi kuwa yayin da muka ga Namiji yana bibiyar mu, mu haka mata muke. Ka fahimta?..."




"Toh ke nan tun daɗe wa kika amince dani?."


Ya tambaya.


"Kana tan tama ne?."


Na basa ina juyawa zan wuce.
Fuskata ɗauke murmushi na musamman cike da jindaɗi.




*Bayan Wani Lokaci.*


Shaƙuwa ce ta musamman mai zaman kanta ta ƙara shiga tsakanin na da Aasief Mai Waje, sai dai har lokacin bance da shi ina son sa ba, haka kuma yake haƙuri dani sosai, domin abin da nakeso yake yi komai wahalar sa kuwa.


Cikin Abokan karatu na da ma ƴan makarantar mu sosai suka saba dashi saboda yawan zuwa makarantar wurina da yake yi.


Yau ma kamar kullum muna zaune ni da shi saman Benchi doguwa muna fira a cikin makarantar mu wurin hutawa.






Miƙe wa tsaye nayi cikin tsananin tashin hankali da tsoro, hango Tantiri a makarantar mu da nayi suna tahowa wurin da muke shi da abokan sa wajen su bakwai dukkanin su mabanbantan ƙasashe suke.
Leo Tantiri ne na ƙin ƙara wa a makarantar mu ya tara Laifuka akan sa babu adadi cikin makarantar, kuma babu abin da ake iya masa sakamakon kuɗaɗen da iyayen sa suke dashi.


Asalin sa ɗan ƙasar ne, cikin Tantiran Abokan sa akwai Rahul ɗan ƙasar India, akwai Indivisi ɗan Poland da dai sauransu, suna tsula tsiyar su yadda suke so, babu mai taka musu burki.




A haukar sa Leo ɗin wai sona yake tun ganin da yayimin na farko a makarantar yake bibiyata, ban taɓa kulasa ba, kuma ban faɗa wa Aasief ba sanin irin zuciyar sa.
Kuma duk zuwa makarantar da Aasief yake basu taɓa haɗuwa da Leo ɗin ba.




Gashi yau komai ya rincaɓe Leo ya ganni da Aasief ban san menene zai biyo gaba ba.😓




Ƙari sowa wurin sukayi ja-ja-yen idanun sa akaina, nima nawa akansa, yayin da na Aasief idanun sa suke akan mu duka cike da mamaki.


Karɓar wani abu kamar gyalle kamar igiya siriri ya yi daga hannun Rahul, sannan ya miƙo min yana faɗin.




"Karɓa wannan."


Karɓa nayi da mamakin menene abin.




"Kin san wacce rana ce gobe?."
ya tambaya


A'a
Na basa amsa, ya ci gaba da cewa


"Ranar shagalin raki ce, bisa al'adar Indiyawan nan makarantar kowa a yau yake shagalin sa Saboda haka karɓi wannan ki ɗaurawa mai."


"A'a."


Na basa amsa.


"Ki ɗaura mai."




Ya kuma faɗa
"A'a."
Nima na kuma faɗa in seriously


Tsawa ya buga min da faɗin


"Ke ba haka nace ki ɗaura masa ba?."


Je far da abin da ya kira da raki ɗin nayi ƙasa ina basa amsa da faɗi cikin tsawa.


"Nima ba nace a'a ba."




Tsayawa kowa daga ɗaliban makarantar ya yi da Abin da yake yi suka mimmiƙe tsaye suna kallon mu.


Kallon kallo muke tsakanin Ni da Leo sannan na fara magana cikin ɗa ga murya.




"Zan iya kiran ka da Yaya."


Na nuna sa, sannan na ci gaba.


"Na kira wannan, na kuma kira wancan, zan iya kiran ko wani Namiji da Yaya a makarantar nan, amma banda shi, saboda Ina Son Sa..."




Juyawa nayi ina kallon Aasief dake sakin ƙayataccen Murmushi na jindaɗi sannan ta ce ina kallon cikin idanun sa


"Aasief Ina Son Ka, da duka zuciya kuma zan Aure ka."


Juyawa nayi na kama hanya nabar wurin fuskata a ɗaure tamau.




"Ke Kyakkyawa ta nima Ina San Ki!!."


Murmushi nayi ba tare dana juyawa ba.




Kallon gargaɗi kawai Aasief yake bin Leo da tawagarsa dashi yana karkaɗa hannu.


Sannan cikin sauri ya biyo baya na cike da jindaɗi, yau dai na faɗa Ina San sa cikin tsakiyar makaranta gaban dubbanin ɗalibai.💃💃






*Zaynerb 💓 Aasief 🤙*




Tun daga wannan Ranar wannan lokaci cikin wannan taƙin.


Salon rayuwata da na masoyina Aasief ya canza.
Dan kuwa wani irin so da ƙauna mara misaltawa muke yi wa junan mu, abin kamar almara.






*One Month Later*


Yauma tsaye nake gefan titi ina jirar ƙari sowar Bus da zata kaini zuwa paint class da yake bani lecture Ranar.


Sanye nake da Doguwar riga da kuma wando irin dai na Pakistan nayi rolling kaina da mayafin rigar, sosai nayi kyau, ina saɓe da handbag ɗi ta.




Gefana kuwa mutumin nawa ne tsaye shima sanye cikin t-shirt da wando jeans ya saka p-cap idanun sa rufe da glass hannayen sa cikin aljihun wandon sa.






"Idan kin kammala ƙare min kallon ki matsa gefe."


Saurin kawar da kaina gefe nayi jin abin da yace ashe yana lura dani.






"Gefe kuma saboda me?."


Na tambaya da mamaki.




"Ke dai ki matsa nace idan kuma ba haka ba, Karki zarge ni da koma miye ya biyo baya aha."






Dariya nayi sannan kuma ban matsa ba, don ni kaina nasan ina da mugun taurin kai.


"Tabbas idan baki matsa gefe ba zaki sumba ce ni a wannan taƙin."


Dariyar rainin wayo na kuma yi ina faɗin
"Lallai toh ma na karɓa Challenging ɗin sannn."




Ban rufe baki ba, na zaro manyan idanuna cike da tashin hankali ina kallon ƙaton karen turawan da ya tunkaro ni, wani ƙato dashi jikin sa gaba ɗaya gashi ne, launin Fatar sa brown, daga bayan sa mai kula da shi ne yake biye da shi cikin fella gudu a son sa na ya tsaya, sai dai ina wannan tunkaro ni kawai yake tamkar wanda ake basa umarni.


Kwata kwata na kasa motsi sai faman zare ido nakeyi ina jiran tsammani don kuwa banajin karen nan idan ya ƙari so wurin bazai yi yaga yaga da nama na a ɗanye ba.






Cikin zafin nama Aasief dake gefena ya kamo hannuna da hannun sa ɗaya yayin da ɗayan ya jefa wa wannan karen key's dake hannun sa.






Gaba ɗaya na binsa nayi, nauyin da nayi masa yasa gaba ɗaya mukayi ƙasa ina daga sama nayi masa rumfa.






Unfortunately lips ɗi na suka sauka cikin nasa ja-ja-yen laɓɓan.




Oh my God kasa motsi dukkanin mu mukayi, ga mutane har sun fara taruwa kanmu cike da son ganin kwakwaf.😅




Cikin yardar Allah na samu na miƙe tsaye ina kama baki cikin zare ido, tuna wai da gaske sumbatar sa nayi.😹




Cikin sauri na nufa Bus da ta ƙari so wurin ko gigin juyawa garesa banyi ba.






"Ke Kyakkyawa ta, ya ya dai baki da abin faɗa ne?."






Tambayar ya yi min cike da shaƙiyanci, ni kuwa ƙin juyawa nayi, da sauri na shige cikin Bus ɗin ina Dariya.🤓










_-_*-_


Rayuwar Duniya daɗi idan ka sama wanda kake so yake ƙaunar ka tsakani da Allah.




A wannan zamanin mace abar tausayi ce, tabbas wurin samun Namiji wanda yake ƙaunar ta da gaskiya.




Yawancin Mazan mu na yanzu bamu suke so ba, jikin mu kawai suke buƙata, yayin da kuma mu Matan yawanci kuɗaɗen samarin muke so.




Ni dai nayi dace na zama mai sa'a cikin masu sa'ar, na sama haɗaɗɗen lu'ulu'u na Aasief Mai Waje, kyakkyawan matashin Saurayi na.😇




Na gwadashi ta ko wani ɓangare amma halayensa masu kyau kawai nake gani, ban taɓa ganin sa da wani mummunar siffa ko hali mara kyau ba.


Aasief ɗi na irin waɗannan samarin ne na kirki waɗanda kafin mace ta sama kalar su sai tasha wahala gaskiya.






Soyayya muke gudanar wa mai tsafta tsakani na da Aasief Mai Waje kyakkyawa na.






**
Murmushi nayi dai dai lokacin da na shiga Elevator da zai sadani kai tsaye izuwa Room na Saurayi na Aasief.




Jiya da dare ina kwance saman Bed saƙon sa ya shigo wayata, wai na samesa a estate nasu yau misalin 4:50pm.


Ba tare da tunanin komai ba, yau na shirya cikin kyakkyawar shiga na fito daga Gidan Madam Joy.


Kai tsaye na hau Taxi na taho zuwa Address ɗin da ya rubuta min a saƙon, koda na sauka a taxi bayan na biya sa kuɗin sa.


Sosai nasha mamaki ganin ba tare da binciken komai ba. Gate man dake tsaron Babban gate na Estate ɗin ya buɗe min na shiga ciki, haka shima mai tsaron gate na biyu.


Ban kawo komai a raina ba, don duk tunani na, shi Aasief ɗin ne ya yi musu umarni da hakan.






Hannu nakai domin knocking Room ɗin nasa, ga Mamaki na a buɗe yake.




Saboda haka cusa kaina ciki nayi. Wannan karon shi ne farkon zuwa ta Estate da yake kuma farkon shigata Room ɗin sa.






Palo ne haɗaɗɗe na gaske, wanda tsantsan kyawun palon ne ya sa na kasa gaba na tsaya ƙare wa palon kallo.






Subhanallah!




Na furta a fili sakamakon hango Boxer da nayi yashe a tsakiyar palon.




Humm wata ƙilama gajiya ya yi jiya Shiyasa bayar Boxer a ƙasa kuma a palo.




Nayi maganar ina mai gaskata kaina da haka ne abin da na faɗa.


Ƙari sawa nayi sannan na kai hannu domin kawar da Boxer ɗin.




Wani irin zilo zuciyata tayi kamar zatayo waje tsaban mamaki da tashin hankali na ganin abin da na gani.




Wai fa da gaske Brazia na gani gefan Boxer ɗin.


Cikin sauri naja baya tamkar wacce shock na wutar lantarki yaja.


Cikin tsananin juriya da dan ne abin da naji yana taso min a ƙahon zuciyata.




Nake takawa a hankali ƙafafuna suna son ƙari sawa dani cikin Bedroom.


Yayin da zuciyata shawara kawai take bani da na juya kawai.






Hannu nakai ba rufe baki jin kuka yana ƙoƙarin suɓuce min sakamakon ƙara ganin Pant na ma ta da nayi gabda zan shiga Bedroom ɗin.




Dishi dishi idanuna suka fara nunamin abubuwan dake gaba na, sakamakon hango sa da nayi kwance saman Bed daga shi sai short yana kwasar bacci.




Juyawa da idanuna da suka yi jajur lokaci guda nayi domin neman hanyar fita.


Cikin rashin sa'a idanun nawa suka sake kallon abin da zuciyata ba zata iya jure gani ba.


Cikin tsananin mamaki da tashin hankali nake ƙoƙarin furta sunan wacca na gani tsaye bakin bathroom da alama fitowarta ke nan daga ciki, kuma ga dukkan alamu wanka tayi, ganin yadda dogon gashin kanta da yake brown color yake ɗigar ruwa gata ɗaure da towel a chest...




"Erisha!!."




Na furta cikin rarrabe war murya, zuciyata tana barazanar fasowa waje.


Tashin hankalin da nake ciki yasa na kusa zubewa ƙasa ba tare da sanina ba, tabbas wannan Erisha ce a gaba na toh Menene haɗin ta Aasief.




Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un


Wannan wata kalar cin Amana Aasief ya yi min?.


Fisabilillah ya rasa wacce zai yi tarayya sai wannan arniyar kafirar Erisha.




Ta kasance University ɗaya muke da ita, class ɗaya course ɗaya, Benchi ɗaya.


Tun farkon ganina da Aasief da tayi hankalin ta ya tashi ta kasa sukuni wai a haukar son Aasief take.
Lokacin da labarin haka ya sameni sosai nayi ma ta warning akan ta fita harkar Saurayi na, idan kuma ba haka zatayi da ta sani.


Ashe kallo na matsayin shashasha kawai suke yi daga ita har shi, tunda gashi yanzu na gansu tare, cikin yanayin da zuciyata ba za ta iya jurewa ba.




Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un


Kawai furta wa ina mai mai yawa, wannan wata kalar mummunar ƙaddara ce?.




Cikin zafin nama na miƙe tsaye na ɗauki wayata da ta faɗi ƙasa, ba tare tunanin sake kallon Aasief dake kwance kamar gawa ba. Ko kuma ita Erisha ɗin.




Na nufa hanyar fita daga Bedroom ɗin ina sha re zafafan hawayen da suke wanke min fuskata. Wasu na ƙara biyo baya masu raɗaɗi fiye da garwashin wuta.🔥




"Nace bakiji ba, please idan kin fita ki rufe mana Room ɗin ko."




Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un




Ji nayi gwara na mutu na huta zaifi min sauƙi bisa wannan mummunar rana da nake ciki.




Ban kulata ba, haka zalika ban juya na kalleta ba.








***


Tun daga wannan Ranar gaza jurewa nayi, gaba ɗaya na shiga damuwa sosai na abin da ya faru, ya kasance bana iya zuwa University, bana ɗaukar wayan da Aasief yake bugomin ba dare ba Rana.




Na rame na fita hayyacina bansan haka ciwon so yake ba, balle kuma ni da aka yaudara.




Tun daga wannan Ranar bamu sake haɗu wa da Aasief ba kuma ni ce bana basa damar haɗuwa da ni, toh idan ma mun haɗu menene zai ce min?.






Wasa wasa tsawon wata ɗaya muna haka dashi zuwa, yanzu ina ɗan zuwa school sai dai wallahi bana fahimtar komai sai dai kawai naje.




Ita kuwa Erisha ita ma tun daga wancan Ranar ban sake ganin ta ba koda a school ne kuwa.






Daga ƙarshe da Aasief ya dameni da kira karairaya SIM card ɗin nayi gaba ɗaya sannan nayi plushing ɗin sa a toilet.






***
Sama sama nake juyo hayaniya daga wajen gate, da alama mai gadi ne shi da wani.




Mutsike idanuna da bacci bai ishe su ba nayi ina miƙa. Ya ye curtains nayi domin ganin abin da yake faruwa.




Nan da nan zuciyata ta fusata damuwar da ta fara rabuwa da ni two days ta dawo sabuwa fil, duka sakamakon hangosa da nayi wurin gate ashe da shi ne gate man yake hayaniya.






Ban san lokaci ba kawai tsintar kaina nayi ina taku ƙafafuna ko takalma babu haka na ƙari sa wurin gate ɗin nan muka shiga kallon kallo tsakani na da shi tsawon mintuna, sannan ya katshe shirun ta hanyar buɗe baki da niyyar ya yi min magana, cikin tsananin sauri da tafarfasan zuciya na dakatar da shi idanuna a rufe nake faɗin






"Menene kazo kayimin?, ko kuwa kazo ka ƙara tayar min da ciwon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login