Showing 6001 words to 9000 words out of 22403 words
Chapter 3 - SARAUNIYAR KYAU Takun Tsakiya FREE PAGE'S BY Nanah KD.txt
zan je na ɗauko su mu dawo nan, tunda na lura sunfi son Ƴan Bauchi akai na, banda haka mai zai sa suna Najeriya tsawon three weeks ban sani ba, sai yau."
"Oh Aunty Sunainah kana da gaza juro fa, yanzu ba gashi mun taho ba."
Ɗaya cikin ƴan matan tayi maganar da gurɓatacciyar Hausanta, wai nan ma a haka ita ce ta iya yaren Hausa sama da sauran."
Taɓe baki Sunainah tayi tana faɗin
"Ki jiki Shaakira da wata Hausar ki a wurin, da'ace nan kuka zo tun farko, da yanzu Hausa ta daɗa zauna a bakinki sama da hakan."
"Okay, don't worry Insha Allah next time before you go labor, we will reaturning back Insha Allah."
Ɗayar budurwar ita ma ta faɗa cikin harshen Ingilishi, dan kuwa tasan ta ce zata gwadayin Hausa dariya kawai za'a ma ta, shiyasa ta rufawa kanta asiri tayi Yaren ta Ingilishi.
"Tohm Ƴan ƙannina Taahira da Shaakira, Official da kuma wannan Bardia ɗin nan wanda ko sanin abin da muke tattaunawa akai bai yi ba, na rasa mai kakeyi da waya haka, tun shigowar ku fa."
Sai da Official ya zauna a motar sannan ya bata amsa da faɗin
"Rabu da wannan Ɗan soyayyar domin kuwa ba jinki yake yi ba, hankalin sa da ruhinsa yana gare ta ta cikin wayar."
Ƙayataccen Murmushi Sunainah tayi cike da jindaɗi take faɗin
"Masha Allah kace dai Bardia mun kusa shan Biki, amma Wacece haka mai Sa'a?."
"Karki damu zan baki labari idan na dawo next, Bye."
Amsa masa Sunainah da faɗin
"Okay Tohm, Bye Allah ya tsare hanya Bardia a gaishe da ƙanwar tawa."
Murmushi mai kyau Bardia ya yi a karo na farko da ya tsoma bakin sa cikin maganar nasu yace.
"Okay, Sweet Anty, Bye."
Sallama suka yi cike da kewar juna, har motocin su guda huɗu suka bar gidan dama tare suke da rakiyar guard's.
Komawa cikin palon wurin Haleesat, Sunainah tajin kewar su tun kafin a je ko'ina duk da cewa ba wani shaƙuwa bace tsakanin ta dasu, da suke yaran Uncle Mohammed Yaqub Muhammad.
Afeefah
Sai da tabbatar ta dawo hayyacinta sannan ta tashi motar suka nufa gida.
Koda ƙari sawar su Gidan ba tare da ɓata lokaci ba, dukkanin su ko wacce tayi Bedroom ɗin ta cike da gajiya, barin ma dai Lailah wacca har lokacin bata cikin nutsuwar ta.
Afeefah tana shiga cikin haɗaɗɗen Bedroom ɗin ta, wanka ta fara yi, ta gurje ko'ina da ina na jikin ta, dan kuwa ita kanta tasan tana ƙarnin jini.
Da fitowarta ta hango wayar ta tana ruri alamar kiranta ake yi, ƙari sawa tayi sannan ta ɗaga kiran cikin sauri ganin Daddyn su ne M.M.K.
Haleesat
Duk yadda taso Sunainah ta faɗa ma ta ko shin su na da wata alaƙa ne da Heart Cheng, bata sa sama amsar da take ba.
Domin kuwa ko da ta nunawa Sunainah ɗin Hotunan Heart ɗin.
Girgiza kai kawai Sunainah tayi lokacin sannan ta ce.
"Bata san ta ba, kuma bata taɓa ganin ta ba, sai yanzu."
Abin ba ƙaramin ɗaurewa Haleesat kai ya yi ba, ƙiri ƙiri ga kamannin su tana gani amma Sunainah ta ce bata san Heart ba.
Ba don ta yarda da maganar Sunainah ba, ta kamo hanyar gida bayan sun ɗan taɓa fira da Sunainah ɗin.
Sosai Afeefah suka sha Fira da mahaifin nata, dan sai da suka kusa one hour suna wayar, sannan suka yi sallama dashi, yana saka ma ta albarka cike da alfahari da ita.
Dan kuwa tuni labarin taimakawa mata mai juna biyu da tayi a Restaurant ya zagaye ƙasar ciki da wajen ta.
Ko minti goma basu yi da gama waya da Daddyn nasu ba, sai ga kiran Zaynerb ya shigo wayar, da sauri tayi picking, nan ma dai duk magana ɗaya ce, a kan karɓar haihuwar matar da tayi ne, sai da suka kwashe fi ye da twenty minute's suna waya da Zaynerb, sannan suka yi Sallama Zaynerb tana faɗa wa Afeefah ɗin gobe ne zata dawo nan Abujan daga Kano ɗin, sosai Afeefah tayi farin ciki da murna, dan kuwa tayi kewar Yayar nata Zaynerb sosai.
Koda gama wayarsu da Zaynerb, kiraye kiraye ne kawai suka ci gaba da shigowa wayar nata.
Duka daga na masu fatan Alkhairi a gare ta, sai masu yaba ma ta bisa taimaka wa mai juna biyu da tayi a matsayin ta na cikakkiyar SARAUNIYAR KYAU, sai kuma ƙawayenta na school a masu kiran nata, har da Ƴan uwanta na nesa da kusa, har ma da Fan's ɗin ta.
Daga ƙarshe da ta gaji palo ta fito, nan ta sama su Lailah da Fadeelah zaune harma da Haleesat wacca ba ta daɗe da dawowa gidan ba.
Yayin da Deejarh take Bedroom ɗin Zaynerb tana gyara ma ta.
Deejarh
Sosai ta gyara Bedroom ɗin na Zaynerb tsaf tsaf komai ya yi clear.
Tana shirin fita daga Bedroom ɗin daga can gefan bed side drawer ta hango wani ɗan akwati da ya tafi da tunanin ta saboda shaining da yake yi gunin ban sha'awa.
Ƙari sawa wurin tayi batare da ɓata lokaci ba, ta janyo akwatin tayo kusa da ita dashi.
Hannu takai domin taji ko'a buɗe yake, ga mamakin ta a buɗe akwatin yake.
"Oh ni Dije ta ƙauye, ko menene anan?. Wata ƙila ma Anty Zaynerb ɗin mantawa tayi tabar shi a buɗe."
Deejarh tayi maganar tana kuma kai hannu ta ciro wani ɗan jotter a ciki.
An kananan naɗe saman shi da igiyoyi masu kyau ƙanana, hannu tasa ta cire igiyoyin da aka kanannan naɗe jotter ɗin dasu.
Take Manyan rubutun da aka yi da manyan baƙi saman jotter ɗin suka bayyana ɓaro ɓaro anyi rubutun ne da jan Biro.
"MY REAL LOVE STORY."
Haka Deejarh ta furta abin da aka rubuta.
Buɗe shafi na farko tayi nan ma anyi rubutu ne, in stylish da red Biro.
"Don't you read this book because it's secret."
Murmushi tayi bayan ta karanta haka tana faɗin
"Ni kuwa wallahi tunda aka rubuta haka saina karanta naga abin da za'a iya"
Tayi maganar tana buɗe next page.
"My Sadness Love Story😫."
Shiru Deejarh tayi bayan ta karanta hakan, tunani take ae idan ba za ta manta ba, akwai wata rana suna zauna a Palo, Lailah take cewa SOYAYYA ce silar rushewar farin ciki a rayuwar Yayarsu Zaynerb.
Tuna wannan abu da Deejarh tayi ya saka cikin sauri ta miƙe tsaye har tana kusan tuntuɓe da ƙofa wurin fita daga Bedroom ɗin.
Da gudu ta ƙari sa palon, sannan ta tsaya tsaye a tsakiya tana sauke haki faɗi take cikin nuna musu jotter dake hannunta
"Balarabiyar India, Anty Lailah, har dake Anty Haleesat wannan shi ne littafin da labarin SOYAYYAR Anty Zaynerb yake ciki, a Bedroom ɗin ta na gani da ina gyarawa."
Za'a iya cewa tsakanin Lailah da Haleesat ba'a san wacece ta riga tashi tsaye ba, ta ƙari sa wurin Deejarh ta karɓa jotter ɗin.
Sai dai kawai ganin jotter ɗin suka yi gaba ɗaya hannun Lailah.
Komawa Haleesat tayi ta zauna taso ace ita ce ta fara sanin ya ya labarin soyayyar Zaynerb yake, wani irin ƙalu bale ta fuskan ta a ciki da har takai ga dawowa Nigeria, sannan kuma da halin shaya shaye?.
"Tunda haka ne ki karanta mana a fili kawai musan abin da yake ciki."
Afeefah tayi maganar tana tashi daga inda take ta koma kusa da Lailah ɗin ta zauna a saman tattausar carpet na palon, dan kuwa ita ma a mugun matse take da jin labarin soyayyar Zaynerb ɗin.
Buɗe shafi na biyu na littafin Lailah tayi bayan ta karanta abin da aka rubuta a bango na jotter ɗin da kuma shafi na farko.
Karantawa ta fara a fili kamar haka....
Mgnr Payment fa
*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*
~Karku bari a baku labari fa🤩~
~*SARAUNIYAR KYAU*~🔥🔥Takun Tsakiya_-_
*Iya kuɗin ki iya shagalin ki Hajiya*
*🔥 SARAUNIYAR KYAU 🔥*
_-_👑ƚαƙυɳ ƚʂαƙιყα👑_-_
ɯ&ʂ_-_📖🖋️📲
💓 The Nainarh Kd 💓
_-_ҽρ.6_10
*Last of free page's idan kinsan bakiyi payment ba, ki gaggauta yi domin ki ci gaba da samu Update's da zafi zafi akan lokaci 💃💃💃💃*
💞💞ƚԋҽ ҽxƚɾασԃιɳαɾყ ρҽɾϝҽƈƚ ʅσʋҽ ʂƚσɾყ Ⴆιƚɯҽҽɳ ρҽɾϝҽƈƚҽԃ ʅσʋҽɾʂ💞💞
*Zaynerb Mai Kyau*:
"Shi ne sunan a kafi sani na dashi, sannan ake kira na Especially ma ƙawayena da ƴan school namu.
Yammacin wata Ranar Lahadi ne, nayi sallama da Ahalina da suka rakoni har filin jirgi na ƙasar Jamus.
Cike da farin ciki, wani ɓangaren kuma da tunanin kewar mahaifina da kuma ƙanwata Afeefah nake a Ranar, harna shiga jirgi na saita zama na.
Karon shi ne farkon shigata public jet.
Sam ban wani iya ɗaura belt na jirgi ba, domin kuwa ko da zamuyi wata tafiya, ko zuwa wani wuri da Ahalina, tofa sai dai Daddyn mu ko kuma Afeefah, tofa ɗaya cikin su ne yake ɗauramin, suyi ta min dariya. Ni kuwa babu ruwa na.
Yanzu haka ma ƙoƙarin da nakeyi ke nan, na ganin na ɗaura belt ɗin dai dai, sai dai kasawa nayi, don ban sakawa raina dama zan iya ba.
Tsaki kawai nake faman ja, ganin ƙiri ƙiri na kasa ɗaura belt na jirgi.
A ba za ta naga fararen hannayen sa biyu ya saƙalo ɗaya ta ƙugu na, sannan ya dai dai, cikin ƙanƙanin lokaci ya gama ɗauramin belt ɗin.
Galala nayi da baki ina kallon sa, yayin da idanuna suke lumshewa a hankali, ina kuma buɗe su saman kyakkyawar fuskar sa mai cike da kwarjini da haiba, sam na kasa masa magana, sai idanu dana zuba masa ina kallo.
"Hello Miss do you hearing, move on this side."
Ƙara lumshe ido nayi jin daddaɗar muryarsa tana ratsa dukkanin magudanar jini da jijiyoyin kaina kai tsaye izuwa ƙwaƙwalwa ta.
Ban matsa gefe kamar yadda ya so ba sai da ya kuma magana, sannan na dawo hayyacina.
Da sauri na matsa gefe ina zare ido, sam naƙi bari mu haɗa koda idanu dashi.
Har jirgin mu ya tashi sararin samaniya, yana daga zaune gefena.
Tabbas a jikina Inajin ana kallo na, sai dai da na juya sai naga bani yake kallo ba, idanun sa suna kan littafin dake hannun sa.
Haka har tafiyar mu tayi nisa dan kuwa mun kusa kai mintuna talatin da tashi a lissafina.
Wani irin jijjiga jirgin da muke ciki ya yi sannan wani irin ƙara ya ziyarci dukkan wani fil_adam dake cikin wannan jirgin, ga wani irin jijjiga na tashin hankali da jirgin yake damu yana gefe da gefe tamkar zamuyi ƙasa.
A mugun firgice ina zare fararen idanuna nake kwalla ihun neman taimako kamar yadda sauran mutanen dake cikin jirgin suke yi.
Sam ban san lokaci ba, sai ganina nayi ɗare ɗare saman jikin mutumin dake gefena, na ƙanƙameshi ƙam ina fitar da ihun wahala da tsoro.
Idanuna a lumshe wasu hawaye suna biyo wa, ganin cewa gaba ɗaya mutuwa zamuyi, gani da burika kala kala a duniya ban gama cika su ba, gashi zan mutu sanadiyar hatsarin jirgin sama, dan kuwa a wannan taƙin babu wanda ya yi tunanin zamu tsira.
Cike da firgici da tashin hankali nake faɗin
"Wayyo! Wayyo! Wayyo ni Zaynerb Ɗiyar Mai Kyau jikar ƴar mutan sudan... Shikenan kwana na ya ƙare zan mutu, shikenan, wayyo ni Afeefah Daddy Yaya Maleek zan mutu na barku, shikenan wayyo."
Ban ma san iya adadin abin da nake faɗa ba, kawai sambatu nake yi cike da tsananin tsoro, na kasa addu'a sai shirme.
Sannan ƙam na riƙe shi ina wannan zare ido da sambatu.
"Hey, Miss relax mana just relax, baki iya Addu'a bane sai ihu da sambatu ki nutsu mana."
Haka kawai yake faɗi yana kamoni a ƙoƙarin sa na ganin na kwantar da hankalina.
Ina jinsa ban kulashi ba, sai dai ina mamaki ganin babu tashin hankali ko tsoro tare da shi.
*After Twenty Four Hours*
Lumshe kyawawan idanuna nayi ina ƙare wa haɗaɗɗen filin sauka da hawan jirgin sama dame ƙasar Amsterdam nayi.
Awanni ashirin da wani abu baya, banyi tunanin zan rayu ba.
Sai dai cikin ikon Allah, jirgin aka samu ya tsaya da jijjgan da yake yi, sannan aka saukemu a wata ƙaramar ƙasa dake tsakanin Jamus da Amsterdam.
A wurin muka kwana domin kuwa dare ya yi sai washe gari wani jirgin ya kwashe mu ya iso damu Amsterdam ɗin.
Wai ashe dalilin hatsarin da muka kusa samu da jirgin mu shi ne, shashashan Driver na jirgin bai duba lafiyar jirgin yadda ya kamata ba, ya tashi damu ya kusa jama na mu mutu.
Aikuwa yasha tsinuwa da zaki kala kala daga wurina dan kuwa bayan samun labarin da muka yi, ya sama rabon zagi da tsinuwa wurina, bama ni kaɗai ba harda sauran jama'an jirgin.
Sai dai nasha mamaki kuma na shiga tunani, na rashin ganin wannan haɗaɗɗen saurayi da muka haɗu da shi a jirgin farko, da banyi ba wannan karon har muka sauka yanzu.
"Wata ƙila ma ya canza jirgi ne tun jiyan."
Haka kawai zuciya ta bani.
Ci gaba da tafiya nayi ina gurgura ɗan keken da wasu abubuwa nawa suke ciki, ina kuma jan akwati na.
A ba za ta naji saukar wasu kyawawan furanni masu fidda ƙamshi na musamman da kuma wasu ƙa na nan balloon's saman kaina.
Washe baki nayi ina tarosu da hannayena.
Ban gama shan mamaki ba gaba ɗaya mutanen dake zagaye dani a wurin suka fara tafi raf raf suna dariya.
Yayin da daga gefe kuma wasu samari da ƴan matan turawa suka fara sakin kiɗa da wasu ababen ƙila dake hannayen ko wannen su.
Ban gama shan wannan mamaki ba, wani abin mamakin ya kuma faruwa sakamakon Juyowar da ya yi yana fuskan tana hannayen sa riƙe da flower's ya tsuguna ƙasa kusa dani fuskar sa akaina bakinsa yana furta kalmar.
"I Love You...Do You Winning To Marry Me?..."
Hakan yake furta wa
A gareni....
Yayin da mutanen wurin cikin tafi suke faɗin.
"Say something for him, please say you love him please please."
Haka kawai suke faɗa suna ƙara wa, yayin da shi kuma gwanin idanunsa suke kaina yana jiran amsa na, kuma bai fasa daga miƙo min furannin da yake yi ba.
Tsaban mamaki da al'ajabi kasa magana nayi, na zama tamkar Statue ina kallon su gaba ɗaya mutanen dake wurin, sannan na mayar da idanuna akan sa.
Tabbas Guy ɗin Jirgi ne, toh menene yake nufi da wannan bazatar nasa.
Abin tamkar wani shirin Film, da za'a ga saurayi ya yi surprising masoyiyar sa irin wannan.
Dariya nayi dan kuwa wannan abin dariya ne a wurina, banda haka kawai daga ganin sarkin fawa a kasuwa sai Miya tayi zaƙi?.....🤔
Kallmashe ƙafa ɗaya nayi saman ɗaya ina gyara tsayuwata tare da gyara goyon da nayiwa backpack ɗi ta, na wani juya idanu fuska ta ɗaure da murmushin rainin wayo nake faɗin
"Kai! Lallai ma kai ɗin nan, toh gaya maka aka yi niɗin wata ƴar Baba nace da zaka shirya wannan ƙaramin wasan domin jan hankalina iyye, bani amsa ta."
Nayi maganar ina kallon sa sannan na ci gaba da cewa
"Toh wannan salon bai burge Zaynerb Mai Kyau ba a canza wani."
Na faɗa hakan ne dan ina da tabbacin cewa baisan sunana ba, toh na faɗa ne saboda ya riƙe aha.🤣😁
*The Next Day*
Zaune nake a palon Gidan Madam Joy wacca na sauka Gidan ta, domin bani da burin zama a ɗakunan makarantar da zan fara, Shiyasa Daddy ya nema min Gidan wannan Baturiyar.
Dariya kawai nakeyi na tuna abin da ya faru jiya a Airport.
A lokacin koda na faɗa abin da na faɗa jan Akwati na nayi na nufa motar drivern Madam Joy da yazo ɗauka na.
"Ke Kyakkyawa ta ki sani muddun muka kuma haɗuwa a gobe, tofa tabbas kina so da ƙauna na."
Ya yi maganar cike da Qwarin gwiwa cikin Murmushi yana bubbuga faffaɗan ƙirjin sa alamar tabbatarwa.
A lokacin Murmushi mai tsada nayi ina basa amsa da faɗin
"Ina maka fatan rashin sa'a."
Dariya na kuma yi tuna hakan da nayi, in banda abin sa ma, ae ba yau zan fara zuwa school ba, sai next week.
Ina cikin haka Lovely Ƴa ɗaya tilo wurin Madam Joy ta fito zata tafi company na Architecture's don zaɓar kalar gidan da zata zauna ita da Saurayin ta bayan sun yi Aure, don Auren nasu ya kusa.
A lokacin naji ina son ganin yadda birnin Amsterdam yake dan ban taɓa zuwa ba.
Saboda haka magana nayiwa Lovely akan ta jira na shirya zan karata.
Bada ɓata lokaci ba, na shirya cikin Gown doguwa har ƙasa ta Shadda galilan milk color sannan ba tare da na ɗaura kallabi ba na yafa Veil ɗina shima brown kalar aikin dake jikin Gown ɗin sannan na saka flat shoe.
Na fito Palo wurin Lovely dake jirana muka fita zuwa mota, sannan muka ɗauka hanyar company.
A motar muna zaune na kalla Lovely ina faɗin.
"Ni kuwa Lovely menene sunan mamallakin company ɗin da zamuje ne, da kuma sunan ɗan sa, sannan ɗan nasa shekarun sa nawa?."
Na jero ma ta tambayar don ina da dalili.
Bani amsa tayi cikin turanci da faɗin
"Sunan sa Mr.John ɗan sa kuma Andrew yana karatun injiniyanci ɓangaren gine-gine."
"Okay..."
Na furta bayan ta faɗa hakan.
Da isar mu katafaren company ɗin muka fito daga motar mu, sannan muka shiga ciki, Elevator muka shiga domin ƙara sawa office na MD. Na company ɗin.
*After Some Minutes*
Zare fararen idanuna kawai nakeyi ina haɗiye yawu, tunani nake anya kuwa wannan mutumi mutum ne kuwa?.🙄
Fisabilillah nan ma sai da yasan yadda ya yi ya biyo ni?.😚
Hannu nakai zan ɗauka cup of coffee da aka kawo mana ni da Lovely.
Cikin rashin sa'a kuwa muka haɗa idanu dashi.
Ƙayataccen Murmushi ya yi min yana mai kashemin ido ɗaya.
Da sauri na kawar da kaina gefe, ban kuma yin gigin kallon sa ba, har suka kammala maganar da suke yi.
Kallon na Lovely tayi tana faɗin nazo mu koma gida sun kammala.
"Am nace ba, ki ɗan bani aron ta five minutes kawai?."
Ya yi maganar yana kallon Lovely ɗin.
Girgiza kai tayi tana faɗin
"Okay.."
Sannan ta fita, da kallo na bita, Lallai ma Bature babu kai.
Yanzu daga cewa ta bashi arona ta amsa lallai.
"Toh ya ya shin yanzu zamu iya magana da kyakkyawata kuwa, nasan dai zuwa yanzu ta kware min?."
Murmushi nayi ina juya idanu sannan na juya da kujerar da nake kai ina fuskan tar sa, nake tambayar sa.
"Garin ya ya, me yasa?."
Murmushi ya yi sannan ya gyara tsayuwar sa yana bani amsa da faɗin
"Duka saboda ke, jiya bayan rabuwar mu a Airport ban zauna ba, har sai da nasan gidan da kika sauka, nasan matar gidan da Yarinyar ta, na kuma san dalilin da zai sa Ni Da Ke mu sake haɗu wa yau, gashi kuma mun haɗun."🥰
Ya yi maganar yana sakin kyakkyawar Smile 😎
Taɓe baki nayi sannan na miƙe na ƙari sa kusa da shi Sannan na ja tunga na tsaya.
Hannu nakai na ɗan kamo Tie na shirt ɗin jikin sa, ina faɗin
"Humm, babu laifi, You will