Showing 3001 words to 6000 words out of 22403 words
Chapter 2 - SARAUNIYAR KYAU Takun Tsakiya FREE PAGE'S BY Nanah KD.txt
Yarona zumuncin mu zai ƙara haɓaka sosai, na biyu kuma saboda dama can inada burin haɗa auren Maleek da ita Fadeelah ɗin, kuma lokaci ɗaya sannan rana ɗaya nakeso ayi dana wacca zai aura ɗin, domin kuwa bazai yiwu ya aura dangin ubansa yabar na uwansa ba, bani da yadda zanyi a fasa wancan shiyasa nace a haɗa duka."
*Turƙashi*
Hajiya Sailuba ta faɗa hakan ƙasa ƙasa tana kallon Yayarnata.
"To amma bakya ganin cewa Maleek ɗin ba zai so hakan ba?."
Ajiye spoon dake hannunta Momy Rafi'at tayi tana faɗin
"A'a sam bazai ƙi ba, saboda Yarona yana yimin biyayya, ga duk abin da naso ya yi, sannan kuma a halin yanzu idan nace masa ya aura Fadeelah bazai min musu ba, sakamakon jiya sosai na nuna masa ɓacin rai na akan abin da ya yi mana sai yanzu ya tuna dani da ƙannin sa ya dawo gida. Saboda haka bana nada matsala dashi, sai dai ita Fadeelah ɗin ban sani ba ko tana da ra'ayi a kansa, shiyasa tun farko nace miki ita Fadeelah ɗin ta biyo ni zuwa Gidan ta ɗan yi kwanaki, nasan zan fahimci komai idan tana da ra'ayi akan Maleek."😒
*A TAƘAI CE DAI*
Momy Rafi'at bata bar gidan ƙanwarta Sailuba ba, har sai da Sailuba ta amince da maganar da taje ma ta da ita, sannan kuma tare da Fadeelah suka bar gidan, dama ita Fadeelah sara ne yazo ma ta daidai da bakin gatarin ta, domin tanada burin bin Momy Rafi'at ɗin, sai kuma ita Momy Rafi'at ɗin da kanta ta nema su tafi gida tare tayi ma ta kwanaki a cewar ta, Aikuwa babu musu Fadeelah ta amince.
*JIDDARH*
Har wa yau mamakin Abin da taji Auntie tana faɗa wa Heesham bai gama barin ta ba, "*KA NEMA SOYAYYAR JIDDARH*."
Wannan magana idan Jiddarh ta tuna tana ƙara mamaki, tunaninta menene abin da ya sa Auntie take so Heesham ya Aureta tunda har ta ce ya nema soyayyar ta.
Abu na biyu da ya kuma ɗaure ma ta kai game da Auntie shi ne hana su zuwa Gidan su Juwairiya Jabir Bici da tayi.
Gefe ɗaya kuma ga Budurwar da suka haɗu da ita acan gidan su Juwairiya ɗin bayan sun je ba tare da sanin ita Auntie ɗin ba.
Tabbas idan idanunta daidai suka gani a lokacin bala'in kamani taga suke yi ita da budurwar da aka ce ita ce*SARAUNIYAR KYAU* ta Abuja.
Gaba ɗaya ta shiga cikin damuwa tarin tambayoyi ne masu yawa a tare da ita, sai dai bata san wurin waye zataje ya bata amsoshin su ba.
Yanzu haka tafiya take yi izuwa garden wurin Heesham.
So take idan taje taji dalilin sa da ya sa yace Humaira ta kira masa ita.
"A gaskiya ina cikin damuwa sosai, sai naji ina kewar iyayena, Allah Sarki ni gaskiya kawai zan je wurin Auntie ita da Abba nace su bani lambar Mahaifiyata indai tana raye ina so na ganta face to face, na tambaye ta dalilin da ya sa tunda ta tafi ta barni a tsumma na haihuwa bata kuma wai waya ta ba."
Da ire iren waɗanda tunane tunanen Jiddarh ta ƙari sa garden ɗin wurin Heesham.
*AFEEFAH*
Basu bar gidan Yaya Shahid ba har sai da taga ta ɗan daidai tsakanin Aeezath da Mah'eesha, duk da dai ita Mah'eesha ɗin ce sai a hankali, amma ita Afeefah ɗin tayi abin da zata iya.
Around 4:10pm_-_
"Kaka ta tohm saduwar Alkhairi mu dai zamu yi gaba izuwa garin Abuja sai kun sake ganin mu idan akwai rabo."
Afeefah ta kammala faɗa wa Amma kakar tasu hakan a lokacin da take daga tsaye cikin palon kakar tasu.
"Afeefah dawo ki zauna ina da magana dake kafin ki fita."
Juyowa Afeefah tayi tana kallon kakar tasu da tayi maganar in seriously daga inda take zaune kamar kullum litattafan Addini gabanta tana dubawa, ba tare da musu ba Afeefah ɗin ta koma ta zauna, yayin da Mah'eesha dake zaune saman 2sieter ta zuba musu ido tana kallo dan jin abin da ita Amma ɗin zata faɗa wa Afeefahr.
"Faɗa min gaskiya kina cikin damuwa ko?."
Amma ta tambaye ta.
Da mamaki Afeefah ta kalla Amma ɗin jin irin tambayar da tayi ma ta.
"Amma wai ni damuwa kuma tona menene ke nan?."
Ita ma Afeefah ta tambaya.
"Kalle ni nan da gaske nake tambayar ki bada wasa ba, ki faɗa min iyakar gaskiya kina da wani abu da kike ɓoyewa wanda yake sakaki a damuwa?."
Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke wasu siraran hawaye suna zubo ma ta, wai ashe duk ɓoye damuwar ta da take yi saboda kar a gane, sai da wannan Kakar tasu ta an kara.
Tana share hawaye wasu suna kuma biyo baya ta fara magana.
"Tabbas haka ne, Amma ina cikin damuwa sosai, kuma ina da wasu tambayoyi da nakeso a amsa min sai dai ban san waye zan tun kara da tambayoyin nawa ba."
Shiru tayi tana nazarin ta ci gaba da magana ko kuwa ta tsaya.
Tsawon mintuna biyu sannan ta ci gaba da cewa.
"Abu na farko shi ne, ina yawan yin mafarki a waɗannan kwanaki, mafarki ma munana waɗanda basu da daɗin faɗa.
Abu na biyu, gaba na yana yawan faɗuwa kuma ban san dalilin hakan ba, ji nake kamar zan rasa wani abu wanda yake da matuƙar muhimmanci a gare ni.
Abu na uku, jiya da muka tafi wani gida naga wata yarinya wacca muke matuƙar kamanni da ita sosai, kuma tanamin kama da Mahaifiyata da na sani a hoto, yarinyar an ce ita ce *SARAUNIYAR KYAU* ta nan Kano.
Abu na huɗu, munyi wani Challenge dasu Lailah akan za'a haɗa lambobi a kira waya, duk wanda ya ɗauka zan faɗa sunan sa da address nasa, kuma zamu ƙulla abota dashi ko wanene.
Toh anyi hakan komai ya wuce su Lailah suna takuramin akan saina kirasa.
Sannan tunda nake kiran sa sau uku kawai ya taɓa ɗauka, sauran kiran sai dai ace switch off, ko kuma layin baya tafiya.
Kuma ina yawan mafarki da muryarsa yana roƙona wai naso shi.🥺
Amma tsoro nakeji kar yaje da Aljani nake waya na rasa yadda zanyi da kaina ga gaba na da yake yawan faɗuwa na rashin dalili ki bani shawara kaka ta."
Ƙarishe maganar Afeefah tayi cikin zubda hawaye har tana shiɗewa.
Tsuru tsuru Amma da Mah'eesha dake gefe suka yi suna kallon Afeefah da tayi maganar, sannan Amma ta nisa tana mai girgiza kai tare faɗin
"Ayya, yanzu Afeefah waɗannan tarin damuwowin suna damunki amma babu wanda kika faɗa ma, kina da hankali kuwa, yanzu idan wani abu ya faru dake fa, ya ya kike so Mahaifin ku da ya ɗauki son duniya ya ɗaura miki uhum, yanzu abu na farko da zaki fara shi ne Addu'a ki riƙe Addu'a ƙam da azkhar na safe da marece, kana ki dinga yawaita karatun Alkur'ani mai girma, sannan ki rage yawan zama ke ɗaya, duk da dai nasan ba haka kike ba, ki riƙe Addu'a sosai kamar yadda na faɗa miki domin ita addu'a takobin Muminine.
Sannan da kika yi maganar Yarinyar, kika ce kuna kama, wannan abu mai sauƙi ne a wannan zamanin, domin ana samun irin haka, ga Misali nan ma da Doppelganger's ae kinga mutane ne ma banbanta masu matuƙar kama fiye ƴan biyu, koma waɗanda suka fito ciki ɗaya, saboda haka zai iya yiwuwa kamanni irin na doppelganger's ɗin kawai kuke yi ke da ita.
Sai maganar saurayi da kika yi, wannan zai iya yiwuwa son sa ne kawai ya kamaki shiyasa.😯
Sai Abu na ƙarshe da kika ce kina yawaita faɗuwar gaba, da kuma mafarkai marasa kyau, duk sharrin zuciya ce da kuma shaiɗan ki riƙe Allah kawai, sannan ki dage da Addu'o'i wannan shi ne, nima kuma zan tayaki kuma nasa ka a dingayi harda saukan Alkur'ani domin Allah ya kawo sauƙi a lamarin."🙏
Shiru Afeefah tayi tana sauraren Kakar tasu Amma, har sai da taji takai aya, sannan ta sauke ajiyar zuciya.
"Amma na gode sosai da nunatar wa kuma Insha Allah, zan kiyaye kuma na ci gaba da ƙara kaimi wurin yawaita Addu'o'i da kuma azkhar."
"Masha Allah, ae haka ake so, sai dai gaskiya Afeefah da'ace zaki bi shawarata da kin haƙura da shiga Gasar SARAUNIYAR KYAU na ƙasa da za'ayi, saboda Inajin tsoro sosai, cuz of kyawunki ya yi yawa sosai, zaki iya samun maƙiya ta ko'ina wallahi."
Mah'eesha ce tayi wannan maganar fuskarta ɗauke da damuwa, domin ita ma tuntuni taji faɗuwar gaba mara wanda hakan ke nufi da wani mummunar abu zai faru.👹
"hahahaha Mah'eesha ke nan. Ni na yarda da Allah, kuma na yarda da ƙaddara ko wata kala ce, saboda haka shiga gasar babj fashi, domin Zama SARAUNIYAR KYAU ta duniya burin mahaifina ne sannan kuma Mafarki na ne zama hakan."💃💃
"Saboda haka ki kwantar da hankali ki kawai Insha Allah babu abin da zai faru sai Alkhairi."🙏
*Ten Days To Go*
*Kwanaki Goma Gaba*
"Yauwa Saira wannan Chinese recipes ɗin muke buƙata yanzu yanzu domin kuwa Afeefah tasa mun kwaso yunwa wannan uban yawo Restaurant Restaurant da muka sha."
Lailah ta faɗa hakan yayin da take miƙa wa Ma'aikaciyar Restaurant na mahaifin nasu book da jadawalin recipes na Restaurant ɗin suke ciki bayan ta kammala duba abin da suke buƙata ita dasu Afeefah ɗin sai kuma Deejarh da tayi musu rakiya.
Ɗan murmushi Afeefah tayi tana gyara zamanta saman kujerar da take a kai, su uku ne ta ɓangaren su na musamman cikin Restaurant ɗin, ita da Lailah da Deejarh da suke zazzaune.
Sun sha yawo sosai domin kuwa Restaurant biyar suka je suka duba yadda komai yake tafiya, bisa umarnin Mahaifin su Mister Mai Kyau, da yake ƙasar Jamus bai dawo ba, abin da yasa sai sune suka je Ma'aikacin da yake kula da ɓangarorin baya ƙasar shiyasa Afeefah kawai ta ce zatae shi ne Lailah da Deejarh suka ma ta rakiya.
Zuwa halin yanzu sosai faɗuwar gaban da take fama dashi ya ragu sosai, dalilin dage wa da tayi wurin yawaita Addu'o'i da azkhar da kuma sallolin dare babu fashi, sannan wannan munanan mafarkan da take yi, ta rage yi sosai, Abin sai godiyar Allah.
"Kai kai kai gaskiya abincin Chinese duniya, kinji irin daɗin da nakeji kuwa Lailah?."
Deejarh ce take zubo wannan maganar yayin da take yagar wawukekan cinyar namar kaza da aka yi ma girki irin na Chinese da kayan haɗin su.
Lumshe ido Lailah tayi ita ma dai dai lokacin da takai loman spaghetti irin na Chinese da irin tsinken su baki, sannan bayan ta lamushe, take faɗin.
"Kedai Deejarh bari kawai ae ina faɗa miki abincin Chinese ya yi ba'a Magana koba haka ba Afeefah?."
Tayi maganar tana mayar da kallon ta akan Afeefah da tayi shiru tanaso ta tabbata tarwa da kanta sautin da take ji yana fitowa daga ina ne kuma na menene?.
Juyawa tayi sai tin hagun ta nan ta hangowa idanunta abin da take so tabbatarwa.
Matashiyar mata ce wacce ba za ta haura 27years ba, da tsohon ciki tare da ita, tana zaune daga gefan su, nishi kawai matar take fitarwa na wahala da alamu haihuwa ce tazo ma ta.😓
Cike da azama Afeefah ta miƙe tsaye da sauri ta ƙari sa wurin ta, sannan ta kamo matar, riƙe ta tayi ƙam, tana ƙwalawa su Lailah kira hardama Saira.
"Saira na ce akwai wani spare room ne wanda za'a iya haihuwa a ciki?. Na lura ta galaɓaita sosai bazai yiwu a kaita hospital a halin da take ciki yanzu ba."
"Eh Miss akwai wani, bari na taimaka Miki a kaita ciki."
Saira tayi maganar tana ƙari sawa sannan suka kama matar ita Afeefah suka shiga da ita cikin wani spare room dake can gefe cikin Restaurant ɗin.
Shimfiɗar da ita suka yi saman katifa dake ɗakin sannan Saira ta fita, kana ta dawo ta bawa Afeefah wani fallen zani, karɓa Afeefah tayi ta rufe matar daga ƙasa, yayin da Deejarh da ta biyo su ciki, tayi tsuru tsuru da idanu, imani na ƙara shigarta na ganin irin nishin wahalar da matar take fitarwa kamar ranta zai fita, yayin da hannayenta duka suke ƙanƙame dana Lailah wacca ganin kalar ruwan da matar take fitarwa, yasa ta fara fita hayyacin ta, hankalin ta a tashe da kyar take iya numfashi, juyi kawai take ji kanta nayi cikin gajimare, yayin da ita kuma ta Afeefah take ta ƙoƙarin ganin ta taimaka wajen fitowar Yaro.
"Yauwa Lailah ɗan zo ki taimaka min ta nan bazan iya ni kaɗai ba."
Afeefah tayi maganar tana yiwa Lailah nuni da wurin da take.
Cikin dauriwa Lailah ta miƙe tsaye domin ƙari sawa wurin Afeefah ɗin, sai dai tashin hankalin da take gani yasa kafin ta ƙari sa ta zube ƙasa sumammiya.
Cike da takaici Afeefah tabita da kallo tsaban takaici kasa magana tayi.
"Balarabiyar India ba kallon ta zaki tsaya yi ba, ki ƙoƙarta Yaron ya fito matar nan tana shan wahala sosai sosai, bari ni kuma na taimaka miki ta nan."
Deejarh ce duk take wannan maganar a yayin da ta ƙari sa ta tsuguna kusa da matar sannan ta kamo hannun matar da hannunta ɗaya, yayin da ɗayan hannun take ɗan bubbuga cikin matar tana faɗin
"One two push, one two push."
Haka kawai take faɗa tana ƙara wa. Yayin da ita ma Afeefah ta ci gaba da ƙoƙartawa wurin ganin ta taimaka matar ta haihu.
"Sorry miss, Breath deep, follow the rhythm, don't move around and just breathe, breath breath.
Just breathe evenly. And just relax, you will be fine. Kawai ki daure ki ci gaba da numfashi kinji ki daure."
Afeefah tayi maganar tana kallon matar tana ƙara faɗin tayi numfashi, sannan ta mayar da kallon ta kan Saira dake gefe cikin faɗin
"We have to boil some water. We have to prepare."
Da sauri Saira ta fita tana amsa ma ta sannan ta Afeefah ta kalla matar tana kuma faɗin
"Breathe deeply, control your breathing. Don't worry, you'll be just fine Insha Allah."
Dawowa Saira tayi da abubuwan da Afeefah ta buƙata sannan ita da Deejarh suka riƙe matar suna ƙara bata baki.
Cikin ƙanƙanin lokaci Afeefah ta kammala bawa matar taimakon da ya kamata ta ciro Baby girl Saira ta taimaka ma ta wurin yanke cibi da sauran su, sannan suka ɗan gyara Room ɗin.
After some minutes
Ambulance tazo ta ɗauka mai jego da jariri domin kaisu asibiti a ƙara kula da lafiyar su.
Shiga motar tayi tana ɗaga kiran Haleesat da ya shigo wayar ta, sannan ta zauna mazaunin driver, yayin da Deejarh da kuma Lailah wacca bata gama dawowa hayyacin ta ba, suke back seat zaune.
"Hello Anty Haleesat what's going on?, Kin ƙari sa gidan Ummyn Farhana ɗin ne?."
Afeefah tayi maganar tana kunna motar sannan suka fita daga Restaurant ɗin. Dama sun yi da Haleesat ne akan, idan ita Haleesat ɗin ta fita wurin reception na wata ƙawarta Maryam, zata wuce gidan Sunainah domin tambayar ta akan Heart Cheng, ko sunada alaƙa ne domin kuwa kamar tasu tayi yawa.
Tunda suka dawo daga Kano dukkanin su babu wacca ta sama lokaci saboda school.
Tafiya Haleesat ta ci gaba da yi daga ɓangaren ta, daidai lokacin da ta isa ƙofar palon gidan Sunainah ɗin take bawa Afeefah amsa da faɗin
"Eh, yanzu na ƙari so gidan, zan ma shiga palon ne bari na mayar da kiran ta video call kawai yadda zakiji komai idan Ƴan uwa ne suɗin."
"Okay Tohm babu damuwa, bari nima na mayar "
Cewar Afeefah tana mayar da kiran ta video call.
"Sannu da zuwa Zaynerba kece a gidan namu ko kuwa dai ba ita bace, kinsan fa ni ba ganeku nakeyi ba."
Cewar tsohuwa Babah Dije tana bawa Haleesat ɗin hanya sannan ta shiga palon.
"A'a Babah wannan Haleesat ce ƴar uwan Zaynerb ɗin, bawai ita ba, Allah ya sa dai Ummyn Farhana ɗin tana..."
Shiru Haleesat tayi sakamakon ganin mutane zazzaune a palon da tayi. Kyawawan Ƴan Mata ne su biyu, sai kuma wasu jigaggun kyawawan Samari su biyu zazzaune saman kujerun alfarma dake palon, Ƴan matan fira suke yi da Sunainah cikin harshen Ingilishi domin kuwa da ganin irin shigar jikin su da alama idan ba Ingilishin ba basa jin wani Yaren.
"Ah ah wata sabon gani Haleesat kece a gidan nawa yau lale lale, barkanki da zuwa "
Sunainah ce take wannan maganar tana kallon Haleesat da ta zauna a 1sieter, yayin da idanunta suke kan waɗannan ƴan matan, tsaban ruɗewan da tayi na ganin kyawawan ƴan matan da samarin da suke zazzaune a palon da tayi, kasa magana tayi, gani take waɗannan ƴan matan sunfi mata kama ma da Heart Cheng ɗin bisa Sunainah.
"Barka Ummyn Farhana yakike ya ƙarfin jikin, ya unborn ɗin mu, fatan yana ko tana lafiya?."
Haleesat tayi wa Sunainah maganar tana saita wayarta saitin waɗannan samarin.
Aikuwa Hakan ya yi daidai da ɗagowar da ya yi kyawawan idanun sa take bada ɓata lokaci ba suka shiga cikin na Afeefah dake tuƙi tana saurare da kallon abin da ke faruwa a palon.
Wani wawan burki taja wanda sanadin hakan har sai da tayi gaba sannan tayo bayan kanta ya bugu da kujera, wayar kuma ta faɗa ƙasa wurin ƙafafuwan ta.
Lailah kuwa da take back seat ita da Deejarh har tana haɓo sakamakon bugewar da hancinta ya yi ta bugi kujerar dake gabanta.
"Ouch Afeefah kashemun kike son yi hala?, Wayyo hancina."
Lailah tayi maganar cike da jin raɗaɗi a hancin nata.
Durƙusawa tayi ta ɗauki wayar sannan tayi saurin rejected call ɗin gaba ɗaya zuciyar ta na mugun bugu, na ganin kyawawar fuskar sa da tayi, toh ya ya ma za'ayi ta manta da wannan fuskar cikin sauri haka.
"Ah ah ban gane ba Official da kake cewa zaku tafi, yanzu shikenan daga nan sai Bauchi ko kuwa ƙasar zaku bari?. Ni da aka cemin su Taahira ɗin kwana zasumin, ko fa five hours bakuyi ba anan?."
Sunainah ta masa tambayar tana miƙe tsaye da cikin ta da ya shiga wata na bakwai ke nan.
"No, daga nan kai tsaye airport zamu wuce zuwa Sweezland, kar ki damu da ga kin haihu. Ni da kaina zan kawo Miki su Taahira ɗin tun da naga kinfi son su akai na."
Ya bata amsar a yayin da gaba ɗaya suka yi waje, harda ita bayan ta ɗan yima Haleesat dake zaune Magana, sannan ta kuma cewa dashi.
"A'a Official bawai haka bane gwara kai, baka sati baka shigo nan ƙasar ba sakamakon yanayin aikin ka, su kuwa wannan ne fa karo na farko da suka shigo ƙasar. Ni Wallahi da'ace nasan acan Bauchi suka zaune tsawon three weeks da zuwan su, da da kaina