Showing 12001 words to 15000 words out of 24136 words
Chapter 5 - YAR BAUTAR KASA COMPELET DOCUMENT BOOK.txt
jin dariyar tata,dan yasan ba iya maganarshi bace tasata dariyar.
Zuwa can de tace.
"da kana karanta novels se ince acan kajiyo wannan kalmar,dan wlh da lokacin ina cikin wani group na novels na surbajo,to admin ɗin batason mutum yana online amman bazeyi magana agroup ba shine tasa dokar duk wand takama yana laɓe seta laɓaɓashi waje,"ta ƙarasa maganar tana dariya.
Murmushi yayi,dan ya fahimci salma har yanzu da akwai yarinta atattare da ita.
"To kika sani ko nima surbajonce ta koyamin?"
dariya salma tasake yi sannan tace.
"tab ayko bade surbajonmu ba,kaide kasan inda ka koyo kayanka"tayi maganar cikin shagwaɓa.
kawar da hirar yayi da cewa.
"to ƙanwar surbajo me kikaci yanzu da safennaɓ?"
"lah banci abinciba,gashi nande ina ƙarasa haɗawa"
"me kike haɗawa?"
"wainar shinkafane,da miyar taushe"
"zaki sammin naci nima?"
"hhh doctor kenan kaida kake Abuja taya zakaci wainar dake kaduna"
"jiya ba Abuja nawuce ba,na shiga kanone nagaida Abbana,yanzu haka ina kawo kaduna,sede in rowa zakimin?"
"babu rowa tsakanina dakai har abada,komai kakeso kawai kafaɗe shi kanka tsaye,ni kuma zanbaka"
"to ki kawomun wainar junction ɗin bakin ruwa inna ƙaraso seki bani naci,ki tafi da kwanunkan"
"haba doctor yazaayi kaci abinci a titi,kabiyo ta gida mana kaci"
"inada uzurine salmah,ki kawomin inda nace"
"Amman de doctor..."
Katseta yayi dacewa.
"Salmah"cikin wata siga data tilasta mata yin shuru,jin tayi shurune yasa yace.
"zaki kawomun ɗin?"
"Eh zan kawo maka"
"to kiyi sauri"
daga haka sukayi sallama ya ajiye wayar,jinshi yake kamar wani sabon ango tada motar yayi yaci gaba da tafiya.
Be jimaba ya isa bakin ruwan,parking yayi daidai tahir plaza,yana jiranta.
Ita ko suna gama wayar gurin ummanta taje ta sanar da ita komai,dan haka umman fitowa tayi ta amshi suyar wainar,ita kuma salma,ta ɗebo kuloli tazuba wainar da miyar datasha naman kan rago da manshanu,a basket tazuba harda plate da cokali,sannan taje ta sauya kaya taɗan shafa hoda ta ɗauki,abincin ta fice,drope ɗin napep ta ɗauka,dan haka bata jimaba ta iso bakin ruwan.
kiranshi tayi awaya ya faɗamata inda yayi parking,dan haka ƙarasawa tayi gurin,tana zuwa ko ta hango motarshi a gurin,ƙarasawa tayi.
Tunda ta nufoshi yake binta da kallo,ba abinda yafi ɗaukar hankalinshi se yanayin tafiyarta,ga kayan data saka fited gown ce wacce tafitar da shape ɗinta da kyau,se siririn mayafi data rufa akanta zuwa kafaɗarta,tayi masa kyau sosai,sede sanda idonshi ya sauka akan wasu maza da suka zuba mata ido se yaji duk ranshi ya ɓaci.
kamin ta iso,ya buɗe motar yafito,yakoma gidan baya,dan haka tana isowa itama ƙofar bayan ya buɗe mata.
shiga tayi da sallamarta tazauna,sannan ta ajiye kayan abincin aƙasan kujerun sabida motar jeep ce to akwai space.
"wayace ki sako wannan mayafin?"
"wlh sauri nakeyine shiyasa nasakosho kuma napep na hawo tundaga gida zuwa nan ɗin"salma ta faɗi kamar me shirin yin kuka.
"zubamin abincin,Allah ma de yasa yayi daɗi kar inci,in haɗu da bacteria"
murmushi salma tayi ta zuba mishi abincin ta miƙa masa plate ɗin gabanshi,amman se yaƙi ɗauka,binshi tayi da ido,tace.
"doctor lafiya kuwa?"
yamutsa fuska yayi sannan yace.
"Hannuna ba awanke yakeba,kuma ni ban iycin waina da cokali ba,so ayki yasameki dan haka kibani da hannunki"
murmushi salma tayi sannan tace
"to ayga ruwa seka wanke hannun"
"nufinki infitar da hannuna waje ina wankewa,ayko bazan iyaba,in bazaki bani bane to na haƙura da abincin"
kunya duk ta gama kam salma haka ta ɗauke plate ɗin ta matsa kusa dashi,tafara bashi abincin abaki,bako kunya yadunga wangale baki yana amsa,har tagama bashi,koda yazo cin naman ba ƙaramin daru sukaib,dan miƙa mushi cokalin tayi yaci dashi,sam yaƙi ams haka tadunga bashi har yagama ci,zat jiye hannunta,yayi sauri yariƙe,wai dole se ya tsotse hannun sabida,ya ƙarasa ladanshi🤣tanaji tana gani ya suɗe hannun tas,sannan yasha ruwa,ya goge bakinshi da tissue.
me makon taga ya sallameta setaga ya jawo kayan abincin yazuba wani sannan yasa hannun nashi dayace ba wankakke bane ya ɗebo abincin yanufo bakinta dashi,ƙuri tayi da ido tana kallon ikon Allah
"zaki amsane ko sena ɗura miki?"
da sauri ta buɗe baki yasakamata wainar,haka yadunga bata har seda tace ta ƙoshi ya ƙyaleta.
wanke hannunshi yayi awajen dayace baze wankeba,ita kuma ta haɗa kwanukan acikin basket ɗin,duk atakure take ta ƙosa ta fice daga motar.
"kinsn ko kabeer yanzu in yaganki baze ganekiba dan haka bari inmana hoto tare sabida innaje na nunamasa yadda prisoner ɗinshi ta kile" dariya salma tayi da sauri ta yunƙura zata sauka a motar,jawota yayo da ƙarfi ta faɗo jikinshi,ɗago da kanta tayi tana kallonshi,shima ita yake kallo,ahaka yaɗaukesu hoton,ganin hasken camera ne yasa salma ɓoye fuskarta ƙirjinshi,shima sake ɗaukarsu yayi ahaka sannan yasaketa.
turo baki salma tayi gaba sannan ta ɗauki kwanunkanta seda taji ƙafarta aƙasa sannan ta waiga tace.
"wannn ay cin zaline,mutum yagama maka bin kirki kuma kaci zalinshi"tana kaiwa ƙarshe tayi saurin ficewa a motar,
Dariya abun yaba doctor sosai.
buɗe motar yayi shima yafice,yaje inda take,dariya take masa shima dariyar yayi sannn ya ɗaukar mata drop din napep,seda tashiga tazauna,sannan yasa hannu yaja hancinta yace.
"to mara kunya ki gaidamin da ummana d Abbana,da sahabi"yana gam magana ya ajiye mata kuɗi akan cinya ya juya ya nufu motar shi Ya tada ita ya kama hanya,yana jinshi cikin matsanancin farin ciki.
muje zuwa
surbajo for life
*👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA*
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Don Allah masuyin editing na yar bautar kasa kudena kubarmin shi ayadda nayi editing din kayana,pls🙏*
*19*
Ya isa Abuja lafiya itama ta isa gida lafiya.
Asibiti yafara zuwa ya sallami marasa lafiya sannan yanufi gidanshi.
Yana isa gida ba jimawa kabeer yazo gidan,da murna suka tarbi juna.
Zama sukai suna hirar rayuwar duniya,danshi kabeer bemasan doctor yayi tafiya har ya kwana ba.
Kamar wanda aka tsikara doctor yaje ya ɗauko wayarshi ya nuno hotunansu ya miƙawa kabeer yace.
"ka gane ta jikin hoton nan kuwa?"
Kabeer ko mamakine danƙare a fuskarshi dan besan doctor yanada budurwar da sukayi shaƙuwa kamar haka ba,
Murmushi kabeer yayi sannan yace.
"haba abokina no wonder kace ba son salma kakeyiba,ashe already anjima da cinye zuciyar taka,kana da gaskiya me mace kamar wannan ba abinda zeyi da salma,gaskiya tayi ba ƙarya,wannan tashiga taroce,kamin lokacin auren tun yanzu naɗauki nauyin events guda uku dazaayi lokacin bikin"
Dariya doctor yakeyi sosai sannan yace.
"daɗina dakai wani sain kai gabi ne,dama seda na faɗamata bazaka gane taba inka ganta,to wannan ta jikin hoton salma ce"
Ido kabeer yaware sosai gamida zooming din hoton,da idonta yagane salma ce,wani ihu kabeer ya saki yana dariya yafara nuna najeeb da hannu yace.
"kana shaaninka mutumina,kagama pretending ɗin kadawo kan hanya kenan,yanzu ka amince kana sonta,tunda gashi harda su runguma ana selfie"kabeer ya faɗi yana kyalkyala dariya.
"ni kaifi ɗayane,bana sauya maganata,sabida gaskiya itace nagartar namiji,wlh kabeer bana son salma bana sonta,kuma bazan taɓa sonta ba,ni tausayinta kawai nakeji,taya zan so salma mahaukaci ne ni?wlh bana sonta,ko hoto dakaga na ɗaukemu,zata gudune nikuma na kamota shine tafaɗo jikina,kuma badan komai naɗaukaba sedan nazo na nuna maka"najeeb yayi maganar ranshi aɓace.
Kabeer dena dariyar yayi ya tsaya yana nazari akan aminin nashi,tabbss aminin nasa yanada matsala,wato ya fahimci sam najeeb bemasan meye soba bare yasan yanayinsa,tabbas yasan najeeb aduniya babu wanda ze gwada masa son salma,to amman matsalar yaƙi yarda da so ɗinma bare ya amince sonta yake,tabbas amininsa yana cikin tsaka me wuya matuƙar Allah be buɗe masa idonsa ya fahimci son salma yakeyiba,sabida duk ranar daya rasata ze shiga tashin hankali,wanda baze masa kyaiba.
ɗagowa kabeer yayi asanyaye yace.
"calm down abokina se yanzu nagano matsalarka,zantaya da addua kuma zanci gaba da tunasar dakai abinda baka amince dashiba,insha Allahu komai zezo da sauƙi"
Dariya najeeb yayi sannan yace.
"kanka akeji"
Daga haka hira suka shigayi.
Tun daga wannan lokacin,azahirin gaskiya duk wanda yaga salma da najeeb yasan masoyane,amman agurinsu su kuma ba haka bane.
Salma nason najeeb kamar ranta,shikuma anashi ɓangaren,tausayinta yakeyi,wanda ita bata gane hakanba ɗauka takeyi sonta yakeyi,shiyasa ko saurayi tayi bata kulashi.
Duk ƙarshen sati najeeb,na hanyar kaduna zuwa gurin salma,har su kansu iyayen salma sun ɗauka najeeb sonta yakeyi.
Se su kwana su yini suna waya da juna ko gajiya basayi,koda feefee ta tambayi salma tsakaninsu,kai tsaye salma ta shaida mata soyayya sukeyi.
ganin irin sintirin da najeeb yakeyine duk sati daga Abuja zuwa kadunane yasa mahaifin salma tuntuɓarta yaji tsakaninsu,dan haka yasa aka kiramasa ita.
"Salamatu,meke tsakaninki da najeebullah ne?"cewar mahaifinta .
Ƙasa salma tayi da kanta alamun jin kunya da ƙyar tace.
"Baba sona yakeyi"
Murmushi yayi sannan yace.
"kekuma bakya sonsa ko?"
cike da kunya tace.
"nima ina sonshi"
"to Alhamdulillahi,nayi farinciki,to amman salma kinsan baze yiwu muzuba muku ido ba dan haka inyazo wannan satin nida kaina zanmasa magana yaturo magabatansa atsaida magana,hirar ta isa haka atiti kuje gidanku ku cigaba".
daga haka ya Sallameta.
Ranar salma har zuba ruwa tayi a ƙasa tasha dan murna,koda suna waya da najeeb seda ya fuskanci tana cike da farinciki ,danhaka yace mata.
"hala tasamune kike ta farinciki haka?"
dariya tayi sannan tace.
"kaide bari wlh ay dawa tayi nama ne"
Dariya yayi sannan yace
"Ah tunda hakane,shafamin nawa tun yanzu,kar kamin inzo yaƙare"
dariya salma tayi tace.
"Sha kuruminka,babu me taɓawa se kazo,kaine ma zaka fara taɓawa"
"Har kinsa naƙosa satin yazo nazo"
Haka de sukai ta hirar su irin ta masoya a zahiri.
Wannan satin shi da kabeer suka zo.
murna gurin salma baa magana,nan tashiga ɗawainiya dasu,har tausayi taba kabeer,sabida ya fuskanci ba ƙaramin so takewa najeeb ba.
seda sukayi sallah azahar sannan mahaifin salma ya buƙaci ganawa dasu,
Zaune suke atsakar gidan su salma suda mahaifin nata inda mahaifin salma yafara da cew.
"Najeebullahi kimanin shekara ɗaya kenan kana tare da salma,batare da ka turo magabatanka an tsaida maganaba,shiyasa nacewa salma ta turomin kai dan nayi maka magana,soyayyar awaje taisa haka,gwanda amuku aure inyaso sekuyi agidan auranku,dan haka katuro magabatanka,atsaida magana,dama kiran danamaka kenan"
Tunda Abban yafara magana zufa take ketowa kabeer,yayinda shiko gogan kanshine yaɗau charge,dan haka beyi ƙasa aguiwaba yace.
"baba ni duk wannan bayanin naka banganeshiba,ita salmar ce tace soyayyace tsakanina da ita?"
murmushi baban yayi sannan yace.
"ita tashaidamin kuma dama idanuwana sunjima da gani,danhaka katuro magabatanka kawai ayi magana"
Ran najeeb gaba ɗaya yagama ɓaci inbanda salma ta ɗaukeshi mutumin banza ubanme zeyi da ita.
"baba nifa bason salma nakeyiba,taya zatace sonta nakeyi,kwatankwacin wannan maganar babu ita atsakaninmu"najeeb yafaɗi ranshi aɓace.
"baka sonta meyasa kake,zuwa gurinta duk sati,kuma kake ɗawainiya damu da ita gaba ɗaya,kaga najeebullahi karka maidani sakarai wanda besan abunda yakeyiba,yazaka ɗauki tsawon lokaci kana huremata kunne taki sauraran kowa alhalin kaibada aure kake sontaba,sannan yanzu kazo kana faɗamin ba sonta kake yiba"
Afusace najeeb yace.
"ya isa haka baba kar kayi yunƙurin cimin mutunci akan abinda bedace da aci mutuncina dominsa ba,ni mahaukacin inane zanso salma har inyi shaawar ajiyeta amatsayin mata agareni uwar ƴaƴana,?baba kode kamantane,?salma shekarunta biyu agidan yari adalilin sata,bayan wacce tajima tanayimin kamin Allah yatoni asirinta,bafa iya sata salma ta iyaba salma taƙware a harka da maza kalakala,ni ganau ne ba jiyau ba,kuma shikenan dan tsabar sonkai irin naka seka ce ni nafito na aureta,in gaskiya kake yi ka nemo me irin halinta ka aurawa sahabi mana".
Tunda najeeb yafara magana mahaifin salma ke zubar da hawaye,yayin da kabeer se hana najeeb yin maganar yakeyi amman yaƙi denawa,kuma tunda yafara magana akan kunnen salma taji komai.
kuka takeyi numfashinta na sarƙewa,daƙyar tajanyo akwatin kayanta ta ɗauko wata jaka,cike da kuɗi kimanin miliyan ɗaya ɗori,ta ɗauko jakar tafito dagudu zuwa tsakar gidan,kuka take kamar ranta ze fita ta ajiye jakar akan cinyar najeeb tace cikin kuka.
"ƙarya kake najeeb kana sona wlh karya kakeyi,inde sabida satar danayimakace to ga kuɗinkanan karka kuma kirana da ɓarauniya,najeeb nimesonkace,karka lalata farincikina,ka saurari zuciyarka najeeb ni takeso kar ka...."numfashintane ya ɗauke ta kife agurin.
A gigice najeeb yayi kanta da sauri babanta yadakatar dashi da cewa.
"inka kuskura kataɓamin ƴa,wallahi se ka raina kanka,kuma yanzu base anjimaba ka ɓacemin da gani,wanda besan darajar manyaba"
Najeeb hankalinshi nakan salma,wacce jini yake fitowa ta bakinta,duk yagigice ya rasa abinda kemasa daɗi,kabeer ne yayi yunƙurin bada haƙuri amman ina be sauraresuba dole kabeer yaja najeeb daƙyar suka nufi hanyar fita,har sunkai ƙofar gidan Abbah yabiyosu,yabasu jakar kuɗinsu,dakyar kabeer ya amsa suka nufi mota,najeeb se tirjewa yake baze tafiba,dakyar kabeer yasashi amota,suna tsaye aka fito da salma akasata a napep,aka wuce da ita asibiti rai a hannun Allah.
Najeeb hawaƴene kebin fuskarshi wanda besan dalilinsuba,ahaka kabeer yaja motar suka ɗau hanyar Abuja.
*INTERMISSION*
Surbajo for life.
*👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA*
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*20*
Tunda suka ɗau hanya bawanda yacewa ɗan uwansa ƙala,se najeeb daya kifa kanshi akan cinya yanata kuka.
"Dallah malam kacikamin kunne da kuka,ubanwa ya sa ka aykata abinda ka aykata,wlh ko yanzu salma ta mutu kaine ka kasheta,wawa kawai wanda besan abinda yake ba"cewar kabeer cikin matsanancin fushin dake nuna gab yake daya doki najeeb din.
Shiko najeeb a gigice ya ɗago yana kallon kabeer yace bakinsa na rawa.
"Kabeer salma bazata mutu ba,salma rayayyace batayi kala da mutiwaba,kar ka kuma alaƙanta tata da mutuwa"
"dallacan yimin shuru kai har kanada bakin magana yanzu,bayan kasa mahaifinta kuka,ita kuma gatacan rai a hannun Allah ,ay wlh ko hakkin hawayen mahaifin salma najeeb bazaka zauna lafiya ba,ace ayi mutum kamar jinin firauna,wacce irin maganace banyimaka akan salma ba,meye ban faɗa maka ba,amman dan tsabar bakasan darajar manyaba ina hanaka magana ƙara ɗaga murya kakeyi kai ga isasshe,wlh kanka kama,ba ruwan kabeer,kuma wannan hawayen da kakeyi,wlh kashirya,seka zubar da dubunsu anan gaba"kabeer ya fadi cikin kakkausar murya.
Najeeb ya kasa magana ware ido kawai yakeyi,yanaso ya hango abinda yayi ba daidaiba a maganganunsa da baban salma,amman shi a iya ganinshi,ba abinda yayi gaskiyar abinda ke ransa ya faɗi.
Har suka isa Abuja najeeb bedena kuka ba,shi kuma kabeer bedena zazzaga masa masifa ba,ƙarshema a bakin titi yasaukeshi,se taxi ya hau ya ƙarasa gidanshi.
Salma ko,likitocin sunyi nasarar daidaita numfashinta,sede ta kamu da ciwon zuciya me tsanani.
Ummanta se kuka takeyi,tana Allah wadai da najeeb,da yaudarar dayazo yay musu.
koda sahabi yaji abinda yafaru jiyayi kamar yay tsuntsu yaje yasami najeeb yaci mutuncinsa,sosai ranshi ya ɓaci.
Haka sukai ta jinyar salma,har tsawon watanni uku a asibiti sannan ta samu sauƙi aka sallamosu.
Tunda ta dawo gida sam batason hayaniya,ko hira ta daina yi da kowa kullum tana ɗaki tana tunani,bata taɓa tsammanin najeeb ze tozartata da ita da iyayentaba,segashi yashayar da ita mamaki,tunda yasanya mahaifinta kokawa a dalilinsa.
tsanarshi ce me girma ta mamaye saman zuciyarta,jitake kamar ta kasheshi.
haka rayuwa taci gaba da tafiya,yayinda najeeb yazama kamar wani mahaukaci,ga kabeer ya fita a harkarsa ko a waya yasashi a black list bashida ikon kiranshi.
Salma itama koya kira layinta sede ace baya ayki,sabida tajima da yarda layin.
yau da sassafe ya shirya yanufi gidan kabeer,sede yasha mamakin,samun mummunan labari agurin megadin gidan nacewa kabeer sati guda kenan da barinshi gidan,sabida ammishi transfer daga Abuja,amman besan inda ya koma ba.
jiri ne yafara ɗibar najeeb ,adaddafe,ya shiga mota ya koma gida.
koda ya isa gida kuka yake kamar yaro ƙarami,ji yake kamar yabar duniyar,yanzu ina ze nemo kabeer yabashi haƙuri su shirya?.
kimanin watanni takwas kenan da faruwar lamarin.
Inda mahaifin salma ya matsa mata akan tafito da miji shi yagaji da ganinta ahaka,inba hakaba ze kaita ƙauyensu ya aurar da ita sadaka.
Sosai batun ya ɗaga mata hankali,dan zuwa lokacin bata da saurayi.
Cikin hukuncin Allah ta haɗu da wani kamal,abokin sahabi,suka fara soyayya dashi,ba laifi tanason kamal shima yana sonta.
Har iyayenshi sunzo antsaida maganar auransu,murna gurin salma baa magana,dan dama zaman gidan ya isheta sabida sa'anninta duk sunyi aure sun haihu se ita tarage agida.
Ranar ɗaurin aure jamaa ba masaka tsinke dangin ango da amarya kowa ya hallara,anɗaura aure lafiya,kowa se murna yake.
wani mutum ne yaja mahaifin kamal gefe yamasa kuskus a kunne.
Ayko tuni mahaifin kamal yafara balai akan dole kamal seya saki salma.
koda aka tambayeshi,dalili se cewa yayi ay tsohuwar karuwace,kuma tsohuwar ƴar safarar cocaine,dan haka baze gurɓata zuriar shi da ita ba.
Haka ya tasa kamal akan dole seya saki salma,haka kamal yana kuka yarubuta takardar sakin yabayar.
Koda labarin ya isa cikin gidan su salma mahaifiyarta rushewa taƴi da kukan takaici.
itama salma sanda aka bata takardar sakin sumane kawai batayiba amman kuka tayishi ba adadi,Allah ya isa ko tajawa najeeb ita tafi kwandon dubu,dan shine yafara yimata tambarin karuwanci gashi nan yana binta.
Haka taro watse kowa se gulma yakeyi.
Tundaga wannan lokacin,mutane sunfi,shida dasuka fito neman auranta ana fasawa in sukaji labarinta,salma tarasa inda zata sa kanta duniyar tamata zafi,kuka yanzu tayishi har ta dena.
Tacire aure aranta dan ko kauyansu da mahaifinta yakai tallanta sadaka bawanda ya amsa sabida sunsami labarinta.
wasa wasa ko fita seda ta gagari salma sabida da zaran ta fita yara sukw binta suna jifa wai ga karuwa ga yar cocaine.
Bata da sakat ko mahaifiyarta tadena shiga taro,sabida da zaran tashiga zaa fara yada mata da habaici.
Yau kabeer ne yakamo hanya zuwa gidan su salma dan yasake ba mahaifin salma haƙuri,koda ya iso ƙofar gidan,parking yayi agefe,yana shirin fitowane,ya hango wata budurwa yara sunbiyota da gudu suna mata waƙar,"ga yar cocaine taƙi aure,waze aura?se ɗan banza,waye banzan?me bin mata"haka yaren suke cewa se jifanta sukeyi har sun fasa mata goshi,sun yaga mata hijabi,
koda suka ƙaraso kusa dashi seyaga ashe salmace yaran suka biyo,da gudu tashige gidansu,sannan yaran suka juya,da sauri kabeer yakira wani yaro me wayau acikinsu yatambayeshi.
"Abokina me wannan tamuku kuke mata waƙa haka kuna jifanta?"
dariya yaron ya kwashe daita sannan yace.
"wannan dakake gani,sau bakwai ana taruwa ɗaurin auranta ana fasawa,wanima seda aka gama ɗaurawa aka saketa,sabida ansamu labarin ashe tsohuwar yar cocaine ce kuma tsohuwar karuwa,sata kuwa ko ɓera albarka"
Hasbunallahu waniimal wakil,itace kabeer ya furta da ƙyar,sallamar yaron yayi yakoma cikin motarshi yakife kanshi akan sitiyari yana kuka,na tausayin salma da iyayenta.
"ina najeeb zekai alhakin salma da iyayenta"itace tambayar da kabeer yayiwa kanshi,jiki a sanyaye yaja motarshi yabar ƙofar gidan yana kuka na tausayin wainnan masoya dake cikin jarabtar ubangiji,yanajin haushin najeeb matuƙa amman yasan ba laifinshi bane haka Allah ya tsaro musu,amman dole zeyi iya bakin ƙoƙarinshi wajen ganin yashawo kan matsalar.
muje zuwa
surbajo for life.
*👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA*
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*DUK WANI MASOYINA YATAYANI JAJE WLH YANZU HAKA ZUCIYATA BUGAWA TAKE DA ƘARFIN TSIYA,INADA DARI BAKWAI A WAYATA,TO KUMA DATAR DUBU DAYA NAKE SAWA,SENAJE TA MOBILE BANKING ZANYI RECHARGEN NA 300 KUNGA YAZAMA DUBU DAYA KENAN,TO WLH TASHIN HANKALIN DAYA SAMENI BAZE MISALTUBA,MEMAKON INSAKA DARI UKU SENASA DUBU UKU,WLH BAN LURABA SEDA BANKI SUKA TUROMIN ALERT,INA CIKIN TSAKA ME WUYA😭😭😭😭😭😭😭ATAYANI DA ADDUA ALLAH YABANI HAƘURIN JURE KADDARAR DATA FADAMIN,DON ALLAH*
*Wannan shafin nakine masoyiyata,Allah yakara daukaka,yakareki daga sharrin duk wani abun ki,MAMAN AHMAD(MARDIYYA KAOJE)MARUBUCIYAR MUMTAZ,CHAIR LADY SURBAJO NA GAISUWA🤝*
*21*
Kai tsaye gida kabeer ya wuce,matarshi a ruɗe ta taryo shi,tana tambayarshi abinda yafaru dashi taga yana kuka.
Be ɓoye mata komai ba yasanar daita,itama rushewa tayi da kukan na tausayin salma dan tafijin tausayinta.
Sati guda tsakani,kabeer ya ɓoye number yakira najeeb,dakyar ya ɗauka,jin muryar kabeer ne yasa yamiƙe zaune yana faɗin.
"haba friend yanzu har abun yakai ga haka ka