Showing 3001 words to 6000 words out of 24136 words

Chapter 2 - YAR BAUTAR KASA COMPELET DOCUMENT BOOK.txt

jakar ta takeyi takasa sakinta.


"Hala de jakarnan taki akwai wani abu me muhimmanci acikine ko?"doctor ya wurga mata tambaya.


A kiɗime ta waigo tana kallonshi tace bakinta na rawa.


"Aa wlh ba kuɗi bane acikiba"ta bashi amsa tana ƙara riƙe jakar da kyau.


"ke ko kode kunnenki beji dakyaune a ina kikaji na ambaci kuɗi?".


Jan bakinta tayi tai shuru,har suka iso camp ɗin yasauketa,har ta sauka daga motar,se ya leƙo da kanshi ta window yace.


"To akashe lafiya".


yana faɗin hakan,yaja motarshi ya barta agurin tana nazarin kalmarshi.


"akashe lafiya,to me yake nufi kenan?"salma ta tambayi kanta,rashin amsane yasa ta juya tawuce ɗakinsu.


surbajo ce,for life.
[8/11, 16:50] Umar Dalha: *👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*




Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*i don't need everybody in my life,i just need few people who truly understand me,#be your own bossssss*




*6*




Tana shiga ɗakinsu tayi sauri taciro kuɗin ta ɓoye acikin kayanta,wanka ta shiga tafito tayi sallah.


Tana idar da sallar ne tasamu natsuwa,dan haka kwalliya ta tsara a fuskarta,kamar amarya,sannan ta ɗauki wasu arnayan english wears ta saka,iya kyau tayi kyau,amman babu me kallonta ya ɗauka tasan abinda ake kira musulunci.


Tana ɗaura takalmi feefee tashigo ɗakin,cike da mamaki take kallon salmar.


Miƙewa salma tayi tacewa feefee.


"ƙawa zani shopping ne pls,kimana girki kan nadawo".


"salma kina nufin wai dawannan shigar zaki fita?anya kinada hankali ƙuwa,wannan shigar mijinki ne yafi cancanta daya ganta fa,wlh inkina yin haka bazaki samu miji nagari dazece yana sonkiba".


"Aniyarki tabiki wlh,miji nagari kuma har se nazaɓa,sabida yadda kike taƙama ke virgin ce haka nima,da ace iskanci nakeyi sekice bazan samu ba,nifa feefee kinfara wuce gona da iri,wanne irin wulaƙanci ne wannan,nayi kwalliya ko ɗan cewa nayi kyau bakiyiba,amman kinzo kina cikamin kunne,da zancen banza,tonide daga yau karki sake yimin haka,jikinki ko jikina?".


Tana kaiwa nan tayi ficewarta tabar feefee atsaye kamar gunki.


Tana isa bakin titi ta fara sauya takunta,dama ga rigar datasa koya ta motsa cibiyarta na fitowa,daga saman wandin kuma jigidar dake jikinta itama tafito,tana tafiya kamar wata tarwaɗa.


Tana isowa bakin titin taja gefe ta tsaya,tana taunar cingum.


Wata venz 4matic ce ta faka agabanta,sannu a hankali glass din yasauka,wani mutumine aciki wanda a haife ya haifi salmar.


A zaton shi ba musulma bace dan haka da turanci yamata magana.


"sexy baby barka da yammaci"


Ɗago ido salma tayi ta haskeshi dasu,sannan tadan murmusa,tace.


"yauwa suger daddy"


amsar tata dariya tabashi,dan haka yace.


"in bazaki damuba muje in rage miki hanya mana"


Su salma abin nema ya samu amman dayake baby ce me class setace.


"Ayya nagode kawai nima nan daka ganni driver na nake jira".


Har ga Allah ya amince da batun nata,dan batayi kala da ƴar talakaba.




"ay daganinki nasan akwai dalilin dayasa kike tsaye anan,amman don Allah kishigo na rage miki hanya".


Dakyar de yasamu ta amince,koda zata shiga motar seda tayi wani juyi da mazaunanta sannan tashiga,wani miyau mutumin ya haɗiye ba shiri.


"Ni sunana Alhaji Adamu canji,ni maaikacine a CBN,ina zaune a Abuja ne,yanzu haka dakika ganni nazo wani meeting ne nan,kefa ya sunanki".


cikin salon ɗaukar hankali,tace.


"Sunana salma hadi medala,nazo nanne bautar ƙasa daga jihar kaduna".


"wow nice name,ashema ke musulmace?"


"sosai ni musulmace,ilove fation ne kawai shiyasa kaganni ahaka"


"thas good,ina kika nufa yanzu".


"zani shopping ne wlh kuma inason in sauya wayata ne,shiyasa kaganni nafito yanzu".


"Ok ba matsala bari nakaiki,ay kin cancanci amiki komai"


Wani haɗaɗɗen super market yakaita,nan tashiga jidar kaya,na kwalliya dana ci,bayan tagama da wannan fannin,sukaje ɓangaran wayoyi.


Alhajin dakanshi ya zaɓar mata,iphone7 da kuma samsung galaxy s6 edge,salma ware ido tayi kawai tana kallon ikon Allah koda sukaje gurin biyan kuɗi akayi total ɗin duka kayan data siya da wayoyin,dubu ɗari huɗu da hamsin.


numfashinta be kusa ɗaukewaba seda taga Alhaji Adamu yaciro kuɗin yabiya cash.


Kasa magana tayi,binsa kawai take da ido har aka gama zuba kayan a leda,aka kaimusu mota,ko tafiya ta kasa yi dan haka Alhaji adamu,hannunsa yasa yakamo ƙugunta،salma kasa hanashi taɓata tayi,ahaka yajata suka bi hanyar fita,suna kaiwa bakin ƙofa suka ci karo da doctor najeeb shima yazo shopping.


Ba ƙaramin mamaki yayi da ganin yarinyar ahakaba,kallon tsana yabita dashi,yayinda itama,ta wurga mishi nata.


Duk da bata ji daɗin ganinta da yayi rungume ajikin Alhajiba amman bazata bari ya gane hakanba.


Shigewa ciki yayi sukuma suka fice zuwa mota.




Surbajo for life.
[8/11, 16:50] Umar Dalha: *👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*






Zahra Muhammad Mahmud




DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION




*7*




Suna shiga mota Alhaji yaja suka tafi,se hannu yake miƙawa yana shafar cinyoyinta da saman wuyanta,sam salma takasa hanashi taɓatan dayakeyi.


(To dama taya zata iya hanashi taɓata bayan tadauki dogon buri game da rayuwarta,tunda ko tasamu,me kudi ay dole tasakar masa ragamar rayuwarta,kukan kurciya............).


A haka har suka iso kamp,complementry card ɗinshi ya bata,koda ta yunƙura zata fita a motar hannu Alhaji yasa ya shafo mazaunanta cikin wani salo,wanda ya tilastawa salma komawa cikin motar.


Hannu yasa ahankali yana shafa wuyanta har yaƙaraso kan ƙirjinta,salma najin daɗin abinda yake mata ba kaɗanba sabida shine karo na farko da hakan ta taɓa shiga tsakaninta da namiji.


Tura hannunshi yayi cikin rigar yadunga wasa da boobs ɗinta,itako wani irin numfashi take ja gaba ɗaya tafice a hayyacinta.


Seda yagaji dan kanshi da wasa da jikinta sannan sukayi sallama tafice ɗauke da ledojin da yaymata siyayyar.


Tana isa ɗakin tasami feefee na karatun qur'ani,wuceta tayi ta isa bakin gadonta ta shirya kayayyakinta sannan tasaka wayoyinta a charge.


Wankan tsarki taje tayi sannan ta ɗauro alwala tazo tayi sallah,feefee de binta kawai take da ido,ga abin magana amman tana gudun kada cibi yazama ƙari,dole taja bakinta tayi shuru.




Abinci feefee taba salma ba kunya ta amsa tacinye,daga haka salma ta nunawa feefee tsarabar da Alhaji yay mata,ta haɗa harda kuɗin doctor data sato tace shi yabata,ta nuna mata ma complementry card dinshi daya bata.


Idon feefee kamar goriba sabida girman daya ƙara dan tsananin mamakin salma da takeyi,har salma tagama jawabinta feefee tagaza ɗauke idonta akanta.


"Salma iskanci kika fara sabida son abin duniya?"feefee tawatso mata tambaya.


"Bangane iskanciba,daga cewa anbani kyauta sekice iskanci nafara,?"


"Wlh salma koshine ya haifeki ƙarshe kenan,inde tarbiyya me kyau yakeson baki bazr baki duka wannan abubuwanba,karfa ki maidani yarinya,salma ba tun yau muke tareba,ko ummanki bazata faɗamin halinkiba,inde ba alada kika gamaba salma bakya jiƙa gashin kanki,hasalima a saloon kawai kike wanke gashi,yau gashi kin wanke a gida kuma ma da daddare bayan kindawo daga yawonki,dan haka nagano komai ayke ba yarinya bace kinsan abu mekyau daga yau salma bazan ƙara yimiki magana akan ki sauya halinkiba,akwai ranar ƙin dillanci ranar da hajar megari taɓace".


jikin salma yamutu murus,dan tasan intacewa feefee ba zina tayiba bazata yarda ba shine yasa ta tattara kayan ta adana tayi kwanciyarta,zuciyarta na hango mata abunda Alhaji yayi mata ɗazu tanajin daɗi.


Washe gari da wuri ta shirya,wata riga tasaka,wacce iyakarta guiwarta baƙa,wacce takamata sosai,sannan tasaka dogon takalmi shima baƙi,da jaka baƙa,ta gyara gashinta ya sauka gadon bayanta wani kuma tazubo tagaban kafaɗarta,sosai tayi kyau.


Koda zata fita abun mamaki yabata ganin feefee fuska ɗauke da faraa tanamata adawo lafiya,gamida koɗa ta da cewa tayi kyau sosai.


Hakanne yaba salma kwarin guiwar tafiya cikin kwanciyar hankali.


Tana isa office,su mary suks shiga koɗata,ita kum se wani efize takeyi ita ala dole ta haɗu.


Doctor kamar kullum ƙarfe takwas ya iso office,koda salma taje gaisheshi,ko alamar yaganta jiya da wani be nuna mata ba,haka har aka tashi agurin ayki.




Haka rayuwar salma tacigaba da tafiya doctor na ajiye kuɗi tana sata,kamin wani lokaci tazama babbar yarinya ga Alhaji dayake mata ruwan kuɗi,ko yaushe,feefee ko bata ƙara yiwa salma faɗan ta shiyuba,saurayi in yanuna yana sonta inde talakane,se tahaɗashi da ƴansanda tace fyaɗe yakeson yimata.


Mugayan halayenta ba abinda ya ragu sema ƙaruwa da yayi.


Yau weekend,salmace kwance akan gadonta suna waya da Alhajinta,wanda yawancin wayar,iskanci kawai suke faɗi.


"Baby yakamata wannan weekend ɗin kizo Abuja muyishi tare,wlh ina missing boobs ɗinki sosai".


"Alhaji kenan,ni wana sani a Abuja dazan zo weekend?boobs kuma ay kullum ina baka su ta waya,to me yayi saura?"


"baby i promise you inkikazo zan siyamiki mota,ladan zuwan dakikayi,yakike abu sekace ba babbar yarinya ba".


ihu salma tasaki awayar gami da cewa.


"Alhaji kana kasheni da daɗi,ayko inanan zuwa anjima,ammanfa kacika alƙawari"


"baki da matsala inde nine,"


haka sukayi sallama,suna ajiye wayar salma ta faɗa wanka,tana fitowa ta haɗe acikin riga da siket amman siket ɗin,mini ne dan ko guiwarta be kaiba.


Kaya kala biyu tasaka acikin jakarta,ta fice,a hanya suka haɗu da feefee.


"Ah a hajiya salma se ina kuma,akaci wannan wankan sikarin?"inji feefee.


Dariya salma tayi sannan tace.


"Kede bari wlh Alhaji ne da rigima,wai senaje gurinshi nayi weekend,shine yanzu zani"


Kai feefee ne yafara charge dajin batun na salma.


"kina nufin Yanzu gurinshi zaki kiyi kwana biyu kidawo?"


"to yazanyi feefee tunda ya buƙaceni,ay dole naje,"




"To salma adawo lafiya"tana faɗin haka tayi gaba abinta.


salma ko ajikinta,tahau mashin yakaita tasha,tahau motar Abuja.


Muje zuwa.


Surbajoce.
*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*


Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*8*


Tafiya sukayi ta tsawon awa guda suka iso birnin Abuja.


Koda salma tasauka atashar nyanya,guri tasamu agefen wani gidan mai takira Alhaji,ba jimawa ya iso gurin cikin wata arniyar jeep,range rover,Alhaji murna yake da ganinta bada wasa ba.


Haka yaja motar suka isa,hilton transcop hotel,dake Abuja.


Suna isa yayi parking a parking space,yazagaya ya buɗe mata ƙofa ya rungumota jikinshi sukayi hanyar shiga cikin gurin.


karab seji sukayi sunyi karo da wani mutum,juyowa sukayi duka sudashi domin aba juna haƙuri.
😳wa salma zata gani,doctor najeeb ne rataye da wani id card a wuyanshi alamar taro sukayi acikin hotel ɗin.


Binshi tayi da ido,duk kunya takamata,yanzu tasan kallon karuwa ze dunga yimata.


Doctor sosai abun yabashi mamaki,ashe yarinyar bin maza takeyi shiyasa take mummunar shiga,ji yayi ya tsaneta sosai a zuciyarshi,dan ya tsani,mace ballagaza,juyawa yayi afusace ya shige motarshi.


Ganin haka yasa Alhaji shima jan salma suka shige cikin hoteƙ ɗin.

ɗaki dama already yakama dan haka wucewa sukayi zuwa cikin ɗakin.


Suna shiga Alhaji ya rungumeta yana mata wellcome,nande suka taɓa ƴan wasanni,suka ci abinci,sannan,Salma tayi sallah,ta yi wanka tasaka sleeping dress.


Alhaji kamar tsohon maye haka yake binta da kallo itako se ƙara kaɗa ƙugu takeyi jigidar ta na ƙara tana daɗa ɗaga mishi hankali.


Jawota yayi jikinshi,yashiga wasa daita,takoina,har yayi nasarar rabata da rigar jikin ta,cigaba yayi da wasa da ita,tana biye mishi.


Sanda hannunshi yadauka akan fant ɗintane tayi sauri tariƙe mishi hannu,tadan ɓata rai tace.


"zan iya mallakamaka komai nawa amman banda nan gurin,duk wuya duk runtsi,banaso narasa farincikin daren farko agidan mijina dan haka ka kiyaye".


Maimakon taga yadamu seji tayi yace yana murmushi.


"Sory baby is a mistake,bazan ƙaraba".


Daga haka suka ci gaba da wasa da juna.suna tsaka da wasan ne wayar Alhaji tayi ƙara,ɗagawa yayi yayi magana,be ɗau lokaciba ya ajiye wayar.


zuwacan taji ana nucking ɗin ƙofar,dayake room and falor ne,Alhaji miƙewa yayi yafit,be jimaba yadawo ɗauke da wata ƙatuwar jaka dakyar yake ɗagata,yana shigowa da ita ya buɗe waldrope yasakata aciki,ya kulle yacire ɗan mukullin yasa a aljihunshi.


Hankalin salma nakan jakar sotake kawai taga abinda ke cikin jakar,Ba jimawa bacci ya ɗauke Alhaji,a hankali salma ta lalubeshi,ta ɗauki mukullin waldrope ɗin,ta buɗe,jakar ta buɗe a hankali.


Kuɗine aciki irin na ƙasar waje wato dollars,ido salma ta ware,gamida murmushi na farinciki.


"Tabbas inna ɗauke kuɗinnan nagama talauci a duniya"cewar salma a zuciyarta,dan haka komawa tayi a hankali tasawa Alhaji filo akusa dashi dan ya ɗauka itace.


Kayanta tasaka,ta ɗauki jakarta ta hannu sannan ta kinkimi ƙatuwar jakar,ta lallaɓa tafice daga ɗakin.


Daidaita tafiyarta tayi dan kar maaikatan hotel ɗin su ɗauka bata da gaskiyane,har tazo ta fice bawanda ya kulata.


Dayake ƙarfe shaɗaya na dare ne tana fitowa tasamu wani me taxi tace yakaita tasha konawane zata biyashi,ba musu yaɗauketa yakaita tashar.


koda sukaje tasha ba motar zuwa keffi dan haka,drope ɗin golf 3 ta ɗauka dan yakaita keffi adaren.


Nan suka tsadance ya ɗauketa,suna cikin tafiya ko nisa basuyiba,suka tarar da shinge na bincike wato jamian tsaro,koda suka ƙaraso se sukaga ashe hukumar,NDLA ce take binciken,sabida,sun kama wata mota ɗauke da hodar iblis,amman direban yagudu,shine suka bazu amanyan tituna suna binciken har dare.


Koda akazo kan motar su salma,bincike ƙaramar jakarta akayi baa sami komaiba,sannan aka buɗe babbar jakar,kuɗine aciki,da har sunce su wuce se wani jamiin yasake tsaidasu ya buɗe jakar,bindigar hannunshi yasa yana tona cikin jakar,ayko yana cikin dubawa,sega hodar iblis wato cocane acikin jakar,me yawan gaske.


"you are under arrest"suka furta atare gamida baibaye motar da bindigu.


Tuni salma tajima da sakin fitsari a wandonta,kamin tayi wani yunƙuri,tuni sunrufeta da duka,ita da direban,ihu take tana faɗin suyi haƙuri amman kota kanta basayi.


A motarsu suka zubasu ita da direban dabejiba be ganiba aka wuce dasu,head quater na hukumar.


Surbajo ce.
*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*




Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*feedo yarficika,Allah yajiƙan mahaifiyarki,yasa aljannace makomarta,Allah yay mata rahama,Allah yasa Annabi ya karɓi baƙuncinta,ku kuma Allah yabaku ikon jure zafi da raɗaɗin rashinta,Muma Allah yajiƙan namu iyayen da ƴan uwa musulmai baki ɗaya,Ameen don alfarmar Annabi da Alqur'ani😭😭🙏*




*9*


Suna kaisu office ɗin kowa yayo ca akansu,masu duka nayi masu tsinemusu nayi.


Kamin wani lokaci halittar salma gabaɗaya ta sauya,dakyar aka samu aka shige da ita gurin shugaban gurin.


Duk tambayoyin da akemata takasa amsawa se kuka takeyi,har abin shocking seda aka samata amman sede ihu data dungayi tagaza amsawa,


ganin hakane yasa aka fara binta ta lallama,tabada shaidar ba ruwan direban daya ɗaukota,wanda shi tuni yajima da sumewa sabida dukan dayaci.


Asibiti aka wuce dashi,ita kuma batare da ɓata lokaciba aka gayyato ƴan jarida,suka fara ɗaukarta hoto,gamida rubuta laifin datayi,duk wanda yaga hoton ma baze ganetaba,dan fuskar ta kumbure gaba ɗaya.


kamin wani lokaci tuni anyaɗata a social media da gidajan tv,da radio,da jaridu.


Kowa se laantarta yake,amman har lokacin taƙi faɗin komai game daita.


Kotu aka turata,ananma ba magana sede kuka,dan haka alƙali yabada umarnin akaita gidan maza ajiya,har zuwa sanda ta shirya bawa kotu amsoshin datake buƙata.


Haka akasa salma cikin mota,aka kaita gidan yarin dake kuje,ɗaure cikin sarƙa.


tun salma na iyayin kuka har takoma tagaza yin kukan.


se alokacin take danasanin,bijirewa iyayenta,da aminiyarta feefee.


Ta tubarwa Allah gameda Halin datasa kanta aciki,danasani tayi ba adadi.


Bakomai yasa salma taƙi maganaba,se kunyar datakeji tace satowa tayi,wanda tasan kota faɗa a ƙasa irin ta nigeria,ba yadda zaayiba,sabida kullum a nigeria me kuɗi shine me gaskiya.


A ɓangaren Alhaji kuwa,tunda yafarka yaga ba salma ba jakar kayanshi yasan itace ta ɗauke.


Ranshine ya ɓaci sosai,dan dama dakyar yaronshi yagudu da kayan da aka kamashi,shine ita kuma zata sace,lalle se ya koyamata hankali.


Tv ya kunna yana kallon NTA abun dayagani ba ƙaramin kiɗimashi yayiba,salma yagani ana nunata amatsayin ƴar safarar miyagun ƙwayoyi.


Tabbas yasan in yabari be ɗauki matakiba tsab asirinsa ze tonu,dan haka da sauri yakira malaminsa,yashaida mishi komai kuma yabashi umarnin a rufe bakin salma karta kuskura ta kama sunan shi.


Ayko malamin beyi ƙasa a guiwaba ya rufe bakin salma inda yakai laya yasa acikin kabari,da nufin inde na kabarin zaa tambayeshi yabada amsa to itama zata amsa tambayar da ake mata a kotu.


Feefee kuwa ganin har monday tayi ba salma ba alamartane yasa tafara damuwa,takira numbarta duka akashe,sunƙi tafiya.


har tsawon sati guda bata ganta ba hakanne yasa takai report,gurin mahukuntansu.


Nanda nan aka bazu zuwa tashar mota dan,aji kode sunyi hatsarine.


Koda akaje tasha,anshaida musu motar batayi hatsariba,amman anfaɗa musu akwai motar keffi data taso daga Abuja,ranar Lahadi da yamma datayi hatsari takama da wuta kowa nacikin motar ya ƙone.


Jin hakane yasa feefee rushewa da kuka sabida salma tashaida mata kwana biyu zatayi a Abuja,dayake ran friday ta tafi da yamma.


da kyar aka rarrashi feefee tayi shuru,can Abujan aka tafi office ɗin ƴan union,inda aka buƙaci dasu bada list na fasinjan dake cikin motar datayi hatsarin,koda aka duba wani ikon Allah sun samu da akwai mesuna salma aciki duk da batasa number wayaba,hakanne yasa kowa ya amince salma nacikin motar datayi hatsari kuma ta ƙone ƙurmus.


feefee ta suma yafi so uku,dan daga ƙarshe dole seda aka dangana da ita da asibiti.


Shiko doctor rashin zuwan salma gurin ayki be dameshiba,dan yasan tanacan yawon barikinta.


Hukumar NYSC ce ta rubuta report gameda mutuwar salma ta tura asibitin datake service.


Sanda takardar ta iso office ɗin doctor ba ƙaramar razana yayiba,wato ashe ganin dayamata na ƙarshene,tunda ance a hanyar dawowarta ne tayi hatsarin.


Mutuwar salma ta shigi docto ba kaɗanba,musamman inyatuno mugayan halayenta,wanda ta dawo daga aykatawane ta mutu tausayinta na kamashi,adduar samun rahama yayi mata.


Daga haka aka shirya jamiai tare da feefee da kayan salma aka nufi gidan iyayen salmar.


Koda suka sanar dasu mutuwar ƴar tasu ba ƙaramin gigita sukayiba sunyi kuka kamar ba gobe.


Sahabi yace cikin kuka.


"ita da aka tura keffi me yakaita Abuja kuma?"


Da sauri feefee tabashi amsa da cewa.


"Anturata wani research ne agarin shine tsautsayin ya rutsa daita".




Nande akaita ƴan koke game da mutuwar salmar,dangi nakusa dana nesa duk sunzo taaziyya.


Kayan salma ko Akwati biyar,haka aka shigar dasu ɗakin mahaifiyarta.


Haka iyayenta suka cigaba da kukan rashinta harsuka dawo suka fawwalawa Allah.


koda wasa mahaifiyar salma ko wani nata basu taɓa shaawar buɗe kayan nata ba,dan daga ƙarshema,ɗakin da suke ajiye tarkace aka Kai kayan aka zuba.


A,B,U zaria ma ta turo wakilanta yin taaziyar mutuwar ɗalibar tasu,harda kuɗi suka bada sadaka.


Feefee ta koma gurin service ɗinta amman kullum jitakeyi kamar zataga salma,takasa sabawa da rashinta.


Salma ko tanacan gidan yari ana gana mata azaba sabida taƙi faɗin koda sunantane bare asan daga inda take.




muje zuwa.


surbajo for life.
*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*


Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*10*


Salma tayi kuka tayi kuka har ta godema Allah,tayi danasani mara iyaka,na halin data jefa kanta.


Tayi Allah wadai da duk wani me kwaɗayi da buri irin nata wanda ƙarshe ga inda yajefata.


Ba abinda ke ƙara sa zuciyar salma zafi kamar tinawa datayi yanzu ta tashi daga ƴar bautar ƙasa ta koma ƴar bautar gidan kaso.


Haka rayuwa taci gaba da tafiya sannu a hankali kowa yamance da wata salma ya rungumi rayuwarshi.


Salma yanzu an mance da ita ma a gidan yarin,dan alƙalin be ƙara buƙatar akawota ba,hakanne yajanyo zamanta a gidan yari ya kankama,dan tun tanasa ran zata fita har tacire,ta maida rayuwarta ga bautar ubangiji da neman yafiyarsa abisa laifin data aykata.


Yau su feefee suka gama service ɗinsu cike da nasarori,lokacin dasuka kamo hanyar zuwa kaduna inbanda kuka ba abinda feefee takeyi,sabida tunowa da tayi da ranar dazasu zo ga ƙugunta gana salma amman yau ba salmar akusa da ita.


Haka suka isa kaduna cike da nasarori na murnar kammala bautar ƙasa lafiya.


*BAYAN SHEKARA ƊAYA DA RABI*


Duk wani mahaluki dayasan salma yajima da mancewa da ita.


Tuni feefee tayi Aure,har tana da cikima tsoho,kuma tana ayki a wani kamfanin dake yin atamfa.


Doctor najeeb an daɗe dayimasa transfer daga Keffi zuwa Abuja,a international hospital dake Abuja Amatsayin babban likita.


Nigeria anyi zaɓe inda akasamu sauyin gomnati,wacce sabuwar gomnatin me adalci ce,dan abu na farko data fara yi shine.


Kama ɓarayin gomnati tana kaiwa prison tana kuma fito da masu gaskiya daga prison ɗin.


ana hakane tawagar dake binciken gidan yarin kuje ta iso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login