Showing 6001 words to 9000 words out of 24136 words
Chapter 3 - YAR BAUTAR KASA COMPELET DOCUMENT BOOK.txt
shingen da su salma suke zaune,dayake da ƴan jarida suke tafe shiyasa akwai maaikatan gidan tv.
Ɗaukarsu suka farayi ana musu tambayoyi,koda akazo kan salma kuka kawai takeyi,ana mata tambaya amman tagaza cewa komai se kuka.
Cikin hukuncin ubangiji ana tambayarta ya suna tace.
"Salma Hadi"
"Daga ina kike,me kikayi aka kawoki nan?"wani ɗan jarida ya wurga mata tambayar
Takasa bada amsa se kuka takeyi,hakanne yasa ,suka juyar da tambayar ga jamiin dake kula dasu,inda yabasu amsa da cewa.
"ita wannan dakuke gani babbar ƴar safarar miyagun ƙwayoyice,shekarun bayane aka kamata da hodar iblis daga Abuja tanaso tashige da ita jahar nasarawa,kuma inbanda yau tunda aka kawota bata taɓa faɗin sunantaba,sede tayi ta kuka,ba irin azabar da baa gana mataba amman raƙi yin magana"
nande ƴan jaridar suka ci gaba da ɗaukar rahotonsu,har suka gama suka fice.
Doctor Najeeb ne zaune agaban tv yana kallon news daga tashar nta,da ze kashene amman headlines ɗin da presenter yakaranto sune suka ɗauki hankalinshi,inda yaci gaba da kallon tv.
"A yaune jamian da gomnati ta naɗa domin bincika gidajan yarin dake faɗin kasarnar suka isa gidan yari dake kuje,inda sukayi gagarumar nasarar tattaunawa da babbar ƴar safarar miyagun kwayoyin nan,wacce aka kama,shekaru biyu da suka wuce,wacce taƙi faɗin sunanta dakuma adireshinta,ga rahoton da wakilin mu ya ɗauko mana".
ƙara gyara zama doctor yayi yana kallon tv.
Gidan yarin aka hasko,tare da masu binciken dakuma ƴangidan yarin,ana musu tambayoyi,har akazo kan salma.
Ido doctor ya ƙuramata,yanaso yagano inda yataɓa ganin zoben dake hannunta na azurfa,dan tabbas yasan yataɓa ganinshi,amman ya manta ko a ina yagani.
Hankalinshine yaƙara tafiya gurin sunan dayaji ta ambata.
"Salma hadi"tabbas sunan yataɓa jinshi amman yamance ko a ina ne.
Bayanin da jamiin gidan yarin yayi shine ya ƙara sawa ƙwaƙwalwar doctor ɗaukar zafi,nason tilasta mata ta gano mishi me wannan sunan.
Fuskar salma aka cigaba da nunawa,wacce babu mecewa itace,kwayar idonta Doctor yaci gaba da kallah,zuwa can yamiƙe a razane ya furta.
"Barauniya ta!!!!yes she is the one"
muje zuwa.
surbajo for life.
*👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA*
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*11*
Gaba ɗaya yagama rikicewa yarasa abinda ke damunshi.
Waige waige yashiga yi yana neman wayarshi amman dayake a ruɗe yake sam yagaza,ganinta,se zuwa can Allah yakai idonshi kanta.
Da,sauri ya ɗauka ya dubo wata number yakira ba jimawa naji yace.
"Hello barrister,kana gidane?"
Dagacan ɓangaren yace.
"eh ina gida,amman kasan ayni ba gwauro bane kamarka,ina fatan de bacewa zakayi zaka zoba?"
Se alokacin doctor yafahimci ashe darene ba safiya ba.
"Da safe in Allah yakaimu inaso mu haɗu"doctor ya faɗi cikin damuwa.
"ok baka da damuwa Allah yakaimu safiyar"
Daga haka kowa ya ajiye wayar.
Doctor safa da marwa yashiga yi,zuface kawai take keto masa.
"Me ya haɗa salma da hodar iblis,adaren daya ganta?meya hanata yin magana a kotu domin ayi bincike?"wani tambayoyin su doctor ya kwana yiwa kansa har garin Allah ya waye.
Da safe da wuri ya shirya ya wuce office ɗin Barrister,be zoba seda ya jirashi na tsawon awa biyu.
Koda barrister yaga yanayin doctor yasan yana cikin damuwa sosai,danga idonshi ya nuna beyi bacci bama jiya.
"bokan turai me yake faruwane?"barrister ya tambaya.
"Barrister komai ma yafaru,wallahi narasa natsuwa tun jiya dana kalli news da aka nuna gidan yarin kuje"
Wata dariya ce ta ƙwacewa barrister inda yace
"kaiko in banda shirme irinnaka ina ruwanka da gidan yarin?"
"Bazaka gane bane barrister,shekaru biyu da suka wuce lokacin ina ayki a keffi akwai wata ƴar bautar ƙasa da aka turo office ɗina daga A,B,U zaria,to yarinya irin wainda suka fiye son kuɗi ɗinnanne,dan sometimes inna ajiye kuɗi tana ɗauka,so biyu ina ganinta da wani Alhaji wanda ni zuciyata bata amince dashiba,ƙarshen ganina da ita,wani darene munje conference a Abuja,naganta tare da mutumin zasu shiga cikin,hilton transcop hotel,to abun mamaki,bayan sati ɗaya dayin hakan sega report daga Hukumar NYSC zuwa office ɗina wai tayi hatsari ta ƙone maana de ta mutu,tsawon wannan lokacin da aka ɗauka ina mafarki da ita tana miƙomin hannu da niyyar incirota daga wani kogi data faɗa,toni tunanina se yabani,maybe ana mata hukuncine game da satar datasha yimin dan haka sekawai nayi sadaka sannan nace na yafe mata,ti kwatsam jiya segashi naganta acikin gidan yarin wai shekaru biyu kenan da aka kamata da hodar iblis,kuma babu irin azabar da baa gana mataba amman taƙi yin magana,kuma koda aka nunota jiyan still kukan takeyi,barrister kaji abinda ya ɗaga hankalina"cewar doctor fuskarshi na nuna tsananin damuwar dayake ciki.
doguwar ajiyar zuciya Barrister ya yi,sannan yace.
"Gaskiya abokina wannan zancan adubane,zeyi wuya idan ba sato jakar tayiba tunda tanayin satar"
"wlh barrister nima tunani na kenan,wata ƙila gurin shegiyar satar tane taje ta satowa kanta masifa"
Shuru barrister yayi kana daga bisani yace.
"ka kwantar da hankalinka,insha Allahu se angano gaskiya,karkadamu yanzu kataso muje gidan yarin mu nemi ganinta,wataƙila mu tayimana bayani"
"To Allah yasa,amman mu biya ta office nayi signing semu wuce kuje ɗin"
Daga haka Asibitin da doctor yake ayki suka je yayi signing sannan suka fice zuwa gidan yarin kuje.
Koda suka isa basu sha wata wahalaba gurin samun izinin ganinta,sabida barrister babban lauyane kuma fitacce.
Gurin da aka tanada domin ganawa da masu laifin aka kaisu,sannan akaje aka taho da Salma ƙafa da hannunta ɗaure cikin sarƙa,koda akace tazo tanada baƙi ba ƙaramin mamaki tayiba dan tunda aka kawota kare bezo yace yan nemanta ba.
Koda aka kawota gaban su doctor,agigice yake kallonta,sabida gabaɗaya,duk wannan kyan da kyan surar duk babu,takoma kamar tsohuwa sabida wahala
Sanda salma ta ɗago idonta taga doctor,wani kukane ya kubce mata,zubewa tayi agabanshi tana faɗin.
"Don Allah kayafemin,kagafartamin,wlh nasan hakkinkune yakamani shiyasa aka kawoni nan,kagafartamin,don Allah"ta ƙaras maganar cikin matsanancin kuka,ta ruƙo ƙafarshi.
Runtse ido doctor yayi yanjin kukan salma na taɓa zuciyar shi.
Hannuns yasa ya ɗagota ya zaunar da ita kan kujera,sannan,yasa hand carchiep yana share mata hawaye,riƙe hannun salma tayi wasu hawayen nabin fuskarta tace.
"shekaru biyu kenan ina irin wannan kukan,babu wanda,yataɓa gogemin hawayen sekai,Allah yasa kayafemin ne?"
Kai doctor ya ɗaga mata.
Shiko barrister,abun nasu tv yazamar masa,danshi bema taɓa ganin masoya irin suba.
Gajiya yayi,da kallon nasu ya dakatar dasu,suka fara abinda ya kawosu.
Muje zuwa
Surbajo for life.
*👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA*
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Safina mum sultan,saly,Queen Aeanarh,wannan shafin nakune Allah yabar so da ƙauna,nagode sosai,kuma insha Allahu bazaku taɓe ba*
*12*
Natsuwa sukayi sosai dan su samu mafita.
Barrister ne yace.
"Malama,Salma,sunana barrister,kabeer,ni lauyane me zaman kansa,sannan ni amini ne ga doctor najeeb,inaso ki bani amsar duk wata tambaya dazan miki tsakaninki da Allah,kinyi alƙawarin bani amsar?"
Kai,ta daga masa tana kallon doctor wanda shima ita yake kallo.
"Me yasa kika jefa kanki cikin sanaar da bata dace dakeba?kina mace meyakaiki safarar miyagun kwayoyi?"
Kuka salma ta rushe dashi,cikin kukan tace.
"Wlh ni ba sanaata bace,hasalima ni bansan akwai kayan laifi acikin jakarba wlh"ta ƙarasa maganar cikin kuka.
"Jakar takice ko ba takibace?"
"wlh batawa bace"cewar salma
"to a ina kika samota?"cewar barrister.
Ƙasa tayi da kanta alamae kunya dajin nauyi sannan tace.
"Satowa nayi"
Runtse ido doctor yayi sabida maganar ta zafafa zuciyarshi.
"a ina kika sato"inje barrister
kuka ta fashe dashi,sam bakinta yakasa faɗin inda tasato jakar,duk yadda su doctor sukayi da ita dan ta faɗi inda ta sato jakar amman ta kasa.
Haka suka haƙura sukayimata sallama akan zasu dawo wani satin.
Koda suka taho a hanya doctor ya kasa magana,gaba ɗaya ranshi aɓace yake
Murmushi barrister yayi sannan yace.
"No wonder mutumina jiya ka kasa bacci,ashe amaryace ke hannun kwalawa,dole hankalinka yaƙi kwanciya"ya ƙarasa maganar yana dariya.
Tsaki doctor yayi sannan yace.
"kai daɗina dakai zancan banza wlh,to bari kaji ni wlh ba son salma nakeyiba,ba abinda zanyi daita,ɓarauniya ce fa"
"to su ɓarayin ba mata bane?,kuma zancan sata ay dana,kaida ganinta a yanzu kasan ko ɗaura mata kayan satar akayi a hannunta seta gudu tabarshi aguri,to kuma shine abun dogaro dan kawai tayi sata ada,ay yanzu ta tuba"
"to komade me zakace ni banasonta,kuma bazan taɓa sonta ba"
"hhhhh ah gaskiyane wannan arashin sonne ma jiya ka kasa bacci sabida kaganta acikin mayuyacin hali"
"wlh bana son salma tausayinta kawai nakeji amatsayinta na musulma"
"tausayi baya zuwa seda soyayya,mutumina kayarda kana cikin soyayyar salma kawai"
"karubuta ka ajiye,ni najeebullah,nafi ƙarfin salma nesa ba kusaba,na faɗa maka ni ba sonta nakeba,karka sake yimin wannan maganar pls"
Dariya yayi sannan yace
"to tuba nake angon salma"
Tsaki doctor yayi sannan yamaida hankalinsa kan titi.
"Amman najeeb nayi mamakin abinda ya hana salma faɗin inda ta sato jakar nan,nifa ina ganin kamar anyi mata sihirin daya rufe bakintane,sabida inkayi laakari tana yunƙurin faɗi amman se ta kasa"
shuru doctor yayi yana nazarin maganar zuwacan yace.
"tabbas naga alamar hakan,to amman yazamuyi,yanzu?"
"ka kwantar da hankalinka kamance mahaifina malamine,aykawai gobe mu shirya muje katsina,gurinshi muyi masa bayani danni banaso mu shiga kotu asake ɗaga ƙara,sonake ayiwa shariar salma zama ɗaya tak dan asallameta da wuri,ayi ayi ashafa fatiha dannaga angon nata kamar amatse yake"
wani duka doctor yakaiwa barrister wanda saura kaɗan motar ta kwace a hannunsa.
Dariya barrister yadunga yiwa doctor shiko yasha kunu kamar be taɓa yin dariyar ba.
Washe gari da Asuba suka ɗauki hanyar katsina,sun isa lafiya.
Inda sukayiwa baban barrister bayanin abunda yakawosu,ayko beyi ƙasa a guiwaba yayi istahara ya tabbatar musu da hasashensu,daganan,rubutu yayi na ayoyin Allah,ya wanke yabasu yace abata tasha awanke mata fuskarta da rubutun.
ba yadda barrister beyi da doctor ba akan su kwana amman fafur yaƙi shide sede su tafi aranar.
Ayko dole barrister yabishi suka ɗauko hanyar Abuja,basu isoba se ƙarfe biyu nadare,barrister se mita yake masa da cewa.
"wlh akan taka amaryar baza ka illatawa tawa amaryar ni ba ehe"
doctor yagaza bashi amsa haka sukayi sallama.
Washe gari takwas na safe a gidan yarin tayi musu.
inda doctor shida kanshi yaba salma rubutun tasha sannan ya wanke mata fuskar.
cikin hukuncin ubangiji tun kan su tambayeta tafara faɗin.
"jakar ta Alhaji Adamu canji ce ma'aikacin CBN"
Daga haka rakwashe komai ta sanar dasu tundaga ranar data fara haɗuwa dashi.
godiya suka yiwa Allah,daya bata damar faɗin sunan me jakar.
Daga gidan yarin,cbn sukaje neman Alhajin amman basu sameshiba dan haka hotel ɗin da abun yafaru sukaje.
Inda suka nuna katinsu na shaidar ayki sannan suka buƙaci da a nuna musu video na wunin ranar da abun yafaru.
Ansha wuya kamin asamo video ɗin,koda aka kunna.
Wani mutumne yashigo sanye da baƙaƙen kaya ɗauke da wata ƙatuwar jaka,wani ɗaki yanufa,abakin ƙofar ɗakin ya tsaya yakira waya,zuwacan sega Alhaji adamu canji yazo ya buɗe ya amshi jakar ya koma ciki shi kuma mutumin ya juya yatafi,baa jima sosaiba sega salma ta fito ɗauke da jakar tana ta waige waige alamar rashin gaskiya,zuwacan kuma seta daidaita tafiyarta tazo tawuce ɗauke da jakar.
gwauron numfashi suka ja dukansu,sannan sukasa aka dubo list ɗin sunaye na ranar,inda sukaga sunan Alhaji adamu canji shine yakama ɗakin da salma tafito daga ciki.
Da ƙyar manajan hotel ɗin ya amince ya basu list ɗin da plate ɗin video,seda suka sha fama dashi sannan yabasu amman dasunan aro.
Daga hotel,kotun ɗaukaka ƙara suka je suka shigar da ƙara inda aka tsadar musu da lokacin da zaa saurari ƙarar.
Amman kamin zuwan ranar,kotun taba hukumar ƴansanda umarnin atsare Alhaji Adamu kamin zuwan ranar.
Ayko cikin saa ƴansanda suka kamoshi a airport yana shirin bsrin ƙasar sabida yasamu labarin komai.
muje zuwa
surbajo for life.
*👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA*
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*13*
Rana bata ƙarya.
Ayaune dubban mutane suka hallara ababbar kotun ƙasa dake Abuja domin suraran shariar su salma.
An fafata ankai ruwa rana tsakanin barrister kabeer,da lauyan Alhaji Adamu,sabida ƙwararren lauya ya ɗauka, daga ƙarshede su barrister kabeer suka gabatar da shaidunsu,da hujjoji,wanda hakan shi yajanyo alƙali ya yanke hukunci batare da ɓata lokaciba.
Kotu ta wanke salma daga zargin da ake mata inda shikuma Alhaji aka yanke mishi hukuncin kisa ta hanyar rataya...
Haka kotu ta watse kowa se barka yakewa salma itako se kuka takeyi,na farin ciki.
Da kyar take taka ƙafarta sabida tsawon shekaru biyun datayi a gidan yari ɗaure take cikin sarƙa.
Ahaka suka fito harabar kotun,ƴan jarida ne suka zagaye salma suna mata tambayoyi,da sauri doctor yasha gabanta,ya kareta,sannan ya dakawa ƴan jaridar tsawa da cewa.
"Dalla malamai ku ƙyaleta,ina ruwanku dason sanin halin farincikin datake ciki,meyasa lokacin da aka kamata bakuje kunyi mata irin wannan dairar ba?to bazatayi magana ba"yana kaiwa nan yajata da ƙarfi suka bar gurin.
A mota suka sami barrister yana jiransu,doctor sakinta yayi yaje ya buɗe gaban motar yashiga,salma hannu tasa zata buɗe bayan motar,da sauri doctor ya dakatar da ita da cewa.
"ke gidan ubanwa zaki bimu kuma?ay mungama aykinmu,dan haka kibi wani sarkin bamuba,dan munan da kika ganmu babu wani me neman mata,acikin mu bare kice ko kinyi kasuwa ne,kuma babu ɓarawo anan bare kice zaki bimu mu ƙara miki sani akan harkar dan haka tun wuri ki kama kanki,useless kawai"
durƙushewa tayi agurin tana kuka jikinta se rawa yakeyi,numfashinta na haurawa sama zuwacan ta kife agurin a sume.
A gigice doctor ya buɗe motar yazo gurinta kinkimarta yayi yasaka abayan motar,sannan shima yashiga bayan ya ɗora kanta akan cinyarshi sannan kabeer yaja motar da gudu suka nufi Asibitin da najeeb yake Ayki.
A hanya kamin suje,najeeb yafara bata taimakon gaggawa,inda ya ɗora bakinshi akan nata yafara hura mata iska ta baki,sannu a hankali tafara numfashi sama sama,a haka suka ƙaraso asibitin.
Doctor be jira akawo gadon ɗaukar marasa lafiyaba dakanshi yaɗauketa yayi cikin Asubitin da ita kabeer na binshi abaya.
Hankalin doctor be kwantaba seda yaga salma ta dawo cikin hayyacinta ba abinda ke damunta.
Abinci yadunga bata abaki harseda tace ta ƙoshi sannan ya ƙyaleta,shide kabeer yana gefe,cikinshi ya cika da dariya amman ya danne shiyasa ya ƙosa su fita.
Allurar bacci doctor yamata,shima da kyar ta yarda,sabida tana kunyar yaga jikinta,shiko ko ajikinshi dan juyawa yayi yana kallon kabeer rai aɓace yace.
"Malam baka ganin zan mata allurane?dan Allah kaɗan je daga waje,haba mutum se shegen sa ido"
Ba musu kabeer yafita,sannan,doctor yajawota jikinshi ya matseta ya ɗaga doguwar rigar dake jikinta,yaɗan matsar da fant,ɗin yayimata allurar,sannan ya saketa se kuka takeyi.
Shiko ba abinda yafi bashi mamaki,se irin dattin da yaga fant ɗin yayi,hakan na nufin shikaɗai take sawa acan kenan,sosai ranshi ya ɓaci dan haka kwantar da ita yayi,yafara yimata general check off na cututtuka,inda yasamu,tana da maleria da typhod.
Magunguna ya ɗauko da suka dace yabata tasha,sannan tafice daga ɗakin.
A harabar Asibitin suka haɗu da kabeer.
kabeer yana ganinshi yamiƙa masa key ɗin motar yace.
"Don Allah kaɗanyi driving ɗin inni nace zanyi komai ze iya faruwa"
ba musu ya amshi key ɗin suka shiga motar yaja suka ɗau hanya.
Ay kabeer kamar jira yake,yafara tuttular da dariyar data cika mushi ciki.
shiko najeeb ƙara shan kunu yayi alamar ba wasa.
"wlh najeeb baka da kunya,wai har zancema son salma kakeyi amman ka ƙaryatani,inba sonta kake yiba ina ruwanka da ƴanjaridar ɗazu,?in ba so meyasa ka ruɗe sanda ta faɗi bayan kaine silar faɗuwar tata?inba so meyasa ka gaza jira mu iso asibiti kadubata,kafara bata taimako tun amota?,finally,meyasa kaji kishin inga jikinta sanda zakayimata allura?"kabeer ya faɗi yana dariya.
wani uban tsaki najeeb yaja,sannan,yace.
"Kaide anyi ɗan iska wallahi,inbanda kaiɗin,bakasan aykinaba,taya zanga mutum asume amatsayina na likita nawuce batare dana taimakeshi ba?kuma shi kenan danni ɗin ɗan iskane se inbari kaga jikin patient ɗina alhalin kaiba muharraminta bane?su kuma ƴan jarida in aka barsu ay zuwa zasuyi su yaɗa ƙarya da gaskiya,shiyasa na hana badan komaiba,sedan ƴar uwatace a musulunci,kainifa kabeer ka isheni wallahi banason salma bana ƙaunarta sam,dan bata jikin jerin matan danakeso,inkuma kasake magana wallahi sena saukeka a titi"
Shuru kabeer yayi amman fa bedena dariyaba,musamman sanda suka tsaya awani boutique,yatambayi najeeb mezasuyi anan,yabashi amsa da cewa.
"salma zamu siyawa kayan dazata canja najikinta sunyi datti"
Sosai kabeer yake dariya ahaka suka shiga gurin,yazaɓo mata dogayan riguna masu kyau guda biyar,sannan ya isa gurin su fant da bra,ido kabeer ya ware yana kallonshi,ba abinda yafi ba kabeer dariya kamar ganin yadda najeeb in ya ɗauko fant ko bra,seyayi ɗan tunani kaɗan,sannan se ya jujjuya,wani yaɗauka wani ya ajiye,hakanne yasa kabeer ya gano,doctor yana kallo salma aranshine sannan ya zaɓi wanda yake ganin ze mata daidai.
"mutumina kace abun yayi zurfi har haka ashe bansaniba,ah lalle salma tagama da zuciyarka sauran mata se haƙuri,princess over the universe ta iso"kabeer ya ƙarasa zancan yana dariya.
Duka najeeb yakaimasa,sannan yace.
"Tunda kazama maye bari na kyaleka duk abinda zakace kaje kaita cewa tunda de ni nasan basonta nakeba ay shikenan"
Har suka dawo Asibitin kabeer bedena tsokanarshiba,sanda suka shiga ɗakin tana bacci dan haka ajiye kayan sukayi,har zasu fita doctor yaga gashi ya rufe mata fuska,komawa yayi ya gyara mata,sannan suka fice.
muje zuwa.
surbajo for life.
*👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA*
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*14*
Salma farkawa tayi taga leda akusa da ita,buɗewa tayi abinda tagani acikine yabata tabbacin natane,to amman waya siyo mata?.
Wanka tashiga,ta jima a toilet tana wanke jikinta,haka ta dunga zubar da ruwa baƙiƙƙirin sabida dattin jikinta,haka gashin kanta,tajima tana wankeshi,dayake a office din doctor ɗakin yake,tamkar de shine emergency ɗinshi,to komai akwai na amfani a toilet din,hadda hand drayer dan haka busar da gashin tayi.
Kusan awa biyu ta ɗauka a bayin sannan ta fito,
Fant tasak da bra ba ƙaramin mamaki tayiba ganin yadda suka mata daidai,dan ko ita taje siyowa da kanta tana mistakes,riga ɗaya ta ɗauko tasaka,rigar,ja ce da gyalenta shi kuma fari ,ajiye gyalen tayi,tafita zuwa cikin office ɗin doctor ɗin tafara neman ko turarene,ayko ta gano wani tafesa sannan tadawo ta ɗauki cumb tafara tace kanta.
Zafi take ji sosai yayin taje kan,amman haka ta daure tanayi ta runtse ido wanda kowa yaganta yasan ba ƙaramin zafi take jiba.
Doctor ne ya shigo ɗakin fuska ba walwala,itako sabida zafin da kanta yake mata batasan yashigo ba,zuwa yayi ya riƙe hannun datake taje kan dashi,da sauri ta ɗago kanta tana kallonshi,ganin shima ira yake kallone yasa tayi ƙasa da idonta.
"Shi taje kan dole ne se anyi shi tunda anajin zafi?"doctor ya faɗi rai aɓace,
Shuru tayi ta ƙara yin ƙasa da kanta,dan yanzu gaba ɗaya nauyinshi takeji.
"kar in kuma ganin hakan,inba hakaba rai ze ɓaci,taso muje kici abinci"yana gama magana yajuya yayi gaba,miƙewa tayi ta yafa gyalen rigar tabishi abaya ƙafa ba takalmi
Yana gaba tana binshi abaya har zuwa harabar asibitin se alokacin ya lura ƙafarta ba takalmi,miƙa mata takalminshi yayi yace tasaka.
tsayawa kallonshi tayi ganin ba wasa afuskarne yasa tayi saurin zira takalmin shikuma yaci gaba da tafiya ba takalmi har suka isa motarshi.
wani gurin saida takalma ya tsaya,ya fita zuwacan se gashi yadawo,da sabon takalmi aƙafarsa sannan itama ya siyo mata nata aka sako a leda.
Restaurant yasamu me kyau ya tsaya sukaci abinci sannan suka fito suka shiga mota.
Hanyar kaduna taga ya ɗauka,wani farincikine ya lulluɓe zuciyarta yau,zataga iyayenta,ɗa aminiyarta.
Suna tafe a hanya ko tari tayi,seya waiga ya kalleta,amman bazeyi magana ba ahaka har suka iso garin kaduna,waigowa yayi yakafeta da ido hakanne yasa tagane Address yake nufi tadunga nuna masa.
Ayko haka ta dunga yimasa kwatance har suka iso ƙofar gidan,sahabi