Showing 15001 words to 18000 words out of 25648 words

Chapter 6 - JININ SARAUTA Book 3 End By oum Aphnan.txt

nan muka d'ingumo zuwa farfajiyar ,inda wainnan maroqan suka haukace da kirari muryoyinsu ya qara d'agawa




"Yooo ko yau nakkoma ga ubangiji ban yarba.....eh bamuyarba....ganin magajiyarmu dacene...eh dacene....tauraruwa mai haske ,dariyar ki fitar nairorine ....eh nairorine....sarauta gadonkune,mulki damarkice....qasaita ajininku take ,kyauta daga hannunku ta qare, nasha rawa don murnan kyauta ban ta6a kuka don kyautabaa....eh jaruma sadauki tauraruwa shalele,Allah yaja da yawan raiiiiii..ehhhh " wani ya dad'a d'aga kai zai cigaba da waqeta a hankali ta d'aga masu hannu




D'if kaji kamar mutuwa ta gifta
Kallon matar da suke tare da ita tayi kosassu ajin karshe,kowa ka kalla naira ta tsumata tawagar matar gwamna hajiya karima




"A raba masu kujera goma,motoci goma,da miliyon biyu susha mai"




Wani gigitaccen sowa suka dauka ,gidan ya rikice kasa waqan sukayi kawai sai suka d'auka da cewa
"Yaro nemo tsaranka ,yaro nemo tsaranka"




A take hajiya karima ta tuttulo ido waje,shifa tsiyar zuwa fada kenan duk isarka sai sun sattar maka da gwuiwa,yanzu jiba ta siyanwa kanta girma ni kuma da basu wainnan gagaruman kyautan




Saida ta furzo da wahalallen numfashi kafin ta kalli wannan matar na dazu da ta bada akwatun daloli




A basu kujerun hajji goma,a fitarda miliyon talatin cikin wannnan fund d'in a bada motoci goma ,da miliyon biyar ,tukwuicin kirari wa gimbiya




Zaman en bori marokan sukayi ,saiga shi suna shesheqan kuka ,lallai dole suyi raki,Allah ya kashe ya basu yau sun tako arziki ,gasu ga matar gwamna ga matar shugaban kasa ,kuma hamshakiya magajiyar fada




Murmushin dole gimbiya khalisa tayi ,don sosai taso ganin iyakan hajiya karima don ta lura ita din irin matan nan ne masu dagawa da qaryan arziki,ga shishigi da zulwajahaini,bata San shi fada bayason izzah ba ,a duk inda sikaje girmamawa auke buqata ba kyautar kashe kaiba,saidai bakomai in halin tane zasu had'e a gaba .....
[8/19, 13:35] Bamalli: *JNS*
71-75
Ina zaune dani da kuyangina a babban falon qasan ,a zuwa yanzu na mallake falon ya zama wajen fadancina ,inkin ganni a sashena to barci yakaini,don ko sallah anan Nikeyi da cin abinci,gashi duk na siye en aikin gidan da kyauta na,har masu aikin gidan haduwa da kuyangina sikeyi aita fadanci da banbadanci,Abu dayane ban jura kawo tsegumi




Kamar ko yaushe ina kishingide akan lallausan tafkeken carpet din falon gabana akushine shashaqe da kayan marmari ,na shimfid'e kafafuwana da sukasha Jan lalle,wannan na matsamun su wannan namun furfita majestically a yayinda sauran ke kewaye dani a zazzaune wata tana bani labarin ban dariya ,nikuwa in anyi abun dariya sun qyalqyale da dariya sai inyi murmushi


Kurum cikin rashin zato sai gata ta shigo dakin cikin takun issah ,ta kalli dukkanmu ta watsar




Kallon sheqeqe tayi mun sannan ,a wulakance tace "tashi...tashi maza kubar nan wajen duk kun ishi mutane da shirme da shiririta bakuba ba shashashar wacce ta tarakuba"


Tsam na mike zaune ,raina na azalzalata


Na dad'e ina shanye damuwar rashin mutuncinta amma nayau yafi na kullum 6atamun rai,ai wannan sai taja su rainani




"A'ah anty tsaya akan 'yan aikin gidan mijinmu,amma ki qetareni da kuyangina"




"Har kenan banzan bazara cikon bencin tarkacen sharan kasuwa,mijinki ko mijina ,mijin da baisan da zaman kiba ,da kwananki da nawa kina kallo zan had'e su zama nawa,ba yanda kika iya saboda dolanci"




Dariyar rainin wayo na bita dashi ,kafin in umurci duk 'yan aikin su fita ,sannan nasa hannuna a baki na dauki ihu "wooowooo,andai aure mata miji wiooooo"


"Ke ni tsararkice? Bakisan ganin damata bane ,na bari presdo ya aureki,ko ya taimaka ya daga sunan fadanku,dabadin hakanba saidai ki qawarewa ngwandu ,dake qarqashin ikonmu,soooo auren miji daya bashine zarran kwacen mijinba,shashasha"






"Sorry anty ai kinrigada kinyi sake ,don kuwa tamkar yanda ake qwace goruba a hannun yaro haka zan qwace excellency a hannun ki ,idan nayi ra'ayi...
Saidai ina tayaki murna ,kuma inason miki kyakyawar albishir cewar har yanzu excellency baya cikin jerin kalar mazan da na ke so kuma zan iya aura....so plz aje a qarawa boka kud'iiiiiyy..."


Ta fad'a tana ca6e baki,tana naqishe hanci tana girgiza qafa


Ayayinda ummah ta mike ta fiddo mata da duk idanuwarta sannan ta doka mata wani gigitaccen tsawa


"Ke er iska fitsararriya,marar mutumci,karamar ja'ia..."


"Shishhhhh🤫🤫..." Ta fada sannan ta gyara zamanta ,ta kunbura naman kasan ha6arta,ta d'aura hannu a kasan kwai6i,ta ca6e baki tana daddallaro ido




"...hmmm anty ni kika kira da er iska,bla ...bla...bla ko? Fine.
Amma tunda nayi maki kara ta hanyar qyale maki miji kin kasa ganewa ko,to zamu canja wasan, saina nuna maki iskanci da salsalolinsu ke kika koyamun ,ni kuma na daura daga kan inda kika tsaya ,nazo na shafeki....zaki ga iskancin akan gadon barcinki ,tsakanin ni da mijinki in bakiyi wasab...."




Da gudu ta taho ta daga hannu zata sharareta da mari.


A daidainan excellency ya turo qofa,a take ya shigo da sauri yina rawar baki "keyyy key...hajiya lafiya kuwa ya mari da girmanki"




Sunkuyar da kai nayi da sauri ina gyara d'aurin ture kaga tsiyar da na turo gaban goshi ,zuwa qasan tuntun gashina...kafin na mike da gudu naje na d'ane bayarsa,na sa hannuna ta wajen qasan mararsa na cukuykuyesa ,ina jin yanda duk jikinsa ya amsa, hakan yasani lekowa nayi mata gwalo kafin na fara magana cikin murya irin na sangartattun yara




"Barka da zuwa ubangidana,gatana ,farincikina...abbah gwara da kai gaggawar dawowa,qila da baka dawo da wuri ba da kazo kaga gawar amaryanka"




Na qarasa ina dudulo ido ina huro mata ido cikin izgilanci,sannan na dad'a shafo saman mararsa kamar ban saniba d'innan


A take ya fara rawar murya ,kundai San tsoho a hannun qwaila




"Ahh...ammm...eh tooo, hajiya baki kyautaba,yakamata ki daina kula khalisa ,matsayin 'ya fa take a wajenki fa"




"Aah Ahmad bansan hakafa,in ita ta maida kai hamago Toni bamzama shashasha ba....(daga nan ta waiga ta kalleni tayi qwafa ) tabbas lokaci yayi da zanbi shawarar da kika bani yanzu ,don na lura yanzu kinason zama er hannu ko?"




Lafe kaina nayi akan bayansa ,ina Jan ajiyar zuciyaa kamar ina cikin tsananin tsoro a wajensa ,amma ita saina lumshe ido na Watso mata su,ina nuna mata bayansa Dana kwanta akai




"Shegiya 'yar iska saina yi maganin karuwancinki mu zuba"


Ta juya zata fita....


"Ashsha ashsha ,ya da cin zarafi kuma ,to gaskiya bazan dauki hakanba, ki kiyayeni fa,ni ba mugun miji bane,in ita bazata iya ramawa ba ,zan iya yin hukunci da kai na"




Tsaki tayi kurum ta haura dakinta dondai batada lokacinsu,don tasan zasu iya zaraar da ita,musamman yanda taga idonsa yina shanyewa ,ai ita tasan alamomin tashuwar sha'awar mijinta....
[8/19, 13:35] Bamalli: *JNS 3*
76-80
Ina ganin ta juya na fara kiciniyar janye jikina, saidai tsam ya riqeni


A kunne ya rad'amun "Yau wa na kama? Kin gama gudun nawa ,wato yau kinga giwar gidan zata zauneki shine kika rugo waje ko?"


Noke kunnena nayi akan kagad'ana yanda naji muryarsa na dukan dodon kunnena yasani jin wani Yarr yamm,readers karkuga laifina ,ni ba ma'asumiya bace I've feelings




Tuno baki nayi "Wallahi nidai ban gudunka ,kawai kewar gida nikeyi da kuma karatuna"




Riqe duk kafad'una yayi sannan ya d'an sakko daidai tsawona ya manna mun kiss a saman le66an da Nike cunowa


Kautar da kaina nayi da sauri ina goge bakina da bayan hannu


"Abbah bari inje sallah"


"Hahhh lokacin sallah baiyiba ,so kije ki huta ,sannan ki jiraceni anjima ,ke ke dani"


Zambad'awa nayi da gudu bayan ya cikani.


Sai da na shige d'akina sannan na qanqame jiki na qwalla qaran murna ,harda er tsalle


Ina tuno yanda Nike hango idanuwar ummah ta cikin glass tana leqenmu
Wohoho Allah ya isana tsakanina da kunyar da ke damu na da wallahi yau sai na kusa haukata umma,na tabbatar na zawwatar da mijinta ganin idonta kamar yanda nayi mata alkawari




Gabana ne yace dam! _"ki shirya yau ke kike dani"_


Me yike nufi?
Wai ni zan kwana a sashen shi yau?


**
kirane ya shigo wayata Wanda tabbas bansan ko wanene ba saboda baquwar numberne ,amma haka nan naji bazan iya d'aukaba saboda yanda gabana ke bugawa


Saida aka kira kusan sau uku kafin text ya shigo
Cikin sanyin jiki na d'aga


*Na gamsu wa kaina duk yanda zan 6illo don ganin mun samu magana dake bazaki bani goyon bayaba,Aminiyatah don Allah kar kiyi ignoring message dina ,inason in fahimtar dakene cewa ina mugun jin farinciki na kasancewarki cikin family dina ,sannan ina roqonki ki tsaya ki bawa abbahna kula ta musamman fiye da Wanda zakiba saurayinki da kike mugun qauna,domin a halin yanzu abbahna yafi buqatar wannan taimakon...kamar yanda akayi auranki bisa tirsasawa haka nima ,saidai ni ban shiga gidana da makaman yaqinaba ,don haka ina Shiga na fara fafitikar Neman gurbi a zuciyar mijina ,kuma alhmdllh na ga canji tun yanzu ,a halin yanzu ina farinciki da godema Allah da ya bani dadynki a matsayin mijina ,banbi qyalqyal banxaba,Mijina yasan yanda za'a sarrafa mace har tasoshi ,kuma dukda anyi mana auren hadine ,yina bani kula da nake jinjina masa ,finally ina muki albishir da momynki ta zama ta gari kuma ta tungumeni tamkar ke a wajenta,so plz ki maida gidanmu tamkar gidana inkin hakan zaki sanya abbahna farin cikin da baisamu ba a baya ...ngd qawata*


Hawayene ya shiga mun karakaina a kuncina ,bansan ina mugun qaunar dady na ba ,sai yau da naji kishin saudah ya kama ni,lallai dadyna jarumine wajen iya soyayya ni kaina sheda ce,maiyasa ban za6i dady ba ,nayiwa kaina za6en abbah matsayin miji?


Kuka sosai nikeyi na dumbin nadama da tunanin mafita.


Ban jima a kwanceba saiga abbah ya shigo dakin


Yina ganina kwance ya hauro da sauri donjin abunda ke damu na


Kamoni yayi ya d'aura akan cinyarsa yina shafa bayana


"Baby lafiya meke damunki? Nine fad'amun plz" girgiza masa kai kurum nayi na cigaba da kukana
Hankalinsa ne ya dad'a tashi
"Baby plz ki fadamun damuwarki,ko in kira maki gidane?"
Girgiza masa kai nayi for d second time


"Shikenan to tashi ki wanke fuskarki muje falon antynki zamuyi magana ,share hawayenki


Langwa6ewa nayi ,banda niyyar tashi
A hankali ya dafe kansa yina furzo huci ta bakinsa ,damuwa qarara ta bayyana a fuskarsa ,shi ya rasa yanda zai sa ransa ,ga khalisa da damuwarta ga ita wancan yanzu suka gama kwasan dambarwa




Magana ya somayi min saidai yana farawa muryarsa ta sarke ,ta fara rawa kamar mai San Kuka


" shikenan tunda abunda Kuka za6ar mun kenan nagode ,ita tayimun kema kiyi mun,nagode ,zan koma office in ringa kwana bazaku sake ganina ba.."
Yina kaiwa aya ya sauke kaina akan pillow sannan ya fara yunkurin sauka




Da sauri na kamosa na rungume ta baya ,inajin tsananin tausayinsa a raina


Dole yina cikin jarabawa ,ga matarsa ba imani allah ya ganar da ita


"So halittace khalisah ,allah ke jarraban bawa da ita,don haka bani na sawa kaina sonki ba ,inda nine ke sawa da na cireta tun kan ta zama babba,ya kikeso inyi ,na kwantar da kaina dukda matsayina ,amma kinqi ki kar6eni a matsayin mai sonki tsakani da allah ,plz ki bani dama mana,,kai bani sharad'inki ta hanyar jarrabani innaci jarabawar sai kya iya gamsuwa ki soni koda kwatan son da Nike makine"
Tuni muryarsa ta fara rawa ,Wanda zai nuna maka Kuka yikeson yi




Qanqamesa na dad'a yi
"Abbah ,wallahi allah tun tuni ina maka so ,amma ba so na aure ba,da zaka taimakeni da ka sada zuciyata da Wanda takeso don wallh ni yanzu dady Nike mahaukacin so..."


6an6aroni yayi a jikinsa da qarfi ya fara mun wani irin kallo


"Me kike nufi khalisah"


"Abbah da gaske ni PA dinka nikeso mijin Saudah..."


Tas!!!
Ya daukeni da wani irin gigitaccen mari ,a take na kife akan gadon na saki wani irin gunjin Kuka


"Wawa ba mahaukaci bane khalisa,don't think don nace ki bani dama yasa ki sakomun maganganun yarinta da shirme,abokina! Mijin qawarki! Babanki a da kicemun shi kikeso?....mtseww" kawai sai ya juya zai fita cikin qunar rai




Da gudu na dirko a gadon nazo ma kama qafarsa katamau ina dad'a gunjin Kuka


"Abbah ka taimakeni wallahi ina kewar soyayyar dadynah ,ka sakeni ka roqeshi ya aureni ,shine zaka biyani da soyayyar da kake iqirarin kana mun..."
[8/19, 13:35] Bamalli: *JNS 3*
81-85
Kallon tsoro ya fara bina dashi,anya khalisah batayi gamo ba kuwa?
"Khalisah bari in wuce"
"Abbah kai ma ka daina sona kenan? Ka yarda in mutu da rad'ad'in soyayyar dady da ka sakeni ya aureni? Ka tuna zafi da rad'ad'in soyayyar da kake ciki nawa na tsawon shekaru ,nima fa kwatankwacin hakan Nike ciki".


" qarya kikeyi khalisa! Akwai wani Abu na 6oye da ya tunzuroki ga maganar PA to amma fa ki sani ,makircin Yusuf a kanki kad'ai zai tasiri banda ni"


"Abbahhh..."
Fincike qafarsa yayi ya fice ya barni anan kife ina rizgar Kuka mai ban tausayi


**
Tundaga nan jin dad'in gidan yayimun qaranci,abbah ya daina shiga harkata,dama momy ta zama first lady bata da lokacin kanta bare kuma ni da ta maida get yafini daraja,a halin yanzu so nikeyi ma abbah ya saurareni ko makaranta in samu ya sakani kona rage rad'ad'in zaman kad'aici,amma banma sanin dawowarsa ko fitarsa,sashen sa da zai had'u da nawa yayi blocking ,wannan ya tabbatar mun da ya yanke duk wata halaqa na zahiri dani,to ya zanyi ne?...
Duk nabi na fige na lalace,amma fa duk wannan halin da Nike ciki zurfin cikina ya hana in fad'ama kowa halin da Nike ciki ,ciki kuwa harda iyayena ,saboda nasan in na fad'amasu ni zan kwana ciki don nice maras gaskiya d'in




A halin yanzu sunan shine shugaban qasan amma yayi luf ,ummah ke komai ,kamar itace ke mulkin,ko yanzuma abunda ya faru kenan a cikin akwatin tvn ummah na hango ta shigo wani filin taro na mata da aka bata goron gayyata takuma samu halarta ,tundaga shigowa cikin gurin taron ake daukanta da mabiyanta,har aka yanke wani qyalle da ya zama barrier tsakanin ta da mutanenta ta fara gaggaisawa da mutane tana raba wa maras galihu kyaututtukan buhunhunan abinci ,kekunan d'inki ,injin markad'e da sauransu




Yabo da godiya kam ta shashi a wajen wa'innan matan ,daganan ita da tawagarta suka fara haramar barin wajen taron


Gidan TV da dama sun samu damar magana da excellency Wanda duk rabi godiya ne gami da yabawa,sai tambayar manufofin gwamnatin nasu.cikin qwarewa take basu amsa batareda gajiyawa ba


sai zuwa can wata mace cikin facemask ta kutso gabanta
"Ranku ya dad'e ,baya Goya marayu allah ya sakamuku da Alkhairi ,nikam tambaya Nike dashi....A lokacin da aka rantsar da me girma shugaban qasa ,an tabbatar da auransa da gimbiyar masarautar Azdajarz ,saidai kawo yau bamu ta6a gani kojin speech d'in taba saidai ke ,wannan ya nuna kece Wanda me girma shugaban qasa ya za6a a matsayin first lady dinsa kenan ko yaya abun yikene?" Cewar wata speaker da ke riqe da mike mai d'aure da gidan tvn DZ TV ,Wanda ya nuna daga gidan tvn ta futo




A take matan wajen suka nema daqilar da wannan er jaridan ,ciki kuwa harda shugaban mata,da sanata baraka,saidai a nutse ummah tayi gyaran murya




"A koda yaushe uwargida itace jagoran cikin gida,tsakanina da gimbiya khalisa kyakyawar fahimtace don khalisah d'iyace a gareni na raineta tun tana qaramarta a hannuna, don haka lokacin fitowar diyata baiyiba in lokacin hakan yayi zaku ganta...."


"To excellency ga qarin tambayar qarshe ..." Hannunta tayi saurin d'aga mata alamar dakatarwa ,sannan ta d'aga farin handkachief dinta ta saqa qarqashin farin tabarau din fuskarta tana goge d'an zufan da ke gangaro mata kadan kadan


"I've to attend others OK?" Ta fad'a tana daga mata gira
Jan baya tayi tana jujjuya mike dinta ,kafin tayi hamzarin fita filin ,sannan ta danna Bluetooth din kunnenta


"Ba wani haske ma!"
"Karki damu i've got d main point ,ki koma kan aikinki" a ka fad'a daga d'ayan sashen sannan ,itama er jaridan ta wuce ta koma cikin taron en jaridan


**
Nikam luf nayi akan gadona kafin na dauki remote na kashe tvn


Kenan tayi benching d'inane inna gaji da masu gadi in fita ko yaya? Duniya ma batasan nidin waceceba a wajen excellency?
To amma sai me ? Hakanma shine daidai kinga da MUN rabu,jejeh zan auri Ngwandu masoyin asalina,batareda duniya tai masa kallon cin amana ba....


Knocking akayi sau uku kafin aka turo qofar aka shigo,qyar na kashe shi da ido sanye yike cikin suit kalar blue black ,da farar Riga ta ciki Wanda tayi azabar kar6ansa ,quruciyarsa ta fito ,Wanda in zan basa shekaru saidai in basa 35years


Qyar nayi masa da ido ban auneba saida naga yayi tsaki ya kauda kai ,hakan yayi saurin dawo dani hayyacina ,da sauri na kife kaina cikin pillow dinda na kwanta tun asali akai


Gyaran murya yayi "kizo su mai martaba sunyi more than an hour baki fitoba nakira numberki baki picking ba ,so na basu uzurin wanka kikeyi,yayi miki daidai ki qaryatani ko ki gaskatani don ki tsira" zumbur na mike cikin murna na nufeshi zan rungume sa ,tamkar shine su d'in a gabana




Da sauri ya janye jikinsa ya bude qofar ya fice.
Turus nayi ,kafin da azama na canja kayan jiki na ,nasaka wata doguwar gown me high neck da nasan zai 6oye qasusuwan wuyan da nayi .
Powder da er man baki na shafa na fito ina sanye da da wani slippers qirar Dubai mai taushin gaske




Tunda nafara sakkowa idona suka carke da na nanneh,ga anty hannatu,ya Khalid ga mai martaba




Tattare qasar doguwar rigana nayi na gangaro da gudu ,cikin zaquwar in cinmasu ,saidai ina hawa kan karfet d'in ,kurum saina ci burki na rasa Wanda zan fad'a jikinsa,kurum saina durqushe a gaban mai martaba na saki marayar Kuka ,da ni kaina bansan ko na menene ba.




Murmushi mai martaba yayi a nutse ya furta bismillah ,sannan ya d'agoni,ya d'aurani akan cinyarsa


"Murnan ne haka?"
Gyad'a masa kai nayi kafin in saka kaina a qirjinsa ,ina kallon kowa na d'akin da duk fuskarsu ya ke dauke da fara'a ,na fara gaishesu a gabad'aya




"Ai mu har munyi fushi zamu tafi,tunda an samu dakin kai an lafe,,bakida laifi kinsan dakin kai me dad'i saidai kinfa d'an fad'a ko idonane my hannah" cewar Dr ya qare zancensa yina kallon anty Hannah




"Gaskiya ba wani nan ,ni banganiba Sai ma fresh da naga kinyi er qanwata"




"Hummm anty gaskiyar yayane na rame"
Dam gaban excellency ya fad'i sannan zufa a take ya fara tsatsafo masa,shikenan zata shaidawa mai martaba ya wofintar da ita




"...Nafayi zazza6i amma now I am recovered"
"Hahhahha kice sabon gida ,sabon gwamnati tafeda new baby,wow congratulations excellency " ya fad'a yina tafa hannu cikeda barkwanci




Sai sannan Ahmad ya saki ajiyar zuciya,sannan ya fara Sosa qeya yina murmushi


Itadai gimbiya diyanah kallon diyarta kurum take yi duk idonta sun shige cikin kwarmi ,ita dama tasan za'a Rina,to ita ya zatayi ga zurfin cikin da ke d'awainiya da ita,bamaijin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login