Showing 1 words to 3000 words out of 25648 words

Chapter 1 - JININ SARAUTA Book 3 End By oum Aphnan.txt

[8/19, 13:32] Bamalli: *🕊️JININ SARAUTA💍*
_Buk 3_




✍️Oum Aphnan
Page 1-5





*Alheri Writers Asso.*






_Bismillahir rahmanir Rahim_








Zaune take a kan stool din dressing mirror tana qara gyara zaman d'aurin dankwalin kanta na wani nannauyan tsadadden leshi da kudinsa sun haura 250k ,tana cikin maqala dan kunnen fashion dinta na silver ,kalar kwalliyar les din saiga kuyanga zubaina ta turo qofa,bakinta na rawa ta soma koro ma gimbiya khalisah zance bayan ta gurfana a qasa cikin tsananin firgici.


"Ranki shi dad'e, yanzun nan mahaifiyar Deen ta bar gidan nan,ta sami mai martaba ,tanata kuka wai a raba d'anta dake, wai yaronta ba ruwansa amma saboda azaban son da yike gwada maki ,ya kaisa da soma yi mata sata ,kama daga gwalagwalanta,manyan gidajenta da sauransu yina saidawa don kawai yayi maki hidima ko zaki soshi..."




Kallon kanta tayi a madubi,ta d'an jujjuya jikinta,kafin ta dauki gira brush,ta Dad'a gyara cikakken giranta,tana wani murmusawa har haqorin gwal dinta na fitowa yina dad'a qara mata wani sihirtaccen kyau da aji .




Saida ta tabbatar kuyangar ta amayar da duk kalamanta kafin ta mike a qasaitance ,ta dauki turare tana yiwa kanta wanka dashi




A hankali ta tako gabanta cikin takalminta half cover silver colour,sauke idonta kuyangar tayi akan takalmin har yanxu jikinta na rawa don tana tausayawa gimbuya khalisat saboda tsananin son da take gwadawa Deen




"Oh kenan mamarsa ta gwada kishinta a kaina ko? Har take claiming ni na 6ata mata yaro....karki damu *Wanda ya fishi ne zaizo*"


Dago ido da sauri tayi don ta ga sirrin fuskarta don duk zatonta kuka zata fashe da shi,amma a sa6anin hakan,sai kurum taga ta taqarqare tana selfie fuskarta fal nishadi.


Tsam ta miqe ta fita cikin tsananin mamaki,anya gimbiya khalisah batada Aljanu kuwa? Wannan fa na uku kenan.


**
Daga Fada airport suka wuce don d'auko Dr Khalid da Matarsa Habiba da suke shirin sauka a wannan lokacin.


Sun isa jirginsu bata samu qarasowa ba,a don hakan ta umurci driver daya budeta tanaso zata dan miqe qafa kad'an


A nutse take tafiya barorinta biyu suna take mata baya cikin atamfarsu da mayafi iri d'aya, wani snacks and ice cream joint ta gani mai kyau well decorated


A nishadance ta qarasa wajen kafin ta sami waje ta kame,qarqashin wani laima mai kyau da kujeru biyu da tebur a tsakiya ,sukuma barorin sukayi tsaye a kanta ta baya.


Er qaramar Jakarta ta ajiye akan tebur din ta zaro chocolate dinta daga jakar ta soma gutsura a hankali tana motsa dan ficilin bakinta dake walainiyar lip balm,tana taunawa,hannunta riqe da rafkeken wayarta tana game tana d'an murmushi.. Can kamar an tsikareta ta kalli daya daga cikin kuyangin nata




"Ke jekice a kawo mana roba uku, musha in da dad'i inyi guzurin na gida"
Rankwafawa tayi kamar me shirin yin ruku'u sannan ta wuce ciki.




Itakuma gimbiya khalisah ta cigaba da shafa wayarta fuskarta da d'an murmushi


*Attahir* dake zaune tun shigowarsu ya Lula duniyarta,komai nata na fuzgarsa ne ya mike da nufin qarasowa inda take.


Guards dinsa da suka kasance cikin Ash din kwat ne suka dafe masa baya da nufin su biyosa.


Da sauri ya dakatar dasu ,sannan ya makala tabarau din fuskarsa ya gyara zaman suit dinsa ya qaraso a hankali inda suke


"Barka da hutawa manyan mata" kallon uku saura kwata tayi masa kafin ta maida hankalinta kan wayarta


"Barka"
Tace a gimtse


Murmusawa yayi ,sai yaji tama Dad'a burgesa


"Allah yasa bazanyi laifi ba inna maye gurbin wajen nan da babu kowa a kai"


Wannan karon saida ta yamutse fuska kafin tayi masa nuni da wayarta ,alamar zai iya zama




A qasaitance ya ja kujeran ya zauna "Nagode mai kyau".
Walai tayi masa da ido ,sannan ta Dan karkace le6enta na sama


" really?🤨"


"Karki cemun ba'a ta6a Fada maki cewa kedin kyakyawa bace ba"
Murmushi tayi tareda dafe kai ,a duniya tanaso ace mata kyakyawa kai a madai zuzutata ko a yabeta




"Ko naji,ai dai dole in yaba Wanda yafito daga bakin Wanda ban wayesa ba"


"Nagode da kika tinasar dani kuskurena ,am sorry ,da fari sunana Attahir Ishaq jingim ,ni mazaunin plateau ne,sannan ni dan kasuwane dawowata kenan daga qasar China ,inajiran jirgin da zai wuce dani gida plateau...sai kuma kwatsam daga sama Allah ya kawo min kyautar kyakyawa"




Muskutawa tayi a hankali ,ta lankwashe bakin ledar chocolate din hannunta ta rufe tareda mikawa kuyangar dake kanta"Ina buqatar ruwa"




Rankwafawa tayi kafin ta tafi amso mata ruwa,ba qishi takejiba tayi hakan ne don su ke6e da Attahir


"Barka da zuwa sir,Attahir "
"Kefa ya sunan gimbiyar tawa?"
"Correct👌sunana gimbiya khalisah magajiyar masarautar wannan yankin"
"Fatan zamu zama abokai "
"U welcome"


Sukayi musayen contacts ,aka kawo masu ice creams dasu Snacks, debit card dinta ta mika mata da nufin a cire kudin




"Ance wancan mutumin ya biya mana ko me zamu siya "
Ca6e baki tayi
"En asara a haka nemanku ke qare anga kyakyawa" ta mike suka bar wajen


Suna qarasawa jirginsu Dr.na sauka, yina sakkowa sa6e da little diyanah da ita ya fara tozali.


Aikuwa nan fara'arsa ta ninku,ya ringa keto mutane bai kallon masu masa Barka da zuwa saida ya nufo gabanta




Dage kanta sama tayi tana kallonsa qerere akanta ya zama wani rusheshe ga tsawo ga qiba...xaman Spain ya chanja sa entirely


Cuno baki tayi cikin sigar shagwa6a ta mika hannu don ta kar6a lukutan babyn hannunsa




Qyar ya kafeta da ido yina kalon yanda ta cika ta batse,Ashe duk kallon da yike mata a photo raihune ,ji yanda ta zama Wata babbar mace




"Zamu fara fad'an ne daga zuwata ko d'an oyoyon nan bazan samu ba?"


Noke kafada tayi kamar Wata small baby


"Uhm uhm,bayan....bayan da zanzo in rungumeka ne in Fada maka how much nayi missing dinka sai naga ka zama wurtumemen wulli gaskiya kaimun girma ,ni bani little dinmu" leqa ta bayansa tayi ta kalli Anty Habiba




"...Anty me kike ba wannan bujumin ,baya damunki da nauyi"


Dariya ta fashe da shi ,ta zo ta rungume ta "Mai zaisa ya dameni er kwanwata ji shifa cas dashi kalan yayi"




Huro hanci tayi
"Ahhh🤭da wannan tumbin,gaskiya matan aure kuna fama ,nifa shiyasa banson auren mai kiba"


Lakuce mata hanci yayi ,yaji xancenta zai sauka akan layi a waje,lallai girma ba hankali




"Hmmm to sannu sai ki nuna mana bolanmu"


Dariya tayi ta kar6e little sannan suka rankaya wajen motocinsu fadawa na masu barka da qarasowa.




**
Attahir kam ya gigice a soyayyar khalisaht don haka fasa tafiya yayi ,ya shiga cikin gari ya kama hotels gwara ya nemeta da zafi zafi,tun kafin ya tsaya sanya ayi wuf da ita🥴🤏


_*Jinin sarauta* bana kyauta bane,ki biya kudinki kalilan ki kwashi labarinki,just #200 via this account 7782217014,Mohammed Hassana ,Fcmb ko ta wannan layin Mtn 09065990265 don Allah a bar fitar da shi,kema sis ko an fitar ki rintse idonki karki karanta ki biyo ki siya na halal,nagode makarata da masoyana Wanda suka biya suka karanta damasu na er sibare ,nasan duk cikin kaunace still nima inasonku_




A sassan Dr.Khalil yau zir gimbiya khalisah ta yini,suna tareda Matar Khalil tana koya mata salo salo na kula da miji,tare sukayi girkin dare,bayan sun hadu a sashen nannah sunci abincin tarban baqi duka,shine ta roki abarta zat iya na dare in sun huta, itace ta tayata shirya baby,sukuma kuyangi suka gyara abubuwan da aka 6ata...kira kam a waya Attahir baya had'a awa d'aya ,tun tana daukar abun wasa har ta fara gajiya tahau qorafi ,Habiba kam sai dariya take mata.


A ranar kuwa bayan magriba tana zaune tana add'ua gefenta wayarta ne,so take in tayi isha'i barorinta suzo ,su rakata cikin gida...wayarta ne ya fara 6urari,tsaki taja ,ta danna abun gefe saman power bottom nan ya daina ringing ta cigaba da abunda takeyi




Yina yankewa ta kuma shigowa
A fadace ta d'auka "Haba wannan wani irin bala'ine Ibadan ma baza'a barka kayi ba ,wannan wani irin mutum ne ? Anya yamayi nasa sallahn kuwa?"


Dariya Dr. Khalil yayi ,ya kasheta da ido, sosai yikejin dadin yanda take qorafi akan samarinta ,symbolize basa kanta




"To kidauka mana kin San kowa da kalar soyayyansa".
" Allah ya ,ya isheni ne"
A lokacin kira na uku ta shigo


"Hello Assalamu alaikum ya akayi kuma?"


"Sorry gimbiyata Allah yasa ba barci gimbiyata ta soma ba"


Waro ido tayi kamar yina kallonta,a ranta tana ayyana anya wannan yasan addininsa kuwa


Amma saita kanne "Barci kuma ? A yanzu bayan magriba".


" oh yes yes,to gadai baqon naki a daga wajen Fada yina bukatar ayi masa iso zuwa ciki ,Allah yasa gimbiyar tanada lokacina"




Kautar da wayar tayi a kunnenta ta ja siririn tsaki ,tareda babbanka ma wayar Harara


"Hmmm y not,barkanku da zuwa ,bara insa a shigo dakai" ta katse wayar tana kallon Dr.Khalid


"Ya nayi baqo ,bari in wuce gida"


Cikin tsananin kishi "No! Yazo nan,Sitting room dina,sannan in kun gama inason ganinsa"


**
_My sister ba lallai ki iya gane inda labarin ta sa gababa,zaifi miki dauki ki biyo wannan Layin 09965990265 don jin samin farhinsa da samun na daya zuwa na biyun a sassauqan farashi_


A Wata hatsabibiyar mota ya cunno kanta cikin doguwar hanyar da zai sadaka da sashen Dr.kafatanin fadawan da masu tsaron qofar sun gigita da ganin motar,amma duk zatonsu wajen Dr yazo,ma'ana baqon sane




Sosai akayi masa tarba mai kyau,saidai hira sama sama sukayi aka kira isha'i


"Yayanah yinason kuga juna,so,in kaje sallah zan Fada masa sai Ku hade kaga va sai na sake fitowa ba"


"Kina nufin kin gaji da ganina, duk zumudinki da na yi"...


" sallah a jam'i bata wajabta a kaina ba,amma kai ta hauka ,kenn zan iya samun rabon zunubi kuma ban kyautawa soyayyah ba in na bari ka rasa jam'i"


"Shiknn in na gama zan dawo".
" a'ah fa ,ni ina sallah lokacin barcina ya shiga,ammm muyi waya gobe inshaallh ...bye"


Dole yaja sahu ya fita yina taune le6e zaki shigo hannune yarinya.


**
Lahaula fi shaatul lah ,jakar brief case ya aiko Wata kuyanga dashi ta kawo mata,tana zaune tana yarfe qananu kalban kanta ,tana shaidawa Anty Habiba yanda sukayi ,kurum saiga yarinya da jakar wai yace a kawo mata


Tsaki taja "this is nonsense, waya Fada masa ana siyan soyayya da irin wannan abun,to meye a cikin jakar ya Fada maki?" Girgiza kai tayi


"To maida masa kice Angode"
Dakatar da ita Habiba tayi da hannu ,kafin tace "Ke jeki abinki" ta kar6a ta bud'e


Ja da bata Habiba tayi a tsarace tareda dafe kirji
kudi ne tsaban daloli sababbi katakal shishirye a bandur bandir dinsu ,ciki FAM




Da sauri taje gaban dinning ta suri wayarta ta kira Dr
"Hello Qalby akwai matsala fa..." Katseta yayi "Nima anan akwai matsalar ,da na gani Wanda yafi ko me zaki fad'amun so ki jirani ina zuwa,ki kuma dakatar mun da Khalisah"


"Tom Allah yasa muji alkairi"


**
"Khalisah kinason wannan baqon da yazo wajenki?"
"Yah me yasa ka tambayeni?".
" Gargadine da hangen nesa,kawai ki Fada min in kinajin 6ir6ishin wani abu a ranki game dashi"


"Eh inaji"


"Ai da gaske? Har kenan kinsan so?"
Tashi tayi taga kumbure kumbure


"Yah tambaya ta fa kayi" daure fuska yayi
"Khalisah inaso yanzunnan ki blocking number wannan a wayarki ,kuma ki tsamesa a ciki ranki"..


Zaburowa Habiba tayi " Ko e yasa?".


"Habiba mutumin nan ba na gari bane kurum tabi umurnina"


Wasu siraran hawayene suka zubo mata da batasan ko na menene ba,saidai tasan na takaicine,duk saurayin da zatayi sai ace bashida hali




"Shikenan yah na fitar dashi shima a raina ,na kumasan *Wanda ya fishi ma zaizo*" daganan ta zura takalminta zata fita




"Khalisah" cikin murtukakken fuska ta kallesa
"Karkice na rabaki da masoyini,ki sani nine masoyinki na gaskiya ,kuma bazanso ganin abunda zai cutar dakeba....zauna infada maki hujjata da na ke son rabaku da wannan mutumin....da fari sunansa *Adamu salansa* d'an asalin garin qauyen Anchau,ya kasance mai zuwa gida gidan jama'a yina sallama da mazan mutane ,da zaran sun futa wajensa to matansu baza su sake ganin sa ba har Abadan ,kenan *D'an mafiya ne* Na samu rahoton nan ne bayan an kamasa yayi nasaran yankewa wani magidanci mazakutansa,a garin Abj. akayi referring case din asibitina a lokacin mutumin bai mutuba saida ga baya ..... Naso bin case dinsa bansami sarari ba,kinga gashi ynx an sakesa ya dawo cikin Al'uma ransa a kwance yina Neman aure...."




"Allah ya kyauta toh muma kaga sununan kudin da ya kawo mana"




"Hhh to qila nima ya siya nawa abarne🍌😉" ya radawa Habiba a hankali yina kashe mata ido


"Ba na ganiba ,barmuna fatan tsiya"Cesar Habiba




"Hmmm to kadai sallamesa ko?" Tambayr khalisah ya dawo d hankalinsu kanta




"Aah inajiran inji amincewarki".
" amincewata?
To in amincewata ne ban yarda ba ,tunda ba abun nawa mijin za a cire ba🤭"




A guje yayo kanta ta fice tana masa gwalo
"Hahaha kin ci bashi"




















Oum Aphnan✍️
A tayani share Albarkacin so da qauna don Allah🥰
[8/19, 13:32] Bamalli: *JNS*
✍️6-10






Duk abun da ya faru bai dameta ba saida taje kwanciya barci,damuwa ya fara bijiro mata,na yanda duk saurayin da zatayi da nasa kalar damuwar,amma Wanda zai biyo bayansa sai yafi wancan girman matsala,bata manta shu'aib da yazo da qudurin aurenta ya 6arar da nairori a fadan,saida yaja kafatanin ra'ayoyin Al'umman gidan harta mai martaba, saboda simplicity dinsa ga kuma uwa uba kyautansa,shine Wanda in yayiwa bafade kyauta saidai kaga bafade na kuka ya rasa bakin kuzuzutawa ,akansa ne sarki ya fara bada makullin gidan shaqawarsa don gimbiya khalisah suje zance yanda zasufi samun sakin jiki,amma kamar Wanda ya shammaci jama'a ba Wanda ya iya sanin usulinsa ko ya damu da yasani,har sai bikin Anty lubnah kanwar Anty zahra ,lokacin ne zasuje dinner yazo ,anan take shaida mashi ita motar gida zatabi amma ya kafe, sannan suna tare da Saudah itace ta roketa da ta barsa yazo ya kaisu ,inyaso sai ta rakata su tafi tare
A lokacin ne yayi masu kyautar da ya gigitasu ,daloline sababbi katakal masu uban yawa cikin wani abu me kama da drawer a cikin motarsa,haka ya bude ya diba ya baiwa Saudah tayi liki ,yadada diba ya baiwa khalisah, sosai Saudah ta furgita dashi ,kuma a take ta saka masa kwalelen alamar tambaya ,saidai tayi shiru har saida biki ya watse kafin ta tunkari abbanta (VP) da maganar kalar kyautan da saurayin bestynta yayi masu ,kumawai shi haka yike kyautarsa .sosai shima ya tsorata da kudaden da yaga ya basu,ko da suke yaran manya bai kamata ana basu sunanan kudi irin wannan ba,saidai ya 6oye damuwarsa a ransa har sai yayi bincike ,hotonsa ya nemi ta Tura masa aiko ta sa ta turo mata ta WhatsApp ta turo masa ,a take ya fara ciccila hotunan a wajajen binciken masu laifi
Kwal din farko aka bayyana masu sunansa tukur na gaskiya dan asalin garin kogi state ne,yayi aure aure da dama saidai da ya auri mace bata sati uku a gidansa take mutuwa anan zargi ya tashi kodai shidin dan mafiya ne? Asirinsa bai Tonu ba saida ya auri Wata yarinya er talakawa mai tsananin riko da addini ,kullum azumi da nafila ,tunda ya kusanceta sau daya ranar biki ,ya tafi da ita a jirgi zuwa portakwat da nufin zai aiko da wani jirgin zaa kwashi En uwanta suga matsugunin diyarsu saidai unfortunately to them ,walqiyansu ko labarinsu basu kuma jiba
In ankira wayarta baya tafiya,a hakan ne ya dimbirawa yarinya ciki saidai ya kasa aiwatar da nufinsa na baiwa dodonsa jininta saboda addu'arta saidai yayi nasaran goga mata qanjamau Wanda ya roro garin barikinsa,har Allah ya bata ikon tserewa a gidan shine ta fito wajen En sandan garin tana bada labarinsa amma baa sake jin duriyars ba ,sai a wannan karon da ya 6iullo a gidan sarautar yina nemanta da aure
Hankalin vp kuwa ya tashi haka ya taso ya labartawa mai martaba abunda ke faruwa ,don haka aka rabasu,don an gano auran kyawawan mata yikeyi yina baiwa gunkinsa shikuma yina basa dukiya .


Murginawa gimbiya khalisah ta dad'a yi a gadon tana sharar qwallah a daidai nan messages suka fara karakainan shigowa wayarta ,kamar bazata daukaba saidai na qarshen da bataga sunaba shi yaja ra'ayinta. A nutse ta bude ta fara karantawa
_“If I get the opportunity to describe you in a word, it would be life, Yes that is true you are my life!_
Coz
_You are my light in darkness,_
_You are the smile in sorrow_,
_I would pleasantly give away_ _everything to be with you tomorrow,_
_I love you! ,have a wonderful Night_
Ur secret crush💔”


Ta maimaita yafi sau uku ta kasa fahimtar komai ,to waye wannan kuma? Ni yanzu nama fara tsanar duk Wata mu'amala da mutane musammam maza,kife wayar tayi ta janyo pillow ta rungume tana kallon sama ,so takeyi ma tayi tunani amma ta kasa ,kiririm wani saqon ya dad'a shigowa


_“Nasan dole zan saki d'imuwa da tunanin koni wanene?...karki damu zan fayyace maki anan kurkusa, saidai kullum ni mai sa'a ne banso akanki in zama kishiyar hakan,na tura maki saqo ta WhatsApp in kin bude datanki zaki gani”_


Tsaki taja zuwa yanzu ta fara jin haushin al'amarin kawai ja bargo tayi ta runtse ido da qarfi saita kora barci yazo ya sureta.
Asubahin farko ta mike cikin muguwar kasala a hakan tayi sallah tana zaune tana lazumi kiran PA ya shigo ,murmushi tayi har yau har kullum tana girma ma babanta "Hello dadynah....ina kwana" "dady yayi fishi da daughter dinsa Sam twinkle dina ta manta dani" "Anya dadynah kana nan cikin raina afuwan ya momyta" "momynki gata a gefena amshi itace tace inkira zakuyi magana"
Sallamartane ya fara mata amsa kuwwa a kunne ,da sauri ta rumtse ido, bazata ta6a manta sanda ta wattakata ba taja mata silar karyewan hannuba.
"Hello daughtern dadynta kina jina?"
"Inajinki momy ina kwana "
A takaice ta amsa kafin ta daura da bata bayanin dalilin kiranta
"Su'adah ta ,magana zamuyi dake ta fahimta ,wallahi wannan maganar da zan maki ,na ratse wlh PA baisan wannan maganar ba...don haka inaso ki natsu muyi magana dake ta kyakyawar fahimta fatan kin fahimce ni"
"Eh ina jinki momy"
"Suada ki ceceni ki ceci dadynki ,ban ta6a kuka akan wani lamari ba yau gani sanye da guiwoyina a qasa ina roqonki ,kinsan munyi rashinki a gidan nan ,kece sayin idanuwarmu sannan har ynx bamu samu wacce ta maye gurbinki ba a zukatanmu musamman mijina dake tsananin kaunarki,saidai iyayenki na asali bazasu bamu keba ,kinga hakan yina nuna kin mana nisa kenan sai gani daga nesa ,a don haka na yanke shawaran rokonki a maimakon mijina ,don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login