Showing 114001 words to 114936 words out of 114936 words

Chapter 39 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt

13 Dec 2024

5026

haka akowane ƙarshen sati biyu akwai jihar da take zuwa bisitin matsayinta na gawurtacciyar likita da ake ji da ita a Nigeria ma baki ɗaya ba Abuja kawai ba. Ga mijinta daya kasance shahararren ɗan kasuwa lamba ɗaya musamman a fanin shinkafa. Dan zuwa yanzu bama a Africa kawai ba, a duniya kamfanin Alhaji Abaan yana cikin wanda ake matuƙar ji da alfahari dasu a harkar shinkafa. Kuɗi dai kam Alhmdllh akwaisu. Ga ɗaukaka ga suna ga taimako duk ALLAH ya basu. Dan Khadijah ta kafa wata ƙungiyar wayar da kan mata musamman ƙananun yara da iyaye akan harkar soyayyar ƙuruciyar nan da dayawa take kashe rayuwar yaranmu da nakasar zukatan iyaye. Tare da ƙarfafa iyaye akan tsayawa akan ƙafafunsu wajen ganin sun tallafawa ilimin yaransu musamman mata. Dan ɗiya mace tana matuƙar buƙatar ilimi kodan sanin yanda zata tafiyar da rayuwar aurenta ma da tarbiyyar yaranta. Domin kuwa wannan ƙarancin ilimin ya taka rawar gani akan mahaifiyar Khadijah a lokacin da soyayyar Dafeeq ke ɗibarta. Maybe da tanada ilimi data kasance mai tsayawa da bin matakan jan ra'ayin ɗiyarta. Hakama iyayen Kainaat. Maybe da sunada ilimi da basu yarda ƴarsu ta zubar da su ba a idon duniya ta ɗauki wasu iyayen barikin. Duk da dai idan mukai dubi da wani faninin kuma Kainaat nada ilimin ai, amma bai hana ƴarsu Banan ta bijire musu ba itama harta maimaita abinda Kainaat ta aikatama nata iyaye. Hakan na nufin koda ilimin sai an haɗa da ƙyawawan halaye da tsayawa wajen biyayya ma iyaye. Dan iyaye basu kasance abin wasa ba a wajen kowanne irin ɗa komai lalacewarsu da baƙaƙen halayensu. Dan kuwa dai Banan taga hakan, dan duk da baƙin halin iyayenta Kainaat da Dafeeq hakan bai hanata itama ɗan ɗana kuɗarta ba. Tunda da ga ƙarshe ta ɓige da ƙasƙantacciyar rayuwar prison. Ta kuma ratayama kanta alhakin rai. Inda ta koma ba dukiyar babu iyayen babu nasarar rayuwar. Hakama a fannin Khadijah sai da ta girbi abinda ta shuka duk da kuwa ita nata iyayyen ma ta roƙa gafararsu kuma sun yafe mata kafin subar duniya. Amma duk da haka sai da UBANGIJI ya ɗanɗana mata irin wannan zafin data ɗanɗanama iyayenta domin taji ta tabbatar da iyaye ba abin wasa bane ba. Hakama bijire musu babbar musiba ce kuma illa ga rayuwa. Sai dai ALLAH ya taimaketa kasancewa mijinta mutumin kirki mai tsarkin zuciya yasa komai ya daidaita cikin sauƙi suka cimma burinsu na aurar da ƴarsu cikin salama ga wanda taso kuma yake sonta a kuma lokacin da sukai fata. Haka dama rayuwa take cike da ƙalubale kala-kala da kuma nasarori. A wasu lokutan gaggawarmu ke hanamu zuwa ga nasarorinmu. Wani lokacin kuma son zukatanmu ke yanke mana igiyoyin nasararunmu. Mun manta cewar UBANGIJI ya ƙaddarara dukkanin ƙaddaririn namu tunkafin haihuwarmu. Babu kuma mahaluki ko alkalamin da takardar da suka isa canjawa daga abinda zuciya ke so zuwa ga abinda ke a rubuce a taskar ALLAH. Dan haka mu kasance masu tsoron UBANGIJI a duk inda muke a kuma duk yanda muke. Mu kasance masu jin soyayyar MANZON ALLAH a zukatansu akowane hali dan ita a garemu wajib ne. Mu kuma kasance masu biyayya da hakuri da iyayenmu koda abinda suke so mu bai mana ba mu so shi in sha ALLAHU zamu ribatun a wata rana koda ƙasa ta lulluɓe idanunsu. Sannan namu ƴaƴan muma zasu kasance masu biyayya a garemu.
Ya rabbi ka shiryemu ka shiryamana yaranmu. Ka tsaremu katsare mana zukatanmu. Ka saka gaskiya a harshenmu, ka saka gaskiya a zukatanmu, ka saka gaskiya a ayyukanmu da gaɓɓanmu. Ya rabbi ka hanemu saɓa maka da ganganci ko akan rashin sanin ka tsaremu daga aikata ZINA. ka shiryi masu aikatawa idan masu shiryuwa ne. Idan ba masu sjiryuwa bane ya rabbi ka nisantamu da su ka nisantasu da ƴaƴayenmu. Ya rabbi ka shiryi masu irin halayyar JJ idan masu shiryuwane. Idan ba masu shiryuwa bane ya rabbi mun kawo ƙarar su gareka ka fimu sanin yanda zakai mana da su.. Ya rabbi ka gafarta mana baki ɗaya. Ka ɗaukaka ayyukanmu da rahamarka.🙏😭✍️.


*_ALHAMDULLAHI!!_*


Ya rabbi Nagode maka daka bani ikon kammala wannan ɗan littafi nawa. Kuskuren da nayi a ciki rabbi ka yafe mini ni da masu karantawa.🙏


Duk wanda na ɓatamawa a yayin rubuta wannan labari ya yafe Mani. Nima na yafema kowa.🙏


Ina sake tallata muku littatafan ZAFAFA BIYAR dake shirin zuwa muku da wani sabon salo na musamman masoya. Dan tafiyar wannan shekarar fa tanada banbanci da saura matuƙar banbanci. Soyayya ce za'a shata kwarya-ƙwarya😋 babu algus. A fanin ilimin ma mun tanada muku romo mai yawa. Hakama faɗakarwar munzo da sabon tanadi. Kai cakwakiyar ma fa da zamantakewar rayuwa duk ba'a barmu a baya ba. Kudai kawai ku kasance da zafafan biyar ɗin nan naku domin samun nishaɗi fiye da yanda aka saba.😁👍👌


Masha ALLAH sai mun haɗu a ZAFAFA BIYAR dan suna nan shirye tsaff da zafinsu. Kuma gab suke da zuwa gareku in sha ALLAHU suma😁🙏






Bilyn Abdull ce🤙.








_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_






🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login