Showing 87001 words to 90000 words out of 114936 words

Chapter 30 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt

13 Dec 2024

5037

labarinsa sai suji ƙyashin badawa. Sai dai kawai idan kaje kaji yanda yake ihun kuka da roƙon likitoci su taimakesa su kashesa dan azabar ƙunar da yake ji zakaji tausayinsa kasancewar ka mai imani.
Watannin JJ kusan takwas nannaɗe cikin bandage a gaba ɗaya jikinsa sai idanu kawai ALLAH yay masa rasuwa. Mutuwa ce data matuƙar girgiza duk wanda yasan sa a zahiri dama wanda ya san labarinsa da hotunansa a kafafen sada zumunta. Dan yanda hotunan nashi da labarinsa suka dinga yawo a baya a yayin mutuwar tasa ma hakan ce ta kasance. To shi dai tasa ta ƙare kuma ai. Sai fatan ALLAH ya shiryi ƴan baya idan masu shiryuwa ne. Idan kuma bazasu shiryu ba ya UBANGIJI ka fimu sanin miya dace akan azzaluman nan. Ka mana maganinsu ka kare ƴaƴayenmu da ƙannenmu dama mu kammu da ga shiga tarkon yaudararsu. Ya rabbi ka yafe mana kurakuran mu. Ka sanya duniya a tafukan hannunmu ka hanata tasiri a cikin zukatanmu. Ya rabbi ka wajabta mana tsoronka da soyayyar ANNABIN MU tsira da amincinka su tabbata a gareshi shi da iyalan gidansa. Ya rabbi kasa ranar mutuwarmu ta zama ranar farin ciki a garemu. Ya sabbi ka saka gaskiya a harsunan mu, zukatanmu, jikunmanmu da ayyukanmu baki ɗaya🙏😭..




___________


A washe garin da aka sallamo Kainaat asibiti ta tattara komai nata ta danƙa a hannun Mom ɗin Nadwa da tazo dubata. Dan hatta kuɗaɗenta na banki kaf ta turasu a account ɗin Mom ɗin. Bayan Mom ɗin ta wuce gida ta kammala nata shirin tsaff akan Dafeeq. Dan zama tai a falo tare da ajiye biro da takarda tana jiran shigowarsa. Kusan awa biyu kuwa sai gashi ya dawo. A kallo ɗaya da yay mata ya gama karantar shirinta. Amma sai ya danne zuciyarsa ya ƙaraso cikin falon. Kusa da ita ya zauna cike da kulawa da kwantar da murya ya ce, “Hajjaju yaya dai! Badai jikin bane ko?”.
Maimakon bashi amsa sai ta miƙa masa takarda da biron data ajiye. Kallonta yake cikin nuna alamun rashin fahimta, kafin yay ƙarfin halin faɗin, “Namiye kuma wannan ɗin?”.
A gatsine ta ta ce, “Takarda ce da biro. A yau ina buƙatar saki na Dafeeq. Dan bazan iya zama da kai ba Dafeeq. Ka sanya min ciwon sanyi saboda tsabar son zuciyarka. Miyasa tun kafin aurenmu baka sanar min kana da infection ba ne?”.
Murmushi yaso saki dan harga ALLAH tama bashi dariya amma sai ya dake. A ɗan ɗage cike da gatsen shima ya furta, “Ai auren mu auren zobe ne Hajjaju, babu saki babu yaji har abada. Banda abinki ma k yanzu ina zaki je da wannan abun da ke a tare da ke”.
A wani kalar razane ta ɗago ta kallesa da faɗin, “Kamar ya?”.
“Kamar yanda kika ji na faɗa mana. Hajjaju tunda har kin tabbatar na saka miki wannan ciwon bai kamata ai mu rabu ba dan kema zaki iya zuwa ki sakama wani. Kawai muyi haƙuri da juna a haka shine zai fi”.
Wata irin ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki, dan da farko ta zata cikin dake a jikin nata ya gane. Harara ta watsa masa da miƙewa ta jefa masa takarda da biron. “Babu ruwanka da abinda zai faru a rayuwata ta gaba, na baka awa ashirin da huɗu ka saken da arziƙi ko ka sakeni ta wuya.” fuuuu ta wuce rai a ɓace. Murmushi ya saki da kaiwa kwance jikin kujera yana wani cije lips. Sai kuma ya ciro wayarsa da ke aljihu yay ɗan danne-danne da kaiwa kunne. Cikin wata iriyar murya dake nuna tsantsar basanci ya furta, “Doctor aikin ka ya fara.”
Murmushi mai ƙayatarwa Doctor Giɗaɗo ya saki da ga can, har Dafeeq na iya jiyo sautinsa. Cike da isa ya furta, “Yes Abokina.”
Yanke wayar Dafeeq yay yana sakin wata shegiyar dariya harda ɗan bubbuga kansa a jikin kujera irin na na gama cin nasarar nan..


*_WASHE GARI_*


Ƙarfe kusan goma na safe Kainaat dake ta shirye-shiryen matakin da zata ɗauka akan Dafeeq ta sakko ƙasa. Kitchen ta nufa neman abinda zata sakama cikinta saboda yunwar data tashi da ita mai tsanani. Tana ƙoƙarin ɗora tukunya a saman gas sabon maigadin ta yay sallama. Daga kitchen ɗin ta amsa masa tana ɗan leƙowa. Ganin yanda yake kamar a ruɗe ya sata tsayawa kallonta. Sai kuma a ɗan tsawace ta furta, “Ɗanjuma lafiya kuwa?”.
“Babu lafiya Hajiya, dan wasu baƙine gasu can a tsakar gida suna dudduba gidan nan, sune suka ce a sanar muku wai masu gidan ne su suna buƙatar magana da ku masu hayar ciki”.
“Haya kuma? Wace kalar haukace kuma wannan, kodai ka fara shaye-shaye ne Ɗanjuma? Kai ubanwa ya faɗa maka haya nake a gidan nan?”. Sai kuma a fusace ta nufi ƙofar fita batare data jira cewarsa ba.......✍️






_Tofa Hajiya Kainaat mike shirin faruwa haka ne kuma?_.


_Amin afuwa da jina shiru kwana biyu, cikin ƴan hutuna ne ta saka bit a hanci gaba ɗaya hankalina ba'a kwance yake ba kwanakin nan🤦._


____________




_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_


_KU MARMATSO KUSA...🔊_




_ZAFAFA BIYAR 2024_


_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_


_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_


_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_


_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_


_________


_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_


_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_


_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_


_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_










*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_Shafi na talatin da shida_






Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/F7aIYP99bGn9mIqLhjUWKR MUNA SAYAR D KAYAN KITCHEN D FURNITURES N TURKEY D ABAYA AKAN FARASHIN SARI DA CAPSULES MASU KYAU D INGANCI.


_________


*_ASHE SUN DAWO😱???!!_*




_Su waye🤔?_


*_ZAFAFA BIYAR MANA_*




*_🤥AMMA NAKE ZAUNE NAN WANGALAU DA BAKI😨 KAMAR ƘOFAR RIJIYA. KAI AMMA DAI GASKIYA TAWAJENA BAKI ƘYAUTABA. MU ZAFAFA BIYAR NA FARA HARKA AI ZAMA YA ƘARE MANA, CIN DATA A BANZA DA GANTALI BABU WAJEN ZUWA A MEDIA KUMA YAZO ƘARSHE. BARI DAI KIGA DA SURUTUN NAN NIMA NAJE NA YANKO NAWA TIKITIN SHIGA A DAMA DAMU. KIN SAN IN ANA ZAFAFA BAKAI BABU DAMUWA, NISHAƊI ZALLA A LITTAFAN SU, KAI HARMA DA GIDAN COMMENTS._*




*_WANNAN GASKIYA NE, INA KUKE MA'ABOTA KARANCE-KARANCEN LITATTAFAN HAUSA. KU GARZAYO MAZA GA WATA SABUWAR DAMA TA SAKE SAMUWA FA. DOMIN KUWA ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN DA KUKE TA JIN LABARI SUN SAKE DAWO MUKU DA WASU DABBIN SALO NA SABUWAR SHEKA MASU ƘAYATARWA_*




*_ILMANTARWA!!_*
*_NISHAƊI!!_*
*_SOYAYYA_*
*_BARKWANCI_*
*_ƘAYATARWA_*


*_ƳAR UWA KE MI KIKE JIRA ANATA YANKAR TIKITIN SHIGA JIRGIN ZAFAFA BIYAR AMMA KE KINA A NIGERIA GASHI KUMA YANA GAB DA TASHI. KIN YARDA DUK WANCAN ABUBUWAN NA SAMA SU WUCEKI? KENAN?_*




*_HABA TAWAJENA MAZA GARZAYO A DAMA DAKE KEMA A WANNAN TAFIYAR. NASAN ZAKIJI DAƊINTA ZA KUMA KIYI ALFAHARI DA ITA. DOMIN MASU IYA MAGANA KANCE SAYEN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA. TO SAYEN ZAFAFA HAR RIBA MA ZAKI MAIDA INSHA ALLAHU._*




*_Ƙayatattun littafan naku sune kamar haka👇🏻_*




*_GUDUN ƘADDARA🏃‍♀️_*
_(Na SAFIYYA HUGUMA. kai daga jin sunan kasan za'a ɗauki darasi tare da ilimi harma da soyayya mai ƙayatarwa. Dan kun san HUGUMA bata kawo muku labaran banza. Za'a warwasa matuƙa da nishaɗi mai gamsarwa🥰🫡)_.




*_KWANKWASON JIMINA...🦃_*
_(HAFSAT MISS XOXO. Masu iya magana kance kwankwason jimina mai wuyar shafawa. Daga ji babu tambaya wannan littafi na ɗauke da darasi, ilimi na musamman, tare da gagarumar cakwakiya, ilimi harma da nishaɗi. Kun san dai Miss xoxo a fagen ƙayatar daku, ga soyayya mai tsayawa a zuciya kaji kamar ana zanata ne a cikin kanka.😍🫡)_








*_AMEENATU🧕🏻_*
_(NA MAMU GEE. Kun dai san Mamun taku a fagen iya tsara labari, ta kasheku da sinƙi-sinƙin ƙauna ziryan mara gaurayen algus. Daga jin sunan littafin ma kasan za'a kwashi romon ƙauna da ilimin ƙulle mai gida a haɓar zane kai soyayya fa tayi. Kun san dai Mamu gee bata kawo muku labaran banza😘🫡)_.




*_TSUTSAR NAMA....🥩_*
_(NA BILYN ABDULL. Tofa cakwakiya. Lallai akwai tsallen tsalli watsanga kenan a wannan littafi. Kun san dai Bilyn taku wajen kawo muku darasin rayuwa, ilimi, nishaɗi, cakwakiya, kai harma da soyayya mai sa kaji kamar dan kai akeyi. Ƴan uwa akwaifa ƙura hummmm🫶🫡)_




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_






🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥


_________




.......“Sunana Alhaji mai-kuɗi. Ni ne mamallakin gidan nan a yanzu. Nazo ne nai magana da masu hayar gidan. Dan haka ina mijinki?”.
Wani shegen kallo na amma ka haukace Kainaat taima dattijon mutumin. Kafin cikin rainin wayo ta ce, “Dama yanzu shaye-shaye ya wuce kan matasa har dattijai ma ɗorawa suke yi. To idan hankalin naka baya a tare da kai bari na dawo maka da shi jikinka. Sunana Kainaat, wannan gidan kuma mallakina ne. Idan ma wani sakaran ɗan damfarar ne ya siyar maka kai maza kafin ya ɓace ma ka karɓa kuɗinka.”
Sheƙeƙe Alhaji mai-kuɗi yay dariya, shima dai kallon ke wawuya ce ya jefeta da shi, kafin cikin gadara da ƙyaɓe fuska ya dubi yaransa a umarce ya ce, “Wannan naga ƴar hau ce. Tunda bata buƙatar masalaha ku gaya mata na bata nan da kwanaki uku in ma ita kaɗai ce, in ma da mijinta suke tare su tattara su barmin gidana dan ina da buƙatarsa. Ku nuna mata shaida maybe ta farka a mafarkinta”. Yana gama faɗa ya fice yana wani takun faɗi kamar bajimin san da girma yayma yawa...
Wani kalar ihun rashin mutunci Kainaat ta musu lokacin da suke ɗaga mata takardun, kafin ta koma ciki fuuu. Kai tsaye ɗakin Dafeeq ta nufa. Jin ƙofar gam-gam ta shiga masa bugun hauka. A fusace ya buɗe ƙofar, daka kallesa kaga wanda ya tashi abarci. Ranta ɓace ta ce, “Kazo nan kana barcin asara na rashin aikin yi. To sai ka fito ga wasu ƙadangarun bariki nan sunzo wai gidan nan nasu ne. Harda bamu notes na kwana uku”.
“Kamar ya Notes?”.
Ya faɗa cikin mamaki. Bata amsa masa ba ta juya a fusace. Da kallo ya bita, sai kuma ya saki wani lalataccen murmushi yana komawa ɗakin bayan ya sakama ƙofar key. Tsalle ya dirga saman gado yana wani ƙaramin ihu. Sai kuma gimtse bakinsa yana waro idanu. Wayarsa ya ɗauka ya shiga dannawa, kafin yay dailing wata no da aka sakama Dr G. Tana fara shiga ya wani yi baya a saman gadon ya kwanta ƙafa ɗaya kan ɗaya like saraki ɗin nan dai. Yay filo da hannunsa ɗaya ɗayan na riƙe da wayar. Harta tsinke ba'a ɗaga ba, bai kawo komai a ransa ba ya ƙara kira. Nan ma dai ba'a ɗaga ba har sai da yay kira kusan huɗu sannan aka ɗaga ana ƙarshe tana gab da tsinkewa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yay sallama a gadarance.
Daga ɓangaren Doctor Giɗaɗo ya amsa murya a sauƙaƙe tamkar yanama murmushi ko yanayin nishaɗi. “Aboki kana kira ina cikin aiki ne. Ykk?”.
“Normal”. Dafeeq ya amsa a gadarance. Kafin cikin yamutsa fuska kamar yana gaban doctor ɗin ya cigaba da faɗin, “Naga mutanenka sun zo. Harya bada kuɗinne?”.
Wata ƴar dariya doctor ya saki, sai kuma ya bashi amsa da, “Yes ai harma na damƙa masa takardun. Suma kuma yanzu haka duk sun iso hannuna.”
Karan farko Dafeeq ya saki murmushi, sai kuma a ɗan zumuɗe ya furta, “Okay good. Yanzu mu haɗu da kai a inda muka saba haɗuwa. Amma kafin nan ka bama yaron nan nasu 1mil..”.
“Okay an gama abokina, amma baka tunanin bama yaron kuɗi zai sa su Nadwan su fahimci abinda ya aikata. Ya kamata mu bari har sai ka bar garin, koma ka tafi da shi mana Please”.
“No no, ai ni bana aiki da mutum sau biyu, na tafi da shi nima wataran zai iya cin amanata. Batun su Nadwa kuma ai bashi kaɗai yay aikin ba da taimakonka ne. Tunda da bata yarda ta sanar maka ina suke ba ai bazaka sani ba?”.
“Yes kuma hakane. Amma inada shawara, bai kamata mu haɗu yau ba, mu ɗan bada ƙafa 3days okay”.
Ɗan jimm Dafeeq yay kamar zancen bai shigesa ba. Sai kuma zuwa can ya furta, “Hakan bazai yiwu ba, nasan yau gidan nan akwai ƙura, anjima kaɗan zan nemeka kazo saika saman anan kawai”.
Doctor ya amsa masa da “To babu damuwa”. Daga haka suka yanke kiran. Sai da yasha dariyarsa sannan ya saka jallabiya ya sauka ƙasa. Ya samu Kainaat zaune a falon da waya a hannu, da alama wani take nema amma ta gagara samunsa. Cikin wani irin sauri ya ƙaraso gareta. “Am sorry Baby. Na ɗan zagaya toilet. Please yimin bayani yanda zan gane ɗazun kin barni a duhu nikam”.
Kamar bazata ce komai ba, sai kuma ta shiga masa bayani a zafafe. Ta ƙare da faɗin, “Dafeeq narasa miyyasa hankalina ya gagara kwanciya. Yanzu haka kuma kiran wayar Nadwa da Mom nake amma babu wacce ta shiga.”
“A'a miya haɗa wannan maganar kuma da su Nadwa?”.
Cikin rasa control ɗin ta ta ce, “Takardun gidan nan fa dama duka documents ɗina suna hannunsu. Ina son jin ko an samu kuskurene da ga wajen su da har mutumin nan ke jin ƙarfin gwiwa, dan wlhy na hango tarin rashin mutunci a idon mutumin nan fa”.
Wani kalar gyara tsaiwa yay cike da salon karyar da murya ya furta. “Oh yanzu Baby tsana da rashin yarda har takai haka a tsakaninmu. Ki ɗauki komai naki ki fita da su a gidan nan saboda ni?....”
Da sauri ta shiga girgiza kai, sai dai ta gagara cewa komai. Shima bai sake cemata koman ba ya koma gefe ya zauna shi adole yayi fushi. Duk da taji wani iri sai dai batashi take ba. Ta cigaba da kai-kawo da neman layin Mom da Nadwa. Sai dai samun ya gagara. Da ga ƙarshe dole ta yanke shawarar fita. Ko kaɗan baiyi yinƙurin binta ba. Itama batako masa tayin hakan ba ta figi key ɗin mota ta fita. Mintuna kaɗan suka kawota ƙofar gidan su Nadwa, sai dai ta samu gida garƙame da kwaɗo. Mamaki ya kamata, tana tsaye tana ƙullawa da kwancewa maigadin maƙwaftansu ya leƙo. Da sauri ta nufesa tana tambayarsa ko ina masu gidan? Cikin rashin damuwa da kuma sanin da yay mata ya bata amsa da, “Ai sun tashi anan, sun kuma saida ma gidan jiyan nan. Ga wannan ma sukace a baki dan da alama dama sunyi tunanin zuwanki ma ashe”. Ya ƙare maganar yana miƙa mata brown envelope. Hannunta har rawa yake wajen amsa. Harta kama zata buɗe suka ji an tada mota. Da sauri suka waiga a tare, sai me har an birka motar a guje. Ihu ta shiga kurmawa tana tsalle da kiran ɓarawo-ɓarawo. Nan fa masu gadin gidajen layin suka shiga firfitowa a guje. Sai dai kamar asiri basu ko kama hanyar cimma ɓarawon ba. Hasalima ya ɓace ma ganinsu ɓat kamar abin rufa ido......


__________★


Tunda ya koma aiki kamar yanda ya saba ƙarfe biyar yake dawowa gidan. Yau ma hakane. Sashen mahaifiyarsa ya fara shiga suka gaisa kafin ya nufo nasu sashen. Tun kafin ya shiga wani ƙamshin turare mai ratsa zuciya ya gama cika masa ƙofifin hanci. Lokacin da ya gama shiga tsakkiyar falon sai yaji kamar ya shiɗe dan daɗin ƙamshin turaren wutar. Kamar mai jin zazzaɓi-zazzaɓi a hankali ya furta, “Baɗɗo am”.
Murmushi Khadijah dake laɓe bayan labule ta saki, kafin ta yaye labulen a hankali jin ya sake kiran sunan nata. Wani kalar luuuu yay da idanunsa kamar mai shirin suman tsaye sai kuma ya buɗesu a slowly. Tabbacin ita ɗin ce dai ya saka shi jin numfashinsa na wani fita guda-guda. A hankali Khadijah da ke kallonsa ta sake sakin murmushi, sai kuma tai ɗan yi juyi a hankali.
“Habba Baɗɗo am kasheni zakiyi? Maza zo gareni karna sume, Baɗɗo am Hammanki mai rauni ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login