Showing 36001 words to 39000 words out of 114936 words

Chapter 13 - Cuta Ta Dau Cuta Complete Hausa Novel By Billyn Abdull .txt

13 Dec 2024

5047

yaudararku ne da ƙananun abubuwan dake buɗe hanyoyin zina koda ba'a kai babban ba).
A ranar da JJ yaci galabar keta mutuncin Anoosh a ranar ALLAH yayma Gwaggo rasuwa. Wannan ruɗanin ya hana Hajiya Lailah fuskantar halin da Anoosh ke ciki. Yayinda Anoosh ke kuka biyu, sai dai JJ nata faman mata daɗin baki ta waya harda kukansa shegen. Ganin yanda ya nuna nadamarsa a zahiri ya sakata jin ɗan sassauci harta saki jikinta. A haka ranar addu'ar bakwai ya sake samunta ya more. Nan ma ta rikice masa da kuka ya koma lallashinta. Al'amari kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba, dan kuwa dai JJ ya gama cin nasara akan Anoosh. Yakai yanzu idan ya ɗauketa maimakon makaranta sai ya kaita wani waje daban. Tun abin na damunta harta fara jin daɗinsa itama. Dan kullum magana ɗaya ce yake mata idan bata bashi ba zai je ya nema matan banza. (Kuji shege. Jeka nema mana bakai da ALLAH ba dan buhun bakon gidanku🙄😡). Sannu a hankali JJ ya gama sauyama Anoosh alƙibla. Sai ya gama moreta ta koma tana kuka da istigifari. Gefe kuma ya saki maganar kawo kuɗin aure. Idan ta tuna masa sai yace ta sake haƙuri rasuwar Gwaggo ta sake nisa kar ace bai damu ba. Ya riga ya ɗaureta da jijiyar kanta, dole take binsa da to kawai.
Ita kanta Hajiya Lailah da abun ke damunta a rai ranar dai ta fidda kunya taima JJ magana, sai yace zasu zo a cikin satin zuwa weekend. Ta ɗan ji nutsuwa, dan burinta a yanzu kawai shine Anoosh tai aure itama ta samu tayi auren dan zama haka bazai cigaba da mata ba ana kallonta wani abu daban a anguwa, ga shi yanzu babu Gwaggo mai tsaya matan. Kwana uku da haka Anoosh ta fara ciwo, Hajiya Lailah bata kawo komai a ranta ba sai zazzaɓin cizon sauro kawai da canjin yanayi, dan haka takai ta camix. Ganin har washe gari zazzaɓin yaƙi sauka ga amai tanayi yasa ya ɗauketa suka nufi asibiti.
Hankali tashe suka dawo gida sakamakon abinda likita ya sanar musu cewar Anoosh nada shigar ciki wata biyu da satittika. Daina gani Hajiya Lailah ta kusan yi, da ƙyar da addu'a suka iso gida. Anoosh nada matuƙar tsoro, dan haka Hajiya Lailah na tsareta da kurari bayan shigarsu gida babu wani ja'inja tace JJ ne. Sumar tsaye Hajiya Lailah tayi, ga hawaye na kwaranya a idanunta. Cikin rawar jiki ta ɗauka waya tai kiran JJ. Batare da tace masa komai ba akan ciki ta ce tana buƙatar ganinsa dan ALLAH. Haka kawai yasha jinin jikinsa da jin muryarta, amma sai yace mata zai zo zuwa gobe ko jibi yanzu yayi tafiya ne Babansa ya aikesa Kaduna. Dole ta danne tace masa babu damuwa har ya dawo ɗin.


Hankalin JJ ya matuƙar tashi, dan ya fahimci Hajiya Lailah fa ba kanwar lasa bace ba. Sannan kanta a waye yake dan tanada iliminta gwargwado. Dan haka ya tattara ya gudu da ga Kano a ranar yacema iyayensa zaije Abuja wani abokinsa na nemansa akan aiki. Sun masa fatan alkairi ya tafi da shirin sai bayan wata guda zai dawo, dan yasan su Hajiya Lailah ba gidansu suka sani ba.......

(Hummm😠)


____________★


Wani irin kalar rawa jikin Khadijah keyi fiye da farko. Ta ƙurama Dafeeq idanunta dake mar-mar kamar zasu zubo ƙasa. So take taji ya musa, so take taji yace ma Hajiyar nan ƙarya take ba haka bane. Amma harta wuce bai ce ba. Sai ma tana fita wani zabura da yay zai bita. Ƙarfin bugu zuciyarta ta ƙarayi jiri na neman ɗibarta. Batama san lokacin data buɗe baki cikin ƙaraji da karkarwar jiki ta furta, “Dafeeq da gaske kana zuwa duba iyayenka?!! Da gaske kaike zubar da cikin da na dinga samu?!!”.
Harara ya juyo ya watsa mata tamkar zai cinyeta da idanun nasa. Sai kuma ya buɗe ƙofar a zafafe ya fita. Dama yana gab da fita ne tai maganar. Ihu Khadijah ta kurma jikinta na girgigizawa. Gaba ɗaya jitake kamar ta haukace ma ita kam...


Da bibbiyu Dafeeq ke haɗa steps ɗin benan. Jikinsa na rawa kamar wani mayuncin zaki. Yanda yay wani irin kumburar ɓacin rai bazaka taɓa ɗauka yaron nan ɗan shekara ashirin da huɗu bane ba. Kai tsaye ɗakin kainaat ya nufa, sai dai yana ɗora hannunsa a handle ɗin ƙofar ya jita a rufe. Cikin ɓacin rai da ihu ya ce, “Hajiya buɗe ƙofar nan kona ɓallata!!”.
Wani shegen murmushi Kainaat ta saki tana taɓe baki. A ranta tace haba yaro bakai kana jin kai ɗan iska bane kana a ganiyar balaga. Indai takamarka kai shege ne nan ma gidan ka taras, waya gaya maka ana shiga gonar Kainaat a fita lafiya babu tabon sarin maciji koda a yatsan ƙafa ne. Ai wasan yanzu ma aka fara, da kanka zaka min abinda nake so kafin ma cikar sati ɗaya. Amma hakan bazai hanani hukunta shegiyar matarka ba tunda ita batasan taci arziƙin a rabu lafiya ba. Taja tsaki tare da fisgar wayarta ta shiga danne-danne tamkar batajin hargowar da yake da jijjiga ƙofa. Wayar na gab da tsinkewa Nadwa ta ɗauka. Cikin yanayin barci ta ce, “Hello”.
“K malama watsakke a wannan barcin nice”.
Da mamaki Nadwa dake tashi zaune tana murzar ido tace “Amarya a wannan daren, ina kika bar mijin naki ke kuwa dan ALLAH. Wai badai da gaske kike bazaki bashi kanki ba?”.
“Humm share ba wannan bane yasa na kiraki Nadwa, so nake da safe ki sanarma Mommy ina son a aika matar nan taje min wajan malamin nan da yay min aiki akan Abaan ina amarya. Ina son a gobe Dafeeq ya saki matarsa”.
“What! Haba! Haba Kainaat mi kuma ya kaiki wannan tunanin? Dan ALLAH kada ki raba ma'auratan nan Please and please. Keda ba zama kikaje yi ba miya kawo miki wannan tunanin a daren nan? Ni dai babu ruwana dan ALLAH kada kiyi haka akan yarinyar nan da abinma tausayi ce. Ki barta da zalincin da yake mata ma na zubar mata da ciki”.
“Haba kema kin san ganganne na ƙyale cuta ban rama ba. Ai rama cuta ga macuci ibada ce. Har ke kike tunanin wai babu ruwanta. Wlhy duk da ban auri mijinta dan na rayu da shi ba ita bata isa ta shiga gonata na ƙyaleta ba. Da ga safiyar yau zuwa daren nan tamun abinda sai ta san ta shiga gonata wlhy”.
“Ya ALLAH calm down mana Kainaat. Mita miki?”.
Kamar bazata faɗa mata ba sai kuma ta kwashe komai ta sanar mata. Tare da ɗorawa da wannan hukuncin nasu ne su biyu, duk da kuwa shima na tabbata dama wannan shine burinsa a kanta ƙarshe. Dan maza irinsu da sukai auren wuri kuma irin kalar auren nan daga ƙarshe mawuyaci ne basu sake su ba kosu ƙaro musu kishiya. To ni zan rabasu ne a gaɓar da suke buƙatar junansu dan ubansu. Duk da ban auresa dan na zauna dashi ba shi har ya isa ya ɗauki kwanana ya kai mata, tsabar son zubar min da mutunci a wajen ƴar cikina kwana ɗaya da auro ni. Ai wannan cin mutunci yakai cin mutunci”.
“To amma baki ganin kema akwai laifinki? Maybe a matse yake bawon ALLAH kin hanashi kanki kin bashi kuɗi tayaya kike ganin tunda yasan yanada wata matar bazaije gareta ba. Ni dai dan ALLAH ki barsu, abinda kika faɗa mata ma kawai ya isa punishment a gareta, shiko nanda sati ɗaya zaki masa nashi punishment ɗin tunda ya saki jiki aure yay kamar kowa zaici banza, bai san nan da kwanaki komai daya samu ba ma zai rasa shi. Hakan kawai ya ishesa ai”.
“Ina hakan yamun kaɗan, idan bazaki min yanda nake so ba barshi, bara na kira Mommyn da kaina dama dan naga darene bana son tadata a barci, kuma so nake tunda safe aje a amso min”.
“A'a miyay zafi, saƙonki kam zan isar in dai nice. Ni dai shawara na baki dan ina tsoratar miki abinda zai iya zuwa ya dawo. Tunda ba gama sanin halin yarinyar nan kikai ba. Koda kike ganinta ƙarama maybe itama ta iya nata kalar hatsabibancin. Kigafa yanda ta maida miki magana har sau biyu”.
“Mtsoww! Riƙe shawararki malama”.
Kainaat ta faɗa tana yanke wayar. Jefar da ita tai gefe tayi kwanciyarta batare fatabi takan Dafeeq dake cigaba da kiran sunanta yana ƙwanƙwasa ƙofar ba. Sai ma taja headphones dake cikin bedside drawer ɗin ta ta saka abinta, daga haka tabar jinsa gaba ɗaya...


Matuƙar tashin hankali Dafeeq ya shiga. Ta ina matar nan ta samo wannan sirrin nasa da yasan da ga shi sai ALLAH sai likitan nan suka sani. Sannan zuwa gida da yake yi kuwa shi kaɗai ya sani sai UBANGIJI. Dan tun bayan aurensu da wata biyar ya yanke shawarar zuwa ga iyayensa kasancewar labari ya sameshi mamansa ta samu karaya a ƙafa. Koda yaje bai wani sha wahalar shawo kansu ba dan suna son sa kamar mutuwa sakamakon shi kaɗai suka haifa a duniya. Bai yarda ya faɗa musu a ina yake ba, ya kuma sanar musu ya saki Khadijah tun kafin yazo garesu saboda yaga basa so, yanzu neman kuɗi yake yi dan ya koma karatu. Sun ji daɗi sosai suka dinga saka masa albarka. Kwanansa biyu batare da ya yarda kowa ya gansa ba ya dawo. Yayinda babansa ya shirya har gidan su Khadijah yaje yayima mahaifinta tas yace kuma su nema ƴarsu acan gidajen karuwar dan ɗansu ya sanar musu ya saketa. Hankalin iyayen Khadijah ya sake tashi, jikin babanta ya sake rikicewa sosai harta kaisa da samun paralysis. Yanzu haka yana kwance gefen jikinsa baya aiki. Karatun ƙannenta ya tsaya, sai da taimakon wani bawan ALLAH da yaga ƙanwarta mai bimata yana so ya maida yaran makaranta, ya kai Baba asibiti. Yanzu haka yana amsar magani jikinsa da ɗan sauƙi, ƙannenta biyu sun kammala secondary sun cigaba da karatu, an kuma saka musu ranar aure dan dama burin mahaifinsu shi dai su fara karatun sannan ya aurar dasu sa ƙarasa a gidan miji, amma Khadijah ta nuna masa bai isa ba. Ƴan anguwar su Khadijah kam da mutane da yawa sun yarda Khadijah tabi duniya saboda tsoron kada ta dawo gida Dafeeq ya saketa a mata dariya ko iyayenta suƙi karɓarta.
Tun daga lokacin duk wata sai Dafeeq yaje gida, dan hatta auren nan na Kainaat iyayensa sun san zaiyi, hasalima a kuɗin data dinga bashi har gidansu yaje ya gyara tare da ƙarama babansa jari........✍️


_🥱 Dafeeq anya zakaga ANNABI ALLAH kuwa🤦🥲🚶_


_Khadijah ke kuma ƙya dawo hankalinki ai yanzu. Koda yake baki ji sauran labari ba ma😩_


_Ke kuwa Kainaat bakiyi wawtaba kuwa?, dan Dafeeq fa Hummm😆_


_JJ banda abin cewa a kanka kai kam yau🥲, na barka da masu karatu da su Alimah suci min ubanka bunsurun banza🧑‍🦯


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_Shafi na bakwai_






INA ƳAN KASUWA MASU SON ƘAWATA KASUWANCINSU TA HANYAN GRAPHIC DESIGN, DA MASU SHIRIN BIKI, KO SUNA, DA MASU SHIRIN WALIMAR SAUƘA, DA MASU SHIRIN YIN BIRTHDAY, KAI HARMA DA MASU ANNIVERSARY 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

MAZA KU GARZAYO "UMMUH FARUQ GRAPHIC DESIGN "TA TANADAR MUKU DA HAƊAƊƊUN DESIGN MASU ƘAYATAR DA MAI KALLONSU.🥰🥰🥰


KAMA DAGA
*FLYER
*3D MOCKUP LOGO
*2D MOCKUP LOGO
*NORMAL LOGO
*IMAGE LOGO
*BANA
*STICKERS
*ADVERT VIDEO
*PROFESSIONAL INVITATION
*INVITATIONS CARD
*BIRTHDAY VIDEOS
*POSTER
*CERTIFICATE.AND MORE......


CONTACT ME ON
👇
09035390383


____________




.......“Please Kainat yaya kika san duk wannan wai?”.
“Humm Nadwa kenan. Na faɗa miki Kainaat ba shashasha bace ba ai, kin san dai bazan jashi jikina ban san wanene shi ba. Inama da fiye da wannan game da shi, sai dai lokaci ne zai sa ki san sauran gaba ɗaya ba yanzu ba”.
Idanu kawai Nadwa ta zuba mata cike da mamaki da tsoro. Maganar gaskiya bata son ƙawar tata tace zata shiga tsakanin waɗan nan ma'auratan dake tsaka da cin ƙuruciyar soyayyarsu. Amma ta santa tasan halinta, in har tace tana son abu sai ta cimma burinta a kansa, dan ita shaidace ko akan Don Abaan da yanda ya fara sonta har sukai aure shirine babba...

★★★.....


“Ina ganin zuwa jibi zamu koma sabon gidan can dan mu samu albarkacin juma'a”.
Da wani irin razana Khadijah ta jiyo tana kallon Dafeeq da ke magana a dake hannunsa riƙe da rigarta data miƙa masa zai shanya a igiya. Babu alamar wasa a kan fuskarsa ga shi ya wani tsareta da idanu. Nata idanun ta rissinar ƙasa tana ƙoƙarin saita rawar da jikinta ya fara. Sai kuma ta shiga jinjina masa kanta dan in har tai magana sai hawayen da take riƙewa sun zubo mata.
“Miye wani ɗaga kai baki da bakin magana ne wai? Khadijah nikam wlhy na gagara gane miki gaba ɗaya. Da ace wani kemin wannan sabon halin naki sai na ɗauka baƙin cikine ko hassada. Gaba ɗaya kin hana kanki zama lafiya. Ki duba fa jiya na shigo da waya gidan nan amma koda na nuna miki baki ko taɓata ba a tsatstsaye kika wani ce ALLAH ya sanya alkairi kika kwanta...”
Duk yanda taso riƙe kukan ta gagara yin haka a wannan gaɓar saboda yanda yake mata magana a zafafe kamar ba Dafeeq ɗinta ba. Miƙewa tai da sauri daga gaban kayansu da sike wankewar ta nufi ɗaki da gudu hannunta toshe da bakinta. A zafafe shima Dafeeq ya miƙe, tana shiga falon yana shigowa shima. Wani kalar fisgota yay baya tai taga-taga zata faɗi ya hankaɗata saman kujera. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa sun gama kaɗewa, cikin nunata da yatsa tamkar zai mareta ya ce, “K! Wai mi kike nufi dani ne? Dan Kinga ina lallaɓaki kike ganin kin samu hanyar wulaƙantani da jana a ƙasa. Ubanmi na miki ba dai-daiba anan?”.
Kuka sosai Khadijah ta sake fashewa da shi, sai kuma ta kai hannu ta hankaɗashi baya iya ƙarfinta tana ƙoƙarin miƙewa. Taga-taga yay zai faɗi ƙasa ALLAH ya taimakesa ya dafe kujera.
“Taauuu!!”.
Kake jin wani lafiyayyen mari a fuskarta. A gigice ta dafe kuncinta tare da fashewa da wani sabon kukan. “Dafeeq ni ka mara?!”.
“An mareki ko zaki rama? Ke har kin isa ki dinga jana a ƙasa kamar wani yaronki! Har kina da ƙarfin min wannan abun. Ko kuma dole sai nayi abinda kike so saboda haihuwata kikayi ƴar marasa tarbiyya”.
“Dafeeq nice ƴar marasa tarbiyyar?!”.
“Kina da ita ne. Ko ƴa mai tarbiyya ce zata bar uwarta da ubanta ta biyo namiji wata uwa duniya. K! Nifa na fiki iya iskanci. Har ni zaki dingama baƙin cikin cigaban rayuwata saboda ke butulu ce. To bari kiji ki kama kanki kafin na sassaɓa miki kamanni a gidan nan. Dan wlhy kaɗan da ga aikina ne na haɗa miki jini da majina wawuya kawai...” fuuu ya fice kamar zai tashi sama.
Ragwaf Khadijah ta zube ƙasa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya.. Tunda ta baro gidansu ta biyo Dafeeq yau itace rana ta farko datai mahaukacin kuka na tashin hankali da har ya saka mata masifaffen ciwon kai tare da jin wani abu kamar nadama nasan ɗarsuwa a ranta. Dan ko daren farkonsu tayi kukan azabar da taci a hannunsa amma baiko kai kwatankwacin wannan ba. Ita yau Dafeeq kema gorin bijirema iyayenta ta biyosa nan?, ita Dafeeq ya ɗaga hannu ya mara. Mari fa, mari mai suna mari da har take iya jin sayin yatsunsa biyar akan ƙyaƙyƙyawar black beauty face ɗinta. jama'a Dafeeq fa, Dafeeq ɗinta data zaɓa akan iyayenta da karatunta. Dafeeq data yarda ta bar komai ta koma mara komai ta ɗaukesa. ya arrahaman wannan wace irin rana ce haka da bata taɓa lissafawa a ciki lissafin rayuwarta ba. ya ALLAH kasa mafarki takeyi ba a zahiri bane ba. Ta sake fashewa da sabon kuka mai tsananin ƙona zuciya.....


(Hummm Khadijah kaɗan daga illar bijirema umarnin iyaye kenan. Ƴammata a dinga sassauta soyayyar da har zata iya saka ido rufewa a bijirema iyaye🤦🥲 dan zancen malam bahaushe nan fa na NAMIJI BA ƊAN GOYE bane gaskiya ne akan wasu mazan).




★★★......




Iya jigata da galabaita JJ yayi a wannan dare zuwa safiya. Dan da salo-salo su Alimah suka dinga firgitashi. Gaba ɗaya ya gama fita a hayyacinsa tamkar wani sabon kamu a hauka. Babu abinda yake iya ganewa tsakanin rayuwa da numfashi. Rana da duhun dare. Duniya da lahira, fari da baƙi. Abinda kawai ya sani a garesa komai ya gama ƙarewa kawai. Yayi masifar zama zuru-zuru cikin ƙanƙanin lokaci. Ba shi kaɗai ba hatta gidan kansa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login