Showing 18001 words to 21000 words out of 28742 words

Chapter 7 - Jaruma Yazila book Complete by Abdul'aziz Sani Madakin Gini

jin haka sai sarki raihan yayi murmushi yace. ” Na yarda zan zauna naci abinci amma bisa sharadin cewa zaki cire™Nasiru Muhammad™ dukkan tsoron dake ranki ki daina tsuma haka”.
Da jin haka sai humaira tayi yar karamar dariya tace. ” Na amince amma ai bai kamata kaga laifina ba domin kwarjininka ne da mamakin wannan ziyara taka ta bazata su suka janyo mini lokaci guda duk su biyun suka yi dariya sannan suka zauna a tare zamansu ke da wuya sai sarki ya bude kwanukan abincin dake gabansa kamshi ya doki hancinsa ya shaki kamshi cikin farin ciki koda ya wanke hannunsa acikin bakinsa ya yanko loma guda ta abinci ya sa acikin bakinsa ya tauna ya tsaya cak ga barin cin abinci ya kurawa kwanon abinci idanu kawai al amarin da ya dugunzuma hankalin humaira ke nan tayi zaton ko abincin ne bai yi dadi ba.
Dag cai saita ga hawaye ya zubowa sarki raihan cikin kaduwa humaira ta dubi sarki kuma ta dubi baki da kyar tace. ” Yake umma dabira kiyi sani cewa baki yi kuskuren komai ba a cikin wannan girki ?” Koda jin haka sai sarki raihan ya gyada kai sannan yasa daya hannun nasa ya share hawayensa ya dubi humaira yace. ” Yake umma dabira kiyi sani cewa baki yi kuskure komai ba acikin wannan girki kuma tsananin dadin girkin ne yasa na tuno da matata marigyiya da kuma yar uwarta ina so ki sani cewa rabona da cin abinci mai dadi irin wannan tun daga ranar dana rasa wadannan masoya nawa saboda bakin ciki rabuwa dasu. Ina so ki sani cewa idan har ban zo bana baiyana miki wata muhimmiyar magana dake raina tsawon shekaru a yau bato har abada ba zan sami damar hakanba.
Yake ummul dabira kiyi sani cewa tundaga ranar da Nassey dey talk mutane suka zo dake tare da jaririyarki dabira naji ina matukar kaunarki a zuciyata, amma sai naji bazan iya furta miki ba saboda tausayinki bisa ganin halin da kike ciki na bakin ciki rashin mijinki wanda aka kashehi a gabanki dakuma yadda kika bani labarinki naji cewar kin rabu da daya 'yar taki wato usainar Dabira wacce kika bayar da ita ga 'yar uwarki Nuzaira. Tun™Nasiru Muhammad™ daga sannan na ji na kamu da tsananin tausayinki da kuma kaunar dabira, shiyasa na rokeki akan cewa komai dadewa kada kisanar da dabira cewa bani ne na haifeta ba har sai bayan shekara ashirin alokacin da zatayi aure murabu da ita an nuna mini a mafarki cewa a gobe-gobennen allah zai kawo wani sadaukin jarumin musulmi daga can nashiya daban wanda yafi Dabira jarumtaka kuma suna haduwa zasu kamu da son junansu akan wannan daliline na yi kundun bala na shirya wannan haduwa tamu domin na bayyana miki sirrin zuciyata. Idan harkin amince da tayina ina son a daura aurena da ke gobe".
Koda jin wannan batu sai humaira ta fashe da kukan farin ciki taji kamar ta rungume sarki raihan humaira ta budi baki domin tace wani abu sai kawai suka ga dabira ta fito daga cikin turakar humaira idanunta sun yi sharkaf da hawaye. Cikin firgici da matukar mamaki sarki raihan da humaira suka mike tsaye suka kura mata idanu. Dabira tasa hannu ta share hawayen ta sannan ta dubesu daya bayan daya tace, "me yasa kuka buye mini wannan sirri tsawon shekara da shekaru ? Na rantse da girman allah duk inda 'yar uwata take sai na tafi nemanta! Waye ya kashemini mahaifina? Kuma ko waye ya kashe mahaifina sai na bincikoshi duk inda yake na hallakashi! Ina tabbatar muku da cewa bazan taba yarda nayi aure ba face na cika wadannan burika ".
Koda gama fadin haka sai taji ta tsani birnin kisra da duk mutanen cikinsa saboda jin cewa asalin mahaifiyarta humaira daga can take. Nassey dey talk
Koda sarki raihan da humaira suka ga dabira ta fashe da kuka sai han kalinsu ya dugunzuma suka yunkura zasu je gareta domin su rarrasheta amma saita ruga waje da gudu ta nufi turakarta. Da zuwa sai ta shiga can cikin dakinta mai kofa ta rufe ta sake fashewa da sabon kuka.
Cikin sauri humaira da sarki raihan suka karaso kofar dakin dabira suka yi ta rokonta akan ta bude kofar amma taki, duk suka hakura suka koma turakar Humaira™Nasiru Muhammad™ suka zauna.
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani

***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {3}
TYPE C
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
====================================
Tsawon lokaci duk su biyun sukayi tagumi basu ce komai ba. Daga can sai sarki ya mike tsaye ya dubi Humaira yace, "yanzu muna cikin tashin hankali da damuwa saboda haka sai gobe naji amsar tayin dana yi miki "
Koda gama fadin hakan sai sarki yajuya ya fice daga cikin falon gaba daya. I ta kuwa Humaira ta bishi da kallo kawai cikin damuwa da tunani.
Har dare ya raba sosai Humaira bata rintsaba saboda fargaba da tunani bisa jin abinda Dabira tafada cewar duk inda 'yar uwarta take saita tafi nemanta kuma sai ta nemi wanda ya kashe mahaifinta. Shima shi.
Abinda ya tayar wa da humaira hankali shine, tasan irin bala'in sarki Daksur da sadauki Zaihar da irin sadaukantakar da karfin tsafinsu,don haka yana tsoron karonta da su don tana ganin cewa zasu iya hallaka farat daya muddin ta kai kanta inda suke.
Haka dai humaira ta kasance acikin tsananin tashin hankali ta kasa zaune ko tsaye ta dinga kai komo acikin turakarta. Tana cikin wannanhali ne ta tuno da batun tsoho kasim nan take ta aiyana zuwa dakin tsoho kasim ta tasheshi koda kuwa barci yake yi. Batare da bata lokaciba humaira tafito daga cikin turakarta acikin dare da durfafi bangaren da dakin tsoho kasim yake duk inda ta ratsa sai taga dakaru a tsaitsaye suna kan aikinsu na gadi kuma gaba dayan gidan sarautar a haskake yake da fitilu gwanin ban sha awa duk inda tazo giftawa sai dakaru su ratse su bata hanya babu inda aka dakatar da ita har ta iso kofar dakin tsoho kasim.
Da zuwanta sai ta iske kofar dakin a kulle take ruf. Haka ma gaba dayan tagogin dakin. Koda ganin haka sai jikin humaira yayi sanyi ta tuna cewa yau fa tsoho kasim acikin matukar gajiya yake sakamakon artabun da yayi™Nasiru Muhammad™ da kurayen nan har maya sami raunika saboda haka bai kamata ta tasheshi daga barci ba nan take humaira ta juya da baya da nufin ta koma turakarta. Amma sai ta jiyo sautin kuka acikin dakin tsoho kasim kuma sautin na muryar mace ne. Al amarin daya matukar bata mamaki ke nan domin ita a saninta ai tsoho kasim ne aciki wannan daki to mene neya shigar da mace cikin dakinsa ? Cikin fargaba da sanda ta Nassey dey talk koma izuwa kofar dakinta leka ta cikin kafar kubar ai kuwa tana lekawa ta hango zabgegiyar kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance zaune akan kujera tana faman sharba kuka a gefe daya daya ga wadannan tufafi na tsoho kasim ajiye a gefe daya wadannda akansu an dora layu da guraye na tsafi humaira ta kurawa fuskar budurwa idanu kawai sai ta lura da idanunta taga iri daya ne sak! Dana dabira. Koda ganin wannan al amari sai zuciyar humaira ta buga da karfi ta dafe kirjinta da hannayenta biyu ta juya baya cikin ajiyar numfashi tace a ranta. ” Duk yadda aka yi wannan yata ce ussainar dabira tazo mana a cikin kamannin tsoho kasim mene ya kawota garin nan ? Shin tazo neta cutardamu ko kuwa ta gano cewa mu jininta ne ta zo domin mu sadu ? ”
Nan fa humaira ta kasa baiwa kanta amsar wadannan tambayoyi cikin tsananin fargaba da tashin hankali humaira ta koma dabaya don ta koma turakarta. Lokacin da ya rage saaura kiris ! Ta iske kofar turakarta sai kawai taga dabira tsulum ! A gabanta kamar daga sama ake jefota kafin humaira ta budi baki tace wani abu sai dabira ta dubeta tace. Yake ummata menene ya kaiki dakin bakonmu tsoho kasim ? Ki sani cewa nida sarki duk bamu yarda da tsoho kasim Ba kuma na fuskanci cewar akwai wata alaka tsakaninki da shi. Da shi saboda haka gobe kafin na bar garin nan zaki yi mini cikekken bayani akan rayuwarki kafin ki baro birnin kisra ki da dawo nan misra da wannan kalami nake miki sallama allah ya tashe mu lafiya ” koda gama fadin ™Nasiru Muhammad™hakan sai dabira tajuya ta koma izuwa cikin dakinta tamai da kofa ta rufe nan fa humaira ta sake rudewa ta kidime ta rasa abin da ke mata dadi a duniya domin bata san bayanin daya kamata ta yiwa dabira da sarki ba a goben. Da kyar humaira ta koma cikin dakinta ta kwanta taci gaba da tunani da zullumi. Har aka yi assalatu bata sami damar yin barciba. Kamar yadda humaira ta kasa barci hak shima sarki raihan ya kasa barci saboda tsananin damuwa har yaje masallaci da asuba. Ya dawo turakarsa bai rintsaba. Itama dabira bata rintsa ba wato dai duk su ukun basu yi barciba amma wani ikon allah ita jaruma yazila batasan saadda barci yasace taba daf da lokacin daza ayi sallar asuba. Lokacin da aka idar da sallah a masallaci sarki ya waiga ko ina bai ga tsoho kasim ba sai jikinsa ya sake bashi lallai akwai wani boyayyen al amari a kansa don haka sarki na baro masallaci sai ya tura aka kirawo dabira yace da ita ta tafi izuwa dakin bako tsoho kasim ta fada dakin cikin shammace taga a halin da yake ciki domin baizo masallaci sallar asubaba lallai akwai wani abu na shin gaskiya a tare da shi. Domin tun da ya garin babu wanda ya ga yayi sallah koda jin wannan batu sai dabira tatafi izuwa dakin tsoho kasim a fusace wadansu dakarunta guda biyu na biye da ita. Tana sanye da hularta ta karfe.
Da zuwan kofar dakin tsoho kasim sai tasa kafarta guda ta daki kofar. Take kofar ta burma ciki ta fadi kasa. Karar dukan kofar na yasa yazila ta farka firgigit! Kafin tayi wani yunkuri sai kawai taga jaruma dabira tare da dakartunta biyu tsaye akanta rike da makamai koda su dabira sukayi arba da yazila sai suka cika da tsananin mamaki. Gashi dai agefe daya kuma suka ga wannan tsufaffun kayan tsoho kasim ga layu da gurayen tsafi akansu sai al'amarin ya daure musu kai.
Nan fa Dabira ta kurawa yazila ido tana tunani a zuciyarta. Abinda ya fadomata a rai shine, tasan fuskar yazila tun da sun gwabza yaki ba sau dayaba, amma ™Nasiru Muhammad™bata taba yimata kallon kurilla ba sai yau. Tabbas dai yanzu ta gane cewa abokiyar gabarta ce tayi bad-da-kama ta shigo birninsu domin ta cutar dasu. Amma kuma me yasa a bokiyar gabar tata take kama da ita? Anya kuwa yazila ba ita ce 'yar uwarta ba? Ai waka abakin mai ita tafi dadi,bari naji daga bakinta.
Nan take dabira ta dubi yazila tace, "wace ce ke, kuma meyasa kika batar da kamanninki kika shigo birninmu?".
Koda jin wannan tambaya sai yazila ta bushe da dariya tace, "Nice jaruma Yazila babbar abokiyar gabarki! Kuma na shigo wannan birnin naku ne domin kawai nayi yakin karshe dake mu bambance tsakanin aya da tsakuwa!!!".
Da jinhaka sai itama Dabira ta bushe da dariya sannan ta hade rai tace, "ke tsohuwar abokiyar gaba kiyi sani sani cewa kinka wo kanki GIDAN MUTUWA! Lallai bazamu kashekiba da azaba ko taron dangi ba, lallai nida ke zamu raba raini a yau dinnan. A matsayin ki na mai laifi, dole ne yanzu nasa a kamaki akaiki kurkuku a tsare ki inyaso yau da farkon yamma yammaci afito dake izuwa filin fada inda zamu fafata yakin karshe ni dake inda za arufe mu a cikin keji har sai dayanmu ya wanda duk ya rayu sai ya bude kejin ya fito. " Nassey dey talk
Koda gama fadin hakan sai dabira ta dubi dakarunta dake tare da ita tace dasu su sawa Yazila ankwa sannan su tafi da ita kurkuku,
Bisa mamaki sai dabira taga yazila ta tsaya kyam! Ansa mata ankwa a hannayenta da kafafunta batare da tayi wani yunkuriba sai murmushi kawai take har aka tusa keyarta a gaba aka tafi da ita. Al'amarin daya matukar jefata cikin tsananin mamaki kenan da wasi-wasi domin a sanin dabira yazila jarumace ta gaske ko ita kanta ™Nasiru Muhammad™ bata isa tasa mata ankwa ba cikin sauki, amma sai gashi dakarunta sunsa mata ankwar sun tafi da ita.
Abin dabata saniba shine yazila tana sane ta saki jiki aka kamata saboda dalili uku. Dalili na farko shine tana son su fafata yaki domin dabira ta cire mata wannan laya dake wuyanta dalili na biyu shine tanason takai dabira kas har ta cire wannan hular karfe ta kanta domin taga kamanninta dalili na uku shine bata son dabira tace zata bita sutafi izuwa birnin kisra don daukar fansa akan sarki daksur shiyasa taki gayamata cewa ita yar uwartace ta jini
Bayan an tafi da yazila izuwa kurkuku sai dabira ta tattara wadansu layu da guru na tsafi ta kunna musu wuta nan take suka kune kurmus ! Suka zama toka. Har tajuya zata fita daga cikin dakin sai taga jakar guzurin yazila a rataye ajikin bango kai tsaye ta nufi inda jakar take zata dauko ta duba abin dake ciki sai kawai taji an kira sunanta. Tana waigowa sai taga ashe sarki raihan ne a tsaye da kansa. Sarki raihan ya dubeta fuskarsa babu walwala yace " yanzu kin daina fushi damu zaki iya sauraron bayanin dazan yimiki ?” Koda jin haka sai idanun dabira suka ciko da kwalla. Tace. ” Ka gafarceni yakai abbana. Kayi sani cewa nima nayi nadamar nuna muku fishina. Ina fatan zaku gafarceni ? ” Koda jin wannan batu sai sarki raihan yayi murmushi yace. ” Babu komai yake. Yata yanzu dai kizo muje fada akwai wani gagarumin abu daya taso wanda zamu zauna mu tattauna tare da sauran yan majalista hukuncin da kika yanke yanzu akan wannan abokiyar gaba tamu dataso ta yaudaremu yayi kyau ”.
Koda jin haka sai dabira ta taho wajen sarki raihan ta ruke hannunsa suka jera suka fice daga cikin dakin ya zamana cewa gaba daya ta manta da batun wannan jaka ta yazila. ™Nasiru Muhammad™
Ita dai wannan jaka babu komai a cikinta face wadansu kayayyakin tarihi wadanda da zarar humaira tayi arba zata shaidasu. Domin kaya nena yar uwarta nuzaira wanda ayanzu haka tana da irinsu aajiye kuma kullum sai ta kallesu don tunowa da yar uwarta ta. Banda wadanda kayan tarihi kuma. Akwai rigarda aka sawa yazila aranda aka haifeta kuma dabira ma tana da irin rigar wacce har yanzu humaira nanan da ita aajiye don tarihi. Dabira ta sha ganin humaira tana dauko rigar tana kallenta kawai har tana kwallah amma duk saadda ta tambayeta dalili sai tace da ita kawai ta tuno wahalar data sha ne a lokacin data sami cikinta saadda ta haifeta. Lokacin da sarki raihan da jaruma dabira suka iso fada sai suka iske gaba dayan yan majalistar a zaune. Suna jiran karasowarsu al amarin daya razana dabira kenan domin ta san cewa duk saadda taga yan majilista sunyi irin wannan taro ya zamana cewa kowa ya zo to lallai akwai wani abu gagarumi al amari daya taso. Ko dai annoba ta barko. Ko kuma yaki zaayi.
Da shigowar dabira da sarki cikin fadar sai suka je suka zauna inda suka saba zama. Zaman su keda wuya sai wazirin sarki Raihan yayi kyaran murya sannan yace, "yaku 'yan majalissar wannan birni namu mai albarka, da yawa daga cikinku sun san dalilin taruwarmu anan. Ga wadanda basu saniba, yanzu sai su sani.
Wannan al'amari ba komai bane face a yau dinnan kimanin sa'a daya data shude mun sami rahoton cewar abokan gabarmu mutanen birnin kisra sun taho da zugasama da dakaru miliyan dari hudu da hamsin domin su yakemu.
Wannan zuga ta hada da dakarun gudummawa daga sauran kasashen kafirai na wannan nashiya, kuma sun taho da alwashin cewa wannan karo adan za a shekara ana wannan yaki bazasu janyeba har sai sun tabbatar da cewa sun baje birnin mu sun kashe mazajenmu sun kama matayenmu da yaranmu a matsayin bayi sun kwashe dukkan dukiyoyinmu. ™Nasiru Muhammad™
Ku sani cewa adadin wadannan dakarun abokan gaba ya ninka namu sau goma, wato gaba dayanmu bamu wuce kaso daya ba a cikin kaso gomansu ba. Yanzu menene abinyi? Tabbas idan muka ce zamu fita mu tari waddannan abokan gaba za su iya murkushemu a cikin dakika kadan. "
Sa'adda waziri yazo nan a jawabinsa sai Jaruma Dabira ta mike tsaye zumbur! A fusace, kuma ta zare takobinta a lokacin da jikinta ya kama tsuma. Cikin fushi ta dubi waziri tace, "yakai waziri kayi sani cewa bamu da wani karfi wanda yawuce karfin allah katuna cewa bayau ne karo na farko da muke fita yaki da abokan gaba da kuma ya zamana sun fimu yawa, amma sai kaga mun yi RAGAS dasu kokuma musami nasara akansu. Duk bawan da yayarda da allah kuma ya sallama al'amuransa a gareshi tabbas allah zai iya masa abinda ya gagareshi. Ina tabbatar muku da cewa koda abokan gaba yawansu ya kai cikin duniyar nan gaba daya idan ni kadai ce na rage musulma a wannan birni na rantse da girman Allah sai na fita na yakesu dan kare martabar addinin allah koda kuwa zasuyi gutsin-gutsin da sassan jikina. Na sani nan dagobe wadannan abokan gaba zasu iso kofar birninmu don haka zan jagoranci dakarunmu mufita mu yakesu wanda duk yake ganin zai bi bayana yabi, wanda ba zai bi ba yayi zamansa!".
Koda dabira tazonan azancenta sai sarki Raihan ya zare takobinsa yace, "Ina bayanki ya ke 'yata, lallai dani za ayi wannan yaki gobe!".Nassey dey talk
Koda ganin haka sai fiye da rabin 'yan majalissar ma suka yi abinda sarki raihan yayi. Kalilanne daga cikinsu basu yi hakan ba, domin sun gama tsorata da wannan yaki daza ayi, kuma imaninsu ya raunata.
Wannan shine a binda ya faru a fadar sarki raihan bayan 'yan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login