Showing 3001 words to 6000 words out of 28742 words

Chapter 2 - Jaruma Yazila book Complete by Abdul'aziz Sani Madakin Gini

sarki daksur wannan al'amarin domin mu dauki matakin gaggawa saboda nayi mamakin yadda abokin gabarmu ya shigo har cikin kasarmu ya sace min mata batare da munsaniba yake matata ki sani yau shekara goma dayin auranmu amma bamu taba samun haihuwaba sai yanzu lallai acikin farin ciki nake mara misal tuwa dan haka yanzu da ganan birnin kisra zamu wuce nanunawa sarki wannan kyakykyawar 'ya" dakika haifa mini kuma na gaya masa maganar makiyammu Sarki raihan koda gama fadin haka sai barzuk ya shiga cikin keken dokin ya zauna kusa da nuzaira sannan daya daga cikin yaransa ya hau gaban keken dokin ya fara sarrafa dawakan aka cigaba da tafiya aka nufi hanyar da ta nufi birnin sin.
Tunda aka fara wannan tafiya zuciyar nuzaira ta fara bugawa da karfi domin ta tabbatar da cewa da zarar sun isa gaban sarki Daksar asirinta ya tonu bisa karyar data shirgawa mijinta cewa yaran sarki raihanne suka saceta domin shi sarki Daksur ka sur gumin ma tsafine wanda ka iya ganin duk abinda yafaru tun gabannin su isa fadar tasa har aka iso cikin kisra hankalin Nuzaira atashe yake bata da sukuni al'amarin dayasa barzuk ya dubeta kenan yace yake matata lafiya naga kamar kina cikin damuwa? Tunda muka fara wannan tafiya bakice uffanba kuma babu walwala da annu shuwa afuskarki koda jin haka sai nuzaira tayi murmushi tace yakai mijina kasani cewa ban taba shiga fadar sarki Daksur ba da girmanaba saboda tun ina yarinya wata rana sa'adda mahaifina ya je dani naga an sare kan wani mutun a gabana saina firgita ainun na tsandara ihu tun daga wannan rana kullun sai nayi mafarkin wannan abu ina firgita acikin barcina saida ma haifina yanaimi taimako awajen bokansa sannan na daina wannan mugun mafarki yanzu dakace zamu fadar sarki daksur sai mafarkin ya fadomin arai saboda haka nidai bana son shiga fadar sarki Daksur ka samomin masauki agari kafin mu isa fadar. Sa'adda Nuzaira tazo nan azancenta sai barzuk ya bushe dadariya yace kadaki damu yake matata lallai bazanje fadar sarki batare dake.
Kamar yadda barzuk yayi alkawari haka abin ya kasance wato da shigarsu birnin kisra sai ya kai nuzaira cikin wani kasaitaccen gida irin na sarakai wanda ke dauke da komai na jin dadin duniya harda barori da kuyangu masu hidima. Al'amarin daya matukar bata mamaki kenan domin bata ga lokacin da aka biya kudin hayar gidan ba kuma da zuwansu kofar gidan ta ga masu gadin gidan sun tsube kasa sun kwashi gaisuwa har nuzaira ta bude baki zata tambaye shi batun wannan gida sai yace saboda me zakiyi mamakin mallakar wannan gida agareni ? Shin kin manta ina daya daga cikin makusan tan sarki? Nuzaira tayi murmushi ta ce bana mamakin mallakar wannan gida agareka amma ina mamakin dalilin da ya hana ka sanar dani labarinsa Barzuk yayi murmushi yace so nake na shammace kine nabaki mamaki kinga kenan zamu tare a sabon gida nuzaira tace yanzu idan katare anan birnin ya zakayi da wakilcin sarki a kauyen Himsarul Aswad? Barzuk yayi dariya yace aiba tarewa zanyi ananba kece dai zaki tare a cikin birnin nan domin na fison 'yarmu tataso da wayewa ta zama cikakkiyar 'yar birni mai wayewar kai in yaso duk karshen mako nazo nata fi daku tare ku biyun.
Bayan barzuk ya nunawa Nuzaira bangarenta a cikin wannan gida harta shiga ciki ta kwanta tana hutawa kuyangi suka fara mata shidima sai barzuk yayi shiri ya tafi izuwa fadar sarki daksur.
Fadace kasaitacciya wadda aka kawatata da kayan alatu iri iri tamkar aljannar duniya sarki daksur na zaune bisa wata kerarriyar kara gar mulki ta ka saita fadawa sun kewaye shi a tsakiyar fadar ga wasu tsala tsalan 'yammata sai tikar rawa suke cikin mummunar shiga mai baiyana tsaraicinsu.
A kaida duk sa'adda sarki ke kallon wadannan 'yammata yayin da suke tikar rawa yana dariya da murmushi amma a yau sai sarki ya turbune fuska babu annuri atare da shi ko kadan kuma tun da ya fito fadar haka ya ka sance cikin rahin walwala da sukuni kallo daya mutum zai masa yasan yana cikin tsananin bacin rai.
Al amarin daya matukar dugun zuma hankalin fadawa kenan domin sun sancewa fushin sarki ba karamin tashin hankali bane agaresu gaba daya. Ana cikin wannan haline akaga hakimi barzuk ya shigo fadar cikin farinciki kamar wanda aka yiwa albishir din mulkin duniya cikin sauri har da hardewa barzuk ya isa gaban sarki Daksur ya zube kasa ya kwashi gaisuwa ya dago kai domin yayiwa sarki bayanin abin farin cikin da ya sameshi sai sarki yayi farat ya tashi tsaye kawai sai ya dubi barzuk yace kabiyoni izuwa cikin dakin gani ina son magana dakai a sirrance. Koda gama fadin haka sai sarki Daksur yanu fi dakin gani nanfa Barzuk ya bishi da sauri aka bar fadawa da jama'ar gari a zazzaune sun yi tsurutsuru da idanuwansu suna mamakin abin da ke faruwa. Yayin da sarki Daksur da Barzuk suka shiga dakin gani sai sarki ya tsaya a tsaye maimakon ya zauna ya juyo suka fuskanci juna shida Barzuk yace kazone kayi mini aibishir bisa cewa matarka ta haifi "ya" mace koba hakaba? Cikin muryar rawar murya burzak yace hakane ya shugabana Daksur yace tokasani kasani wannan "ya" data haifa ba "yar ka bace "yar" dan uwanka ce Hukairu amma ita matarka "da" na miji ta haifa kuma a mace yazo duniya hakika matarka ta yaudareka kuma karya ta shiryama domin ka jaddada magana ta yanzu zan nuna maka duk abubuwan da suka faru azahiri. Kagani da idanuwanka. Gama fadin hakan ke da wuya sai sarki yayi nuni da hannunsa izuwa ga jikin bango take hoton al'amarin suka rinka gudana tun lokacin da Nuzaira tayiwa 'yar uwarta Humaira alkawarin cewa lallai awajenta zata haihu har lokacin da aka bata jariri yarnan koda ganin wannan al'amari sai barzuk ya kwarara uban ihu cikin tsananin bakin ciki jikinsa gaba daya ya kama tsuma ka wai sai ya zare ta kofi ya juya da nufin yaje ya sare kan Nuzaira amma sai sarki daksur ya daka masa tsawa ya tsaya cak ya juya ya durkusa bisa guiwowinsa a gaban sarki daksur ya mayar ka takofinsa bisa kubenta ya sunkuyar da kansa kasa alokacin da hawayen takaici yake zubo masa yace ya shugabana yanzu me ya kamata nayi? Sarki daksur yayi ajiyar numfashi sannan yace ya kai Barzuk kayi sani bisa bin ciken da nayi idan muka ka bar matarka da wannan "ya da aka bata wannan fari da annoba da muke fama dasu a gari zasu kare nan da sati biyu kacal gari zaiyi lafiya amma inda masifar take shine wannan jaririyar da matarka ta zo da ita idan har ta girma zama gawurtacciyar jaruma kuma mayakiya fiye da sarkin yakinmu sadauki Hauzar bin Mausus duk yakin da muka taro sai ta sami nasara amma fa duk sanda ta san sirrin tsafina mun banu mun lalace sai mulkimmu ya rushe. Kuma sai talakawanmu sun zama shugabanninmu sun dauki fansar zaluncin da muka dade muna yi musu tsawan shekara da shekaru ta han ya daya ce ka dai zamubi kada azo da ita fadata kada abari tayi arba da fuskata kuma kada ka nunawa matarka bacin ranka koka gaya mata abin da muka tattauna anan yanzu.
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani

***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {1}
TYPE D
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
====================================
A can daji kuwa inda manomi hukairu yayi gidansa sun wayi garine a cikin farin ciki da bakin ciki dalili farincinsu shine na haihuwa da humaira tayi nayaya tagwaye mata duk da cewa tayi kyautar bayar guda ga 'yar uwarta nuzaira shi kuwa mummuna mafarkin wanda himaira tayi a jiya da daddare da safe sa adda humaira ta farka daga bacci ta fara bawa mijinta hukairu labarin mafarkinda tayi a jiya al amari daya matukar dugunzuma humaira duk hankalinsa kenan dalili kuwa shine a iya saninsa da matarsa humaira duk abin datayi mafarkinsa saiya tabbata a gaske. Bawani abu humaira ta ganiba acikin mafarki ba face saukar wadansu dakaru kamar daga sama wadanda suka bukawa gidan wuta ya kone kurmus babu abin da ya tsira. Lokacin da hukairu yaji labarin mafarkin da humaira tayi sai hankalinsa ya dugunzuma ainun rasa abin dake masa dadiya shiga tunani mai zurfi daga can saiya dubi ita humaira yace yake matata kinsani cewa wajibine a garemu muyi hijra mubar gabadaya yankin wannan kasa tamu idan har muna son mu da abin damuka haifa mutsirada rayuwarmu naji ajikina cewa sarki daksar kasurgumin matsafine don haka na tabbatar da cewa abinda ya faru tsaka nimmu da 'yar uwarki nuzaira ya gani kuma ya nunawa barzuk bisa wannan da lilinne za su turo a hallakamu lokaci yayi da zan gaya miki wani sirri wanda bantaba gaya mikiba. Tun muna yara nida dan uwana barzuk bokan ma haifina wanda muka sami sirrikan tsafi a wajensa yace mana cewa agaba daya kasar nan babu wani mahaluki mai karfin sihirinmu face sarki daksar amma duk 'yar da muka haifa idan tayi arba da idan sarki daksar to zata samu duk irin sihirin da sarki daksar yake da shi a cikin kwana uku harta samu nasarar Hallaka shi ta hau kan karagarsa face ya kasheta kafin cikar kwana uku shi kansa sarki daksar ya san da wannan sirri don haka bazai taba barin abun da muka haifa arayeba dun haka ba zai barmuba yazama wajibi muyi shirin gaggawa yanzu muyi hijira mukara gaba. Sa adda hukairu yazo nan azancensa sai humaira ta ce yanzu ina kake tsammanin zamu shiga mu buya ba tare da sarki daksar yaturo an kashemuba Hukairu yace waje daya ne zamu iya zuwa muyi rayu wa acan kuma mu tsira daga sharrin sarki daksar da dan uwana Barzuk. Bawani waje bane face birnin misra inda sarki Raiyan ke mulki. " Koda jin haka sai idanun Humaira suka zazzaro tace "ya ya za ayi muje birnin misra kuma muyi rayuwa alhalin mutanen can sun kasance musulmai mukuma ma abota tsafine da gunki?
Humaira tace "shin ka manta ne sarki daksur bashi da wani makiyi wan da yafi sarki Raiyan na birnin misra? Ai idan sarki raiyan ya fashinci cewa mu mutanen birnin kisra ne sai yasa anyi mana kisan gilla domin ya dauki fansar ran 'yar uwarsa gimbiya Numaira wacce sarki daksur ya ka she yayin da aka fafata kazamin yaki da su a shekaru uku baya. "
Hukairu yayi ajiyar numfashi sannan yace "duk nasan da wannan al'amari amma abinda nake so ki fahimta shi ne abinda ya koro bera yafada cikin wuta ya fi wutar zafi. " Koda gama fadin haka sai hukairu ya mike tsaye yakama hada kayyayyakinsu domin suyi hijira. Bayan ya gama hada hada komai a waje guda ya dora a kan rakumansa wasu kuma akan shanunsa sai yaje tsakiyar filin gidan ya haka rami sai ga shi ya tuno wata laya. Nan take ya rataya layar a wuyansa, sannan yakira Humaira ta fito da ga cikin daki goye da jaririyarta. Ba tare da bata lokaciba suka hau kan rakumansu biyu sukayi gaba suna janye dabbobinsu. Koda hukairu ya juya ya dubi gonarsa da wannan gida nasa sai idanunsa suka cikoda kwalla saboda takaicin ya tafiya bar kasa mai albarkar noma wadda abu ne mawuyaci ya sake samun irinta.
Bayan kamar sa a hudu da tafiyar hukairu da matarsa humaira sai ga sarkin yaki haizar bin mausus bisa doki tare da dakaru dari biyar suna take masa baya dukkaninsa dauke da muggan makaman yaki tun daga nesa haizar ya dauko wani gilashi na sihiri wanda sarki daksur ya bashi ya ce da shi da wannan gilashi ne kadai zai iya hango gidan hukairu. Haizur yasa gilashin a kan idanunsa amma bai hango komaiba dan haka sai suka kara kaimin gudu bisa da wakansu. Jim kadan da faruwar haka sai suka hango gidan daga can nesa. Daya daga cikin daka runnasane ma ya fara hangowa ya nuna masa al'amarin daya matukar ba shi.mamaki kuma yaba shi tsoro ya fara tunanin duk yadda a kayi su Hukairu basa gidan kuma lallai ya tone wannan laya wacce sarki daksur ya bashi labarin cewa hukairu ya binneta a tsakiyar gidansa. Tun da ga inda suka hango gidan Haizar yabada umarnin a fara harba kibiyar wuta izuwa gidan. Ai kuwa cikin kan kanin lokaci gidan gaba daya ya kama ya kama da wuta yana ci balbal. Su sarkin yaki haizar suka karqso gaban gidan aguje bisa dawakansu suka yiwa gidan kawanya kuma suka dana kwari bisa baka suna jira suga wani abu mairai yayi fitar burgu don ceton ransa su harbeshi amma hargidan yagama konewa kurmus yazama toka ko kyanwa basu ganiba. A sannanne sarkin yaki haizar ya sakko daga dokinsa ya duba tsakiyar gidan nan take kuwa yayi arba da wannan rami wanda hukairu tone ya cire layarsa ta sihiri. Cikin tsananin ta kaici da fushi haizar ya kwarara ihu sannan ya dakko mudubin tsafinsa ya shafeshi sau uku yana mai karanta wadansu dalasiman tsafi guda uku. Faruwar hakan keda wuya sai ga fuskar sarki daksur ta bayyana akan madubin suka dubi juna. Kafin haizar ya budi baki yace wani abu sai sarki daksur ya tari numfashinsa yace "maza ku ruga gaba domin tuni Hukairu da matarsa sunyi nisa, taza rarku da su ta kai nisan sa'a hudu. Idan kuka yi sakaci suka shiga yankin kasar misra shi ke nan baza ku taba riskar suba. Tun da hukairu na tare da wannan laya baza ku taba ganin koda sawunsuba amma i dan kayi amfani da wannan gilashin sihiri da na baka zaka i yaganin sawayensu. Idan har kana son kariskesu sai kunyi ta fiyar kwana uku bayada zango babu barci. Idan har kasami nasarar cika wannan aiki kana dawo wa birnin kisra zanbaka wazircina kuma zanbaka dukiya ninkin goman abin da ka mallaka a yanzu. Koda gama wannan jawabi sai fuskar sarki daksur ta bace bat, daga cikin madubin sarkin yaki haizar nan take yaji farin ciki ya lullubeshi dan haka sai yaruga kan dokinsa yayi tsalle ya haye kan dokin ya zabure shi cikin matsanancin gudu koda ganin haka sai suma ragowar dakarun suka sakarwa dawakansu linzami suka rufa masa baya.
Tun dasu sarkin yaki haizar suka cigaba da wannan tafiya basu tsaya ba har rana ta fadi, gari yasoma duhu. A wannan lokacinne yunwa da kishirwa ta suka fara addabarsu. Sai da ta kai suna ta fiya da wakansu suna sassarfa domin suma sun gaji dokin haizar ne ka wai bai gaji ba saboda shi ba doki bane na gaskiya, dokine na sihiri. A duk sa'adda daya daga cikin dakarun yayi yun kurin tsaya wa don ya huta kodan ya nemi ruwan sha sai haizar ya da ka masa tsawa ya shiga taitayinsa, idan kwa yaki bin umarni nan take haizar zai zare takobi yasare kansa nan take bisa dole suka hakura suka hakura suka ci gaba da tafiyar a hankan bayan kwana daya ne dakarun suka rinka yanke jiki suna fadowa daga kan dawakansu matattu saboda tsananin yunwa da kishirwa sakamakon basu taho da isasshen gazuri ba masu tsananin juriya da taurinri ai ne suka kai kwana na uku amma suma alfijir na ketowa suka fadi kasa matattu ya rage saura sarki haizar shi kadai bisa dokinsa shi kansa in badon yana tsafiba ya sami ruwansha da tuni ya mutu saboda azababben zafi ranar da ake yi ga shi dazuzzukan da suke ratsawa gabadayan su saharane ko bishiya daya mutum ba zai gani ba. Lokacin da rana ta take ne haizar hango su hukairu a can gabansa tazarar da bata wuce taku dari biyar ba tsakaninsu sun doshi kofar birnins misra koda ganin haka sai haizar ya zare takofinsa yasa karwa dokin sihirinsa linzami ya zabureshi cikin masifaffen gudu. Su hukairu na cikin tafiya sai suka jiyo sukukuwar doki a bayansu. A firgice suka juyo hango wanda ke kokarin kawo musu hari cikin hanza hukairu yazare takobinsa ya tsaida rakuminsa sannan ya dubi humaira ya ce maza ki ruga bakin kofar binin misra ni kuwa zantsaya na tari wannan mahayi da ya durfafomu. Ba wanibane.face sarkin yaki haizar lallai sarki daksur ne yaturoshi ya hallakani. Koda jin wannan batu sai humai tafa she da kuka ta ce ni kam bazan tafiba na barka sai dai mutafi tare. Cikin tsananin fushi hukairu ya dakawa ya dakawa humaira tsawa ya ce idan ban tsaya ba na tareshi zai cimmanane ya hallakamu gaba daya har jaririyar dake goye a bayanki. Fatana shine ke da jaririya kutsira da rayuwarku ai ni nagama cika burina kunda har na kawo kunan bakin birninmu da na misra. " Koda jin wannan batu sai humaira ta zaburi rakuminta da gudu tanufi bakin kofar birnin misra, a wannan lokacin baifi taku arba'in ba haizar ya iso gaban hukairu Hukairu ya juya yayiwa Humaira kallon kar she cikin guntun murmushi, a lokacin da kalla ta cika idanunsa. Wai gawar da zaiyi haka sai yaga sarkin yaki haizar dab da shi har ya kawo masa wawan sara da nufin ya sare masa kai. Cikin zafin nama hukairu ya sunkuya ta kobin haizar ta sari iska shima ya zare takobinsa suka fara a zababben yaki. Nanfa suka fara kai wa juna sara da suka cikin tsananin zafinnama, juriya da bajimta ya zamana cewa dayansu ya kasa cutar da dayan al'amarin da ya matukar baiwa sarkin yaki zaihar mamaki kenan domin bai taba sanin cewa HUkairu jarumine haka ba.
Lokacin da ake wannan mugun artabu
tsakanin Hukairu da Zaihar tuni humaira
ta isa bakin kofar birnin misra amma sai
ta ja linzamin rakumin ta ta tsaya cak ta
kasa shiga birnin ta juyo cikin tashin hankali tana kallon gumurzun da akeyi
tsakanin mijinta da sadauki zaihar.
Lokacin da sadauki zaihar yaga wankin
hula zai kai shi dare sai ya fusata ya fara
amfani da karfin sihiri domin ya hallaka
hukairu amma sai ya ga ashe shima hukairu ba kyalle bane abangaren tsafi
domin karfi ya zo daya. Haizar yaja da
baya yaduru daga kan dokinsa ya tsaya
cak a waje daya yana tunanin dabarar da
ya kamata yayi. Koda ganin haka sai
shima hukairu ya duro daga kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login