Showing 9001 words to 12000 words out of 28742 words

Chapter 4 - Jaruma Yazila book Complete by Abdul'aziz Sani Madakin Gini

tun da basu sankiba kema baki sansuba. Shekara goma sha takwas ai ba kwana goma sha takwasbane. Na tabbata yanzu 'yar uwata Humaira ta tsufa, kamar yadda nima na tsufa, ta yaya zata shaidaki alhalin rabonta da ke tun kina jaririya?".
Lokacin da nuzaira ta zo nan a zancenta sai yazila ta mike tsaye ta kama kai kawo sannan ta tsaya cak ! Ta dubi nuzaira tace, "yake ummina ki sani cewa dan uwa-dan uwane, har abada idan ka hada jini da mutum sai kaga wani abu ya zamo iri daya da nasa bare kuma ni da 'yar uwata mun kasance tagwaye ai dole ne asami kama ni da ita kamar yadda kika bani labari cewa tamkar an tsaga kara muke. "
Nuzaira tayi ajiyar zuciya sannan tace, "nidai na umarceki da kada ki kuskura kice zaki ce zakiyi wannan ta fiya izuwa birnin misra kuma ina mai gargadinki da kada ki kuskura kice zaki je kiyiwa sarkin yaki zaihar wani abu, domin kina tabashi mijina da sarki daksur zasu gane cewa na sanar dake sirrin rayuwarki don haka komai zai iyafaruwa a gareni. Yake yazila ki tuna cewa nice na shayar dake harkika girma kika zama mutum, ki tuna nice naci kashinki, na sha fitsarinki, kuma nice na sha wahalar renunki idan kika bari su sarki daksur suka cutar dani lallai kinci amanata kuma kinci amanar zumuncin dake tsakanina da mahaifiyarki."
Koda gama wannan jawabi sai nuzaira tayi shiru bata kara cewa komai ba , sannan ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin ta bar jaruma yazila a zaune cikin tsananin damuwa, gami da tunani mai zurfi.
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani

***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {2}
TYPE B
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
====================================
Haka dai yazila taci gaba da sake-sake acikin zuciyarta ta kulla wancan ta kwance wancen har dare yaraba ya zamana taka sayin barci sai kai kawo kawai takeyi acikin dakin nata tana zarya.
Bayan tayi dogon nazari da tunani akan abinda zai fishsheta sai taje ta dakko takadda da alkalami ta rubuta wata wasika ta ajiye a karkashin matashin kanta sannan ta cire kayan jikinta ta sanya wadansu bakaken sulke na yaki ta dauki makamanta na yaki ta soke a jikinta nan take tayi girgiza bace bata bayyana ako ina ba sai a kofar gidan sarkin yaki zaihar da baiyanarta sai taga masu gadi a tsaitsaye suna kan aikinsu kai tsaye jaruma yazila ta durfafosu koda masu gadin suka hangota sai suka cika da tsananin mamaki bisa ganinta a cikin wannan lokaci na tsawon dare cikin ladabi da biyayya masu gadin suka risina suka gaisheta yazila ta dubeshi a fusace tace kubude mini kofa da salama na shiga domin naga mai gidanku idan kuma kuka yi gardama yanzun nan takobina zata sha jininku !“.
Koda jin wannan batu sai jikin masu gadin ya kama karkarwa cikin firgita sukayi sauri suka bude mata kofar ta kunna kai ciki da shigar yazila cikin gidan sai tazare takobinta taci gaba da kutsa kai tana leka cikin dakunan gidan domin taga inda sarkin yaki zaihar yake. Karar zare takobin yazila daga cikin kubbenta ne yasa sadauki zaihar ya bude idanunsa alokacin da yake kwance tare da matarsa acikin turakarsa dama bai dade da kwanciya ba bisa bata lokaci da yayi wajen bincike a hallarar tsafinsa. A cikin binciken da yayi ya ga wata gagarumar masifa dake shirin afko masa amma sai ya kasa gane irin masifar da kuma lokacin dazata zo masa abin da ya saya kasa barci ke nan ya kwanta kawai yana tunani cikin fargaba. Koda zaihar yaji karar zare wannan takobi sai yayi wuf ya mike daga kan gadonsa yayi sauri yasanya kayan yakinsa sannan ya zare tasa takobin ya fita waje yana neman wanda ya shigo masa gida cikin wannan tsohon dare. Nassey dey Talk
Lokacin da jaruma yazila ta shigo cikin wani katon falo na gidan wanda babu komai acikinsa face shimfidar jan kilishi mai taushi da kujeru na alfarma sai tayi kicibus ! Da sarki yaki zaihar tsaye ruke da takobi a wannan lokaci falon a haskake yake dahasken fitilu tazarar dake tsakanin zaihar da yazila bata wuce taku asirin ba.
Koda zaihar ya ga ashe yazila ce ta shigo masa gida acikin wannan dare sai ya cika da tsananin mamaki kuma yaji ajikinsa cewa lallai ba lafiya ba akwai wani abin daya faru da dai dai ba saboda haka saiya tsaya a inda yake ya dubeta yace yake halifata mene ne ya kawoki gidana a wannan dare?“ Yazila ta dubi zaihar a fusace tace ,“ nazo na dauki fansar mahaifina dakakashe ne ya kai babban azzalumi !“
Cikin matukar mamaki zaihar ya dakawa yazila tsawa yace ,” wannan kuma wacce irin maganar banza kikeyi ? Shin ke ba yar mai girma barzuk bace ? Yaza ayi kice na kashe mahaifinki alhalin barzuk na nan araye ?”.
Dajin haka sai hawaye ya zubowa yazila tace ”
Kayi tunani izuwa shekaru goma sha takwas baya lokacin da kabi bayan hukairu dan uwan barzuk sa adda ya gudu tare da iyalinsa izuwa birnin misra daf da kofar birnin misra kuka fafata yaki kai da matarsa humaira tan goye da jaririyarta to ka sani cewa wannan jaririr yar uwata ce mun kasance tagwaye nida ita kuma hukairu ne ya haifemu ita kuwa nuzaira abin data haifa mutuwa yayi sai humaira taba ta daya daga cikin tagyayen data haifa kuma ni ce jaririyar da aka bata kagake nan hukairu shine mahaifina ba barzuk ? Lallai mahaifina ka kashe , babu makawa sai na dauki fansa a kanka kuma a yanzu ”. Nassey dey talk
Sa adda yazila tazo nan a zancenta sai sarkin yaki zaihar ya bushe da mahaukaciyar dariya. Ya ce ” yake yarinya karyarki tasha karya. Ba a zama wane a banza. Kafin na sami wannan matsayi na sarkin yakin birnin kisra sai dana taka mukamai masu daraja da yawa kuma sai dana sha bakar wahala. Duk abin da kike takama da shi a yanzu na mallakeshi tun kafin kizo duniya saboda haka yanzu ga fili ga mai doki idan kina ganin zaki iya daukar fansar mahaifinki ki jarraba ki gani ina tabbatar miki da cewa kamar yadda na kashe mahaifinki haka kema zanka sheki !”.
Kafin zaihar ya gama wannan jawabi tuni zuciyar yazila ta fara tafarfasa kawai sai ta daga takobinta sama ta ruga gareshi shima sai ya daga tasa sama ya rugo gareta suna haduwa kowanne su ya kaiwa dan uwansa mugun sara kowannensu ya kare saran da takobinsa da takobinsa tara tsatsin wuta ya fantsama izuwa kas. Nan fa suka rugunzume da azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta.
Wohoho ! Idan sabon hannu da tsohon hannu akahadu a gumurzu dolene aga tsagwaran jarumta t ban al'ajabi. Ita yazila tana ta kama da kuruciya gami da sadaukan taka ta zamani shikuwa zaihar yana ta kama da kwarewa da sanin makama ne. Da dabarun yaki irin na tsofaffin sadaukai inda aka sami babban bambanci shine, ita yazila tafi zaihar juriya da dadewa ana gumurzu, shi kuma yafi ta zafin nama.
Sai da aka shafe rabin sa'a ana wannan gumurzu dayansu bai sami na sarar komai ba, ya zamana cewa dauki ba dadin da sukeyi yasa gaba daya hadiman gidan sun rugo izuwa falon da suke fafatawa a dimauce. Itama matar zaihar saita farka daga bacci a firgice ta ruga izuwa dakin da danta ke barci, wani karamin yaro dan shekara hudu kawai, saita sungumi yaron a kirjinta taruga izuwa falon da ake gumurzu tsakanin yazila da zaihar.
Dazuwa sai ta iskesu cikin masifaffen artabu. Gaba daya hadiman gidan sun ra kabe a tsorace suna kallon abin dake faruwa. Nan fa itama matar zaihar ta kasa yin komai saita tsaya ka wai tana kallon fafatawar cikin tsananin tsoro da fargaba da mamaki bisa ganin wacce ke gumurzu da mijinta. Nassey dey talk
Saboda zafin naman zaihar sai ya shammaci yazila ya yanketa acinya. Kafin tayi wani yunkuri ya sake yankarta a damtsen hannunta na hagu. Bisa dole yazila tayi alkafira da baya ta koma nesa kadan da shi ta durkushe kasa bisa guiwowinta a lokacin da ta dafe raunikan jikinta biyu cikin jin zugi da radadi.
Koda taga jini na zuba saita fusata ainun kuma tayi sauri. Ta daure raunikan da wani tsumma dake daure a kugunta. Ka wai sai ta mike tsaye ta sake zare wata takobin a kuibin cinyarta ta hagu ya zamana cewa ta hada takubba biyu ahannunta.
Koda ganin haka sai shima zaihar yaciro wani gatari dake rataye a bayansa ya hada da takobin hannunsa ya fuskanceta. Kawai sai yazila ta rugo gareshi suka sake kacamewa da sabon azababben yaki amma awannan karon sai yazila ta sauya salon fadan ya zamana cewa tana tsalle tana alkafira a kasa da sama. Nan da nan kuwa ta ruda zaihar, bai ankara ba sai yaji ta dankara masa sara acinyarsa. Take wajen ya dare jini yayi tsartuwa. Zaihar ya rankwala uban ihu yatafi da baya taga-taga ya fadi
Koda matar zaihar taga abinnda aka yiwa mijinta zaihar sai itama tarusa ihu ta fashe da kuka. Yazila ta kara rugowa da gudu izuwa kan zaihar ta ci gaba da kaimai sara da suka cikin iya zafin namanta bata yarda ta bashi damar da zai daure raunin nasaba. Nan fa jini ya cigaba da zuba daga cinyar zaihar har jiri yafara dibarsa amma saboda naci da juriya irinta 'YAN MAZAN JIYA sai yaci gaba da yakin a haka. Ya yin da zai har ya fuskanci cewa idan akaci gaba da wannan gumurzun a haka har izuwa wani lokaci mai tsawo zai iya gala baita yafadi saka makon jinin dake zuba a kafarsa sabo da haka sai ya fara amfani da karfin sihirinsa yana watsawa yazila mugayen abubuwa kamar; masu, wuta, kibiyoyi da sauransu. Bisa mamaki sai Nassey dey talk yaga tsafin baya tasiri ajikinta, domin karfin sihirin nasu yazo daya duk abin da ya watsa mata sai itama ta watso masa irinsu sulalata juna. Al'amarin daya dugunzuma hankalin zaihar kenan ya tabbatar da cewa bashi da wata mafita face yayi amfani da iyakar karfin dmtsensa da kwarewarsa ta yaki. Bisa dole yakara ZAGE DAMTSE suka cigaba da bakin gumurzun, yazamana cewa sun tashi hankalin komai da kowa dake cikin falon.(Ni ma dakyar na rakabe a ani lungu) Sai da suka shafe sa'a biyu suna wannan gumurzu ya zamana cewa kowannensu yasake samun nasarar yiwa abokin gwaminsa rauni. Zaihar ya sami nasarar saranta a kirji, ita kuma ta sami nasarar sokarsa agefen kirjinsa na dama alokaci guda duk subiyun suka kwala ihu suka ja da baya taga taga kamar zasu fadi amma sai suka sake rugowa suka kacame da a zababben yaki.
Hakika idan mutun ya ga irin wannan juriya, naci da jarumta irin ta zaihar da yazila dolene ya jinjina musu ya tabbatar da cewa sun cika zaratan sadauki ababan misali. Bayan sun dada kwarmazuwa bisa hadawa da naushi da bugun juna sai suka jigata ainun ya zamana cewa da kyarma suke kaiwa juna hari.
Duk wannan abu dake faruwa matar zaihar na rakabe a gefe daya rungume da danta ta na kallongumurzu cikin tashin hankali kuma tana kuka.
A na cikin wannan fafatawar ne duk su biyun sukA yiwa juna wani irin mugun naushi a fuskokinsu har jini yai tsartuwa bakunansu suka zube kasa kafin yazila tamike tsaye sai zaihar yayi sauri ya zaro wata wuka siririya mai kaifi da atsini ya wurgawa yazila wukar ta tafi tsananin gudu zata cake ta cafi wukar ta maida ita inda aka jehota nan take tsinin wukar ya lume acikin goshin zaihar nan take zaihar ya sulale kasa matacce koda ganin abin daya faru sai matar zaihar ta kwala ihu ta rugo kan gawar mijinta ta ajiye danta a gefe daya ta rungume gawar tana kuka sauran hadiman gidan kuwa sai suka firgice suka kama guje guje suna ficewa daga cikin gidan gaba daya jaruma yazila ta taka kafafunta da kyar ta nufi inda matar zaihar take koda ganin haka sai matar zaihar ta dago kai ta dubeta ba tare da tsoron komai ba tace.” Yake dirkar birnin kisra ma zaki kasaro ki kasheni ni da dana domin na huta da wannan abin takaicin da kika bar mini ban ga amfanin rayuwarmu a duniya tun da kin yanke mana farin cikin rabamuda masoyinmu. ”.
Yazila tayi shiru bata ce komai ba har ta iso kan gawar zaihar kawai saitasa hannunta ta zare wannan wukar wacce ta lumamai acikin goshin zaihar sannan ta dubi matarsa a lokacin da hawaye ya zubo mata. Tace ina bukatar alokacin wannan wuka domin da sonki san cewa bazan kashe kiba kuma bazawara kamar yadda uwata humaira ta zama bazawara kuma inason wannan da naki ya zama maraya kamar yadda ni da yar uwata muka zama marayu ina son ki isar da sakona ga sarki daksur cewa ni “jaruma yazila ” na kashe sarkin yaki zaihar bisa sanin cewa shi ne ya kashe mahaifina na gaskiya bisa umarninsa don haka ya saurari ranar Nassey dey talk da zanzo daukar fansa a kansa ki sanar dashi cewa na san sirrin layar da suka rataya mini a wuya tun ina jaririya kuma na tafi inda za ayi cire mini layar koda gama wannan furuci sai jaruma yazila ya goge jinin dake jikin wannan wukar daga jikinsa ta daura a kugunta kawai sai ta juya ta fite daga cikin gidana tana tafe tana tangadi ita kuwa matar zaihar sai ta bita da kallo kawai cikin tsananin mamaki bisa jin abubuwa data zaiyano mata a matsayin sako sarki daksur.
* * *
Al'amarin hadiman gidan zaihar kuwa, dasu da masu gadin gidan Bayan yazila ta sami nasarar kashe maigidansu Sai suka ruga da gudu izuwa gidan sarki daksur suka isar da labarin abinda ya faru ga man yan hadiman gidan. Ai kuwa acikin wannan dare labari ya riski sarki Daksur. Cikin tsananin firgici da dimauta sarki daksur yamike zumbur yayi shigar yaki ya jagoranci dakaru dubu a shirin da kansa acikin dare suka bazama neman jaruma yazila acikin birnin kisra amma sai da suka duba ko ina basu gantaba.
Shikuwa hakimi barzuk yajin labarin abin da yafaru sai ya ruga izuwa dakin yazila a fusace rike da takobi. Da shigarsa cikin dakin sai ya iske matarsa nuzaira atsaye rike da wasika tana karantawa tana zubar da hawaye cikin fushi barzuk ya fisge takardar ya karanta jawabin dake cikinta kamar haka.
YAke ummata ki gafarceni bisa abinda zan aikata. Kiyi sani cewa bani da wani zabi face na aikata hakan kuma ki gayawa mijinki da sarki daksur abinda ya faru da sarkin yaki zaihar suma yananan tafe garesu nan da wani lokaci a ko yaushe kuma ina gargadinsu akan idan suka taba lafiyarki nima saina taba lafiyar dukkanin danginsu, sai na tabbatar da cewa na share dukkanin zuri'arsu daga doron kasa. Idan har sun matsu. Da son ganina su nemeni acan birnin misra..........."
Koda barzuk yazo nan akara tun Nassey dey talk wasikar sai zuciyarsa ta kama ta farfasa kamar zata kone. Saboda tsananin fushi da bakin ciki ka wai sai yasa hannu ya fyade nuzaira ta fadi kasa sumammiya. Nan take ya kwalawa wasu hadi mansa kira yace su dauki nuzaira su kaita can babban kurkuku na kasar suce asamata sarka atsareta har sai ranar daya nemeta. Nan take kuwa wadannan hadiman suka cika wannan umarni. Bayan hadiman sun tafi da nuzaira sai yafita da sauri ya hau dokinsa yatafi gidan sarki da zuwansa kuwa ya iske sarki daksur ya dawo daga neman gimbiya yazila bai gantaba. Yana zaune a fada shi kadai cikin tsananin fushi tamkar zai kona gidan sarauta gaba daya barzuk ya zube kasa gaban sarki daksur ya sunkui da kansa kas cikin tsananin ladabi alokacin da gaba daya jikinsa ke karkarwa don tsoro kada fushin sarki ya kare a kansa
Bazato ba tsammani sai barzuk ya bushe da ma haukaci yar dariya. Al'amarin daya matukar bashi mamaki ke nan ya dago kai a tsorace yana kallonsa.
Sarki daksur ya turbune fuska sannan yace , "hakika matarka taso ta watsa mana dukkan shirimmu ta tona mana asiri bisa sakacinka na kula da sa ido akanta. Hakika in ba don kayi mata hukunci ba da kanka kasa ankaita kurkuku da tuni kai da ita duk nayi muku hukuncin kisa. Bisa bincike da nayi a halin yanzu na gano cewa tuni jaruma yazila tayi nisa da barin wannan birnin wannan kasa tamu saura tafiyar kwana daya da yini daya jal ! Ta isa kofar birnin misra. Jaruma yazila tana da matukar karfin sihirin tsafi don haka bani da wa dansu hadiman aljanu da zan turasu su hallakata kafin ta isa cikin birnin misra. A cikin binciken da na yi na gano cewa idan ta shiga cikin birnin misra bazata sami nasarar samun abinda taje nemaba. Kuma zata sha tsananin wahala wacce zata iya zama sanadin ajalinta. A kwai wani lokaci da zaizo muyi yakin karshe da sarki raihan na birnin misra a wannan yaki ne zamu sami nasara akansa mukama birnin nasa gaba daya a sannanne zamu shiga har cikin birnin mukama yazila da mahaifiyarta humaira sannan mu binciko duk inda 'yar uwarta take dabira itama mu hallakata. "
Sa'adda sarki daksur yazo nan azancenta sai farin ciki ya lullube barzuk bai san sa'adda ya bushe da dariyar murnaba. Nan fa duk su biyun suka ci gaba da kyakyata dariyar kamar bazasu dainaba.
A dai-dai lokacinne matar zaihar ta shigo cikin fadar ita kadai rungume da danta tana zubar da hawaye. Batare da fargabar komaiba ta iso har gaban sarki Daksur ta risina ta kwashi gaisuwa sannan ta zaiyana musu sakon da jaruma yazila tabata.
Koda matar zaihar ta gama jawabi sai jikin sarki daksur ya kama tsuma. Nan da nan zufa ta karyo masa. Zuciyarsa ta kama bugawa da karfi kamar zata fado kasa cikin tsananin zafin nama ya zare ta kobinsa ya fille kan matar zaihar ta saki dan dake Nassey dey talk hannunta ya cafeshi da hannu daya. Gangar. Jikin matar zaihar ya sulale kasa alokacin da dan nata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login