Showing 15001 words to 18000 words out of 28742 words

Chapter 6 - Jaruma Yazila book Complete by Abdul'aziz Sani Madakin Gini

jerawa tare da tsoho kasim suka bi hanyar komawa birnin misra sauran tawagar na rufamusu baya
Haka dai akaci gaba da tafiyar inda hira karde tsakanin Dabira da tsoho kasim inda taringa tambayarsa tarihin rayuwarsa dakuma irin gwagwar mayar da yasha a rayuwarsa a cikin daji bisa wannan sana'a ta farauta.
Koda jin wannan tambaya sai tsoho yai tashara karya kala-kala haryana ta bayani irin gumurzun da yayi da manyan dabbobin daji yana samun nasarar kashesu.
Kodajin wadannan labarai sai mamaki yakama jaruma dabira ta dubi tsoho kasim taga babu alamar sadaukan taka atare tashi saita aiyana aranta cewa duk yadda akai wannan tsoho da kuri Nassey ke magana yakeyi kawai donhaka sai tace aranta, "Nikuwa in allah ya yarda sai na kure wannan tsoho na gwada iyakar jarumtakarsa na gani lokacin da yarage saura tafiya kadan a iso kofar birnin misra sai jaruma Dabira ta sake nausawa cikin wani dajin daban al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan daya daga cikin dakarun dabira yadubeta yace "ranki yadade meyasa kika komar damu cikin daji alhalin gashi farautar tayi kyau munsamo abinda muka fito nema, koma kinsani cewa wannan daji dakika shiga damu dajine mai hadarin gaske wanda ke dauke da mugayen dabbobi?"™Nasiru Muhammad™
Koda jin wannnan tambaya sai dabira tayi murmushi ta dubi mai tambayar tace , tace """ai gani nayi mun fito bamu sha wahalar komai ba mun sami tsun tsaye ai yana da kyau mu dan motsa jini?".
Dajin haka sai hankalin sauran dakarun ya dugunzuma domin sunsan halin dabira idan tace tana son motsa jini dai-dai yake data ce tana son tayi yaki.
Shikuwa tsoho kasim ko gezau baiyi ba sai kawai yakara kaimi ya wuce kan gaba ma a cikin dajin. Al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan har ita kanta dabira kuwa tce a ranta "yanzu shi wannan bushashshen tsohon gani yake zai iya wani abu kenan ? To ai inda bakasa anan ake gardamar kokawa. Zamuga iya kar koka rinsa
Abinda ya kara baiwa su dabira mamaki shine tsoho kasim ya sakarwa dokinsa kaimi ya zabureshi da gudu ba tare da shakkar komaiba
Kwatsam! Sai gasu sun iso tsakiyar wani babban fili dazuwa sai suka ga wadansu manyan kuraye ayari guda akan bishiya. Tsoho kasim ne yafara farga da dabbobin don haka sai yaja linzamin dokinsa yayi turjiya ya daga hannu yana mai yiwa su dabira nuni da su tsaya.
Nan take kowa yaja tunga ya tsaya. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin kuraye da tsoho kasim
Kurayen sun kasance manya-manya masu matukar kwarjini da ban tsoro sai Nassey dey talk gurnnani suke yi suna wangame baki gami da dalalar da yawu kamar suci babu. Kai dagani kasan cewa yunwa sukeji kamar suci babu. Nanfa kuraye suka fara motsa jikinsu alamar cewa akoyaushe zasu iya daka tsalle su fado kan kasim
Tsoho kasim ne yafara zare™Nasiru Muhammad™ takobinsa daga cikin kube. Sannan sauran sauran dakarun dabira ma suka zare tasu takobbinsu itakuwa dabira komotsi bata yiba daga kan dokinta sai murmushi take yi kawai tana kallon kasim da dakarunta alamar cewa tayarda da kanta su takeji.
Koda kuraye sukaga su tsoho kasim sun zare takubbansu sai suka dako tsalle gaba dayansu alokaci guda asama suka fado kansu aka rugun tsume da a zababben yaki. Sai gashi kuraye sun jeho yaran Dabira daga kan dawakansu su duka kuma suka turmushe su suna kokarin cinyesu. In badamma dakarun sun kasance zakakuran gaskeba da farad daya kura yen zasu gama dasu. Nan fa akacigaba da bakin artabu ya zamana cewa kuraye sunfara yiwa dakarun Dabira rauni suna kartar jikinsu da faratan hannayensu da kafafunsu kuma suna kai musu cizo suna kaucewa da bugun bakunansu da takobi.
Al'amarin tsoho kaasim kuwa, abin al'ajabin da yake yine yasa Dabira takasa motsawa daga inda take ta kaiwa dakarunta dauki kawai sai tabude baki tana kallonsa cikin tsananin mamaki.
Tunda kurayen suka afkawa su tsoho sai yazama kamar shaidani a tsakiyarsu ya dinga ra gargazarsu da takofinsa yana kaftara musu sara yana tarwa tsasu suna faduwa kasa, amma saboda naci da taurinkai irin na kurayen saikaga suna dada tasowa suna afkawa tsoho kasim duk da cewa jikinsa yai fata fata da jini. Nan dai tsoho kasim shika dai ya zamewa kuraye alakakai alokacin da suka gallabi sauran dakarun Dabira.
Yayinda kuraye. Suka ga tsoho kasim yana yi musu muguwar barna sai duk suka bar da karun dabira suka yiwa tsoho kasim rubdugu Nassey dey talk gaba dayansu suka lullubeshi. Da yake sarkin yawa yafi sarkin karfi sai nan da nan kuraye suka fara ruda tsoho kasim saboda suna kai masa muggan hare-hare ta kowane bangare. Inbadan ma yana yana da tsananin zafin namaba da tuni sun ya galgala shi. A nan cikin wannan gumurzu ne wadansu kuraye guda uku masu mugun naci suka shammaceshi suka karci jikinsa da faratan hannayensu lokaci guda.™Nasiru Muhammad™ Daya ta dankara masa sara akirjinsa waje uku, wajen ya dare har jini yai tsartuwa daya a gadon baya taimasa saran iri daya dana kirjin nasa, dayar kuma a cinyarsa, saboda tsananin zafi da zugin da tsoho kasim yajine ya kwala ihu kuma ya fusata ainun kawai sai yadaka wawan tsalle sama na bammamaki sannan ya sallamo kasa kafafunsa na sama kansa na kasa. A haka ya dinga gididdiga kurayen. Duk wadda yayiwa sara daya sai kaga ya fille mata kai ta fadi kasa mutacciya nan fa jinin kurayen ya dinga fantsama har yana bata jikin Dabira. Kafin ta ankara jikinta gaba daya ya rine da jini. Babbar jarumtar da tsoho kasim yayi shine tunda ya fara sare kan kurayen a sama hannunsa ko kafafunsa basu taba kasaba asaman yayi shawagi a kan kurayen tamkar tamkar tsuntsu mai fuka fukai sai da ya gama kashe kurayen gaba daya ya zamana babu guda daya mai rai sannan ne ya duro bisa kasa. A sannan ne dabira ta lura da wadansu tsofaffin manyan raunika a jikin tsoho kasim wadanda tuni sun warke abin da fara fadowa Dabira a rai shine ta yaya wannan tsoho yake irin wannan jarumta irin ta masu jini a jika wato matasa masu karancin shekaru ? Nan take taji cewa lallai akwai a yar tambaya akan tsohon.
Abu na biyu wadannan tabon data gani a jikinsa da gani kasan gumurzu yayi da wani gagarumin sadaukin da ya illatashi. Dabira ta kudurce a ranta cewa lallai sai ta tambayi tsoho kasim yadda akayi yasami wadannan raunika.
Bayan tsoho kasim ya gama Nassey dey talk kashe kurayen nan sai yaji Dabira tayima tafi gami da jinjina nan take dabira ta sakko daga kan dokinta ta taho izuwa inda tsoho kasim yake. Sai da tazo daf dashi har suna jin numfa shin juna sannan tatsaya cak tadube shi tace "ya kai wannan gwarzon jarumi kasani cewa rabon da naga jarumta irin taka tun sa'adda nayi gumurzun karshe da babbar abokiyar gabata Jaruma Yazila ta birnin kisra".™Nasiru Muhammad™
Koda jin wannan batu sai tsoho kasim yaji zuciyarsa ta buga da karfi ya tsorata ainun domin ya zata Dabira ta gano ko wanene shi. Kawai sai yaji dabira ta kyalkyale da dariya sannan tace, "ka gafarceni yakai wannan jarumin tsoho, ka sani ina sani nace a shigo wannan dajin domin na gwada iyakar jarum takarka bisa labarin daka bamu kan hanyarmu bisa irin gwagwarmayar Da kayi. Tabbas yan zu na yarda kai jarumine a bin kwatance. Amma duk da haka zan sake yimaka wata jarrabawar ta karshe wadda ina ganin asannanne zanga karshen jarumtakar taka.
Koda gama fadin han sai jaruma dabira ta bude jakarta ta guzuri ta dauko wani magani ta mikawa kasim tace, "ga wannan sai kasa a cikin raunin naka ".
Nan take kasim ya karbi maganin ya shafa a raunikan da kurayen suka jimasa. A sannanne suma dakarun dabira suka yiwa kansu magani bayan kowa ya kimtsa sai aka hau dawakai aka nufi hanyar birnin misra.
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani

***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {3}
TYPE B
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
====================================
Humaira na zaune a cikin harabar gidanta tana hutawa wadansu kuyangi hudu sun zagayeta suna tayata hira kawai sai ta hango Dabira da tsoho kasim sun taho gareta, wani bawa na rike da tsuntsayen da suka farauto. Tun daga nesa da Humaira tayi arba da idanun tsoho kasim sai taji zuciyarta tabuga da karfi. Ba komaine ya haddasa hakan ba face jida tayi a jikinta cewar kamar ta taba ganin irin idanunnan arayuwarta amma sai ta kasa tuno a inda ta taba ganinsa.
Shima tsoho kasim tun daga nesa ya kurawa Humaira idanu ko kiftawa bayayi. Koda suka iso daf kuwa sai yaji idanunsa sunkico da kwalla suna neman su zubo da hawaye. Babu shiri kasim ya ™Nasiru Muhammad™ sunkui da kansa kas.
Nan take Humaira taji kaunar tsoho kasim ta shiga zuciyarta tamkar dama can tadade da sabo dashi. Cikin fara'a Humaira ta dubi dabira tace "yake 'yata wannan kuma wanene haka kika zo mini dashi?"
Kafin dabira ta budi baki tace wani abu sai tsoho kasim ya zube kasa gaban humaira yace "Ni bakone daga birnin rum nake wannan matar sarki. Na zo gareku da salama kuma da yardar allah zan Nassey dey talk barku a cikin salama da karamci ina fatan zaku karbi bakun cina na kwanaki kadan cikin jin dadi?"
Koda jin haka sai Humaira ta sunkuya. Da sauri ta kama kafadun tsohon kasim ta tashehi tsaye a lokacin da ta sake kura masa idanu tace, "haba ya kai wannan tsoho saboda me zaka durkusa min alhalin ka haifeni a haife?"
Koda jin wannan tambaya sai idanun tsoho kasim suka sake cikowa da kwalla ya dubi Humaira yace, "ai duk inda 'ya mace take dole ne namiji ya girmamata tun da kune kuka haifemu. Duk da cewa shekaruna sunfi naki ina ganinki na tuno da ainahin mahaifiyata wadda kaddara taa rabamu".
Dajin haka sai hankalin Humaira ya dugunzuma ta kasa sakin kafadun tsoho kasim tace, "wacce kaddara ce ta rabaka da mahaifiyarka?" Sa'adda kasim yaji wannan tambaya sai hawaye ya zubo masa yace, "makiyane suka rabamu tun ina jaririya har yau har gobe bamu sake saduwaba. Babban abikin cikina shine yanzu idan ma haifiyata na nan araye ko mun sadu ba zamu shaida junaba tunda bata sanni ba nima ban santaba".
Koda Jin wannan batu sai hawaye ya zubowa Humaira tace, "ya kai wannan tsoho kayi sani jininka jininkane har abada. Ina tabbatar maka dacewa koda mahaifiyarka bata shaida kaba indai kukayi arba da juna saikun ji wani abu ajikinku, tabbas na tausaya maka matuka bisa jin labarinka domin al'amarine mai ban mamaki"".
Lokacin da HUmaira tazo nan a jawabinta sai Dabira ta cika da tsananin mamaki domin a iya rayuwarta tare da ™Nasiru Muhammad™ humaira bata taba ganin ta zubar da hawayeba sai yau. Abin daya kara daure mata kai shine Humaira ta sha jin labarai na abubuwan tausayi wadanda ma suka fina tsoho kasim amma bata yi kukaba. Menene dalilin daya sa Humaira tayi kuka a yanzu bisa jin labarin tsoho kasim?" Nassey dey talk
Tambayar da Dabira takasa bawa kanta amsa kenan. Nan dai dabira ta baiwa humaira labarin yadda ta hadu da tsoho kasim da duk abubuwan da suka faru a tsakanin su a daji. "
Koda jin haka sai humaira ta kamu da tsananin farin ciki ta sake yiwa tsoho kasim barka da zuwa sannan ta umarci wata kuyanga safina ta tafi da tsoho kasim izuwa dakinsa kuma a kai masa ruwan dumi yayi wanka gami da abinci.
Nan take kuyanga safina tatafi da tsoho kasim suka nufi bangaren da ake saukar baki. Har suka kuLe tsoho kasim bai daina waigowa ba yana kallon Humaira tamkar baya son rabuwa da ita. Kai kace 'yar uwarsa ce ta jini. Ita kanta Humaira sai taji bata son tsoho kasim yayi nesa da ita amma sai ta rasa dalilin hakan, mussamman a duk sa'adda ta dubi idanunsa wadanda take ganin cewa basu dace da shiba domin idanune irin na matasa masu karancin shekaru dabasu kai ashirin ba shi kuwa gashi ya kasance tsoho dan kimanin shekaru tamanin da doriya.
Bayan kulewar kuyanga safina da tsoho kasim sai dabira ta dubi Humaira ta Baiyana mata sakon sarki cewar yana son a dafa masa wannan tsuntsu kuma zai zo da kansa bayan magariba yaci naman tsuntsun a turakarta.
Koda jin wannan sako sai Humaira taji zuciyarta ta buga da karfi kuma ta cika da tsananin mamaki domin ita a zatonta sarki bazai taba zuwa kusa da ita ba sai bayan cikar shekaru ashirin da zuwanta birnin misra.
Cikin sanyin jiki da yake HUmaira ta dubi Dabira tace, "shi kenan zan cika wannan umarni na abbanki"™Nasiru Muhammad™
Nan take Humaira ta juya ta nufi turakarta itama dabira sai ta nufi tata turakar zuciyarta cike da tunani da wasi-wasi. Abin da yafara fadomata a rai shine wai shin menene ya kawo sauyin al'amura ne a yau tsakanin mahaifiyarta Humaira da abbanta sarki Raihan alhalin hakan bata taba faruwaba ? Anya kuwa sauyin al'amarin ba shi da nasaba da zuwan wannan bakon tsoho? Koma dai menene zan gani da idanuna kuma zan yi aiki da shawarar abbana nasa ido sosai Nassey dey talk akan wannan bakon tsoho don kada ya mamayemu ya cutar damu duk da dai yace shi musulmine, ai dole ne mu tabbatar da musuluncin nasa da kuma amanarsa.
Wannan shine abinda ya faru tsakanin jaruma Dabira da iyayenta bayan ta tsinto tsoho kasim a can bayan gari.
Al'amarin tsoho kasim kuwa lokacin da aka kaishi masaukinsa aka shigar da. Shi cikin wani daki mai kyau aka kai masa ruwan wanka kewaye kuma aka kawo masa abinci sai ya mike tsam yaje ya rufe kofar dakin yasa sakatu sannan yarufe duk tagogin dakin gaba daya suma ya samusu sakatu. Bayan ya tabbatar da cewa babu ta inda za a iya hangoshi daga waje sai yayi girgiza nan take ya rikide ya dawo izuwa ainahin siffarsa ta gaskiya, wato siffar JARUMA YAZILA. Nan take yazila ta shiga kewaye ta cire tufafin jikinta gaba daya sannan ta shiga cikin baho tayi wanka. Bayan ta fito daga wankane taje gaban madubi ta tsaya tana kallon fuskarta. Koda taga irin kyawun da allah ya bata kuma ta tuna yadda ta sauyawa kanta kamanni ta zama tsoho tukuf ta boye ainahin kamanninta ga mahaifiyarta Humaira sai ta fashe da kuka. ™Nasiru Muhammad™
Dama tun sa'adda yazila ta taho izuwa birnin misra tayi bincike a cikin tsafinta har ta gano cewa lallai mahaifiyarta na nan a raye a cikin gidan sarauta kuma duk wadda tayi mata jagora izuwa wajenta itace 'yar uwarta ta jini wadda aka haifesu tare. Bisa haka ne yazila ta gane cewar lallai Humaira ce mahaifiyarta kuma Dabira ce 'yar uwarta wadda take dokin gani. Yanzu gashi tana son taga fuskar Dabira a matsayin 'yar uwarta ba akan matsayin abokiyar gabarta ba tana son dabira ta gane cewa ita 'yar uwarta ce ta jini. Tayaya zata biya duk wa dannan bukatu a cikin kwanciyar hankali?
Sa'adda yazila tazo nan a zancenta sai ta fashe da kukan bakin ciki kuma hankalinta ya dugunzuma ainun domin ta sancewa a koda yaushe a sirinta zai iya tonuwa idan kuwa asirinta ya tonu kafin humaira da dabira su gano cewa ita jinin suce tata takare wata kila ma zata iya rasa rayuwarta a wannan lokaci.
Koda yazila ta aiyana haka a cikin zuciyata sai ta sake fashewa da matsanancin kuka.
Bayan an yi sallar isha'i sai Humaira ta caba ado sannan ta shirya kasaitaccen abinci akan teburin dake falonta wanda aka yi shi da farfesun irin wannan tsuntsayen da su dabira suka farauto a daji.
Lokacin da Humaira ta gama wannan kintsi sai ta sallami dukkan kuyanginta suka fice daga cikin turakarta gaba daya sannan ta zauna tasa wannan abinci agabanta tana kallonsa kawai a lokacin da jikinta ya kama tsuma saboda mamaki da fargabar zuwan sarki Raihan. Nassey dey talk
Tana cikin wannan hali ne taji anyi mata sallama. A razane ta amsa sallamar ta dago kai tayi arba da sarki Raihan a tsaye shima ya caba ado na kure a daka fuskarsa Cike da annuri. Nan take kamshin turaren jikinsa ya cika falon gaba daya.
Koda ganin sarki Raihan sai Humaira ta mike tsaye zumbur a lokacin da jikinta yaci gaba tsuma, yayinda ™Nasiru Muhammad™sarki raihan yaga Humaira a cikin wannan hali sai shima ya kasa bude baki yace wani abu har ya zo kusa da ita ya tsaya.
Tsawon 'yan dakiku suna tsayen dayansu baice uffan ba kuma kowannensu kansa na sunkuye suna kallon kas, sai sarki Raihan yayi gyaran murya sannan yace, "ya ke ummul Dabira shin na iya zama akan wannan kujera?".
Koda jin wannan tambaya sai Humaira ta dago kai ta dube shi cikin mamaki gami da murmushi tace, "ya shugabana ai da wannan kujera da kuma wannan dakin duk a karkashin ikonka suke. "
Koda jin haka sai sarki raihan yayi 'yar karamar dariya sannan yace, "A'a ina shakka. Na yarda cewa da wannan kujera da wannan daki a karkashin ikona suke amma banda mai dakin. Ya ke Humaira ki tuna cewa tun da kika zo garinnan tsawon shekaru goma sha takwas ban taba umartarki da wani abuba sai yau, kuma yau ne karo na biyu da muka taba kebewa tare. Kin ga kuwa ashe ke ba a karkashina ikona kike ba, kina dai karkashin alfarmata. Na san zaki yi matukar mamaki bisa ganina ayau na kawo miki ziyara har cikin turakarki, kuma bama keba hatta gaba dayan hadiman gidannan suna mamaki don gudun zargin wani abu shi yasa ban rufe kofar wannan daki ba leka bayanki ki gani".
Cikin sauri humaira taleka bayan sarki sai ta hango wadansu dakarunsa mutun biyu a tsaye suna hangen duk abin dake faruwa tsakaninta da sarki amma kuma basa iya jiyo abin da suke tattaunawa koda ganin haka sai humaira tayi murmushi sannan tace. ” Haba ya shugaba ai shi kansa shaidan ba a ko ina yake samun nasara ba na yarda da imaninka da tsoron Allah ka don haka ina da yakinin cewa babu wani mugun abu da zai shiga tsakaninmu face alkhairi yanzu sai ka zauna kaci wannan abinci wanda ka umarceni da na dafama maka ”. Koda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login