Showing 6001 words to 9000 words out of 28742 words

Chapter 3 - Jaruma Yazila book Complete by Abdul'aziz Sani Madakin Gini

rakuminsa ya gyara tsayuwa yana mai
fuskan tarsa sannan ya kyalkyale da
dariya yanuna haizar da dan ya tsa ya ce
"ya kai wannan tsohon azzalumi ba wan
azzalumai ka sani burin mai gidanka
bazai cikaba a kan iyalina domin sun tsira daga sharrinkku a yanzu tunda sun haye
iyakar kasarku. Ko a yanzu ka kashe ni
bani da na damar komai. Yayin da haizar
yaji wannan batu sai shima ya kyalkyale
da dariya sannan yace "ai kuwa yanzu
zan kasheka sannan nabi iyalinka har bakin kofar birnin misra suma na
hallakasu tun dadai sun kasa shiga cikin
birnin sun tsaya suna kallo domin suga
irin mutuwar dazakayi. "
Koda jin wannan batu sai hukairu yajuya
da sauri domin ya dubi bakin kofar birnin misra kafin ya juyo da kansa tuni Haizar
ya zaro wata wuka siririya mai kaifi da
tsini ya wurga masa take wukar ta cake
atsakiyar kirjinsa ya dur kushe bisa
guiwowinsa koda humaira ta hango
abinda ya faru da sai ta tsandara uban ihu al'amarin da ya janyo hankalin masu
gadin kofar birnin misra kenan suka rugo
waje da gudu rike da makaman yaki suda
yawa. Yayin da sarkin yaki ya hango fito
war wadannan mayaka sai ya juyo da
sauri ya ruga izuwa kan dokinsa na sihiri ya zabure shi da gudu yanufi baya. Ita
kuwa Humaira sai ta diro kasa daga kan
ra kuminta ta falfala da gudun tsiya tana
kuka izuwa inda mijinta yake durkushe.
Koda zuwanta gabansa sai ta tabashi sai
taji ya bingire kasa ko motsi baiyiba alamar cewa yamutu ba shi da rai nan fa
ta rungume gawarsa tasake fashewa da
matsanancin kuka. Tana cikin wannan
haline dakarun misra suka zo gareta suka
banbareta daga jikin gawar da karfin
tsiya suka tafi da ita izuwa cikin birnin misra tana ta iface iface da koke koke
tamkar sabuwar mahaukaciya. Wannan
shine abin da ya faru ga Humaira matar
Hukairu bayan srkin yaki ya riskesu ya
kashe hukairu, ita da jaririyar sun tsira
A can birnin kisra kuwa lokacin da hakimi barzuk ya
koma wannan gida nasa inda ya ajiye matarsa nuzaira
sai ya shaida mata duk wadannan dokoki wadanda
sarki daksur ya shimfida masa a kan jaririyar data
haifa ko da jin wadannan dokoki sai ta cika da
tsananin mamaki ta dubeshi tace to wai shin laifin me
mukayi harda sarki zai kafawa yarmu irin wadannan
dokoki masu tsauri dayawa haka?” Koda jin wannan
tambaya sai barzuk ya tumbune fuska yace ” ni kaina
bansan daliliba amma babu mamaki akwai babbar
hujja data janyo mana hakan saboda haka indai kIna
son mu tsira rayuwarmu da mutuncinmu lallai
kikiyaye wadannan dokoki ” daga wannan rana kowa
nuzaira tacigaba da renon jaririyarta da ranar suna
tazo sai aka radawa jaririya suna yazila tunda nuzaira
ta acikin wannan gida na mijinta acikin birnin kisra
batata bin hanyar gidan sarauta ba bare ma taga sarki
da idanunta bare kuma jairiyar datake raino. Tafiya
sannu sannu kwana nesa darare na wucewa kwanaki
na shudewa sai aka wayi gari yarinya yazila ta cika
shekara bakwai a duniya nan da yazila tazama
sananniya a birnin kisra saboda kasancewarta tataso
da tsananin kyau dakuma jarumantaka domin tun a
sannan tana iya daga kato komai girmansa ta
rankwalashi da kasa har sai datakai cewa ana shirya
mata gasar kokawa da mazaje majiya karfi tana zama
zakarar gasar daga nan kuma sai lamari nata kara
samun cigaba domin ta fara koyon sarrafa
takofi`mashi`kwarida baka. Duk mutumin daya fara
koya mata amfanida kayan yaki sai yaga tafi kwarewa
acikin kwanaki uku kacal. Tun da yazila ta taso taga
wata farar laya a wuyanta bata son abin da zai rabata
da layarba dare da rana har kwanciyar barci kuwa. A
takaice dai batata cire layarba kuma tana iya tuno
lokacin da mahaifiyarta hakimi barzuk ya samata layar
sa adda batafi shekara biyarba aduniya. Koda wasa
yazila batata bin hanyar gidan sarki ba kuma kojitayi
sarki zai shigo cikin gari tobazatataba fita daga cikin
gidan domin a rayuwarta babu data tsana tagani ko
taji zancensa face sarki. Abinda batasaniba shine.
Wannan laya da aka rataya mata awuya itace sanadin
dataji batason taga sarki.
Ana nan cikin wannan hali har yazila ta cika shekara
goma sha takwas. Alokacin ne kyawunta yaruda gaba
dayan jama ar birnin kisra ya zaman cewa duk inda
mutun yaje saidai yaji ana labarinta. Afagen jaruman
taka kuwa al amarin maya wuce tunanin mai tunani
domin duk sa adda aka fita yaki da mutanen birnin
misra tana ya musu mummunar barna wata jaruma
guda daya takeci mata tuwo akwarya wadda itace
sarkin yakin mutanen birnin misra a wani lokaci ita
dai yazila taji ana yiwa jarumar kirari da basadaukiya
dabira babban abin takaici a wajen yazila shine
bata taba ganin fuskar wannan abokiyar gaba tata ba
domin duk sa adda zata fito yaki tana rufe fuskarta ne
da hular karfe. Akalla yazila da dabira sun fafata
kazamin yaki kamar sau hudu amma duk sa adda suka
hadu.kare jini biri jini sukeyi. Koda rauni suka yiwa
juna sai kaga raunin yazo adadi daya baya gotawa
sukansu suna matukar mamakin wannan al amari
babu irin kokarin da yazila batayi ba don ganin ta cire
hular karfen datake dabira taga fuskarta amma abu ya
gagara.
Akwai.wata rana da yazila ta tambayi bokanta wanda
ake kira mushrid bin affan tace dashi yakai abin
dogarona yaza ayina sami nasara akan abokiyar gabata
basadaukiya dabira na kai kasa kuma har na cire
hular karfen dake kanta naga fuskarta ?”
Koda jin wannan tambaya sai boka mushrid ya
kyalkyale da dariya sannan yace ” idan har kina son ki
sami wannan nasara sai dai ki cire wannan laya dake
wuyanki kije har cikin fadar sarki daksur ku yi arba da
juna in dai kikayi haka sai kin nasara akan jaruma
dabira har kiyi mata rauni sama da adadin wanda
zatayi miki. Kuma ki kaita kasa ki cire hular karfen
dake kanta kiga fuskarta amma ki sani cewa ranar da
wannan abu ya faru zaki shiga tashin hankali irin wanda baki tabaga
shigarsa ba”
Koda jin wannan babu sai jaruma yazila tasa hannunta
ta kama wannan farar laya dake wuyanta da nufin ta
cireta amma sai ta ji kamar an soka mata allura guda
dubu a sassan jikinta. Ba shiri ta saki layar ta kama
ihu kuma ta fadi kasa a matukar galabaice tana haki
kamar wadda aka yi yunkuri zare ruhinta. Nan ta jike sharkaf
da gumi da kyar ta dago da kanta ta dabi boka
mushrid tace ” me yasa na kasa cire wannan laya daga
wuyana kuma taya ya zan iya rabuwa da ita ?”
*WACCE AMSA BOKA MUSHRID ZAI BAIWA JARUMA
YAZILA?
*YAUSHENE JARUMA YAZILA ZATA YI ARBA DA
FUSKAR SARKI DAKSUR?
*YAYA AKAYI BASADAUKIYA DABIRA TAZAMO SARKIN
YAKIN BIRNIN MISRA?
SHIN ITAMA TA ZAMA MUSULMA CE?
*INA LABARIN MAHAIFIYARTA HUMAIRA?
*SHIN NUZAIRA DA HUMAIRA ZASU SAKE GANIN
JUNA?
MUHADU A JARUMA YAZILA NA BIYU DON
JINCIGABAN WANNAN LABARI.
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani
-----------------------------------------------------------------

***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {2}
TYPE A
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
====================================
Lokacin da jaruma yazila ta tambayi boka musrid bn Affan dalilin da ya sa takasa cire wannan laya daga wuyanta da kuma yadda zata iya rabuwa da ita sai ya yi ajiyar nunfashi sannan yai shiru ya sunkui da kansa kasa cikin halin tunani tsawon lokaci mai tsawo yana tunani baice komaiba daga can sai ya dago kai ya dubeta cikin tsananin damuwa sannan yace ya ke jarumar jarumai ki yi sani cewa yau kin tambayeni babban al amari wanda yafi karfina domin idan na ce zan matsa bincike bisa wannan al amari zan iya rasa rayuwata. Ita dai wannan laya ta wuyanki tun kina jaririya mahaifinki Barzuk ya sanyata a wuyanki kuma duk ranar da kika sami damar cireta a ranar ne zaki san wani babban sirri dangane dake kanki da kuma mahaifinki da sarki daksur har kiyi arba dashi in kuwa kika yi arba da shi duk irin sihirin tsafin da yake da shi sai kin sameshi. Ina tabbatar miki da cewa duk duniya a halin yanzu babu wanda zai iya cire maki wannan laya face abokiyar gabarki dabira ta birnin misra. Sa'adda boka mushrid yazo nan a zancensa sai jaruma yazila ta cika da tsananin mamaki kuma zuciyarta tayi bakikkirin ta dubi boka mushrid ta ce, "yanzu ashe ke Nan akwai wani babban sirri dangane da rayuwata wanda mahaifiyata da mahaifina suka boye mini?"
Boka mushrid yace kwarai kuwa akwai wannan sirri kuma kada kiga Laifinsu domin sanar dake bazai haifar da komaiba face tsananin tashin hankali agareki baki daya.
Koda jin haka sai hawaye ya zubowa jaruma yazila tace, "Ai kuwa a yau dinnan sai na tambayi mahaifiyata wannan al'amari ko menene zai faru kuma zan yi shiri na tafi birnin misra wajen abokiyar gabata jaruma dabira domin na san dabarar dazan yi tacire min wannan sarka bare bata saniba. "
Cikin firgici boka mushrib ya kama kafadun jaruma yazila yace, "yake jarumar jarumai, kiyi sani cewa abinda kike shirin yi tamkar ki aza gammo ne a kanki kice zaki dauki duniyar nan gabaki daya ina mai shawartar ki da ki hakura dayin wannan abu domin a karshe allura ce zata tono garma."
Koda jin haka sai yazila ta mike tsaye zumbur! A fusace tace, "ya kai wannan amintaccen bokana kayi sani cewa babu wani abu da ya isa yahanani yin waddannan abubuwa guda biyu face mutuwa kuma yanzu_Yanzu zan tafi na fara gabatar dasu ." Koda gama fadin haka sai yazila ta juya ta fice daga daga gidan boka mushrib tana isa kofar gidansu tayi kicibis da boka mushrib tsaye gabanta fuskarsa a murtuke babu annuri.
Mushrid ya dubi yazila yace, "bazan barki kije ki
ai'watar da wannan al'amariba domin nifa zaki jefani
cikin masifa da bala'i".
Yazila tayi murmushi sannan tace, "kayi sani cewa dan
zaki ya girma banga ta yadda zaka iya hananiba, idan
kuma kana ganin zaka iya toka jarraba".
Gama fadin hakan ke da wuya sai ta yun kura da nufin
ta wuce ta gabansa. Take mushrid yayi nuni da
hannunsa izuwa gareta sai wata irin murtukekiyar
sarkar tsafi ta kanannadeta tun daga kan kafafunta har
zuwa kanta ta daureta tamau, idanunta da fuskarta ka
dai ake gani. Yazila ta girgiza jikinta don ta tsinke
sarkar amma ta kasa kwancewa. Koda ganin haka sai
boka mushrid ya bushe da dariyar mugunta yace "kika
ce dan zaki yagirma kodai dan kyanwane?" Yazila ta
kyalkyale da dariya sannan ta ce, tabbas dan zakine
wannan ba dan kyanwa bane. "
Kafin boka mushrid ya kara cewa wani abu sai yazila
ta ambaci wata kalma daya daga cikin da lasiman tsafi.
Nan take wannan sarkar tsafi ta narke tazama ruwa.
Kafin boka mushrid ya yi wani yun kuri tuni yazila ta
fincikoshi da hannu daya tayi hajijiya da shi a sama ta
fyada shi da kasa kuma tatake masa wuya da kafadaya
ya fara kakarin mutuwa.
Yazila ta dauke kafarta guda daga kan boka mushrid
tacce, "kaci albarkacin kyautatawar da kayimin abaya
da yanzu zan kasheka. Kasani cewa dokata ta
farko akan kowa itace, ba ayimini dole, kuma idan
nabada umarni ba a ketare shi daga yau idan ka sake
saba wannan doka zan kau da batun mutunci dake
tsakaninmu na yi maka hukunci dai-dai da laifinka. "
Koda gama fadin haka sai jaruma yazila tayi girgiza ta
bace bat ! Tamkar bata taba wanzuwaba a wajen.
Al'amarin daya matukar baiwa boka mushrid mamaki
kenan ya bita da kallo ka wai zuciyarsa cike da wasa-
wasi yana mai cewa, "yaya akai yazila ta sami wannan
sihirin tsafin mai karfi haka ? Abinda bai sani ba
shine, yazila ta ziyarci manyan bokayen duniya ta
sami sirrikan tsafi da yawa. Wadan da suka finasa. "
Lokacin da jaruma yazila ta isa gida sai ta iske
mahaifiyarta nuzaira zaune a turakarta. Ko magana
yazila bata mataba sai ta wuce kai tsaye izuwa cikin
turakarta, al'amarin da ya matukar baiwa nuzaira
mamaki kenan domin a duk sa'adda yazila ta dawo
gida da gudu take shigowa turakarta, ta rungumeta
cikin farin ciki ta sumbaci goshinta.
A rayuwar jaruma yazila babu take kauna sama da
nuzaira ko kadan bata son taga abin da zai sosa mata
zuciya, haka kuma duk abin da nuzaira ta umarci
yazila tayi sai tayi shi bata taba yimata gar dama.
Bayan yazila ta shige cikin dakinta sai nuzaira ta mike
tsaye ta kira wata kuyanga mai suna rafina wacce itace
ke kula da komai na yazila ta ce da ita taje ta kawo
mata abincin yazila. Cikin mamaki rafina ta dubi
nuzaira tace , "ya shugabata ai yanzu zan je na kai
mata abincin". Nuzaira tace yau ni da kaina nake son
na kai mata"
Koda jin haka sai rafina ta juya da sauri tatafi dakin
girki ta dakko abincin yazila bisa faranti ta kawowa
nuzaira ita kuma ta karba ta tafi dakin yazila ".
Yazila na zaune bisa gefen gadon ta tayi ta gumi cikin
halin tunani mai zurfi. Ka wai sai taji anturo kofa an
shigo. Yazila ta dago kai da sauri tayi arba da ma
haifiyarta Nuzaira kawai sai ta kau da kai ga barin
kallonta ta sun kui da kanta kas. Cikin sanyin jiki
nuzaira ta matso daf daf da yazila ta ajiye farantin
abincin wani benci karami sannan ta zauna bisa wata
kujera dake fuskan tar yazila ta dafa cinyoyin yazila
tace, "yake 'yata yau kuma wanene yabata miki rai a
waje har da fushinsa zai shafeni?" Koda jin wannan
tambaya sai hawaye ya zubowa yazila ta kasa cewa
komai. Al'amarin da ya matukar razana Nuzaira kenan
ta cika da tsananin mamaki. Kawai sai yazila ta kama
hannun nuzaira ta dora akanta tace, yake mahaifiyata
ina son ki yi ran tsuwa bisa dara jar kaunar dake
tsakaninki dani ki gaya mini gaskiyar al'amarin da zan
tambayeki a yanzu. Kisani cewa idan kika gaya mini
sabanin gaskiya kuma na gano hakan anan gaba lallai
zan kashe kaina domin ban ga amfanin rayuwataba a
duniya tunda wadda na aminta da ita fiye da kowa
bata aminta daniba".
Cikin rudewa Nuzaira tace mene ya kawo duk wannan
al'amarin haka yake 'yata ? Shin wani ne yace akwai
abu dana boye miki ?" Yazila ta share hawayen i
danunta tace, "dafarko ina so n'ki gaya mini asalin
wannan layar dake wuyana da kuma dalilin da yasa
aka sakamin ita. Ina son ki gaya mini sirrin dake tare
da rayuwata da taki. Na ran tse da darajar soyayyar da
nake miki idan kika boye mini gaskiyar al'amari bazan
taba yafe miki ba "
Sa'adda Nuzaira taji wannan tambaya sai tacika da
tsananin mamaki bisa abin da ya janyo yazila tayi
mata wannan tambaya.
Nuzaira ta dubi yazila tace, "mene ne dalilin daya sa
kika yi mini wannan tambaya?"
Koda jin haka sai yazila ta kwashe labarin duk abin da
ya faru tsakanin ta da boka mushrid ta zaiyane mata.
Sa'adda nuzaira taji wannan batu sai han kalinta ya
dugunzuma ta dubi yazila tace, "yake 'yata hakika yau
kin zomini da babban al'amari don haka yana da kyau
ki bani lokaci. Isasshe nayi tunani tukunna. Yanzu dai
ina son ki kwantar da hankalinki sannan kici abincinki
inyaso nan da wani lokaci na dawo gareki muci gaba
da wannan magana".
Har nuzaira ta mike tsaye zata fita daga dakin sai
yazila taruko hannunta ta zaunar da ita alokacin da
hawaye yaci gaba da zuba akan kumatunta. Yazila tace,
"ya ke Ummina ina tabbatar miki da cewa idan baki
bani amsar tambayata a yanzu ba ba zan kara cin
abinci ba a rayuwata sai dai yunwa da kishirwa su
kasheni".
Koda jin haka.sai hankalin nuzaira ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe domin ta san halin yazila duk abin da ta ce za ta aikata bata fasawa kawai sai yaZila ta ga hawaye ya zubowa nuzaira sannan kuma ta fashe da kuka al amarin. Da ya matukar dugunzuma hankalin yazila kenan taji ta yi nadamar matsawar datayi mata a kan wannan tambaya batare da nuzaira tace komai basai tamike tsaye taje ta kulle kofar dakin sannan ta kulle tagogin dakin ta dawo daf da nuzaira ta zauna ta fara ba ta labari tun daga lokacin da hukairu da humaira suka yi hijra daga kauyen himsarul aswad suka koma can da birnin kisra suka cigaba da rayuwa kawo izuwa lokacin da nakuda ta kamata ta tafi can inda su humaira ta haifi yan mata tagyaye ta dauki daya ta bata ta dawo wajen mijinta barzuk suka koma cikin birnin kisra da zama da duk irin dokokin da sarki daksur ya kafawa jaririyar har barzuk ya kawo wannan laya aka sanyawa jaririyar a wuyanta.
Lokacin da nuzaira ta gama baiwa yazila wannan labari sai yazila ta fashe da matsanancin kuka kamar baza ta daina ba. Kuma tacika da matukar mamaki da bakin ciki da kyar da sidingoshi nuzaira ta rarrashi ta tadaina kukan sannan ta roketa akan tabar wannan magana a zuciyarta domin idan tace zata dauki wani mataki akan barzuk da sarki darkus bazata sami galababa. Yazila ta gyada kai cikin matukar takaici sannan tace yake ummata kiyi sani inda na san cewa niba yarki bace bazan tsaya nayi yaki da mutanen birnin misra ba tsawon shekaru kuma ina tabbatar miki da cewa lallai sai na sami nasarar cire wannan laya daga wuyana kuma komai dadewa sai naga bayan mijinki da sarki daksur. Domin sun kasance azzalumai kuma bara gurbi a doron kasa shin yanzu kina da labari yar uwarki humaira da yar uwata dake tare da ita ?“
Koda jin wannan tambaya sai nuzaira tayi ajiyar zuciya tace ai rabona da su tun sa adda na rabu da su a can gidansu daji amma na taba ji a bakin sarkin yakin garin nada wato sadauki zaihar cewa hukairu da humaira tare da yarsu sun gudu izuwa birnin misra amma ya bisu har ya riskesu kafin su shiga birnin har ya fafata yaki da mahaifin naki hukairu ya sami nasarar kasheshi amma bai sami damar kashe humaira da yar uwarki ba domin dakarun birnin misra ne suka yiyo kansa ya gudu ya yin da yazila taji haka sai zuciyarta ta kama tafarfasa kamar za ta kone tace yanzu sarkin yaki zaihar ne ya kashe mahaifina ?“.
Nuzaira tace tabbas haka ne babu shakka “ yazila kuwa indai mahaifiyata da yar uwata suna raye tabbas suna cikin birnin misra ni kuwa ta kowanne hali sai na shiga birnin misra na sadu da su dama ina da burin naje na sadudA jaruma dabira domin ta cire mini wannan laya dag wuyana kuma ina son muyi yakin karshe da ita domin nasami damar kaita kas har na cire hular karfen da take sawa a kanta domin naga fuskarta kin ga kenan ina da manyan bukatu har guda uku acikin birnin misra don haka zama bai kamani ba dole ne nayi shiri na tafi birnin misra".
Koda jin wannan batu sai hankalin Nuzaira ya dugun zuma ta dubi yazila cikin firgici tace, "yake 'yata kin sani cewa mutanen birnin misra sun kasance ma'abota addinin muslunci saboda haka zuwanki birninsu abu ne mai hadarin gaske da zarar sun ganki zasu hallakaki tun da kin kasance tsohuwar abokiyar gabarsu. Ki tuna cewa kin kashe musu jama'a ba adadi. A bu na biyu koda 'yar uwarki da mahaifiyarki suna nan araye yanzu kodai suna kurkuku kokumaa suma sun zama musulmai don haka baza suyi mar haban da keba tun da kun banbanta addini da yanayin rayuwa. Ke koma dai babu banbancin komai ai baza sutaba shaidakiba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login