Showing 3001 words to 6000 words out of 50321 words
Chapter 2 - AURAN BAZAWARA COMPLETE DOCUMENT BY UMMUH HAIRAN-.txt
hayewa gadon ta kwanta harda jan bargo domin tayi bacci amma Ina baccin ya gagareta kalqman Nasir ne kawai sukeyi mata kuwwa wai zai aureta bada dadewa ba kada ta duba qanqantarsa zai iyayi mata abinda namiji me forty years bazai iyaba to meye taqamarsa?……………
More comments
More typing
*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[4/22, 9:58 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
_Sayi daya a baka daya kyauta Mulkin Gargajiya da Auran Bazawara (Luwai)_
_Karku manta single section 200 ne VIP 500_
_Tura ta wannan account number_ : _0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar GTbank_
_Ko katin waya MTN ta wannan number_ : _09031307566_ _sai kiyi screenshot ki turo ta wannan WhatsApp_ _number din_ : _09013718241_
Saina jiku👌🏻
*AURAN BAZAWARA*
*(LUWAI)*
_typing_ ✍🏻
*UMMUH HAIRAN...✍🏻*
*3*
Juyi tayi ta janyo wayarta da take kan bedside drower saboda baccin neman gagararta yakeyi ta bude Datan ta saqonni suka rinqa shigowa tanabinsu da kallo har suka gama shigowa ta farabi tana dubawa a hankali wanda zataba da amsa ta bada wanda kuma zatayi ignoring nashi tayi wasunsu da yawa daga abokan karatunta sai abokan aikinta duk wani wanda ya biyota da kalmar soyayya block nashi takeyi saboda a ganinta batada lkcnta bata karbeta ba soyayyar.
Number Nasir tagani da alamun shigowar saqonsa Saida ta gama abinda takeyi sannan ta bude saqon nasa _“My Wife"_ abinda taga ya rubuta kenan a farko tayi dariya ta raini tace “ _qanina dana ya kk_ " turo mata yayi alamun ta sosa masa rai sannan yace “ _na kasa bacci kin rikitamin lissafina My Feesah sha'awarki nakeji wlh"_ tsuke fuska tayi tace “ _banason rashin kunya My Son waini sa'arka ce?"_
Tana tura masa ya sake turo mata _"aa kin girmeni a shekaru amma na fiki ta bangarori da dama saboda ni namiji ne Nafeesah wlh inasonki kuma indai numfashina yana zagayawa a jikina saina aureki saina nuna miki cewa yaroma namiji ne warning nake baki ba shawara ba kada ki qara cemin yaro mace irinki uku zan iya kwakulewa har nakaisu ga kwanciyar asibiti saboda haka ki kiyaye"_
Wani malolon baqin ciki ne ya damqi zuciyarta ta miqe zaune tace “kutmar uba ni yaronnan yake fadawa haka lallai ka girma yaron nan" bata gama tunanin ba wayarta tayi ring ta duba da sauri number sa ta kuma gani tayi sauri dagawa da nufin fara zazzaga masa bala'i yace “sheet kada kicemin komai My wife ki kwanta kiyi bacci da safe zanzo naji amsarki a gobe zanzo naji amsarki kuma a goben zanje na sanar da Abba shikuma ya sanar da Baffa dole asan me zaayi kafin tafiyata Rasha"
Tsaki tayi ta kashe wayar tayi jifa da ita ta fada bathroom ta sake sakarwa kanta ruwa tayi wanka ta fito ta kwanta tanata juyi daqyar bacci barawo ya saceta, da asuba ta tashi tayi sallah ta sake kwanciya har yanzu zuciyarta zafi takeyi kuma lamarin qanin nata yana qara bata mamaki dayake litinin ce da azumi ta tashi bata tashi daga kan gadonta ba sai bakwai tayi wanka a gurgurje tasa kayanta ta dauki wayarta ta cire kudin da Habeeb yabata jiya ta ajiye a wardrobe ta juya zata dauki wayarta taji an bude qofar an shigo.
Gabanta ya fadi lkcn da taji qamshin turarensa ta juyo a fusace ta kalleshi shima ita yake kallo ya tako gabanta ya tsaya tare da sanya hanunsa ta bayanta ya dora bakinsa a wuyanta yayi peck nata ya dago fuskarta yana qoqarin dora bakinsa a nata ta janye da sauri tare da tureshi yayi baya ya tsaya yana kallonta tundaga sama har qasa ya sauke numfashi yace “kin tashi lfy My Wife" harararsa tayi tace “kauce ka bani guri ni na wucce" tana fadin haka ta figi jakarta ta juya zata fice yayi saurin janyota ta cake tare da hankadeshi ta fice da sauri ya cije lebansa tare da lumshe idonsa yace “duk inda kikaje zaki dawo gareni"
Shima fitowa yayi daga dakin ya dawo parlour ya tarar da ita gurin Baffa suna gaisawa tana ganin fitowarsa ta tashi zata fice Baffa yace “Nafeesatu ki tsaya ga danki nan ya saukeki mana tunda ba lfy kika cika ba" wani takaici ne ya cikata ta juyo ta galla masa harara ya daga mata gira ya zo ya giftata ya wucce tare da zare key din motarta a hannunta ya fice ta jima a tsaye kafin taja qafarta ta fita ta tsaya a jikin motar tana wani huci ji takeyi kamar ta rufeshi da duka.
Murmushi yayi ya bude mata qofar ta shiga ya zagaya ya shiga ya dora hannunsa saman dogayen yatsunta yace “Baffa bai taba burgeni irin yau ba" bata bashi amsa ba ta bude system dinta ta fara dubawa bawai don tana gane komai ba sai don bazata iya jure rainin hankalin yaron ba kadan ya rage ya sanya jininta hawa haka suke tafe tafiya irinta kurame, sunyi tafiya me tsayi kafin su shiga arear da office din nasu Nafeesah yake yayi parking a parking space din ta sanya hannu zata bude qofar yayi sauri danna mata key yace “ina buqatar amsar mgn ta ta jiya Mummy na saboda nasan abinyi Allah ki daina rainani a zahiri nake yaro amma a badini ni ba yaro bane inason aure kuma na shirya yinsa a kowanne lkc daga yanzu saboda ni nasan kaina idan banyi aure yanzu ba Allah akwai matsala, ki fahimceni My Feesah qaninki Nasir yana sonki kuma zai rayu dake"
Harararsa tayi tare dayin tsaki ta sake jan murfin motar ya riqota da sauri yace “wlh kinji na rantse matsawar baki bani amsa ba saidai muyita zama anan dama Abbane ya aikeni kinga idan na koma sai nace masa naje zance ne dama da naje gaisheshi na fara yimasa hannunka me sanda" haushine yasata ture hannunsa tace “waikai wanne irin mara kunyan yarone kaine Naseer yanzu tsabar idonka babu ruwa a ciki ni kake kallo kake fadawa wadannan banzayen maganganun Naseer meyasa ka rainani ne yaushe ma ka balaga ne ko kuwa irin naka tashen balagar kenan kazo ka rinqa yimin wadannan matsiyatan kalaman meyasa Naseer meyasa..."
Kawai sai ta fashe da kuka ta buga kanta saman dashboard tace “nikam na shiga ukuna ni Nafeesah masifa daga wannan sai wannan Ya Allah ni yaushe zanyi farin ciki ne" yanda take kukan yayi mugun razana shi ba yau ya fara ganin kukanta ba amma nayau yafi kowanne daga masa hankali saboda yasan shine sanadin komai kawai don yace yanasonta ne take wannan kukan, jikinsa yayi sanyi ya bude motar ya fita da sauri tare da bude ya tsaya a kanta ta jima tana kukan shikuma ya kasa bata hqr kafin ta saki niqaf dinta ta dauki baqin glass tasa a idonta ta zuro qafafunta ta fito ta shigeshi a gurin.
Binta yayi da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a ransa aikin ma dole ta dainashi don bazai jurewa matarsa tana fita tana barinsa a gda da sassafe haka ba komawa yayi cikin motar ya jima yana tariyo kalamanta “ko kuwa irin taka tashen balagar kenan da tasa kakw zuwarmin da wadannan matsiyatan kalaman?" Sosai wannan kalma ta caki zuciyarsa ya qudurta a ransa dole ne ya nunawa Nafeesah shifa ba yaro bane cikakken namiji ne fiye ma da sauran maza yasa a ransa duk ranar data qara kiransa yaro wlh sai ya nuna Mata ya wucce tunaninta kuma saiya nuna mata tsaf zai iya cika mararta komai zurfinta saiya ritsata harma yayi mata ciki ta haihu………….
More comments
More typing
*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[4/22, 9:58 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
_Sayi daya a baka daya kyauta Mulkin Gargajiya da Auran Bazawara (Luwai)_
_Karku manta single section 200 ne VIP 500_
_Tura ta wannan account number_ : _0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar GTbank_
_Ko katin waya MTN ta wannan number_ : _09031307566_ _sai kiyi screenshot ki turo ta wannan WhatsApp_ _number din_ : _09013718241_
Saina jiku👌🏻
*AURAN BAZAWARA*
*(LUWAI)*
_typing_ ✍🏻
*UMMUH HAIRAN...✍🏻*
*4*
Key yayiwa motar ya fita daga harabar ma'aikatar ya nufi companyn Abbansa yayi abinda zaiyi ranar ko aikin kirki bai iyaba saboda gabadaya zuciyarsa babu dadi tunanin Mummynsa ne ya hanasa sukuni ga damuwar ganin yanda maganganunsa suka sanya ta dauki fushi na gaske dashi, dama yasani wannan dabi'arta ce a wannan karon duk wanda yazo Mata da mgnr soyayya tsanarsa takeyi balle kuma shi da tariga ta rainashi take masa kallon yaro gani take kamar baikai matsayin da zata iya rayuwa dashi ba.
Da wannan tunanin ya tashi ya nufi gdan babbar yayarsu Aunty Amina saboda ita kadai ce yake fara tunkara da mgn ko wacce iri ce kuma ta bashi mafita yayarsa ce ubansu daya.
******
*TUSHEN LABARI*
Alh Tahir Jafar Rano shine cikakken sunan Mahaifin Naseer wanda yake yayane a wajen Alh Hayat Jafar Rano wato mahaifin Nafeesah asalinsu mutanen Rano ne ta jihar Kano wanda harkar aiki takaisu garin Abuja Alh Tahir da Alh Hayat irin yan'uwan nanne na gani kasheni da wani baya tabajin cikinsu, matar Alh Tahir ta farko itace Hajiya Rabi'ah wadda ya aurota aure irin na ladan noma ma'ana matarsa ce ta rufin asiri tun bashi da komai take tare dashi a garinsu Rano da yaransu uku Amina itace babba sai Jamila wadda take Saace a gurin Nafeesah da sati biyu Jameelah ta girmi Nafeesah wadda itace ya ta farko a gurin Alh Hayat kasancewar shi bayan yayi auren Saida suka dauki shekara uku sannan Hajiya Juwaira ta haihu ana haka Abba Tahir ya qara aure ya auro Hajiya Nafisa bafulatanar Gombe tana zuwa babu dadewa Allah ya basu rabo ita da uwargidan suka haihu kusan lkc daya Jafar shine aka fara haifa dane a wajen Hajiya Rabi'ah wanda suke Kiransa Maje Rano saboda Saida suka tafi bikin sallah Rano acan aka haifesa bayan sun dawo da sati biyu Hajiya Nafisa ta haifo danta itama namiji Wanda ya amsa sunan Naseer lkcn Jameelah da Nafeesah sunada shekara bakwai a duniya nan fah aka rinqa daru a tsakanin yaran Jameelah take hana Nafeesah daukar Maje Rano ita kuma gata Allah ya jarabceta dason yara tun tana qarama hakan yasa ta daina zuwa gdan tanata kuka tana cewa da Hajiya Juwaira itama ta siyo mata Baby irin nasu Jameelah sosai abin yake taba zuciyar iyayenta duk da sunsan quruciya ce to lkcn da aka haifi Naseer nefa tunda taje gdan ta gansa ta tattara kayanta tabar gdan iyayenta dake kusa suke ta koma gdan Alh Tahir ta tare a dakin Hajiya Nafisa tun Hajiya Nafisa tana hanata danta tana korarta harta sake matashi kullum yana gurinta itace komai nasa tun basuyi arba'in ba ta fara daukeshi ta gudu dashi gdansu tace nasune danta ne.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya shaquwa tsananin Naseer da Nafeesah abun baa cewa komai kyakkyawan yaro me shiga rai kamar uwar goyonsa lkcn da ya fara wayo ko makaranta da aka sashi kuka ya rinqayi saida aka mayar dashi tasu Nafeesah kasancewar ita da Jameelah matakin karatunsu daya inda Aunty Amina take jss 3 sukuma suna primary 4 to da zaa sanya Jafar da Naseer play group sai aka sasu wata a kusa amma Nasir ya rinqa kuka yana cewa Mummy na wannan dalilin yasa ba arziqi Alh Tahir ya dawo dasu tasu Nafeesah shikenan aka samu lfy.
Shaquwar yaran burge kowa takeyi amma banda Hajiya Nafisa itadai batason alaqar dan nata da Nafeesah ko kadan dan dai bata Isa tayi komai bane a family din amfi qarfinta saida takai ta kawo Naseer ya tattare komai nasa daga gdan iyayensa tun yana shekara uku ya koma gdansu Nafeesah gdan nasu ma yace shifa a dakin Mummynsa zai zauna hakanan suke zaune komai nasu tare hatta bacci idan zasuyi suna manne da juna hakanan shekaru sukayita tafiya Nafeesah tana girma surorinta suna bayyana tanada 14 years Naseer yanada bakwai komai na matantakarta ya bayyana qirjinta ya fara cika amma duk da haka bata raba kanta da Naseer ba saboda kallon yaro takeyi masa har lkcn idan dakinsu daya ko an rabasu sai ya dawo kuma shi bazai kwanta a shimfida ba saida kansa yana qirjinta idan ta hanashi kuma yace “Mummy na kinsan akwai lkcn da zaki hanani kwanciya a jikinki meyasa kika sabarmin da hakan tun farko?" Idan yayi Mata wannan mgnr dole haka take qyaleshi hatta yankan farce Naseer bai iyaba komai itace takeyi masa duk sallar idan akabasu kudin kashewa sai ta karbe nasa ta bashi nata shikuma nasa ta tara masa ta siya masa kayan wasa a hakan kuma duk sallar duniya sai tayi masa dinki ko ta siya masa yan kanti.
Wannan dalilin yasa Hajiya Nafisa ta sake sakin jikinta da rainon Nafisa ga danta abubuwa da yawa idan tace masa yayi sai yace shi saiya tambayi mummy dinsa iyayensu maza sunajin dadin hadin kan yayan nasu biyar lkcn da Nafisa take SS 3 ne lkcn Baffanta ya qara aure ya auri Hajiya Zainab wadda suke kiranta da mama to dama duk wata rigima guri take samu itama Mama da tazo taga kan iyalan a hade yake haka ta zauna dasu da zuciya daya ta kama Nafeesah da Naseer ta riqe dama sauran yaran gdan kuma tun daga kan Nafeesah Allah bai qara bawa Baffa haihuwa ba.
Lkcn da sukayi candy lkcn akasa bikin Aunty Amina satinsu biyu dayin candy lkcn sunada 18 years Naseer da Jafar sunada 11 years aka fara hidimar bikin komai nasu iri daya akayi musu yammatan sunsha kyau sosai sun hadu iyakar haduwa musamman Nafeesah da kyawunta yake daukar hankalin kowa tunda aka fara bikin take haduwa da samari kala² kowa sonta yakeyi amma taqi bawa kowa fuska.
Ranar dinner ne da daddare sunyi kyau su hudun kamar aljanu Nafeesah tana riqe da hannun Son dinta inda Jameelah take rike da hannun Jafar haka suka shiga kallo ya dawo kansu sukasha hotuna sakin hannusa tayi tace “My Son tsaya Ina zuwa na manta wayata a mota kaji" riqe hannunta yayi yace “Aa mummy na ki tsaya na dauko miki" sunkuyawa tayi tayi kissing lips dinsa tace “kasan banason musu ko?" Daga mata kai yayi tace “to ka jirani" tana fadin haka ta saki hannunsa ta nufi wajen hall din da sauri tana tafe tana gyara agogonta ji tayi tayi karo da mutum tayi baya da sauri tace “Subhanallahi" dagowa tayi kawai taga wani kyakkyawan matashin saurayi fari tass dogo sosai sanye cikin blue din shadda da hula blue yayi kyau sosai shima.
Kallonta yakeyi da kyawawan fararen idanunsa da take ganin wani ruwa ruwa a ciki a hankali ta sakeja da baya tace “kayi hqr don Allah ban kula ba" ajiyar zuciya yayi yace “bakiyimin komai ba dama nazone saboda ke Nafeesah" kallonsa tayi da sauri tace “ni kuma" daga mata kai yayi yace “kin tuna ranar da wani mutum akan farin doki a gefen bolar dake bayan gidanku ya rogeki ki basa ruwan dake hannunki zaisha kika bude jakarki kika dauko gudan robar faro kika bashi?"
Daga kanta tayi ya sakeyin murmushi yace “to nine tun ranar nake bibiyarki kuma nake burin mallakarki yau burina ya cika na sameki kuma na mallakeki matsayin mata sunana Anwar..." Yana fadin haka ya dafata kawai jikinta ya dauki wata girgiza ya rikide ya zama haske ya shige jikinta ta saki wata firgitacciyar qara daidai lkcn da Naseer ya gaji da jiranta ya nufo inda yake tunanin ganinta hasken gurinne ya bashi damar hangota a gasa tanata juye² tana riqe wuyanta tana wata jijjiga, da gudu ya nufota ya fada jikinta ya qanqameta yana jijjigata yana fadin “Mummy! Mummy!! Mummy na!!! Meye ya sameki tashi Mummy ki tashi kada ki bata jikinki da qasa tashi muje mu yanka cake Mummy ki tashi don Allah ki tashiiiii" kukansa ne ya janyo hankalin mutane gurin ciki harda Mukhtar wanda yake aboki ne ga mijin Aunty Amina suka ciccibeta suka sata a mota Mukhtar nayi mata fifita Sani mijin Aunty Amina yana tuqa motar shikam Naseer kuka kawai yakeyi yana kiran “Mummy na ki tashi kada ki mutu ki barni waye da dakeki waye yayi miki fada Mummy na"
Suna zuwa gda aka hau mayar da zance kowa baisan asalin abinda yake faruwa ba kawai dai kowa cewa yakeyi yajiyo ihunta daga haka shikenan, asibiti suka kaita amma a banza har dare ya raba baa samo kanta ba kukan da Naseer yakeyi ne ya sanya masa shima wani mugun zazzabi ya rufeshi da yasa shima aka bashi nasa gadon............
More comments
More typing
*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[4/22, 9:58 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
_Sayi daya a baka daya kyauta Mulkin Gargajiya da Auran Bazawara (Luwai)_
_Karku manta single section 200 ne VIP 500_
_Tura ta wannan account number_ : _0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar GTbank_
_Ko katin waya MTN ta wannan number_ : _09031307566_ _sai kiyi screenshot ki turo ta wannan WhatsApp_ _number din_ : _09013718241_
Saina jiku👌🏻
*AURAN BAZAWARA*
*(LUWAI)*
_typing_ ✍🏻
*UMMUH HAIRAN...✍🏻*
*5*
Kwana uku tayi a asibitin batasan waye ke akanta ba sai daga bisani ta farfado shima taimakon abokin Baffanta ne da yace a gwada mata Addu'a saboda abin yafi kama da shafar aljanu aikuwa ana farawa sai gashi ta fara samun sauqi ta dawo hayyacinta, Wai ranar zo kuga murna gurin Naseer ya rinqa rungume ta yana shigewa jikinta