Showing 27001 words to 30000 words out of 50321 words

Chapter 10 - AURAN BAZAWARA COMPLETE DOCUMENT BY UMMUH HAIRAN-.txt

juya saboda kunya amma kafin ta fita yace “wai dama Hajiya My millon batada lfy baku fadamin ba jibi yanda duk tayi laushi sai amai take sheqawa amma kunje asibiti kuwa"
Kada kai tayi tace “aa saidai idan yau abin ya Sameta amma koda rana ma qlau take" gumi ya sharce yace “gsky ta jima tanajin jiki zazzabi ne sosai a jikinta" juyawa Hajiya tayi ta turo musu mama hankalinta ya tashi da ganin yanda taketa rawar sanyi ya dagata cak jikinsa na rawa suka fita yasata a mota suka nufi asibiti.
Suna zuwa akasa mata ruwa shigar ciki ke gareta ga kuma damuwa da take damun zuciyarta.












More comments
More typing








[4/22, 9:58 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_A B_*






*21*








Kallon juna sukashi shida Mama yayi wani ihu ya rungumeta yace “kingani ko kinga rabo ko Mama ciki fah Mama cikina ne a jikin My millon Allah na gde maka da qananun shekaruna ka azurtani da mata gashi harda ciki" sakin Mama yayi da tayi mutuwar tsaye saboda tsananin mamaki tanabinsa da kallon mamakin yaron “shi wannan dan abun shine har yayiwa mace ciki?"
Ta tambayi zuciyarta cikin mamaki wai Nafeesah take dauke da cikin Naseer abunda ta kasa samun da sauran mazan data aura dama ashe rabon na Naseer dinne.








Shiga yayi dakin ya tarar da ita tana bacci ya zuba mata ido yana kallonta sai yanzun ya gano hasken data qara sosai ta rame kuma murmushi yayi yace “zakiyi qiba kwananan zanyi miki kiwon da baa tabayi miki ba" qarasawa yayi gabanta ya sunkuya ya daga rigarta yayi kissing cikinta yana jin wani farin ciki a ransa, turo qofar Mama tayi yayi saurin janyewa ya tsaya sosai kallonsa Mama tayi tace “amma Naseer kayi shiru da bakinka kada ka fadi a cikin gda tunda kun kusa tarewa kasan abin mgn ba kadan gareshi ba" kallon Mama yayi yace “au Mama yanzu saboda nayiwa Mata ciki sai ayi surutu?" Ji Mama tayi kamar qasa ta tsage ta shige amma dole tayi masa bayani yanda zai gane.








Bayani tayi masa sosai har saida taga ya gamsu sannan ta qyaleshi ya fita ya siyo mata magunguna ya dawo kafinnan Feesah ta tashi tana zaune ya matsa da sauri ya riqo hannunta ta janye yayi murmushi yace “kada dana yaga kina gudun babansa fa akwai matsala kinsani ko" shareshi tayi ya zauna kusa da ita ya dauko fruit ya fara bare mata ayaba yana bata da farko qinci tayi saida taga ya hade rai yana neman fashewa sannan ta karba yana bata yana murmushi ya dauko Apple ya bata taci kadan ta kawar da kanta yace “kada ki horamin baby na da yunwa don Allah nafison ki haifamin qaton da wanda da anganshi ansan yaron nan yana qoqari kuma yana kaiwa har maqogoro"
Harararsa tayi yayi dariya yace “Allah cikine dake sati biyu dayan kwanaki kai likita kwai jarababbe wai har ya gano abinda akayisa a sirr..." Juyowa yayi ga mamakinsa kuka takeyi tana girgiza kai tana fadin innanillahi wa innah ilaihirraji'un ciki kuma ciki Naseer wanne irin ciki kuma ana zaune qlau" kallonta yakeyi baki a sake yace “ciki na haihuwa kuma na sunnah" gabanta ya sake faduwa tace “aa Naseer kada muyi haka dakai wlh banaso Allah ya kiyaye kaima nawa kake rainonka fa aka bani sannan kacemin wani ciki aa nikam banaso wlh tun muna mutunta juna ka canza zancenka bazan iya haihuwa da yaro kamarka b..."








Rufe mata baki yayi yace “kada kuma ki shegantamin ciki wlh wannan kadai idan kinada hankali ya isheki ishara ki gane cewa ba yawan shekaru ne girma ba kinga cikinnan na jikinki Nafeesah wlh ko ciwon kai yayi kece saboda haka ki kiyayeshi ki tsaremin shi sonsa nakeyi fiye da yanda nakeson kaina"
Ficewa yayi daga dakin ya nufi motarsa ya zuba kayan nasu a ciki Mama ta kuma diban wasu ta fita dasu ya dawo ya matsa ya kamota ta miqe tare da tureshi ta nufi hanyar fita yabita a baya yana mata fadanci da bambadanci takaici ya cikata sosai, ta rasa irin Naseer da baya da zuciya akan duk abinda ya shafeta baya ta bude ta shiga yana zuwa ya tsaya yace “gsky baki isaba fitowa zakiyi aini ba drivenki bane" kwanciya tayi ma a bayan dole ya qyaleta Mama ta shiga gaban sunajin Jan zuciyarta alamar kuka takeyi shareta sukayi har sukaje gda tun kafin ya gama daidaita parking dinsa ta bude ta fice ta shiga gdan, binta yayi da sauri yana Kiran sunanta har yana tuntube amma tamaqi sauraronsa dakinta ta shige ta datse da key bugun duniya taqi bude masa.








Dole ya haqura ya qyaleta ya juya ya fita nufi gdan yana shiga a parlourn ya tarar da Ummansa kasancewar yar tsama sukeyi jam'u yayi musu sannu zai wucce ta daga murya tace “Kai nake jira Naseer" sake tsare gda yayi yace “to lfy?" Yanda yayi mgnr yayi mugun bata mamaki tace “zan samu arziqin ka zauna muyi mgn ko kuwa a tsaye zaka tsayamin akaina kamar ubana?" Jan qafarsa yayi kamar bazai takaba ya zauna a hannun kujerar ya fito da wayarsa yana dannawa yace “inajinki"
Takaici ne ya cika Ummah ta yarda har zuciyarta an gama mata dada an shanye kurwarsa dubi yanda yake mata mgn a gadarance kanar wani ubanta dan da abaya duk tsagerancinsa yana daga mata qafa amma Wai yanzu shine yakeyi mata abu isa² dole ta dauki mataki akan Hayatu da zuri'arsa bazasu rabani da dana ba, dubanta yayi yace “inason zan shiga ciki idan bakida abin fada nasan dai bai wucce kice Ina naje ba to kafinma ki tambaya bari na fada miki matata ce batada lfy mukaje asibiti ashe ma qaruwa muka samu cikine da ita kin kusa daukan jika"








Wata zabura tayi ta miqe ta qunduma ashar tace “Billahil lazi qaryane Naseer ciki kai yanzu dan ubanka yaushe ma ka tafasa da har zaka qone inama abin yake dahar zakace wani wai matarka cikine da ita ina matar take? Tsohuwar guzumar kaini banma yarda cikinka bane wannan kawai dai liqa maka akeson yi ni dama nasan da wata a qasa cutata akeson yi aka qaqaba maka auren wannan tsohuwar yarinyar kusan saata" miqewa yayi yace “haba haba Ummah ki rinqa tsoron Allah ai kema saida kika tsufa kika auri Abbanmu don Moddibo ya fadamin rasa me aurenki kikayi a Adamawa har saida kikayi shekara talatin sannan aka bawa Abba sadakarki balle Nafeesah yarinya qarama ni wlh ganima nakeyi batan lissafi kukayi na girmi Nafeesah nesa ba kusa ba, ke komadai menene nidai inason matata kuma wlh zan sabawa kowa akanta sannan dole ne idan anason a zauna lfy dani a daina yimin shisshigi akan iyalina domin yanzu lkcna na Nafeesah ne da dan tayin dana dake cikinta yauwa" yana fadin haka ya juya nufi dakinsa kare da waya a kunnensa yace “My millon ina sha'awarki sosai Allah yau bazan iya bacci..."








Iya abinda taji kenan ta toshe kunnenta saboda kalaman Naseer din sun wucce tunaninta, miqewa tayi tana zagaya dakin zuciyarta cunkushe da damuwa da kuma tunanin yanda zatayi da Naseer duk inda ta biyo masa zillewa yakeyi, wayarta ta wawura ta danna number aminiyarta tace “Talatu akwai matsala fah duk inda kike tunanin tsagerancin yaron nan Naseer ya wucce haka wlh an busar masa da zuciya baya ganin kowa da gashi sai yarinyar nan bansan daya zanzo masa da mgnr auran Lateefah ba bama zai taba yarda ba nasani balle kuma babansa" wata muguwar ashar Hajiya Talatu ta saki tace “wlh baki isaba Nafi dolene kiyi amfani da power ki ta uwa ki tursasawa Naseer ya auri yata Lateefah wato bakeson bacin ran danki nikuma tawa yar ta mutu ko? To baku isaba wlh"
Qasa Ummah tayi da muryarta tace “ba haka nake nufi ba Talatu kaina ya kulle bakiga diban albarkar da yaron nan yayimin ba harda cemin wai nima tsohuwa babansa ya aureni garama Nafeesah ita yarinya ce wani kayan takaici duk da dokar da malam ya bani ta kada ya kusanci yarinyar nan nima na gindaya masa dan banzan yaron nan baiji ba saida ya kusanceta yanzu yake fadamin wai asibiti sukaje cikine da ita..."








Salati Talatu tasaka ta fashe da kuka tace “shikenan ta faru ta qare kinyi sake danki ya zama ba naki ba kinajin abinda malam yace laqaninta a jikinta yake indai ya kusanceta to yariga ya gama mallakuwa sai yanda tayi dashi amma dake ke wawuya ce baki kishin danki kika sake har ya kusanceta, Uhmmm! Hmmm!! To nidai koma menene indai akwai malamai da bokaye a duniya ko zanyi yawo babu dan kamfai zan tsayawa yata ta samu cikon burinta wato Naseer kuma saina wulaqanta Nafeesah a duniya tunda ta shiga gonar yata"
Kit ta kashe wayar tabar Ummah da “hello! Hello!! Talatu..." Sauke wayar tayi ta zabura ta miqe tana zagaya parlourn ta koma ta zauna tace “qarya kake Naseer ni na haifeka bakai ka haifeni ba dole nima kayimin biyayya" miqewa tayi ta shiga dakinta ta dauki mayafinta ta fito ta nufi gdansu Nafeesah, tun daga qofar parlourn ta fara kiran sunan Hajiyan Nafeesah tana fadin “Zuwairah kike ko Juwairah to koma me kike bai dameni ba kashedi nazo nayi miki tun dare baiyi miki ba ki koma gurin bokanki kice ya kwance asirin da yayiwa dana wlh ban haifawa guzumar yarki da taqi zaman aure miji ba Naseer yafi qarfin auran bazawara na riga nayi masa mata kuma ki fadawa yarki ta nemawa shegen cikinta uba amna ni dana burarsa batayi qwarin da zaiyiwa mace ciki ba yaushe ma aka haifi Naseer din da har yayi balagar da zaiyiwa wannan tsohuwar yar taki ciki?"








Hajiya ce da take saukowa ta cafe da cewa “Haba Nafi ai duk abin baikai na hakaba da Naseer da Nafeesah duka yayanmu ne kuma dukkansu ikonmu ne ba dole akayiwa danki ya auri Nafeesah ba hasalima ita akayiwa dole duk da itace take da yancin zabar mijin aure kasancewarta bazawara..." Mama ce ta cafke da cewa.
“Kuma da kike wannan babatun waye ya gaya miki baikai ba aini tun ba yau ba nasan danki ya isa burarsa ta cika wandonsa idan kinada ja kije ki duba ai danki ne ya kamata ace kin riga kowa sanin hakan kuma ma da kike cewa an liqawa danki auran bazawara wlh bani na haifi Nafeesah ba Amma tafi qarfin a liqawa namiji ita balle harijin danki ke bandama dabbancin ki ai taimakonki akayi don da ace baa daura masa auranba memakon dan sunnah da zaki goya da shege zaki goya a matsayin jika, shashasha kawai da batasan ciwon kanta ba wlh Nafi ki fita idona idan ita wannan sullutuwar bazata iya qwatarwa yarta yanci ba toni zanyi yaqi dake akan Nafeesah dama danda kike iqirarin nakine shege ka fasa ni dake"








Sosai suka rinqa musayar kalamai ita da Mama itadai Hajiya Juwaira hqr take basu da taga abin yaqi saita kira Baffa a waya ta fada masa shikuma ya kira Abba tunda shi baya gari a fusace Abba ya shigo ya zafga mawa Ummah Nafi mari ya nuna mata hanya yace “kika qara second talatin a gdannan a bakin auranki ki wucce Adamawa" juyawa yayi ya kalli Hajiya Juwaira da Mama yace “kuyi hqr matar nan batada hankali saina nutsar da ita Ina Feesahta" daki Hajiya ta nuna masa tace “tana ciki batada lfy" numfashi ya sauke yace “ku hada mata kayanta yanzu Naseer zaizo ya dauki matarsa su wucce kawai ayi bikin daga baya idan ta haihu"………….












More comments
More typing










*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[4/22, 9:58 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_A B_*






*22*










Kallonsa dukkansu sukayi Hajiya tace “amma Abba da ambari ko zuwa gobene an gama shirya musu gdan a nutse" murmushi yayi yace “aa su tafin kawai ko Suma sa huta musamman Nafeesah tana buqatar hutu da kulawar mijinta cikin fari akwai wahalarwa"
Basu da yanda zasuyi su qaraja da mgnr Abban dole Mama ta haura saman ta shiga dakin Nafeesah a kwance ta tarar da ita tanata juyi a cikin bargo matsawa tayi ta janye bargon tace “ki tashi kije Abbanku yana son ganinki" miqa tayi ta share guntun hawayen daya zubo mata ta miqe tanajin jiri har tasa rigar baccinta ta dauki hijjab dinta har qasa tasa suka sauko qasan.






A tsaye ta tarar da Abban shida Naseer din gabanta ya fadi saboda irin kallon da taga Naseer din yanayi Mata ta tsugunna tace “gani Abba" murmushi yayi mata duk tayi laushi a tausaye yace “sannu uwar iyaye ya jikin?" Qasa tayi da kanta cikin kunya yayi dariya yace “sai haquri dama ki tashi maza na kaiki gdanki kema ki huta da wannan rayuwar banason kice komai mamana komai yayi farko yana da qarshe ki ninka hqrnki akan na baya insha Allahu biyayyarki alkhairi ce nasan bakison qaninki Naseer a matsayin miji amma babu yanda zamuyi wannan hadin ba namu bane na Allah ne idan kika rungumi qaddarar ki kikayi hqr zakiga ribar hakan a gaba da yardar Allah"
Kuka takeyi sosai tana kallon Naseer din da yaketa murmushin farin ciki tana kallon Abba cikin sarqewar murya tace “amma abb..." Katseta yayi yace “bansanki da jayayyaba mamana kada ki fara akan wannan kinji" ya juya gurin Naseer yace “ka takura ka tursasa na tauyewa Nafeesah haqqinta na zabin miji da kanta da Allah ya bata na baka to ina shawartarka kar naji kada na gani Naseer Nafeesah amanarka ce idan kasata kuka zakayi wanda yafi nata idan tayi baqin ciki zakayi ninkin nata sau casa'in da tara nasani mamana batada matsala Naseer bata iya jayayyaba tana da sanyin hali da taushin zuciya inada tabbacin duk wata matsala bazata bullo ta bangarenta ba saidai kai da kake tashen tsageranci da gadara kake ganin kowa bai iyaba saikai to ka sauke isarka da izzarka kayiwa matarka mu'amala me taushi kai shaidane kaidin ba zabinta bane Allah ne kawai ya baka"








Qasa yayi da kansa shima kukan Nafeesan ya karyar masa da zuciya sosai ji yakeyi kamar shima zaiyi kukan yace “Insha Allahu bazakuji komai ba sai alkhairi Abba ku tayamu da addu'a sannan ka fadawa matarnan ta fita daga harkar iyalina ni ba yarone ba da zaa rinqa kafamin sharrudan qarya akan matata" sarai Abba yasan dawa yake amma sai yace “wacce matar kake nufi" sake tsuke fuska yayi yace “Ummah mana banason taja abinda zan nuna mata kalata wlh bazan dauki qananun raini ba zan iya jure komai amma bazan iya jurewa cin fuska wa matata ba inasonta a duk inda take kuma ita kadaice matata sannan uwar yayana ce saboda haka tayi taking care"
Ido Abba ya zuba masa zafin zuciyarsa da tsayayyan raayinsa akan abinda yakeso yana burgeshi tsarin rayuwar dan nasa yana bashi sha'awa bai yarda da raini ko wargi ba wannan alama ce ta cewa zai jajurce a gdansa saidai idan abu fin qarfinsa yayi, kamo hannun Nafeesah Abba yayi ya miqar da ita ta fada jikinsa ta saki wani marayan kuka daya karya zuciyar duk wanda yake parlourn musamman Hajiya data haye sama saboda tana tsananin tausayin yar tata ita ba isasshiyar lfy ba ga baqin ciki wannan aure da yake cin zuciyarta ga kuma ciki da ya liqa mata tun haduwar farko ga kuma mahaukaciyar surukarta da ta tusota a gaba zama tayi a parlourn saman tace “zan sanya a rinqa yi miki addu'a kuma nima zan dage Allah ya tsaremin ke Nafeesah Allah kar yabawa maqiyanki nasara akanki Allah ya daidaita tsakaninki da mijinki"








Abba ne yaja hannunta ya bude mata motar yasata mama tasa mata akwatun kayanta ta miqa mata jakar hanunta ta leqa tace “kiyi hqr Nafeesah ki daina kukannan badon muba saidon cikin jikinki kada kisa qinki da aurannan yayi tasiri wa abinda ke cikinki shi ciki kwakwayo gareshi ki godewa Allah Nafeesah wannan wata dama ce Allah ya baki kada kiyi wasa da ita ki kama mijinki ki riqe kiyi masa duk abinda zakiyiwa wani bashi ba ki dauka cewa shine samanki kicire mgnr qani ki daukeshi sama dake ta kowanne bangare kisa aranki Naseer yayanki ne hakan zai cire raini tsakaninku kinji" kada kai tayi cikin kuka tace “na gde mama kizo da safen don Allah saurin cafewa yayi da cewa “amma ki bari sai irin qarfe dayan nan saboda kada ki hanani hutawa" dariya Mama tayi tace “bakwai zanzo dan qaniyarka ja'irin yaro kawai"
Murmushi Abba yayi yaja motar suka tafi wata sabuwar unguwa ce ta yayan manya a cikin garin Abujan Abba ya ginawa yayan nasa biyu gda a ciki kowanne ya bashi kyauta anan ne aka kai Nafeesah kasancewar komai Abba ya zuba musu kayan abinci ne kawai babu a ciki, suna zuwa sukayi parking Naseer ya bude ya fita Abba ya budewa Nafeesah ya kama hannunta yace “ki shiga gdanki da Bismillah insha Allahu daganan sai kabari Nafeesah kinzo kenan"






Tana kuka tana komai Abba ya shigar da ita cikin gdan ya shigar da ita daya daga cikin dakunan dake qasan guda uku ya zaunar da ita a saman carpet din dake shimfide a qasan gadon yace “ku rayu cikin aminci mamana Allah ya hade kanku kunji ubangiji Allah yayi muku albarka" Naseer ne kawai ya amsa da amin itakam ba abinda da takeyi sai kuka tana qarewa dakin kallo ta cikin hijjab din da taja ta rufe fuskarta idan ta tuna wai itace a gdan qaninta Naseer matsayin matarsa ta sunnah sai taji wani sabon kukan ya kuma kwace mata.
Juyawa Abba yayi ya fita Naseer din yabi bayansa ya dauko kayan ya shigo dasu ya ajiye a parlourn ya koma Abban yace “me kuma ya fito dakai?" Shafa kansa yayi yace “tun rana take amai bataci komai ba ka saukeni a Durban zan samo Mata abinda zataci" ajiyar zuciya Abba yayi suka fita ya zari dubu hamsin a cikin dashboard dinsa ya miqawa Naseer din ya kalleshi yace “na mene?" Murmushi yayi yace “ka siyi abinda zaka siya da ita sai kazo muje ka dauko daya cikin motocinku a gda" kawar da kansa yayi yace.






“Iya hakama na gde Allah ya qara girma da arziki Abba bana buqatar taimakon kowa wajen riqe iyali na zan iya da kaina haqqi ne a kaina ba akanka ba kabarni nayi qoqarin koyon riqewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login