Showing 18001 words to 18613 words out of 18613 words
Chapter 7 - GIDAN YAN BARIKI BOOK ONE Na Pinky Darling Mrs Jay.txt
yace "Hana wace unguwa zakiji a fara sauke ki.?"
tace "GRA zanje." Yace "Kai Unguwa ɗaya zamuje." Suka shiga Direba yaja sai Unguwar GRA suna kusa isa get ɗin gidansu, "Suhana tace "Direba saukeni a nan." tsayawa ya yi da mota ta fita kai tsaye get ɗin gidan ta nufa, Dirba ma get ɗin gidan ya tsaya tana danna horn, mamaki ne ya kama Jamal wa Suhana ta sani a gidan dama nan ne zata zo,
koda Get Man ya buɗe ƙofa, Suhana har ta shige ciki, bata tsaya ko ina ba sai babban parlon gidan, Jamal na bayanta yana tare suka shiga, gaba ɗaya mutanen gidan suna parlo, Alhaji da Hajiya BINTA da Hajiya Kuluwa sai wani matashi kusa da Daddy tare da wata mata Kamar su ɗaya da matashin kamar da ga sama Hajiya Binta ta ga Suhana ta faɗo cikin, paroln,
da sauri ta miƙa tsaye bakinta na rawa tace "Zai zai Zainab kice kuwa ko mafalki nikeyi!.?" Suhana ta fashe da kuka tana faɗawa jikin Matar tace "Ummie nice ba mafalki bane." Jamal kuwa baki ya saki da hanci yana kallon ikon Allah Alhaji ne ya yi gyaran murya kana yace "Hajiya BINTA ki samu wuri ki zauna kun cika min kunne da haya niya"
Suhana na jikinta suka zauna Hajiya Kuluwa, sai lokacin ta kula da Jamal kana ta bashi damar zama gaba ɗaya ta rikice, amma ta dake saboda kar ayi daurin fahimtar ta, Alhaji yace "To Alhmdllh Buhari ga Matarka Zainab ta dawo bazan tambayata inda taje ko daga ina ta fito ba kawai ka ɗauketa ku tafi.!"
wata dira Jamal ya yi a gaban Alhaji yace "Na shiga uku don Allah karku yi min haka wallahi Suhana itace rayuwata, bazan iya rayuwa babu ta, don Allah karku yi min haka." Ya dawo wurin Suhana dake kuka jin abinda Abbanta ke faɗa yace " Please Hana ki faɗa mai nine Mijinki dan Allah, kar a rabamu.!"
Buhari ne ya tashi Kamar wani mahaukaci yanyo hannun Suhana, tana tirjewa Hajiya BINTA, tariƙe hannun ƴarta, tace "Wallahi Wallahi na rantse da Allah Zainab bazata zauna da wannan ɗan iska ba mashayi!." Matar dake Zaune tace "Ashe abinda ake gayamin gaskiya ne, baki da mutunci a gabana kike zagar min ƴaro."
Hajiya BINTA tace "Na zage shi ai wallahi koke hajiya Luba zan iya zagi saboda kece marar mutunci bani ba." Alhaji yace, " wallahi idan kika koma magana a bakin aurenki ke koma Zainab idan baki bi Buhari ba, saina tsini miki albarka.!" Haka Buhari yaja Suhana Kamar kayan wanki ya fita uwarsa ta mara mai baya suka fita,
Jamal ya bisu da gudu yana kuka su dawo mai da matarsa, Hajiya BINTA kuwa sama ta haura tana kuka,
Koya wannan chakwakiyar zata kasance idan Sultan ya dawo hayyacinsa ta ina zai fara neman Suhana gashi tana ɗauke da cikinsa a jikinta shin ya zata kasance tsakanin Suhana da Buhari mahaifinta ya ɗaura mata aure bayan ta ɗauke shekaru bata gida shin auren wa aka fara ɗaurawa na Buhari ko na Sultan, menene sanadin barinta gida, ta shiga barki, har ta chanza suna daga Zainba zuwa Suhana ,
Ya Jamal zai ƙare da rashin Suhana?
Burin Suhana zai cika na gina ƙaton gida ta saka mai suna GIDAN ƳAN BARIKI,
Ya su Afiya zasu ƙare da Hajiya Uwani? Suwaye dangin Mahaifiyar Sultan? Duk waɗannan tambayoyi zaku samu amsar su a cikin Book2 karku bari ayi wannan tafiyar babuku,
Writer ✍️ Bey *PINKY DARLING MRS JAY*
anan na kawo ƙarshen wannan littafi na ɗaya duk mai buƙatar Book2 zai biya ₦500 ne duk mai buƙata ya yi min magana ta wannan number 09033580667