Showing 12001 words to 15000 words out of 18613 words
Chapter 5 - GIDAN YAN BARIKI BOOK ONE Na Pinky Darling Mrs Jay.txt
me kyau,
Kallonta ya yi kana yace "Kai Ƴata duba dai ki gani ai na tsufa, na wuce zama matashi." Afiya tace "Ni dai banga haka ba santalelen saurayi na gani ko kika gansa Lili.?" Lili tace "%fasenr wallahi matashi mai jini a jiki, ai har ya fi wani saurayi ɗan sha 18." Wani baƙin ciki ne ya kama Hajiya Uwani, tace "To Karuwan kan tati, nan ba GIDAN ƳAN BARIKI bane,
sai ku tashi ku ƙara gaba." Daddy kuwa ya riga ya rufta, tarkon su Afiya yana juyawa yace "Hajiya Uwani wallahi banason haka ya zaki kira ƴaƴan mutane da karuwai kamar ba matsayin Uwa mace kike ba, Please don Allah ki koma bana son wannan rakiyar!." Wani abu taji ya tokare mata zuciya, idan ta cigaba da tsayuwa a nan zai cigaba da yarfa ta,
fuuuu ta wuce, Daddy yacewa su Afiya "Kuyi haƙuri haka nan take, sai a hankali, Ƴata ƙannenki ne.?" Ya tambaye Suhana tace "A'a Daddy Ƴan uwana ne kuma ƙawayena." wani daɗi yaji kana ya ce "To shikenan sai mun haɗu anjima da yamma zan dawo, kana ya saka PA ɗinsa ya damƙa musu manyan kuɗaɗe, suka wuce,
duk abinda ya faru a idanun Hajiya Uwani Daddy na wucewa ta fito ta sha ga bansu Afiya, ta ci kwalar rigarta tace "Wallahi idan baku fita sabgar Mijina ba duk abinda ya faru da yarinya ita ta janyowa kanta, ke ganni nan shaiɗaniya ce wallahi ko duk abinda zan mallaka zai ƙare bazan taɓa bari wata mace ta raɓe mijina ba,
Kekuma Suhana shi wanda ya baki damar kwaso ƴan uwanki karuwai har suna neman shiga wurin mijina be gayamiki tarihina da na Uwarsa ba, ni nan da kika ganni na wuce barki da ƴan bariki na damesu na shanye, saboda haka kafin yarinya ta fara neman Hanyoyin shigowa cikin gidan Mijina ta fara binciken wacece ni.!"
tana gama faɗar haka ta shige part ɗinta ta barsu nan tsaye cikin dakiya Afiya tace "kuwuce mu tafi mun wani tsaya akan wannan sakarar wallahi duk abinda take taƙama dashi saina sauke mata shi, saina gwada mata ruwa ba sa'an kwando bane, ba boka ba Mallam saina kassarata!."
Lili tace ni yanzu ma naji inason Mijinta wallahi." Suhana tace ni ba wannan ba ina son sanin abinda ya faru da Mommyn Sultan, dashi kansa." Lili tace wannan sai Kamal ya san komai shida mahaifiyarsa." Suhana tace "zanje gidan wurin Umma idan Kamal be zo ba." Haka suka bar wurin suna tattaunawa,
Daddy kuwa a mota banda tunanin su Afiya babu abinda yakeyi, gaba ɗaya ƴan matan sunyi mai, kowace da kalar ƙirar da Allah ya yi mata, PA ne ya kula da yanayinsa yace "Sir kamar kana cikin damuwa.?" Daddy yace "Haka ne Mustafa kaga dai abinda ya faru a gabanka nidai gaskiya aure nikeson yi ƴan matan sunyi min amma ya kake ganin za'ayi.?"
Wani murmushi Mustafa ya yi dama ya jima yana son ganin wannan rana yace "Sir ai ba wata matsala bace yanzu kamata ya yi kaji ta bakinsu idan sun amince, kawai sati mai zuwa a ɗaura aure, batare da kowa ya sani ba." Daddy yace "Ya zanyi da Uwani.?" Mustafa yace "Ai ba sanar da ita zakayi ba sai an dawo ɗaurin aure, saboda a masallaci za'ayi,
kuma sai munje sallah za'a sanar da Liman ka sanar da Alhaji Abubakar, saboda shine waliyinka." Dafa ƙafaɗar Mustafa Daddy ya yi kana yace ". wannan shawara tayi haka za'ayi, suna wannan hira har suka isa officer ɗinsa dake cikin gidan gwamnati, Suhana kuwa Kamal ta kira tana son ganinsa, yace anjima zaizo, Sultan kuwa sai ƙarfe biyu ya tashi wanka ya yi
ya gabatar da sallah kana ya shirya cikin manyan kaya, kana ya ɗauko wasu takardo ya fito, zaune ya sameta parlo yace "AM na fita Abuja zan tafi, sai zuba gobe zan dawo." tun da ya fara magana Suhana ke kallonsa saboda ya yi mata masifar kyau, tace "Allah ya tsare amma me zakayi Abuja.?" "Company zan koma buɗewa." Shine kawai amsar da ya bata
addu'o'i tayi mai sosai na fatan nasara har cikin ransa yaji daɗin addu'ar, har ta tuno mai da Mommynsa, tashi tayi ta karɓe takardon tace "muje na raka ka." Ba musu ya shiga gaba tana bayansa, har wurin Mota ta rakasa yai da Direba ya fita, saboda ya dawo da motar jirgi zai shiga, ta kallo direba ya ja motar suka wuce,
harda kwalla ta cika mata idanu, kamar ta bishi su tafi tare,
tana komawa ciki su Afiya suka shigo nan suka shiga hira saiga Kamal ya zo bayan sun gaisa ta kawo mai lemo da ruwa tace "Ya Kamal dama inason dan Allah ka sanar dani labarin Sultan!." Shiru yayi na wani lokaci kafin yace da kesan labarinsa baki fatan koma tunanin wannan labari har kibawa wani,
amma yanzu dole na sanar dake saboda zaki samu damar ƙara taimaka mai ki fallasa wannan muguwar matar azzaluma marar imani,
*PAGE* 15&16
Kamal yacce "nidai Sultan abokina ne tun muna yara saboda Mommynsa na zuwa wurin Ummana kitso, nan muka shaƙu da juna, har ta kai Babansa ya san da Abotarmu ya maida ni makarantar da Sultan yake karatu komai tare yake muna, babu wani banbanci, har kwana Sultan yakeyi gidanmu, nima haka,
saboda tun ina ciki Allah ya yi Babana rasuwa, sunan Mommynsa Hajiya Zainab mace ce mai mutunci da sanin ya kamata tana girmama nagaba da ita, bata da girman kai, ga kyauta bata da ƙyamar talaka bayan mun kammala karatun sakandare Daddy ya tura mu Ingila wurin karatu,
Sultan ya karance gefen business, harkokin tafiyar da mulki, nikuma nayi karatun computer, mun chan kwatsam muka samu labarin Daddy ya yi sabon aure sati ɗaya da cin zaɓensa na gwamna, tun daga lokacin Mommy ta fara fuskantar matsala wurin Daddy da matarsa,
Hajiya Uwani ta mayar da Mommy Bora, saboda yawon wurin malamai,da bokaye,ita da ƙawarta Hajiya Ruky, haka Mommy ta samu wani ciki, saboda tun bayan haihuwar Sultan bata koma samun ciki ba sai wannan lokaci, cikin yazo mata da laulayi da rashin lafiya,
Daddy na fahimtar cikine da ita, asirin da Hajiya Uwani tayi mai ya karye ya dawo kulawa da Mommy yana riritata, nan fa Uwani ta bazama wurin Malamai sai da Daddy ya tsane cikin dake jikin Mommy komai ya dawo cin zarafin da wulaƙanci ban bancin Mommy da ƴar aikin gidan kawai aure,
gaba ɗaya ko ganinta Daddy baya sonyi, haka zata zauna tayi ta kuka saboda ta gayama Ummana akan auren Daddy ƴan uwanta suka rabuda ita, saboda iyayensu basa raye, sai dai Umma tayi bata haƙuri akan ta dage da addu'a watarana sai labari, haka cikin ya shiga watan haihuwa a dai-daita sahu Mommy ta shiga ta kaita hospital, ta haihu ɗa namiji,
gaba ɗaya yaron baya kama da Mommy Har Daddy kamarsa da ban Mommy tace Yayanta ne yaron ya biyo, bayan ta dawo gida Daddy na ganin yaron yace bazaiyi masa suna ba saboda ba ɗansa bane, haka Mommy tayi kuka tana roƙansa amma Daddy yace idan ta matsa mai zata bar mai gidansa
haka ta zauna gidan Lokacin Hajiya Uwani ta haife ƴa Mace ba haka taso ba ɗa namiji taso ta haifa, saboda ta mallake gidan gaba ɗaya, haka muka kammala karatu muka dawo muka tarar da Mommy cikin wannan hali, iskancin Uwani kuwa sai abinda ya ƙaru, ta mayarda Daddy bita zai-zai duk inda ta ajeye shi nan yake,
sai abinda ta bashi umurni, duk Mommy tayi banza da ita, saboda bayan dawowar mu Sultan na kuwa da ita sosai da ƙanensa, ta bashi ragamar shugabancin kasuwancin da takeyi a ƙasashen waje, saboda tun kafin ta aure da Daddy take kasuwanci da dukkyarta ta gadon mahaifinta, da ya rasu,
saboda cin zarafi har wurin da Mommy Ke zama Uwani ke janyo Daddy ta ware ƙafa ta saka shi lasar gindinta, har sex sukeyi wurin, Idan Mommy zata bar wurin ta saka Daddy ya hanata idan har ta bar wurin bakin aurenta, haka ciyon zuciya ya kama Mommy, har ta kai ga kwanciya, hospital, saboda har aman jini takeyi,
Sultan na shirin fitar da ita ƙasar waje, ranar Alhamis Allah ya yi mata rasuwa, Sultan kamar ya yi hauka lokacin, sai da aka haɗa da roƙon Allah ya dawo cikin hankalinsa, Ummana taso karɓar Usman ƙanen Sultan amma saboda makircin Hajiya Uwani ta hana Daddy ya Bata shi, haka ta riƙa azabtar da yaron,
Sultan na son ganin ƙanensa amma ta hana mai ganinsa, ƙarshe piya piya ta zubawa yaron cikin madarar da ake bashi ya sha, ya mutu, lokacin mutuwa ce kawai Sultan beyi ba,
Writer ✍️ Bey
*PINKY DARLING MRS JAY*
More comment more typing please share my friends
Following this link to join my WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e Masu neman gidan ƴan bariki daga farko kuyi following channel ɗina zaku samu tare da sauran littatafai na
*GIDAN ƳAN BARIKI*
(*Hot love and Romantic Story*)
Story and Writer ✍🏻 bey
*Zainab Abdullah Usman*
(*PINKY Darling Mrs Jay*
*PAID BOOK*
₦500 only account number 7060577995
*Zainab Abdullah Opey*
Evidence of payment 👇
09033580667
__________________________________
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝♀️*
(*we stand together*)
🤝🤝🤝
*Bissmillahi Rahamanin Raheem*
PAGE 1️⃣7️⃣▶️1️⃣8️⃣
Ya Sha wahala sosai saboda yafi wata ɗaya a hospital bayan an dawo dashi gida Hajiya Uwani taso kashe sa amma da taji zancen dukiyarsa da Mahaifiyarsa tabar masa gado,sai ta ta ƙirƙiro da maganar ayi mai aure,a haɗa shi da Farida ɗiyar Yayarta, Daddy baya musu da duk abinda ta faɗa,
ya kira Sultan ya sanar da shi amma be yarda ba, saboda haka ta taje wurin malaman ta da bokaye aka saka shi dole ya amince da auren Farida ga kuɗaɗen da Uwani ke karɓa wurinsa wai na hidamar biki, saida aka zo zancen ɗaurin aure tace a nan gidan za'a ɗaura ko a masallaci, haka Daddy ya but maganarta,
Alhaji Abubakar shine waliyin Sultan, Daddy waliyin Farida haka akayi shagalin biki babu dangin uban Farida, saboda bata da Uba wurin yawon bariki aka samu cikinta, sunyi iya yinsu wurin zubar da cikin amma abin beyi ba dole suka haƙura har aka haife Farida, bayan nan uwarta ta samu wani mai kuɗi ta aure yanzu haka tana Nijar,
Kuma batasan waye uban Farida ba, saida akayi kwana biyu da ɗaura aure kana Farida ta tare bayan sun jiƙata da kayan tsisbace-tsisbace-tsisbace, saida sam Sultan baya sha'awar ta, nan ma saida sukayi da gaske ya fara kusantar ta, nan fa ya haukace akanta dukiyarsa ya zuba mata sai yadda taga dama,
Saidai yanzu ba iya kuɗi kawai suke so ba takardun kadarorinsa suke buƙatar ya mallakawa Farida amma sun kasa samun wannan damar, sunyi iya yinsu wurin Malamai amma a banza, Farida ta kasa haƙuri, watarana suna kwance, take tambayarsa inda yake aje takardun kadarorinsa,
yace mata ai shi sam baya aje wani abu mai daraja, a Najeriya ƙasar waje ya adana komai nasa, kuɗine kawai yake ajewa duk inda ya ga dama, shine ta matasa mai wace ƙasa yake ajeye abubuwan, ya ce mata duk inda ya ga dama, ba haka taso ba bayan ta koma bedroom ɗinta,
takira Mahaifiyarta, ta sanar da ita halin da ake ciki, washegari da safe, Sultan ya shirya ya samu Farida parlonta yace yana son fita, ya zaga gari bata hana shi ba, saboda yau tana son fita zuwa wurin wani sabon Malami, yana fitowa gidanmu yazo kusan wata shida zuwa bakwai da aurensa,
baya zuwa ko ina, ko naje Uwani bata bari na gansa ita da Farida haka Ummana dole muka haƙura sai dai Addu'a mukeyi mai, Uwani ta saka aka koreni Company nin Sultan shine dalilin da ya saka na fara ɗinkin tela, ina zuwa gidan Ƴan Bariki, har na haɗu da ku,
yana zuwa gidan Umma gaba ɗaya ya rame ya yi baƙi kamar ba Sultan haɗadɗen gaye maiji da kyau ga kuɗi, amma duk ya zama wani iri, kamar a tsorace yake, Umma na ganinsa ta fahimci halin da yake ciki ruwa ta ɗibo a ƙofi, ta karnta mai fatiha 7 falaƙi7 nasi7 ikilas7 kafirun 7 ayatul kulsiyu 7 tayi mai rufi cikin ruwan ta bashi
ba musu ya karɓa ya sha, ya rage saura ta sakani na shafe mai jikinsa, ya kwanta sai bacci, wannan da ku ka ji na faɗa anayinsu ne idan akayiwa wani asiri, ko baya da lafiya anyi magani ba dace ba, da izinin Allah komai zai zo karshe musamman asiri, tsawon sati ɗaya akeyi ba'a ƙetare rana,
UMMA tace min Kamal yaron nan asiri ne a jikinsa dole sai yayi sati yana shan wannan tofin, nace mata kawai ta rabuda shi, ya zauna nan gidanmu, saboda bada tare da direba yazo ba, haka kuwa akayi be falka ba sai ƙarfe huɗu tare muje masallaci mukayi sallah, kana muka dawo gida,
saiga kiran Farida Umma tace ya sanar da ita tafiya ta kama shi, yanzu haka, jirgi tashi zaiyi, sai nan da sati mai zuwa zai dawo haka ya sanar da Farida ta rufe sa da masifa kamar wani ya ronta, amma taji daɗin tafiyar ta shi saboda tana wurin Malamin da taje yace sai yayi sati ɗaya yana kwanciya da ita,
zata samu biyan buƙatar da takeso, cikin kwana biyu Sultan ya fara wankewa kamr ba shi ba, haskensa ya dawo, saboda yana samun kulawa wurin Umma sosai, ranar da ya cika sati, ɗaya, komai ya dawo mai sabo ya gayama Umma shi besan yadda akayi ya aure Farida ba yanzu gida zaije sakinta zaiyi,
Umma ta lallashisa tace ya kwanatar da hankalinsa, yabi komai a sannu kar ya nuna musu ya dawo cikin hankalinsa, har sai ya gano abinda suke shiryawa, kana ya riƙe addu'a da yawan ibada kar ya yi a gaban Farida saboda zata iya hana shi da wannan shawarar ya koma gida ya riga Farida dawowa, ya shige bedroom ɗinsa ya kwanta,
saboda bacci yakeji, amma ya kasa yi, sai juyi yakeyi kan bed yana tunanin halin da Su Hajiya Uwani suka saka shi, muryar Farida yaji itada Hajiya Uwani cikin parlo, suna magana , akan wurin Malamin da Farida Hajiya Uwani tace ai shine ya yi mata asirin Daddy ya aureta ya walaƙanta Mommy suna wannan magana Saiga Umman Farida ta shigo nan suka baje suna hirar abubuwan da sukayiwa Mommy har zuwa haɗa aurensa da Farida,
akan dukiyarsa, yanzu shirin su na gaba su kashe sa shine kawai, Farida tace gaskiya tana son sa adai yi mai wani abu da ban amma banda ƙisa, da farko basu yarda ba sai da tayi ƙaryar tana da ciki wata biyu a bari idan ta haihu dole dukiyarsa ta dawo hannunta, da wannan shawara suka aje,
sai maganin da zata saka mai cikin abinci ya cigaba da yi mata biyayya, suna wannan zance Sultan ya fito jikinsa har rawa yake, gaba dayan su sun firgita da ganinsa, sai da suka tashi tsaye, wani murmushi ya yi wanda yafi kuka ciyo yacewa Farida ya saketa saki biyu, su fita su bar mai part,
ko ya halaka su, haka suka fito jiki a mace, babu wanda yake magana, Sultan kuwa Umma ya kira ya sanar da ita duk abinda ya faru bayan dawowarsa, tace ya cigaba da addu'a saboda ba rabuwa da shi zasuyi, haka kuwa akayi wurin Malam suka koma ya basu wani garin magani yace su zuba akan hanyar da Sultan yake bi,
yana taka shi, aljanu zasu samu damar shiga jikinsa su barkita mai tunani, sumayar da shi mahaukaci ranar suka zuba maganin yana fitowa sallar magrib yana taka shi sai wani ihu sukaji, na Sultan, securityn gidan suka taso duk wanda ya matso inda yake, to sai ya karya mai hannu ko ƙafa,
wani masifar ƙarfi ne ya shiga jikinsa, ranar duk wanda ke gidan yaji jiki, abin ban mamaki part Hajiya Uwani ya shiga parlo ya same su,
sai dariyar mugunta sukeyi na halin da suka jefa shi ai kuwa sun sha duka don saida ya karya mata hannu, Farida kuwa ya sauya mata fuska da jiki aka duka, har su Maryam, an kira Daddy aka sanar da shi saboda baya ƙasar yana London, sai da aka samo gardawa masu ji da ƙarfi suka fito da Sultan suka dannesa akayi mai allurar Bacci,
suka saka shi part ɗinsa, kusu sun sha wahala, saboda duk ƙaton da ya kaiwa naushi ya zuɓe ƙasa, abu kamr filim ɗin indiya, haka suka mayar da Sultan Mahaukacin ƙarfi da yaji, banda allurar Bacci babu abinda Daddy kesa anayi mai ya fi wata uku a haka watarana naje gidan su Hajiya Uwani sun fita,
na samu damar shiga part ɗinsa na tarar da shi, cikin wannan hali cikin masu tsaron lafiyarsa wani ya bani labarin abinda ya faru da Sultan, nan na yanke shawarar ɗakarsa na tafi dashi gida, saida Umma tayiwa Sultan Kuka, duk wani mai tausayi da imani sai ya tausayawa Sultan,
wanka nayi mai na saka mai kayana duk allurar baccin bata sake shi, yana tashi zai fara bige -bige yana ganin Umma ya zauna sai ya fashe da kuka, Limamin Unguwar mu Umma ta kira, shi ya yiwa Sultan ruƙiya, da ƙyar aljanun suka fita jikinsa, saboda ba iya waɗan da aka turo bane wasu na jikinsa, da jimawa,
bayan sun fita, ya bashi magani, da wasu addu'o'i Umma nayi mai da ruwan zan zam, da zuma, yana sha,
Uwani kuwa batasan wainar da ake toyawa, sai da safe Dr dake zuwa yimasa allura yaje amma be gansa ba, haka sukayi ta nemansa amma shiru tana komawa wurin Malam yace musu zai dawo ai ba nesa ya yi da gida ba, kuma yana nan cikin hauka, da wannan bayani, suka gamsu,
suka dawo gida bayan sati ɗaya, Umma taje ƙauye wurin ƴan Uwanta a chan ta samowa Sultan tsarin jiki yadda asiri be saurin kama jikinsa idan ma ya samu shiga to bazaiyi tasiri, ba a jikinsa, zai fita,
sai da ya yi sati biyu, ya dawo Sultan