Showing 3001 words to 6000 words out of 18613 words

Chapter 2 - GIDAN YAN BARIKI BOOK ONE Na Pinky Darling Mrs Jay.txt

more typing please share my friends 😍




Following this link to join my WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e


*GIDAN ƳAN BARIKI*


(*Hot love and Romantic Story*)


Story and Writer ✍🏻 bey


*Zainab Abdullah Usman*
(*PINKY Darling Mrs Jay*


*PAID BOOK*
₦500 only account number 7060577995
*Zainab Abdullah Opey*
Evidence of payment 👇
09033580667


__________________________________
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)




*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️*
(*we stand together*)
🤝🤝🤝




*Bissmillahi Rahamanin Raheem*




*PAGE* 5️⃣▶️6️⃣




Kamal kuwa suna gama waya number Suhana ya fara kira amma bata ɗauka ba, sai text ya tura mata amma ba amsa, Suhana kuwa bata duba wayarta ba sai da ƙarfe huɗu na yamma nan ta ga kiran Kamal da text ɗin da ya tura mata, kiransa tayi bayan sun gaisa yace "Hana Baby wani aiki ne ya samu na kuɗi."




nan ya gaya mata abinda Sultan yake buƙata tace zata yanke shawara zuwa gobe zata kirasa, tunani ta fara idan tayi aure burinta fa na gina gidan kanta ta saka mai suna GIDAN ƳAN BARIKI, wata zuciyar tace ai auren da wani lokaci ne ba jimawa zakiyi ba, kafin ma a ayi auren zaki iya fara ginin gidan da wannan tunani ta tsaida shawara,




zatayi auren saboda ko ba komai zata samu kuɗin da zata kula da rayuwarta da sauran ƙayenta, cikin washegari ta kira Kamal ta shaida mai ta amince amma matsalar, ina iyayensa zasu zo neman auren ta Kamal ya tambaye ta, tace "Kamal nima abinda nike tunani kenan."




Yace "Yanzu dai ki shirya zaku haɗu a taraka hotel, zanzo na ɗauke ki." Ta ce Okey sukayi sallama ƙarfi biyar na yamma kamal ya zo ɗaukarta lokacin Jamal ya fita, zuwa gidansu, suka wuce taraka hotel, sun isa room 30 suka shiga kai tsaye, wani ƙamshin turare ne ya dake hancinta, mai sanyaya zuciya,


saida ta lumshe idanu, Kamal na gaba tana bayansa, har suka ƙarasa parlo zama sukayi kana ya kira wayar Sultan, sai ringing ɗinta yaji kan kujerar da Suhana take zaune, yace "Ashe yana kusa ma ina zuwa." Yacewa Suhana kana ya fita parlon Bar ya nufa dake cikin hotel ɗin a chan ya same shi zaune yana shan maltina,




Kamal yace "Sultan mun ƙaraso tana ciki." beyi magana ba sai da ya kammala abinda yake yi kana ya tashi yana gaba Kamal na bayansa har suka shiga ciki lokacin Suhana ta ɗauko wayarta tana waya da Jamal ya dawo be sameta ba sai rigima sukeyi sai ta faɗa mai inda taje ya zo ya sameta,




faɗa sukayi sosai ta kashe wayarta, Sultan kuwa zama ya yi kan kujera ya ɗora ƙafarsa kan teburin dake parlon, ya rufe idanunsa, yana jiran suyi magana Suhana kuwa sai lokacin ta kula da Sultan ne, wani dukan uku-uku ƙirjinta ya yi, amma ta basar kamar bata san shi ba , saboda ta kula ɗan jan aji ne,




Kamal ne ya ga shirun ya yi yawa kana yace "Sultan ga Suhana munyi magana da ita nayi mata bayanin komai , yanzu sai ku tattauna akan yadda za'a yi auren." Shiru Sultan ya yi na lokaci kafin ya buɗe baki da kyar kamar wanda akayiwa dole ya fara magana cikin muryarsa mai daɗin sauraro,




yace "kamar yadda Kamal ya miki bayani inason yin aure na wani lokaci maybe na shekara ɗaya ko wata uku zuwa 7 mouth, ki faɗi ko nawa kike so zan biyaki duk abinda kike so zan yi miki, amma fa dole kiyi min biyayya, duk abinda nikeso shi zakiyi, cikin gidanmu zan ajeki, nan kowa da kowa yake,


banaso ki ragawa duk wanda ke cikin gidan kiyi duk abinda kikeso duk wanda ya taka ki kema ki taka shi ko wanene ban ɗauke miki kowa ba, karki yarda da kowa duk yadda akayi karki aminta da ko ɗaya, abinda na saka ki shi zakiyi, idan lokacin da na ɗiba ya cika zan sakeki.!"


shiru Suhana tayi saida Kamal yace "Hana kiyi magana." Kana tace "Ni yanzu matsalata shine bansan inda iyayenka zasuje neman aurena ba saboda banda kowa!." Sultan yace "Okey Kamal ka kaita gidanku, wurin Umma, saina zo anjima zamu yi magana yanzu ku tafi ta tattara kayanta gaba ɗaya,




ku wuce bana son a samu matsala, gobe da safe zan turo ILiya ya zo ya kwashe kayanku zaku koma cikin gidana guda dake Unguwar, baifas." Cikin jindaɗi Kamal yace "Badamuwa yadda kace haka za'ayi." Sultan be koma magana ba, sai ma tashi da ya yi tare da ɗaukar wayarsa ya riga su fita,




Suhana kuwa tace "Kamal yanzu ya zanyi da Jamal wallahi idan yaji wannan zance bazai taɓa bari ayi auren nan ba.!?" Kamal yace "Ai wannan mai sauƙi ne, yanzu idan muka tafi ki kwashe komai naki kosu Lili da Afiya karki gaya ma wannan zance sai bayan aure, ki sanar da su, anjima zan siyo miki sabon sim card,




ki cire wannan, kega babu yadda za'a yi Jamal ya gano inda kike." Suhana tace "Kamal baka san waye Jamal bane amma bazan ƙi shawarar ka, yanzu dai mu tafi, nasan yanzu haka ya fita zuwa GIDAN ƳAN BARIKI yana jiran dawowa ta." Kamal yace "mutafi."




haka suka tafi ta kwashe kayanta gaba ɗaya, suka wuce gidansu Kamal zaune suka tarar da Umma tana jan chalbi, saida ta kammala kana Suhana ta gaida ta cikin girmamawa, Umma ta amsa cikin sakin fuska, gyara zama Kamal ya yi kana yace "Umma Sultan ne yace na kawo miki ita ki kula mai da ita,




matar da zai aure ce bata da Iyaye gidan marayu ya ɗauko ta kesan na gaya miki matslar gidansu da halin da yake ciki, shine ya ce don Allah ki riƙe mai ita a matsayin ƴar ki, gobe Yaronsa zai zo ya kaimu gidansa dake baifas, nan zamu ci-gaba da zama har lokacin da za'a yi auren."




Umma tace "Ai ko kare Sultan ya kawo a gidan nan dole na kula da shi bale yarinyar da zai aure, gaskiya naji daɗin wannan labari ashe ina da rabon ganin auren Sultan, Allah ya kaimu lokaci lafiya, ya sa iyakar wahalar da yashi kenan!." Kamal yace "Amin Umma."


sunjima suna hira kafin Kamal ya fita, Umma kuwa sai Jan Suhana takeyi ajiki har sun saba da juna, Umma najin Suhana kamar ƴar da ta haifa, Kamal ne kawai ɗan da Allah ya bata, shine kuma yanzu Allah ya saka mata ƙaunar Suhana,




Jamal kuwa ya yi ta kiran wayar Suhana a kashe haka ya gaji da zama gidan ƴan barki ya koma gidansa da tunanin ta dawo amma shiru, ko da ya duba babu kayanta da ke gidan ko tsinke bata bari ba, hankalinsa ne ya yi masifar tashi to ina Suhana ta tafi kar dai gudawa tayi ta bi wani,




fita ya koma yi wurinsa Afiya idan sun san inda Suhana take amma shiru sosai suka shiga ruɗani ina taje gashi wayarta a kashe ba'a samu, haka ya yi ta yawo a gari duk inda yasan tana zuwa sai da yaje amma babu labarinta, washegari, da safe






Writer ✍️ *Bey PINKY DARLING MRS JAY*


Following this link to join my WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e


*GIDAN ƳAN BARIKI*


(*Hot love and Romantic Story*)


Story and Writer ✍🏻 bey


*Zainab Abdullah Usman*
(*PINKY Darling Mrs Jay*


*PAID BOOK*
₦500 only account number 7060577995
*Zainab Abdullah Opey*
Evidence of payment 👇
09033580667


__________________________________
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)




*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️*
(*we stand together*)
🤝🤝🤝




*Bissmillahi Rahamanin Raheem*


*PAGE* 7️⃣▶️8️⃣


Yaron Sultan ya so da mota aka kwashe kayan su Kamal gaba ɗaya aka mayar da su Unguwar baifas, sabon gida, akwai duk wani abu na buƙatar jin daɗin rayuwa da sauransu, Suhana kuwa gaba ɗaya kwana ɗayan nan da tayi babu Jamal taji babu daɗi, gaskiya bata kyauta mai, ba




amma ai bashi da niyar aurenta, zaman bariki kawai yake so su cigaba da yi, yanzu kuma ta samu damar yin aure dole tayi shi, ƙarfe biyu na rana Sultan ya zo gidan lokacin ta fito wanka ta shirya cikin riga da siket na atamfa blue, da fari ɗinkin ya zauna jikinta sosai, tayi kyau ma sha Allah,


sai zuba ƙamshi takeyi, parlo ta fito, tana danna wayarta bayan ta saka sabon sim card ɗin da Kamal ya siyo mata, sam bata san da zuwan Sultan ba, ƙamshin turarensa da cika paroln ne ya tabbatar mata da zuwansa, tana ɗgowa, sukayi ido huɗu da shi, wani irin ƙwarjini ya yi mata gaba ɗaya ya cika mata idanu,


bazata iya jurar kallon ƙwayar idanunsa ba, sunkuyar da kanta tayi haka kawai ta tsince kanta da faɗar "Sannu da zuwa Yallaɓai." tana nufar wurin firij ta ɗauko mai madara mai sanyi da ruwan gora ta ajiye tare da cop, sai lokacin yace "Lafiya." bedroom ɗin Umma ta shiga




lokacin ta idar da sallah tace "Umma ga Sultan nan yazo." Addu'ar da Umma keyi ta shafa kana tace "Kai ma sha Allah bari nazo mu gaisa." Ta faɗa tana tashi tsaye, ita kuma Suhana ta fito tace "Umma na zuwa." Ta bar parlon, ta kula yau kamar ransa a ɓace yake, ai kuwa ta chanka dai-dai




Umma na fitowa tace "Me nike gani haka waye ya taɓaka Sultan lafiya dai ko.?" Ta jero mai waɗannan tambayoyi tana shafa kansa, da ba hula, rungumeta ya yi kana yace "Umma wai Abba ne be yarda nayi wani aure ba sai dai na mayar da Farida, nikoma wallahi har abada ko mai sunanta bazan koma aure ba."




shiru Umma tayi kana ta zauna kusa da shi tace "Gaskiya wannan maganar bata taso ba yarinyar da aka haɗa kai da ita a kashe ka shine za'ace ka maida ta gidanka, ni yanzu shawarar da zan baka kaje wurin Alhaji Abubakar ka sanar dashi ya yiwa Abbanka magana,


Ya bari ka aure wacce kakeso." Sai lokacin Sultan ya saki ranshi yace "shiyasa nike sonki Umma yanzu daga nan zan wuce gidansa na sanar da shi duk yadda akayi zan dawo gobe na sanar da ke." Umma tace "Yauwa ɗan albarka, Allah ya shige muna gaba." Yace "Amin ni zan wuce." Addu'a tayi mai kana ya wuce,




duk abinda suke tattaunawa Suhana ta jinsu, Wai dama Sultan ya taɓa aure har matarsa ta nemi kashe sa? Yana fita Unguwar Bado ya nufa, gidan Yayan Abbansa, har bar gida ya same shi zaune yana duba jarida cikin fara'a ya tarbe Sultan bayan sun gaisa cikin girmamawa Sultan ya kora mai bayani,




ya samu wata yarinya gidan marayu ya ɗauko ta, aurenta za shiyi saboda suna son juna amma Abba ya hana sai dai ya maida Farida, Alhaji Abubakar najin wannan magana ransa ya ɓaci yace "Wai har yanzu Yusuf beyi hankali to wallahi ƙarya yake ni nan zan ɗaura ma aure da ita, ko yaƙi ko yaso,




ai nima Mahaifinka ne barni da shi kawai yanzu ina yarinyar take.?" Sultan yace "Tana gidan Umman Kamal." Alhaji yace "Ma sha Allah kace yarinyar zata ƙara samun tarbiyya, mai kyau gaskiya kayi tunani mai kyau da ka ajeta gidan Fateema, yanzu ka tafiyarka gobe zan kiraka."




godiya Sulatn ya yi mai sosai kana ya bar gidan Alhaji ya rakasa da idanu, cike da tausayin Sultan,


Niko nace wai menene ya samu Sultan haka kowa kejin tausayinsa? Muje dai zuwa,


Umma ya kira a waya ya sanar da ita yadda suka yi,


Jamal kuwa da Afiya sun karaɗe garin Sokoto wurin neman Suhana amma shiru kakeji tsabar iskanci har da Kamal ake yawon nemanta,hhhhh gaba ɗaya hankalinsu yafi tafiya akan Suhana bata garin ta koma Abuja, dole suka haƙura da nemanta,




Washegari Alhaji Abubakar ya kira Sultan ya sanar da shi, zaije wurin Umma ya ga yarinyar kana ranar juma'a a ɗaura auren a babban masallacin juma'a, Abbansa yace dole sai dai ya haɗa biyu, da Suhana da Farida saboda haka ya yi haƙuri ta mayar da Farida kawai a ɗaura aurnsu da ita ranar assabar,




Sultan yace a ɗaura rana ɗaya, Alhaji Abubakar yaje gidan Umma ya duba Suhana sosai ta kwanta mai a rai miliyan ashirin ya bata tayi hidamar biki duk da tace bata komai saboda bata da wasu dangi, Umma ce ta kira Sultan yazo ta kai Suhana gidan kitso da lalle, saboda ,




lokaci ya ƙore, ƙarfe sha 11:00 na safiyar Alhamis yazo ya ɗauka ta zuwa unguwar, Tudun Wada wani shagon gyaran jiki ya kaita wanken kai aka fara yi mata kana akayi mata kitso da lalle, ga Dilka, da halawa, lokaci ɗaya Suhana ta sauya kamar ba ita ta ƙara wani haske ga kyau ma sha Allah!


ta fito kamar ko wace amarya, sai bayan sallar isha'i yazo ya biya kuɗi kana ya dawo da ita, gida, wasu mahaukatan akwatina. ta samu tsakiyar paroln Umma har dozin uku, shaƙe da kaya na Alfarma ga sarƙoƙin zinari kamar a banza, aka ɗauko so, Umma tace Bayan ya kaita wurin lalle ne ya kawo kayan tare da Kamal,


Wai lokacin suka haɗo kayan Dubai ya yi odarsu, ta bawa Kamal kala ashirin a ɗinko mata kala goma ta samu na sakawa gobe, idan telan ya ɗinke saura sai ta saka Kamal ya karɓo mata, tare suka shigar da kayan ciki, kana tayi wanka




Umma ta zaunar da ita bata Naman kaza tanaci tana ɓata fuska har ta kammala wasu ruwan tsimi ta bata tace ta shanye, su tafi bathroom, ta haɗa mata ruwa ta zauna a ciki sai sun huce daren dai gaba ɗaya Umma sai jiƙa Suhana takeyi, washegari da safe, haka suka ɗora, a dama mata wannan a jiƙa wancen taci wannan,




ƙarfe ɗaya Umma ta saka tayi wanka da ruwan lallen da ta jiƙa ya kwana ya sha turaruka, ma sha Allah! Kozo kuga yadda Suhana ta ƙara kyau zama tayi gaban mirror ta shafe jikinta da wasu mayuka, masu kyau, kana ta shafa kwalli da man baki saboda bata kwalliya, Kamal ne ya shigo da wasu manyan ledodi,




Yace "Madam Suhana ga kayanki na karɓo wurin ɗinki gaba ɗaya an ɗinkee su jiya kan tela muka kwana." Dariya tayi kana tace "Godiya nike." Kana ta janyo ledar ta fara duba kayan sunyi kyau ma sha Allah! Wani farin lees ta saka anyi mai ado da blue, ɗinkin dogowar riga ne,




ta kafa ɗaure tayi kyau sosai ta saka takalmi blue da mayafi, da jaka, ƙarfe biyu na rana bayan an gama sallar jumu'a aka ɗaura auren Muhammad Sultan Yusuf, da Suhana, Kabir, bayan a ɗaura ne aka ɗaura na Farida Aliyu Da Muhammad Sultan Yusuf, ana gama ɗauren auren,




Sultan ya wuce hotel ya yi kwanciyarsa, saboda baya son hayaniya, Matar Alhaji Abubakar ce Hajiya Sauka ta shirya ita da wasu ƙawayenta, sukaje da mayan motoci na Alfarma, wurin ɗaukar Suhana, koda sukaje wasu ƴan uwan Umma sunzo sai hidima akeyi Umma ta saka Suhana wani wanka ta shirya cikin wani Black ɗin les tsadadde mai taushi,




ta saka farin mayafi, da takamli, Umma nayi mata nasiha mai ratsa jiki sai da Suhana tayi kuka haka dangin Umma sukayi mata faɗa haka su Hajiya Saima suka iso sun samu tarba mai kyau sun yaba da mutuncin Umma, aka kawo musu ruwa da lemo da abinci, kafin Umma ta fito da Suhana sai kuka takeyi,




wasu ƙannen Umma ne guda uku suka fito da ita waje aka wuce da cikin mota har da kwallah Umma tayi, ji take kamar ƴar cikinta ce, ta aurar da ita, Direba ne ya shigo ya kwashe kayan Suhana gaba ɗaya, kana suka tafi, gidan Alhaji Abubakar suka sauka, Hajiya Saima sai jan Suhana takeyi ajiki, saboda sai bayan sallar isha'i zasu kaita,




Gidan gwamnati, a chan zasu zauna, ana gama sallah kuwa Hajiya Saima ta saka Suhana wanka da ruwan turare ɗan Maiduguri, kana bayan ta fita da kanta ta shirya Suhana cikin wata jar atamfa, kana ta saka mata alkibba, ta feshe ta da wasu turaroka, masu ɗaukar hankali,


ta janyota suka fito, sai kai tsaye gidan gwamnati suka wace, da ita bayan sun isa babban paroln Hajiya Uwani suka wuce da ta duk da Hajiya Saima ta san ba tabar arziki zasu samu ba haka kuwa ta faru, ko wurin zama ba'a basu ba, sai kallon banza suke watsawa Suhana da bata san sunayi ba,




Saima tace "Hajiya Uwani ida Yusuf na ciki magana nikeson yi da shi, ga surukarsa an ɗauko." Cike da tsiwa Uwani tace "Baya nan." Daga haka ta bar parlon ta haura sama, Hajiya Saima taja hannun Suhana suka fito, sunyi tafiya ba sosai ba wani part suka shiga, tace "Ki shiga da ƙafar dama kiyi addu'oi."


bayan ta kammala suka shiga ciki Wow parlon ya haɗu sosai ya sha kayan more rayuwa, aljannar duniya kenan, kai da gani kasan naira tayi kuka a wurin , komai na parlo blue and white ne, har kujeron dake ciki da labulaye, sama suka haura, nan wani babban parlo ne mai ɗauke da 3bedroom da kitchen da stor,




ɗaya daga cikin dakunun Hajiya Saima ta kai Suhana kana ta saka direba ya kwaso mata kayanta zama tayi ta kira Sultan ashe yana ciki bayan ya zo tayi musu nasiha sosai, kana ta wuce, ta barsu, tashi ya yi kana yace "Kije kiyi alwala kizo muyi sallah."




daga haka ya fice ɗakin, ta jima zaune kafin ta shiga bathroom tayi alwala, ta fito, akwatin kayanta ta fara dubawa tayi sa'a da hijab a ciki ta saka, kana ta fito, tsayawa tayi, tana tunanin wani room yake, na kusa da nata ta shiga yana ciki, yana jiranta, kallo ta ƙarewa bedroom ɗinsa ya yi kyau sosai, sai ƙamshi yake, yi,


gyaran murya ya yi kana ta hau kan sallaya ya tada sallah bayan sun kammala ya dafa kanta ya yi addu'oi kamar yadda addini ya tana nadar, kana ya shige bathroom, ita kuma ta dawo ɗakinta wata rigar bacci ta saka red color, duk jikin rigar net ce, ta shife jikinta da turaren da Hajiya Saima ta bata kana ta kwanta,




zuciyarta fal da tunani kala-kala Sultan kuwa wanka ya yi ya shirya cikin kayan bacci, kana ya fito parlo da niyar kallon ball, wani ƙamshin turare ya dake hancinsa, sai da yaji Dick ɗinsa ta halba, da ƙarfe, kasa zama ya yi ya fara biyar inda yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login