Showing 15001 words to 16222 words out of 16222 words
Chapter 6 - RUHIN FANSA By Maryam Majidadi part 2 -1-1.txt
ta Kuma saki tace"Ahaad karka kashe d'an uwanka,dan Allah kabarmun yarona Ahaad"ta wuce gabansa zata duk'a,da sauri ya riketa ya kawar da kansa gefe"daku kamani gara na kashe kaina,bazan tab'a bari na mutu a hannunku ba"kanshi ya saita Mama tana kiran"a'a Amaan karkamun haka".kallonta yayi hawaye na zubowa daga idonsa yace"ki yafemun Mummyna"kafin tayi magana ya harbe kansa a take ya mutu a wurin ko shurawa beyi ba.y'an sanda suka kwashe su sai office dinsu Fadila kam a sume aka kwasheta sai asibiti,har Dr Jamil an kamo tare aka rufesu a office din y'an sanda.duk abunda sukeyi Daddy yana jinsu daga part dinshi be fitoba ,ya rasa meke masa dadi,kwakwaran motsi baya iyayi.cikin sati d'aya aka shirya komai aka Kai ,Mummy ,Hajiya Sadiya da Dr Jamil kotu,Shuhada da barista Abbas sune suka tsayawa Shuzna,ba wani b'ata lokaci suka ansa laifukansu,kotu ta yankewa Mummy da Hajiya Sadiya zaman gidan yari na shekara biyar da tarar dubu d'ari bibiyu,sannan su mayarwa Najma da dukiyarta.Fadila kam Shuzna bata yarda an kaita kotu ba,yarda taga tanata faman kuka da rokon Shuzna gafara ,ga tausayina Nasirah da Shuzna keji yarinyar bata da damuwa,tun kafin ayi wannan rigimar dama aka dauke Mama da Nasirah aka had'asu dasu Ummu dasu Faida.cikin sati biyu aka sallami Fadila suka dawo gidan Shuzna,ga Umti da Daddy Bashir sunzo Family ya hadu sai tattauna sukeyi da sanin abubuwan da suka faru a da.da gudu Shuzna ta shigo rike da wasu takardu ."a'a har yanzu kina nan da wannan shiriritar taki ?"Ummu ta tambaya, murmushi Shuzna tayi ta rungume Mama tace"Hajiya Mama yau jikarki ta koma da sunanta Najma Jafar Bindawa,Komai nawa ya koma da sunansa na da".Alhmdllh Umti ta fad'a ta dafa kafadar Shuzna tace"y'ata Najma kiyi hakuri da rasa fuskarki"rungume Umti Najma tayi tace"ba komai Mamana".tureta Muslim yayi yace"dallah malama tashi anan,zaki karyamun Mama".rigiman hakan suka fara Ummu ta janyoshi tace"barsu suje Sojana ae nima ga y'ata nan"ta fad'a tana janyo Shuhada jikinta ta had'asu ta rungumeta,hannuwansu ta had'a wuri d'aya tace"nima ga ma'auratana na had'a,zanyiwa Muslim da Shuhada aure"kowa dariya ya saka ,Shuhada ta boye fuskarta jikin Ummu,janyo hannunta yayi yace"haba masoyiya kunyata kikeji ne?".dungure masa Kai Mama tayi tace"gaba d'aya baku da kunya Kai da wancan labcecen bayahuden"harara Ahaad ya maka Mata wanda tunda ya zauna saika dauka baya d'akin.shigowar Aiban d'akin yasa suka takaita dariyar sai da ya gaishe da kowa sannan ya zauna kusa da Mama,"kaga yaron kirki mai tarbiya ,sannu da zuwa Aibanu".danna k'afar Mama ya farayi sannan yace"Mamana nazo neman aure fa"."yi sauri gayamun wace mai sa'ar ce?,gaskiya na gaji da zamanku hakanan dama".sunkuyar da kansa yayi alamar kunya sannan ya rad'a Mata a kunne,"Alhmdllh,Alhmdllh,Allah na gode maka,Aiban Allah yayi maka albarka Kuma na maka alk'arin baka abunda kake so Koda hakan zai Zama abu na k'arshe da zanyi,Allah ya shiga lamuranka,na baka Najma duniya da lahira".wani irin bugawa da k'arfi zuciyar Ahaad yayi ,"toshi Papa waye zaku bashi ya aura?"Fayyam ya tambaya."baba ko ubanwa,aeshi wannan fad'in ran nashi bazai barshi yayi aure ba".turo baki Fayyam yayi yaja hannun Nasirah yace"sai kiyi dama ae halinkine"tunda Nasirah ta dawo gidan Fayyam yake kula da ita,baya yarda kowa ya tab'a ko da wasa,"tsohon marar kunya Wanda yayi gadon ubanshi".
Bayan sati biyu
Ko wanne b'angare Shirin biki sukeyi ba k'akkautawa, yayin da Ahaad tun ciwo yana cinsa a tsaye har yakai gaya kwantar dashi ko fita bayayi kullun yana kwance kawai.ko kad'an Mama ta hana kowa ya kulashi tace a barshi can shiya sani.
Kaya Muslim ya ajiye masa yace"ka tashi ka shirya mu tafi,lokaci yana kurewa".Jan pillow yayi ya rufe fuska cikin dishewar murya yace"kuje kawai bazan iya fita ba".sai da Ummu tayi da gaske sannan Ahaad ya shirya cikin blue din shadda suka saka mai matuk'ar tsada sai black din huda da black din takalmi sai fitar da sihirtaccen kamshi sukeyi.haka suka tafi daurin auren.wuri ya cika makil da mutane na nesa dana kusa,baka iya banbance wurinwa wane yazo,dafe Kai Ahaad yayi da yaji yana barazanar tarwatsewa juyawa yayi yaga babu mai kallonshi ya samu ya fito daga cikin masallacin can baya ya koma ya zauna tare da had'e Kai da gwaiwa yana jin jiri,jin hawaye masu dumi yayi suna bin fuskarsa..kamar daga sama yaji ana cewa an daura auren Muslim da Shuhada,Aiban da Fadila sai Ahaad da Najma akan sadaki naira dubu d'ari.a firgice ya d'ago yana jin tabbas mai shelar nan bejiwa kunnensa daidai ba.murmushi Aiban yayi masa lokacin da suka had'a ido yazo ya kamashi ya d'auki babbar rigarsa daya cukurkude ya ajiye a k'asa"ace ango ya b'ata kwalliyarsa haka?,kakkabe rigar yayi ya saka masa ya Kama hannuwansa yace"Congratulations angon Najma Allah ya bada zaman lafiya".tangare k'eyarsa Muslim yayi yace"raggon maza,ashe kasan kana Santa ka saketa"kasa furta komai Ahaad yayi sai murmushi kawai da godewa Allah da yakeyi a ranshi,"kada ka damu,ni bazan raba zuciya biyu ba,ina tabbatar maka itama Najma tana sanka ".Jan hannunsa sukayi zuwa cikin mutane fara'a kawai yakeyi yana gaisawa da mutane haka har suka samu damar komawa gida bayan hotunan da suka sha sunyi kyau kamar y'an ukku.koda suka shiga gidan an tsara wurin sosai anayin y'ar dinner,kujerune ukku inda su Najma suka zauna komai nasu iri d'aya fuskarsu a rufe sunyi masifar kyau.rike hannun Ahaad Umti tayi tace"yarona muje ka fara zab'ar matarka a can"binta kawai yayi a wurin ta tsakiya ya tsaya inda Shuhada take kenan,har zai budeta Kuma ya fasa ya tsaya yana k'are masu Kallo su duk'a,matsawa yayi can hannun dama sannan yasa hannu ya yaye lullubin take fuskar Najma ta bud'e Tasha kwalli,ihu mutanan wurin suka dauka tare da tabi ana masu ruwan nera da turare,sosai abun ya k'ayatar.
5years later.
Yarinya kyakyawa ke gudu ta fad'a jikin Ahaad tace Daddy "kacewa Ammi ta kyaleni ni bazan koma gida ba"Farna ta fad'a tana fad'awa jikin Aiban,dariya Ahaad yayi yace"Captain kibar yarinyar nan wurin Babanta,bazata bimu bafa"dariya sukayi Najma tace to"nima zan tafi da little Najma kuwa"ihu Farna ta saka ita bazata yarda ba,fuska Fayyam ya yatsina yace"u idiot keep queit mai bakin parrot kawai"ba musu ta hadiye ihun da takeyi tasan yanzu sai tasha dukan tsiya..
A yanzu Fadila yaranta biyu Little Najma da Mahamud,sai Nasirah da take wurinta, Shuhada kuwa ukku dan Muslim yace saiya ta taddosu yara,Islam itace babba sai Afnan sannan Salim shine auta,Najma kam Faida da Fayyam sai Farna kawai data k'ara.sosai suke kaunar junansu suna zaman lafiya komai ya koma lafiya suna sada zumunci,a cikin satinne Kuma aka saki Hajiya Sadiya da Mama,shikam Jamil shekara Goma zaiyi dan haka yanzu yayi rabi,sosai Mama da Hajiya Sadiya suka canza zaman lafiya sukeyi suna Kuma San jikokinsu da iyakansu gaba d'aya suma ko wacce ta koma d'akin mijinta,Ummu ce kawai taki yarda ta sake aure take zauna da tsohuwa Mama Wanda tsufa ya fara kamata.
Fadin irin soyayyar da Najma da Ahaad sukewa junansu b'ata lokacine yanzu kam Babu abunda ke rabasu zaman lafiya sukeyi da nunawa juna matuk'ar soyayyah.
*alhmdllh, Alhmdllh,Allah na gode maka daka bani ikon kammala k'arshen littafin nan,Allah ka yafe mana kurakuren dake ciki,Allah kasa kuma a amfana da abunda ke cikinsa*
*Sakon godiyata ga masoya Ruhin Fansa,na gode kwarai da nuna kauna a agareni,sanso fisabilillah,wannan littafi sadaukar ne ga masoya labarin Ruhin Fansa*
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.
Stylish star
Jorderh majidadi