Showing 9001 words to 12000 words out of 16222 words
Chapter 4 - RUHIN FANSA By Maryam Majidadi part 2 -1-1.txt
wurin tabi layi cikin sabbin ma'ae katan da aka dauka sannan ta sanya hular dake hannunta tayi,kamar yarda aka tsara taron yayi kyau sosai kuma anyi jawabai,manyan sojoji aka gabatar ciki harda Ahaad Wanda yanzu yake rik'e matsayin General Muslim ma haka,lokacin da aka gabatar da Shuzna a matsayin Captain ta gidan soji wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta,ta d'aga kanta sama tayi magana a hankali tace"Allah na gode maka,Ina nan zuwa gareku iyalan Kabir Bindawa,wasan yanzu aka fara",tana fitowa daga wurin Nani ta rungume tace"y'ata Allah yayi albarka,wannan ma wani matakin nasara ne a rayuwarki,na tayaki murna sosai y'ata"haka y'an gidan suka koma gida cike da farin ciki ga Shuhada ta zama cikakkiyar lawyer itama ta cika burin nata.
"Ki tashi,ba lokacin baccinki bane wannan,lokaci yayi da zaki cika alk'awarin da kikawa Ruhina ,ki tashi Najma ,ki tashi". firgigit Shuzna ta farka daga baccin da ya d'an dauketa bakinta dauke da addu'ar bacci,duk lokacin data kwanta bacci takanyi mafar amma na yau ya banbanta da ko yaushe,lallai Najwa tana tunanin kamar ta manta da burin d'aukar Fansa dake cikin ranta Wanda ko yaushe yake cin Ruhin ta,"a'a Shuzna lafiya dai ko?"Umti ta fad'a tana kallon yarda Shuzna ta jik'e da zufa,da gudu Fayyad ya k'araso ya rumgumeta cikin kwarancinsa yace"Aunty kice ya daina",Fayyam ne ya rugo wurin shima yana cewa"bani abuna"b'oye abun wasan Fayyad yayi,kallonsa Shuzna tayi tace"my boy kaga Yayanka ne Fayyad ,ka daina binsa haka da gudu sai kunje kun fad'i?".tsalle Fayyam ya daka tare da kwala ihu ya fad'i akan tayil yana kururuwa,wata zuciya tazowa Shuzna ta fizgoshi ta dalla masa mari tare da sakar masa dundu.bai fasa abunda yakeyi ba,cikin Sauri Ahaad ya safko daga bene yace"karki k'ara dukanshi haka,yaron zaki wa duka kamar kina filin daga?,ke waye ya dakeki?". murgud'a baki Shuzna tayi cikin zuciya tace"shi yaro ba'a da ikon masa magana?,Babu abunda ya ajiye sai dukan y'an uwansa,nan jiya sai da ya fashewa Faida goshi yanzu kuma ya biyo Fayyad wallahi bazan dauki wannan iskancin nashi ba"ta d'auki Fayyad tayi wucewarta,k'wafa Ahaad yayi ya d'auki Fayyam yayi ciki dashi.
"Bazai yiwuba Muslim,wannan ba abunda zan iya yarda dashi bane,kayi hakuri bawa Shuzna fuskar Zeenart ba shi yake nuna kazo kace kana sonta ba Kuma,Shuzna tana da miji Kuma gidan uban y'ay'anta zata koma da yardar Allah"Umti ta fad'a.
Dafe kai Muslim yayi yace"Umti kada kiyi mun haka dan Allah,na tsaya tsawan shekaru ina kallonta kamar Zeenat na bari ta haihu ne kafin na bayyana mata soyayyata,Umti ki taimaki d'anki Wanda tsawan Shekara 5 kenan aka kashe masa masoyiya ya shiga tashin hankali har yanzu ya kasa samun wacce zata maye gurbinta".d'aga masa hannu Umti tayi tace"ya isa haka Muslim bawai bana tausayinka bane ko wani abu ba a'a ,kasan zanfi kowa san ganin farin cikinka,amma kaddara bata zo da Shuzna gidan nan danka aureta ba,na gama magana Kuma kada in k'ara jin kayi maganar da wani".duk'ar da kansa yayi cikin ladabi yace"to Umti insha Allah zanyi kamar yarda kike so,amma ki sani babu ranar da zan iya yin aure ko naga wata da kaina nace ina santa".yana gama fad'an haka ya tashi ya fice daga wurin.tashi Umti tayi ta wuce d'akin Shuzna samunta tayi kwance tayi rubda ciki ,jin an bud'e kofa yasa Shuzna juyowa ganin Umti yasa ta tashi tace"a'a Umti aeda kin aeko sai nazo basai kin taso da kanki ba"kallon Faida tayi yarinyar kyakyawar gaske gata fara tas tace"kije wurin Ummanku(Nani)Ina zuwa kinji".da gudu Faida ta gice daga d'akin.gefan gado Umti ta zauna tace"Shuzna yau zan sauke alk'awarin dana dauka kanki,kinga komawarki nan Nigeria ina tsoronsa sai dai babu yarda zanyi tunda aeki ya kaiki can(zataje yin wani aeki Nigeria),Kuma ko ba aeki nasan tabbas zaki koma gida,wannan fuskar dana baki Wanda nasan kinsan fuskar Zeenart ne y'ar aminiyata,Kuma itace wacce D'ana Muslim zai aura,wannan fuskar bata cancanta a badata ga kowa ba,saboda ba kalar kowa bace,lokacin da aka kawoki,duk da kina a sume amma naga idanuwanki suna fitar da hawaye,naga kina da San k'ara rayuwa,baki da wani muradi daya wuce wannan,shine dalilin da yasa na dage wajen neman mafita a kanki cikin yardar Allah kuma muka samu nasara,Ina so ki sani Zeenart kasheta akayi ba mutuwa tayi ba,yankan rago akayi mata saboda sanin wani sirri da tayi,zan gaya maki Wanda yayi mata haka,amma ko da wasa kiyi mun alk'awarin bazaki tab'a fad'awa kowa ba".jinjina Kai Shuzna tayi tace"Umti basai kin rok'eni ba,zan iyayin komai a kanki". murmushi Umti tayi taci gaba da cewa"Amaan shine Wanda ya kashe Zeenart"a matuk'ar firgice Shuzna ta kalli Umti baki na rawa tace"dama ya santa ne?"."dalilin mutuwarta ne yasa ta gitta a rayuwarsa,tabbas zaki fuskanci k'alubalan da yawa daga wurin Amaan,amma insha Allah zaki tsallake Kuma duk wani sirrin da yasa ya kasheta Zeenart ta gama bayyanamun komai insha Allah idan lokaci yayi zan baki,ke dai ki kula da kanki".Umti bata jira cewarta ba tayi waje abunta.jujuya Kai Shuzna takeyi a tsawace yace"Wai kai wanne irin mutunne Amaan?,tabbas ka kasance azzalumi mai rusa farin cikin kowa,tabbas ka shirya ina zuwa gareka,ba Kuma zan tab'a tunanin kai D'an uwana bane".wayarta data soma ruri ta dauka ganin Barista Abbas yasa ta dauka da sauri tace"Ina zuwa yanzu"kashe wayar tayi bata jira komai ba tayo waje kawai,masu tsaronta suka taso tare da bud'e mata mota ta shiga ,kamar kullun da mota biyu suka fita .ba wani nisan tafiya sukayi ba ta k'arasa inda zasu had'u da Barista Abbas zama tayi a d'ayar kujerar dake kusa dashi tace"barka da zuwa Barista, harka huta daka fito haka da wuri?". murmushi yayi yace"ae dole nayi abunda ya kawoni k'asarnan,balle Kuma aeki daku manya ranki ya dade,nasan zaki shiga rud'ani dajin abunda zan fad'a maki amma karki wani damu kaddara ne yazo da haka,Fadila itace wacce tayi niyar sakawa ayi maki Fyad'e a Kuma ranar da Dr Jamil yayi maki wannan allurar,ta ajiye lemu a firij dinki shine Ahaad ya taka sawun b'arawo ko ince Allah yana sanki ya kub'utar dake daga tarkon Fadila,Ahaad yasha lemun da Fadila ta ajiyene kuma shine Wanda yayi maki Fyad'e a wancan lokacin a tak'aice dai shine uban y'ay'anki".jefar da glass Cup din hannunta tayi a matuk'ar razane ta mik'e tace"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,ni ,ni Shuzna Ahaad shine Wanda yamun wannan abun?"take kalamansa da yake kiranta da Dabba,mazinaciya,dak'ik'iya suka soma dawo mata radau a kunne kamar yanzu yake fad'a mata haka,ihu ta saki Allah ya taimaka wurin rufe yake da glass Babu Wanda zai iyajin sautin muryarta,hannu tasa ta dod'e kunnuwanta tace"a'a,a'a hakan Sam bazai yiwuba,na tsane shi,na tsane shi,meyasa duk wani farin cikina Ahalina suke k'ok'arin rabani dashi".dafata Aiban yayi yace"meye haka kikeyi?sai kace wata warda aka fad'awa mutuwa?meye da Ahaad din?Wanda yanzu zaki godewa Allah kin haifi yaranki da aurene,ba shegu bane da ubansu".lokaci d'aya fuskarta tayi jawur harda k'asan idonta had'e fuska tayi kamar an saukar mata da mutu ta kalli Aiban da idanuwanta Wanda suka firfito waje alamun tsananin b'acin rai cikin kausashiyar murya tace"na tsane shi,na tsane shi,har abada bazan tab'a sassautawa wani daga cikinsu ba,sun tarwatsamun rayuwata"."duka abunda aka yi maki ke shaidace Babu saka hannun Ahaad a ciki,wannan ma kaddara ce kawai,Ina so ki sani zafin kiyayyah baya canza komai Shuzna"."haka zalika bazan tab'a bari suyi nasa a kaina ba wannan karon,yanzu ne zan fuskancesu,meye amfanin rayuwa idan har za'a rayu babu martaba?,zalinci kawai suka saka gaba,suyi farin ciki yau Baba Kabir ya zama Governor a garin katsina ,dan zuwa gobe tunaninsu zai hargitse ne gaba d'aya"files din da Barista Abbas ya ajiye mata ta dauka ta fice daga wurin suka bita da ido.
Tunda ta shiga mota take kuka harta k'arasa gida,goge fuskarta tayi ta fito cikin izza tana tafiya shan gabanta yayi yace"Najma daga Ina kike?".a hassale tace"daga inda ka aekeni malan".sosai ran Ahaad ya b'aci da ansar data bashi ya daure fuska ya nunata da hannu"yake ki kiyayeni,niba tsaranki bane da zakina fad'amun duk abunda yazo bakinki,sake maki da nakeyi baya nufin ki rainani kuma,ki rika shiga yarda kike so kina fita Kuma ki dawo lokacin da kike so". murmushi tayi tace"kasan Dabba abunda yazo kanta kawai takeyi ,yawan kasuwancin Dana saba na tafi".ji kakeyi tas tas tas ya daiketa da kyawawan maruka.ko gezau batayi ba bare Kuma ta nuna masa Marin ya shigeta ta nunashi da hannu tace"wannan ya zama na k'arshe da wannan k'azamin hannun naka zai sake tab'a wani b'angare na jikina,bazanyi mamaki ba tunda gadon zalinci kayi,Ahaad na tsaneka ,na tsaneka ,na tsaneka bana son sake ganin fuskarka ina Dana sanin kasancewa a cikin zuri'arku"wata irin zuciyace kecin Ahaad ya rud'e gaba d'aya tunda yake a rayuwa ba'a tab'a gaya masa ba'a sanshi ba,ko wacce macce burinta ya kulata,amma yau shi ake gayawa haka,dandanan idonsa ya canxa yace"ni kike gayawa haka"."ka sani bazan tab'a yafe maka kusantata da kayi ba,ni yarana ba yaranka bane,kada ka k'ara nuna wata alak'a a tsakaninku,ka fita daga rayuwata dan Allah".
7years later
Allah ka gafartawa iyayenmu kasa muyi kyakyawan karshe
Stylish star
Jorderh majidadi
ππππππππ
*RUHIN FANSA*
ππππππππ
Na
*Maryam ismail Majidadi*
Part 2 ,part 2 ,part 2
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*ππ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Page 36-40
7 years later
Jirgin ne ya sauka babban filin jirgi a Kano,cikin takun k'asaita ta safko ,sanye take da kakin soji ba kad'an kayan sukayi mata kyau ba,lumshe idonta tayi tana jin wani sanyin dad'i na shigarta ga iskar garinta dake ratsata,lallai yau dole ta godewa Allah,tsawan shekara goma bata garin amma yau gashi ta dawo mahaifarta,bayanta Nani ce da Shuhada sai y'aranta Wanda suka gama Zama samari Faida an Zama y'an mata ko wanne cikinsu fuskarsa dauke da murmushi,cikin yaran dake k'ark'ashinta ne suka zo daukarsu saukar safiya sukayi dan haka suka d'auki hanyar katsina dan nan ne zatayi aekin nata a k'asarta Kuma a garinta,titi kawai take Kallo tana tuna rayuwarta ta baya har suka iso tank'amemen gidanta na katsina batace da kowa komai ba.Fayyam kam sai yatsine fuska yakeyi yace"Ni Mamie ki mayar dani wurin Umti bana son zama garin nan".dafa kafad'arsa tayi tace"Son nan ne fa garinka na asali ,nan ne garin kowa naka".zaro daradaran idonsa yayi yace"Mamie kina nufin su Daddy dinmu nan ne garinsu?"dariya kawai tayi tace"kuje ku huta anjima kayi tambayar naka"Mai aekinsu ta jasu zuwa d'akinsu,sai Nani ta ja Faida dan tayi mata wanka.
Da gudu yaran ke riga rigan fitowa jin Muryan Aeban,kowa so yakeyi ya fara rungumeshi,duk'awa yayi ya ware duka hannuwansa ya tungumesu gaba d'aya,dingure kan Faida Fayyad yayi yace"harda wani saurin riga na fitowa".wani mugun Kallo Fayyam ya wurga masa Wanda yake fitowa yanzu cikin takun izza yace"wallahi idan ka k'ara ture mun k'anwa saina karya maka hannun gobe inga da wanne zakayi".ya samu Chair ya zauna sai huci yakeyi,"k'anwarka ce kai kad'ai malan?ko nakaga wasa mukeyi bane ,Fayyam ka fiye neman tsokana"Fayyad ya fad'a.glass cup din dake kusa dashi ya dauka yayi jifa dashi amma ya kasa furta komai da sauri Shuzna ta safko daga sama tana fad'in"subhanallah lafiya?"tsaye tayi turus tana kallon ikon Allah,sakin Fayyad Aiban yayi ya k'arasa ya Kama Faddam yace"haba son kullun ina gaya maka ka daina fad'a da y'an uwanka baka bari,kai kullun sai kayiwa wani duka".cikin d'aga murya yace"to Daddy ae laifinka ne,kaine ka bari Fayyad da Faida suka fara rungumarka kafin inzo,Ni bana son sai wani yayi abu sannan in yi".murmushi kawai Shuzna tayi ta k'arasa shigowa parlon tace"Fayyam ka cika rigima da yawa ,to su ba Yayanka da k'anwarka bace".alama Aiban yayi mata da tayi shiru ya rungumo Fayyam jikinsa yace"am sorry son".Shima Fayyam din rungume Aiban yayi saboda yana matuk'ar sonshi.
Bayan sati d'aya da sukayi a Nigeria ,komai ya daidaita Aiban ya saka yaran makaranta boko da islamiyyah makarantu masu kyau ya Kuma d'aukar masu mai lesson komai yana tafiya yarda suke so,yaune kuma plan din Shuzna zai fara aeki dan ta gama shirya komai ,musamman yanzu da Abba(Kabir)ya Zama Governor na garin Katsina.bayan yara sun tafi scul, Shuhada ta yafi wurin aeki tayi wanka ta shirya cikin dogon riga Purple colour sosai tayi mata kyau ta dauko k'aramin bak'in veil ta daure kanta dashi,hand bag ta dauka bak'a sai hills shoe dinta ma bak'ak'e sai fitar da sihirtaccen kamshi takeyi tana fitowa ta rungumi Nani tace"saina fawo Nani,ki kula da kanki".shafa kanta Nani tayi tace"Allah ya tsare hanya y'ata,kinyi matuk'ar kyau sosai".Shuzna tana fitowa masu tsaronta suka taso da mota biyu suka fita kai tsaye wurin shak'atawar da yasan kamar yanzu zata samu Wanda take nema ta nufa,Koda suka isa da aka bud'e mata mota bata fito ba sai da ta tabbar ta hango Wanda take nema,murmushi ta saki sannan ta ziro k'afarta fari tas ta jima kafin ta idasa fitowa gaba d'aya,Masha Allah shine mutanan dake wurin suke fad'a saboda tsananin kyan halittar Shuzna da suka gani.kallon Islam Fadila tayi tace"Islam waccan ba itace wacce taci gasar nan a k'asar India ba?".kallon Shuzna Islam tayi sosai tace"Masha Allah itace ko,a filima tafi kyau akan a hoto"tsura mata ido sukayi,ita Kuma kai tsaye ta wuce daidai inda suke cikin wata murya mai dadin sauraro tace"zan iya zama?,bana son side dincan".har had'a baki sukeyi wurin fad'in"sure madam". murmushi ta sakar masu ta zauna,order tayi masu na kayan ciye ciye kala kala kafin kace me an cika teburin gabansu,ruwa kawai Shuzna ta kurb'a ta soma aekin latsa waya,amma a bad'ini tana nazartar su ne,cikin felek'e Fadila tace"sis bazakici komai bane?".gyad'a kai Shuzna tayi tace"am owk don't worry".bata dad'e a wurin zaune ba ta mik'e tace"na gode zan wuce"ATM dinta ta mik'a wa d'aya daga cikin yaranta tace"ka biya bill din".cikin girmamawa ya k'arb'a yace "owk Madam".cikin sauri Fadila ta mik'a mata hannu tace"am Fadila Kabir bindawa y'ar Governor ta nan garin".sakin fuska Shuzna tayi ta bata hannu tace"nice to meet u am Shuzna Bashir".Islam ma hannu ta bata tace"Islam Sadeeq,ko zamu iya zama friends".hannu ta bata itama tace"why not?,sure".Jakarta ta bud'e ta fiddo card dinta ta basu ta d'aga masu hannu ta wuce.
Da gudu Fadila ta k'arasa shiga parlon Hajiya Sadiya tsakiyar su Mummy ta fad'a tace"albishirinku".da goro Hajiya Sadiya ta ansa tace"yau Kuma wanne kamun y'an matana suka yomun?"washe baki Islam tayi tace"Umma yau babban kamu mukayu,Ina Shuzna Bashir yarinyar nan da taci gasa a k'asar India ta computer?".cikin sauri Mummy tace"eh,eh meya faru?".carab Islam ta ansa da cewa"wallahi yanzu muka rabu da ita,kunga katinta data bamu mun Zama k'awaye".gud'a Hajiya Sadiya ta saki tace"lallai yau babban kamu,kuyi kokari ku janyota jikinku mu dangwali dukiya mu barga inda take,ae ba abun wasa bane wannan".kafin kace me harsun gama tsara yarda zasu janyo hankalin Shuzna zuwa ciki su"."ae insha Allah Mummy kada kuji komai ae mun janyota mun gama kawai".sun dade a gidan kafin Mummy da masu tsaronta suka daukesu tare da Fadila zuwa gida.
Cikin k'ank'anin lokaci Shuzna dasu Islam sun gama jonewa kowa k'ok'arisa ya fara janyota cikinsu,yayinda take cike da matuk'ar farin ciki tasan ba zata wani sha wahala ba wurin cinma burinsu,tunda suka had'u ko wacce ke kwakwar Shuzna taje gidansu amma bata maida hankali ba,yau ta kasance babbar rana a wurin Shuzna dan yaune Nani Fammah ta k'arb'i muslunci ta koma da suna Fatima,zaune suke cikin babban Parlonta zaune suke Shuzna ,Islam sai Fadila fira kawai sukeyi,duk tsawon zuwansu gidan ko kad'an basu gane Nani ba dan ta k'ara kyau ta murje bare yanzu da takeyin shigar hausawa duk daukarsu Su Faida kannen Shuzna ne,"ya kamata yau dai ki cika alk'awarin ki Shuzna,yau kikace zakije gidanmu,daga nan mu wuce gidansu Islam"."yes of course ina sane fa,zanje na shirya yanzu".tayi matuk'ar kyau cikin shigar farin wando da blue din riga yau toms ta saka ta ja jakarta wurin Nani taje tayi mata sallama tare da yaranta sannan ta fito yau bata fita da masu tsaronta ba,ita ke driving sai Fadila a front seat sai Islam a baya,fira kawai sukeyi har suka isa k'ofar gidan su Fadila , Shuzna ta fara danna Horn aka bud'e suka shiga,kallon get man din tayi shine dai tun nasu na da,sai dai yanzu a gidan akwai tsaro sosai saboda gidan gwamna ne,basu da wani nisa tsakanin gidan Shuzna da gidansu Fadila,jin komai takeyi kamar a mafarki Wai yau itace a cikin Family dinta bayan tsawan shekara goma,a hankali ta fito da k'afarta suka wuce cikin tankak'amemen gidan,a ranta tace lallai Mummy ta samu abunda take so,tunda suka shiga Fadila ke kwallah Kiran "Mummy Mummy Ina kika shige?",part din Mummy suka shiga ,zaune a chair suka sameta tasha wanka ga jikinta duk zinarai,fad'ad'a fara'arta tayi tace"a'a sannunku da zuwa ,tun d'azu nake tsimayen isowarku"ta k'arashe maganar tana mik'ewa ta nufosu,sun kai minti d'aya suna kallan Kallo tsakanin Mummy da Shuzna sannan Shuzna ta wayence tare da rungume Mummy tace"barka Mummyna".rungumta Mummyn tayi tace"lafiya qlau y'ata ,Allah yayi maki albarka sannu da dawowa k'asar haihuwa".dariya Shuzna tayi sannan Mummy ta rike mata hannu suka zauna a chair kafin kace me tuni an cika gaban Shuzna da abubuwa iri iri,Mummy sai rawar kai takeyi tace"ki gama ku gaisa da Governor da kuma Hajiya Mama".
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi Mana kyakyawan karshe
Stylish star
Jorderh majidadi
ππππππππ
*RUHIN FANSA*
ππππππππ
Na
*Maryam ismail Majidadi*
Part 2 ,part 2 ,part 2
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*ππ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Page 41-45
Da fara'arsu suka k'arasa akan milisar da Mama ke zaune,kallonta Shuzna takeyi cike da matuk'ar kewarta,Babu laifi Mama ta k'ara tsufa babu laifi,cikin d'oki Shuzna ta k'arasa gabanta ta duk'a tare da rungumeta ta baya ta sark'o kanta dai dai wuyanta,da sauri Mama ta d'ago fuska a hankali tace"Najma",da yake suna hayaniya babu Wanda yaji me tace sai ita Shuznar,murmushi kawai tayi tace"Mama barka da hutawa".k'ara kura mata ido Mama tayi jin muryar Shuzna sharewa tayi ganin ba fuskarta bace tace"yauwa yarinya"labari sukeyi amma kab hankalin Mama yana kan Shuzna yarda takeyin abubuwa