Showing 12001 words to 15000 words out of 16222 words

Chapter 5 - RUHIN FANSA By Maryam Majidadi part 2 -1-1.txt

da matsa k'afa yasa take ganin kamar Najma ce zaune a wurin,a b'oye sai share hawaye takeyi.shigowar Amaan yasa Shuzna mik'ewa tsaye tana kallonsa,wani irin zaro ido yayi bakinsa na k'yarma ya d'aga hannu yana nuna Shuzna yace"ke..e..ke...Zee...na...t"da sauri ya dafe kanshi ya fice da gudu yana k'ok'arin sakin ihu yana bubbuga kanshi yana so ya gane ko dai yana da hankali.Daddy suka gaisar sannan suka isa gidansu Islam,anan da taga Shuzn yi tayi kamar bata Santa ba,anan suka had'a kawancen yarda babu Wanda zai zargesu.sosai Hajiya Sadiya ta k'arbeta.ta jima sosai a gidan kafin tayi masu bankwana tace su zauna zataje gida ga Driver dinta nan yazo,tun da suka fita ,Amaan kam baya ya bisu dan yana so ya tabbatar da abunda ya gani,da sauri tasa Driver ya taka burki daidai wani super market,har kusan Faduwa takeyi data fito tayi kan wata kyakyawar mata dake shirin shiga mota hawaye suka wanke fuskarta tace"Ummu,Ummu"juyowa matar tayi ta kalleta kawai ta shiga mota kafin Shuzna tayi wani yunkuri tuni Driver din yaja motar yabar wurin,hawaye suka Kuma zubo mata da k'yar ta k'arasa mota ta shiga,Amaan ko ihu ya saki a cikin motar yace"menene haka yake neman zautar dani?,ni da hannuna na kashe Zeenart ,haka Ummu amma meya sa sukemun gizo a idona?,wannan ba abunda zai tab'a yiwuwa bane"da gudu ya taka mota ganin tasu Shuzna tayi masa nisa har suka iso bakin gate dinsu yaga gidan sannan ya koma gida a matuk'ar rude.
Har yanzu Shuzna hawaye sun kasa tsayawa akan idonta,ga k'afarta da takejin kamar bazata dauketa ba tunda ta shigo parlon tayi wurki da Jakarta hannu tasa ta b'aro glasses din dake wurin ta cusa hannuwanta cikin yalwatacciyar sumar gashin kanta ta zube a wurin.Ahaad shine Wanda ya fara ganinta kafin Nani ta k'araso gareta shi harya iso da sauri ya rike hannunta dake zubar jini yace"subhanallah,meye haka kikeyi,kin jiwa kanki ciwo"."meye yake samunki y'ata?"Nani ta tambaya.kuka Faida ta saka tace"Aunty ki tashi please".rike hannun Ahaad Shuzna tayi tace"naga Mamana,Allah itace na gani,kafin nayi wani abu ta b'ace ta barni"riketa sosai Ahaad yayi ganin yaran sun rud'e yasa ya dauke Shuzna cak ya wuce sama da ita,Nani kuma ta Kama su Faida zuwa d'akinsu.koda ya kaita d'akin gefen bed ya ajiyeta ya dauko first aid box ya soma gyara mata hannun,duk zafin iodine a ciwo ko motsawa Shuzna batayi ba ,kanta k'asa kawai yake kallo idanuwanta sunyi jajawur.kallonta yayi yace"ki kwantar da hankalinki,wannan ba shine mafita ba,kinsan kina da aeki a yau da dare nan,idan kika kuskure kin fad'i daga amincewar da abokan aekina suka baki".ganin yarda yayi maganar a daure ya koma mata tsab oganta a wurin aeki .mik'ewa tayi tare da Sara masa tace"insha Allah General Ahaad".kallonta kawai Muslim keyi Wanda yake tsaye bakin k'ofa,da hanzari ya k'arasa shigowa ya rike hannuwan Shuzna hawaye na silalowa daga fuskarshi yace"Ashe kece Najma k'anwata,Ashe ke jinina ce?".a razane Najma take kallonsa tana son tuno abubuwan da suka faru a baya,bakinta na rawa tace"tabbas kaine Yayana Wanda Mummy ta kashe d'aya kai Allah yasa ka rayu,sai yau na gane dalilin da yasa nake matuk'ar son Daddy Ashe shine Uncle Bashir dinmu,na dade ina ganin kamarsa da Ummuna amma na share hakan,Ashe a cikin Family dina nayi rayuwa,Allah na gode maka".da gudu ta fad'a jikin Muslim tana sakin kuka,Nani ma kukan takeyi had'e da dariya ,matsowa tayi tana shafa fuskarshi tace"munyi kewarka sosai Muslim,ka yafe mana tabbas dani aka had'a kai aka rabaka da mahaifiyarka,amma munyi hakan ne dan ceton rayuwarka"sunkuyar da kai Ahaad yayi yana jin wata matsananciyar kunya ta rufesa da sauri yabar d'akin yana jin wani iri daban saboda halin Mummy.nan Nani ta basu labarin komai,kwafa Shuzna tayi tace"nikam bazan tab'a iya yafewa wad'annan mutanan ba,ko yaushe su suna kawo hari akan farin cikinane".dafata Muslim yayi yace"ko dan Hallaccin da Aiban yayi maki bai isa ace kin gafartawa k'anwarsa da Ummansa ba?,duk da nasan Islam itace ta kawo shawarar a zuba maki Acid Kuma ita ta siyo ta bawa Fadila kuma ita tasa Fadila tasa ayi maki Fyad'e".murmushi Shuzna tayi tace"Kuma Mamanta harda hadin kanta aka yimun allurar mutuwa ko?,Kuma Islam itace wacce ta gayawa Ahaad nice Shuzna bayan daya saka aka kamo masa ita".zaro ido yayi yace"a ina kika San wannan?"."ina tare daku a India amma ruhina yana nan Babu wasu bincikena da ban gama ba,abunda ya rage shine sora d'aukar hukunci".
Da dare ta shirya cikin Uniform dinta na kalan Soji tayi matuk'ar kyau sosai ,sai dai har yanzu idonta akwai alamar ja ja a jiki,sai fidda kamshi takeyi,da gudu Fayyad ya shigo d'akin tare da rungumeta yace"Ummu kije dani bana son Zama anan",k'arasa daure igiyar takalminta tayi tace"haba Super hero ,kasan bazan dad'e ba kuma Ummanku na tare daku,aeki ne na gaggawa yazo mun"ta k'arashe maganar tana janyo hannunsa suka sauko daga bene ,har a ranta tana matuk'ar son Fayyad saboda Shima yarda yake tsananin sonta da nuna kula gareta,a kusa da Nani ta zauna ta rungumota tace"Nani zan tafi"."kai kinyi matuk'ar kyau y'ata,bara muyi photo a tare"wayarta ta d'akko take hotonsu da Shuzna ya bayyana tun bata girma sosai ba,camera ta shiga ta soma daukarsu tare,d'aya ta rungumeta,d'aya ta Mata kiss a kumatu,d'aya Kuma sukayi duka harda yara,mik'ewa tayi ta sumbancesu su duka ta nufi hanyar fita da gudu Fayyad ya k'araso ya rike hannunta Cuo din madara ya bata yace"kinyi mantuwa baki sha madarar ki ba"duk'awa tayi murmushi dauke fuskarta Tasha madaran sannan ta shafa kanshi tace"na gode".kanne Mata ido d'aya yayi tare da sakin murmushi yace"Allah ya tsare,ya Kuma karemun ke Ummina,ki kulamun da kanki,ko yaushe ina alfahari dake,kedin garkuwace ta gari garemu,ko yaushe zaki kasance a zuciyar Fayyad Aiban"sak fuskar Ahaad ya koma mata,duk wani abu nasu yayi kala d'aya,rungume yaron tayi tare da saka masa albarka hannu ya d'aga mata yace"masoyiya am gonna miss u"dariya duka suka saka a parlon,sannan duka yaran sukayi mata Allah ya tsare sannan ta fita daga gidan, Driver yaja motarta zuwa babban barikin soji a katsina,da d'an gudu gudu ta shiga d'akin taron,k'amewa tayi tare da sarawa manyanta irinsu General Ahaad, General Muslim,General Akiyy da dai sauransu duk manyansu sun hallara ,ansa Mata sukayi kafin ta k'arasa jikin wani k'aton allo Wanda Computer ke ajiye a gefansa bisa tebir ta soma masu bayani tiryen tiryen akan yarda akayi aka kwashe kud'in matai Makin shugabansu,sannan ta Kuma fad'a hanyoyin da za'abi a kawar da irin wannan b'annar tasha wahala sosai kafin ta gano Wanda sukayi aekin dan da gani Shima k'warone a computer.
Tafa mata sukayi tare da Mata jinjina dan tabbas sun jiniinawa k'ok'arinta ba kad'an ba,hakan ya k'ara Mata kima a wurin aekinta,gabanta ne yayi mugun fad'uwa da sauri ta soma karanto addu'a ta samu taji daidai sannan taci gaba da godiyar kyaututtukan da take samu.ba su suka Kama hanyar gida ba sai bayan sallar asuba,Muslim yaja Ahaad yace"muje idan an ajiye Captain Shuzna gida sai driver dinta ya mikamu kaga Amaan bai bada motar an kawo ba"ba yarda ya iya haka suka shiga motar sai faman had'e rai yakeyi,yayinda Shuzna keta jan siririn tsaki dasun had'a ido ta b'allah masa harara.murmushi kawai yayi ya kawar da kansa yana Mata akamar zaki gane kuranki.
Daidai k'ofar layin sukaga motar Ahaad fitowa sukayi tun a nan,Ahaad yace"to Kuma waya kawo motar anan?".jinjina kai Muslim yayi yace"nima ina zan sani".ko kulasu Shuzna batayi ba ta wuce tare da tura k'ofar parlon tanajin gabanta yana dukan ukku ukku kamar zuciyarta zata bud'e kirjinta ya fito,ganin duhu yasa ta matsa wurin makunnin kwan fitilar ta kunna,a hankali ta soma juyowa kamar mai tsoron d'akin baya tayi tana jin jiri na neman kwasarta ,murza idonta tayi ganin kamar dishi dishi take gani,lallai ba mafarki bane,wani irin zananniyar k'ara ta saka wacce ta karad'e duka illahirin gida ta Kuma kwala wata k'arar tace"Nani,Fayyad"jin motsin mutum ta bayanta yana niyar shak'areta yasa ta juya da sauri zaro idonta tayi cikin muryar kuka tace"sai kayi dana sani,sai kayi nadamar zuwanka duniya,Amaan ka tabka babban kuskuren k'ara kashemun farin cikina"duka ya kai Mata a fuska ta goce ta kai masa wani duka a wuya,k'ara ya saki ya nemi hanyar fita,yaransa guda biyu suka rufa masa baya,cikin zafin nama ta rufa masu baya ta zare bindigar dake jikin wandonta ta soma harbi ta ko ina ,da gudu Muslim da Ahaad sukayo cikin gidan jin ihun Shuzna,bangajesu Amaan yayi sukayi waje,itama turesu tayi ta rufa masu baya,cikin sa'a ta harbi Amaan a k'afa,sai yaronsa d'aya akan cinya ,kafin ta k'arasa garesu suka shige mota suka ja da gudu.dafe kai Ahaad yayi yana Kiran"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"Nani da Fayyam ne kwance cikin jini anyi masu yankan rago,gaba d'aya parlon ya b'aci da jini,da gudu Ahaad ya k'arasa ya d'ago gawar Fayyam sai yaji hawaye nabin kuncinsa,yau d'ansa ne a hannunsa Kuma wai k'anensa ya masa yankan rago ya kashesa.jin muryar su Ahaad yasa Faida da Fayyam fitowa da sauri,mak'alk'ale Muslim Faida tayi tace"Uncle suka kashesu ,suka yankasu muna kallo,Uncle a idona,wani ne mai Kama da Papa,muma suna nemanmu Fayyam ne ya buga masa katako a kai ya janyeni ya b'oyeni a bayan k'ofa"nuna gawar su Fayyad kawai takeyi a take ta sulale jikin Muslim sumammiya,shikam Fayyam jikin Ahaad ya kwanta ya kasa cewa komai .girgiza Faida Muslim yakeyi amma shiru,ruwan sanyi ya zuba mata amma ko motsawa batayi ba,sai yanzu tunanin Ahaad yazo masa akan Shuzna janye yaran yayi daga jikinsa ya fito da gudu yana kiranta duk da ji yakeyi kansa tamkar zai tsage,Shuzna kam fad'uwa tayi akan gwaiwowinta tana sakin kuka ,da gudu Aiban ya fito daga mota ya k'araso ya rumgumeta yace"kiyi hakuri,kada ki d'auki doka a hannunki,nayi maki alk'arin zanbi hakkin D'ana a ko wanne yanayi".ganin hakan yasa Ahaad sunkuyar da kai ya koma ciki tare da jingina da bango ya dafe kansa.Aiban yanayin tozali da hawar su Nani,besan ya soma hawaye ba.ruwa da yawa Fayyam ya ebo ya watsawa Faida ya girgizata da k'arfi yace"kema tafiya zakiyi ki barni?,ki tashi kada ku barni ni kad'ai ina sanku sosai"ya k'are maganar tare da sakin kuka mai karfi,wani dogon numfashi Faida ta saki itama tana sakin kuka,ba arziki aka Kira Dr yayiwa yaran allurar bacci su duka biyu dan nema sukayi su zare masu.
Cikin awanni kad'an aka gama shirya gawar Nani data Fayyad,Shuzna kam ta koma kurma ko motsi batayi ha daga inda take,har aka fita da gawarsu.ganin Shuhada ta shigo a rude yasa Shuzna sakin kuka ta rungume Shuhada suka saki kuka a tare. Kamar daga sama sukaji magana"yanzu ba lokacin kuka bane,ki Zama jaruma ki share hawayen kije ki gama da makiyanki,ki kawar dasu daga datsewa duk wani bawa farin ciki,ina so yau ki Zama ta k'arshe wacce zasu tarwatsa wa rayuwa Najma"jin muryar Ummu yasa suka juyo da sauri su duka.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.


Jorderh majidadi
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*RUHIN FANSA*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Na
*Maryam ismail Majidadi*


Part 2 ,part 2 ,part 2


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*_________________________________*


End


A kallon Ummu kawai Shuzna takeyi sannan ta fad'a jikinta cikin dishewar murya tace"Ummuna Ashe zan k'ara ganinki?".
Shafa fuskarta Ummu tayi tace"kwarai kuwa y'ata,komai kike ciki ina sani,ina jiran lokaci kawai yayi kafin nazo gareki,saiki godewa Yayanki Kuma Baban yaranki danshi ya dauke maki Ummarki ya kula da ita duk tsawon wannan shekarun yana bata tsaro"sunkuyar da kai Shuzna tayi ta kasa cewa komai,sai dai tana jin dadin yarda Ahaad ya kula da Ummanta duk da Shima tashi ce ita ta rainesa,rasa kalmar da zatayi amfani tayi.matsawa kusa da Ahaad Ummu tayi ta Kama duka hannuwansa ,kansa a k'asa yace"Ummu dan Allah kuyi hakuri,nasan Familyna sun cuta maku da yawa"rufe masa baki Ummu tayi tace"nima Family dina ne ae,kayi hakuri bana nufin Shuzna ta cutar dasu,sai dai ina San a d'auki matakin da irin haka ba zata k'ara faruwa ba".murmushin k'arfin hali yayi cike da kunya amma bece komai ba,shi kanshi tsiyar dasu Amaan suke aekatawa ya ishesu haka.cikin k'an k'anin lokaci ta sauya kayan dake jikinta ta fice daga gidan.
Da matuk'ar gudu ya shiga gidan tsaye yayi turus ganin Daddy yana balbale Mummy da bala'i yace"kinyi abunda kika iya,amma ki sani bazanyi maki baki ba,sai dai yau iyalan y'an uwana zasu dawo gida,kin cutar dani Bilkisu,bansan iya wanne abubuwa kika saka na aekata ba,bazan tab'a yafewa kaina ba"ya k'are maganar yana fita daga parlon.
Hannu Mummy ta saka a Kai tace"Amaan aekin komai ya bud'e,mun shiga ukku idan Alhaji ya juya mana baya".
K'arasowa yayi cikin d'akin yace"ae wannan bakiga komai ba akan abunda ke dosomu,Ummu Sha'awa tana raye Ashe Yaya Ahaad shine Wanda ya dauke Ummu,Shuzna k'awar Fadila Kuma itace Najma"dafe zuciya Mummy tayi tace"Amaan karkasa zuciyana ta buga,na mutu ka huta".sallamar Hajiya Sadiya da Islam ya mai da hankalinsu garesu,fuska daure Hajiya Sadiya ta shigo a hassale ta nuna Mummy tace"Ashe ke baki da mutunci?,yanzu mijin nawa kike tunanin zaki iya sakawa a ture daga Gwamnati?,to wlh kinyi kad'an ke baki kaiba,duk wani abunki bayana kika biyo"."Kai Kai Wai meye kukeyi haka ?,yanzu ya kamata mu nemi mafitar tsiratar da kanmu ne,duk abunda muka dade muna shiryawa zai rushe rana d'aya".murgud'a baki Islam tayi ta soma zagaye Amaan cikin d'aga murya tace"naku dai ya tarwatse maciya amana,koka manta yanzu Kai kaje ka kwanto wata rigimar?,Kaine kaiwa yaran Najma yankan rago,ka kuma kashe Mata Naninta ,bayan a baya kayiwa y'ar uwarta Fyad'e ka kasheta,Kuma ka kashe Mata Babanta,kayi hari akan Ummanta sai dai ita bata mutuba,Zeenart kam daka kashe ta mutu sai dai fuskarta aka bawa mak'iyiyarka,Kuma Najma tasan komai akan abunda ka aekatawa zeenart,abun farin ciki da zan gaya maku shine Muslim shine yaron Umma da Kuka kashe Mata y'an biyu to D'an uwanta Bashir yaji komai Kuma shiya dauke Muslim ya renesa,yana nan zuwa gareku".Mari Fadila ta katsawa Islam tace "ke marar mutunci yanzu Iyayen nawa kike gayawa haka?,ae duk abunda ake k'ullawa da Uwarki Sadiya aka yishi,hasalima itace mai kawo shawara,banzaye masu bak'ar zuciya kawai"shak'e Fadila Islam tayi tana kiran"ke harkin isa?,wallahi ko uwarki Bilki bata kaini tasha ba balle ke tsohuwar guzuma jaka dake".jin an banko k'ofa da k'arfi yasa suka juyo da sauri,Shuzna ce cikin shigar Uniform dinta na soji,sai yaranta su hudu suma duk a shigar Uniform.ko wannensu rike da bindiga k'arasa shigowa tayi cikin d'akin tana kallonsu da tsantsar tsana tabbas wa'annan mutanan sun cuta mata da yawa bata ma san meye zata iya aekatawa akansu ba inhar ta biyewa zuciyarta.jin an fasa k'ara yasa suka juyo da sauri ganin Fadila na niyar faduwa yasa Shuzna ta k'arasa da sauri ta fad'o a hannunta Islam ce ta caka mata wuk'a a gefen cikinta,girgizata Shuzna keyi tace"Fadila ki tashi" hannu Mummy ta daura saman Kai tace"wallahi yau saina kasheki kema,baza'a tab'a d'aukar gawar y'ata ita kad'ai ba,hakan bazai tab'a yiwuwa ba"kan Islam tayi gadan gadan Hajiya Sadiya ma tayi kanta nan suka had'e kamar mahaukata suna kokuwa da juna,fizgo hannun Islam Amaan yayi ya wanke ta da maruka har hudu ya soma jibgarta,da sauri yaran Shuzna sukayi kansu,hannu ta d'aga masu tace"stay out of this"Shima k'ok'arin jaka masa wuk'ar takeyi tana zage zage,ganin da gaske shima zata illatashi cikin bak'ar zuciya ya saita bindigar dake hannunsa akan Islam ya danna kunamar ,wata irin ihu Hajiya Sadiya ta saki tayo kan Islam ,Islam ta fad'o a saman hannunta ga jini yana zubowa daga kanta,ko shurawa batayi ba ta mutu a wurin.innalillahi wa'inna ilaihir raju'un kalmar da Hajiya Sadiya ke maimaitawa kawai kenan hawaye na wanke fuskarta yaranta biyu Islam da Aiban Kuma kowa yasan Islam itace rayuwarta yau ga gawar Islam a gabanta ,wani kukan ta kuma rushewa dashi,k'ara kad'an Shuzna ta saki lokacin da Amaan ya janyo yalwataccen gashin kanta take ribom din ya zare gashin ya watsu a fuskarta da bayanta,saurin sakin Fadila tayi ta mik'e ta samu ta kwace kanta tace"kada ka kuskura k'azamin hannunka ya k'ara tab'ani".dariya ya fashe dashi yace"Babu Wanda zaiyi rai a nan daga Ni sai Mummyna Babu wani sarki sai ni a wurin nan"halbi ya soma saki kota ko ina cikin zarin nama Shuzna ta goce ta koma bayansa,rike hannun da keda bindigar tayi suka soma kokowa ,yayi mamakin yarda Shuzna tayi k'arfi haka duk da yasan ko a da can tana da k'arfi ba ragguwa bace amma beyi tunanin a yanzu zai kasa kwace hannunsa gareta ba,a tsawace yace"ki sakeni ko kuwa kiyi ta ranki"Murmushi Shuzna tayi ta kallesa ido a ido tace"aeni Amaan tun daga ranar daka rabani da iyayena,yar uwata,D'ana da Kuma Nanina from that very day u took my life,shiyasa yanzu bana tsoron na mutu,amma sai naga bayan tantiri marar tsoran Allah irinka,saina tabbatar nice ta k'arshe da zaku lalatawa rayuwa a duniya gaba d'aya".murd'eta yayi ta dur'usa k'asa,cikin dabara ta samu ta d'ago ta zare hannunta daga jikinshi ta wanka masa maruka har biyu ta kuma ingijesa yayi baya,juyawa tayi zata dauki waya ta Kira y'an sanda ,cikin sand'a ya daura Mata bindiga a Kai yace"tabbas yau saikin mutu,haka sauran yaranki da tsohon mijinki da Uwarki sai sun mutu kinga duk abunda kika mallaka nawa ne"motocin y'an sanda dana soji ne suka shigo gidan,kafin kace me sun zagaye gidan ,daga ciki harda General Muslim da General Ahaad,sai shugaban Shuzna kuma Wanda take jagorancin team dinsa a yanzu haka,parlon suka shigo harda Aiban,"ku tsaya daga nan idan Kuma har kukayi wani abu marar kyau to tabbas zata mutu yanzu",ganin da gaske yake yasa suka ja baya,kallonsu General Asam yace"dole fa yanzu ayi zab'i na k'arshe ,sai an harbi Amaan"zaro ido Aiban yayi da sauri ya k'arasa wurin Mamanshi tare da riketa jikinsa ta fad'a ta saki kuka tace"Aiban ya kashe mani ita,ya kashe mani Islam,Islam ta tafi ta barni Aiban"juyar da fuska yayi yana share guntun hawayen dake zubo masa rungumeta yayi yace"Hajiya kiyi hakuri,hakan Allah ya rubuta".kamar daga sama sukaji k'arar halbi Wanda basu gani ba harsunyi saranda kowa daukarsa Shuzna ya harba,ganin Ahaad da bindiga a hannu yasa kowa ya kalli inda yake Kallo,k'ara Amaan ya saki ya dafe k'afarsa da Ahaad ya harba ya zube anan wurin,wani kukan Mummy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login