Showing 3001 words to 6000 words out of 16222 words
Chapter 2 - RUHIN FANSA By Maryam Majidadi part 2 -1-1.txt
ya k'awatashi duk da yadda ta kaga fuskarta kamar ba'a toyata ba Kuma tabbas fuskar da aka saka mata mai matuk'ar kyau ce,lallai Umti tayi mata zab'i na gari sai dai fatanta kada hakan ya janyo wata matsalar Kuma.hawaye Umti ta fara da sauri tazo ta rungume Najma tace"Shuzna basan iya misalta maki irin farin cikin da nake ciki ba,kece kika dawomun da fuskar yarinya mafi soyuwa a gareni,wanann fuskar dana bada aka saka maki fuskar yarinyar da Yayanku Muslim yaso ne wato Zinatu,a daren daurin aurensu ta rasu,y'ar aminiyata tace ita,garinya mai ladabi da biyayyah da sanin ya kamata ,fatana dai Allah yasa ki daukemu tamkar iyayenki".hannu Shuzna tasa ta gogewa Umti hawayenta tace"insha Allah bazan baku wata matsala ba,ni dinnan y'arku ce,Zan bada dukkanin biyayyata gareku kun taimakeni lokacin da nawa y'an uwan suka gujeni"sosai sukaji dadin bayanin nata ,kallonsu Daddy yayi yace"wannan ya zama sirri a tsakaninmu,kada Wanda yasan asalin yarinyar nan Kuma daga yau sunanta Shuzna ta tashi daga Najma,gobe Shuhada zata dawo ina so ku gabatar mata da Najma a matsayin Shuzna Kuma y'ar uwata,nasan zata dauka Kuma tayi tunanin kamace kawai sukeyi da Zeenatu"sai da suka daukar masa alk'awarin rufe sirrin har Drs din da sukayi aekin Wanda Aunty Maryam na cikin sannan ya k'arb'i magungunanta da ita kanta suka wuce gida.harta takardun makarantarta sun koma Shuzna Bashir dan haka aka fara neman mata scul danta dage ba zata bari ta haihu ba,ga ciki harya soma d'an nunawa a jikinta,saukinta d'aya bata laulayi mai wahala bazaka tab'a gane a lokacin tana da ciki ba.
Girke girke aketayi a gidan fitowar Shuzna kenan daga d'akin da aka bata ta safko kitchen ta nufa ta samu Umti suna aeki tare da masu aeki,sirrinawa tayi tace"Umti barka da safiya,sannu da aeki"murmushi Umti ta sakar mata tace"yauwa y'ata Shuzna sannu da tashi"d'aukar rova da Shuzna tayi yasa Umti k'arb'a tace "a'a y'ata jeki zauna ki huta yanzu jikin naki ya fara nauyi,ae munma gama rigimar Shuhada ne yasa aka yi aekin nan da yawa".jin ihun murnar Shuhada yasa suka gane har Aiban ya dawo daga d'aukota daga airport kenan,Umti kawai take kwalawa kira,ta shigo kitchen din da gudu turus ta tsaya tana kallon Shuzna tace"wow Masha Allah ,Umti ina kika samo mai Kama da Aunty Zeenat?"ta k'arashe maganar tana rungume Umti,dariya Umti tayi tace"y'ar uwar Baffanku ce tazo daga Canada y'ar Auntynku data rasu"hannu Shuhada ta mikawa Shuzna tace"am Shuhada nice to meet u"dan a tinaninta Shuzna batajin hausa ma.fara'a Shuzna ta fad'ad'a duk da sarai ta gane Shuhada amma ta wayence tare da mika hannu itama tace"naji dadin haduwa dake Shuhada,sunana Shuzna "zaro ido Shuhada tayi tace"la ashe kinajin hausa,Allah nayi tunanin bakiji dan wannan kyau ae sai a dauka balarabiya ce ke"dariya duka suka saka sannan ta janyo hannun Shuzna da sauri wai su fita da sauri Umti tace"ke malama kiriniya kiyi a hankali tana da juna biyu"turus Shuhada ta tsaya tace"u mean matar aurece Umti?"."eh amma sun rabu da mijin shiyasa ta dawo zata zauna damu"cike da matuk'ar tausayi Shuhada tace "Allah sarki Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi".da ameen suka ansa sannan suka fito,Shuhada sai zubawa Shuzna labarin garin lagos takeyi,cikin rai Shuzna tace lallai rayuwa wai mahaifata ake bani labari irin haka.kafin kace me har Shuhada ta Kira Muslim ta fad'a masa y'ar uwarsu mai Kama da Aunty Zeenat tazo,shikam bancin aeki yasha kanshi niya yayi ya gudo yazo yaga mai Kama da zeenart dinshi.
Bayan wata hud'u.
A yanzu rayuwa kam ta matuk'ar camzawa Shuzna ga wata irin Shak'uwa da sukayi da Shuhada komai tare sukeyi sun zama kamar y'an biyu,a dole Shuzna ta hak'ura da school saita haihu saboda tun wata biyar cikinta yayi wani irin nauyi ya fara girma sosai ga kumburin k'afa data fara fama dashi,sai dai computer scul da taketa zuwa danta k'ara gogewa kafin ta koma makaranta,Shuhada ma tsaida karatun tayi duk da ita Law take son karanta sai dai ta koma zuwa computer scul din itama.sanye ta fito da doguwar riga batayi wani k'iba ba sai dai jikinta ya canza ga ciki ya fito mata sai dai tayi wani irin haske da kyau,wani irin fad'uwa gabanta yakeyi tunda ta tashi yau,da k'yar take janyo k'afarta harta safko daga stairs da sauri Shuhada ta k'araso tare da riko hannunta tana mata sannu dariya Shuzna tayi tace"sai kace wacce take dauke da wasu uwayen kaya?","ae yanzu kinfi ma koma fama da nauyi,Allah dai ya raba lafiya"ta rikota ta taimaka mata suka zauna a chair d'agowar da zatayi sukayi ido biyu da Ahaad kallan kallo aka shiga yi tsakaninsu,kauda Kai Shuzna tayi tare da tab'e baki wata irin tsantsar tsanar Ahaad takeji a kanta da k'yar take had'a yawu har wani d'aci d'aci takeji a mak'oshinta maganar Shuhada ta dawo da ita daga tunanin data tafi ta d'ago tana kallonsu wannan shine"Yaya Muslim sai wannan Yaya Ahaad ,shima kamar d'an gidan nan yane,duk in sukazo garin nan anan suke zama"gyad'a Kai tayi ganin su Umti sun tsareta da ido yasa tace"sannunku da zuwa ,ina wuni".da "lafiya "kawai Ahaad ya ansa ya wuce ciki abunsa.shikam Muslim zama yayi yana kallonta yana jinjina tsananin Kama tsakaninta da Zeenat ji yayi ciwansa ya zama sabo Amma a haka ya daure ya ansa gaisuwar sannan shima ya wuce ciki.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.
Stylish star
Jorderh majidadi
ππππππππ
*RUHIN FANSA*
ππππππππ
Na
*Maryam ismail Majidadi*
Part 2 ,part 2 ,part 2
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*ππ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Page 16-20
Sosai Umti ta fahimci halin da Shuzna take ciki dan haka ta matso kusa da ita tace "taso muje d'aki ina son muyi magana"yunk'urawa Shuzna tayi Umti na rik'e da hannunta sai jera mata sannu Nani takeyi ,suna shiga d'akin Umti a gefen gado suka zauna duka hannuwanta Umti ta Kama tace"Khadija ki tattaro duka hankalinki ki bani,naga yanayin da kika shiga Kuma na fahimta lokacin da kika ga Sulaiman,Sulaiman dai anan yayi karatu gidan nan tamkar gidansu yake,baya da maraba da d'ana Muslim,ni ina da tabbacin Sulaiman bazai wani kulaki a gidan nan ba,to kema ki share kada ki sake ki bashi k'ofar dazai gane kece Najma,ki bari harya safko da kanshi ya nuna soyayyarki sannan ki bashi kai"a matuk'ar razane Shuzna ta d'ago dara daran idanuwanta tana kallon Umti cikin k'asa da murya tace"Umti har abada,har abada bazan tab'a iya komawa gareshi ba"murmushi Umti tayi tace"y'ata kada fushin yayi yawa,kici gaba da addu'a insha Allah komai zaiyi daidai,Ahaad ba mugu bane kawai kun samu matsalan fahimta ne".
"Wallahi ki taso in yi tafiyata ni kad'ai ,bana so ruwa ya samemu a waje,yau tafiyan bamai nisa zamuyi ba"Shuzna ta fad'a tana k'ara kallon bubun dake jikinta na atamfa,murmushi tayi ,hannu Shuhada ta karkad'a akan fuskar tata tace"yadai uwar biyu,ko sirikin nawa yayo waya a sasanta ne kike ta cika fuska da fara'a haka"yunk'urawa tayi zata kamo Shuhada,aeko ta kauce tana babbaka dariya"wallahi zanyi maganinki a gidan nan,inawa kaina dariya ganin nasa atamfa,inaga tun ina yarinya na yarda saka Kaya haka ko da nayi auren bana sakawa"."Kuma kinsan kinyi bala'in Kyau sosai,fatana dai Allah ya saukeki lafiya mu koma school".haka suka fito suna tattaunawa gwanin birgewa suka Umti da Nani sallama suka fita a k'afa dan Shuzna ta samu ta motsa jikinta.fitarsu ba dad'ewa sama tayi bak'inkirin hadari ya soma cida iskar damuna mai sanyin dad'i ta fara kad'awa ko da wanne lokaci ruwa zai iya tsugewa,kamar Shuzna zatayi kuka ta k'ara k'ank'ame d'an k'aramin gyale dake jikinta tace"wayyo Allah,bana son ruwan nan ya tab'ani".kallonta Shuhada tayi tace"aeko to inmun tsaya bamu san yaushe ruwannan zai Kai ba,gashi babu abun hawa,ki daure mu k'arasa".Jan k'afa kawai Shuzna takeyi dan takai k'arshe ji takeyi kamar zata fad'i a wurin ga sanyi da takeji har k'arma ta soma,jin ruwan ya fara sauka yasa Shuzna lunshe idanuwanta tanajin safkar ruwan har cikin ranta,kafin wani lokaci sunyi sharkab da ruwa har d'igan ruwa sukeyi.
Motace ta gittasu sai dai baka iya gane waye yake ciki,tsayuwa Shuzna tayi tana mayarda numfashi.motarce ta dawo gabansu ta tsaya,lek'owa driver din yayi wanda yake zaune da kayan sojoji yace"madam ".dariya Shuhada tayi tace"la Samuel"haba bata tsaya komai ba tayi gaban motar tace"Shuzna ki shiga baya zakifi sakewa".da k'yar Shuzna ta shiga k'araso gaban motar,gabant ne yayi mugun fad'uwa,ga k'amshin turarenshi daya addabi hancinta bata da wani zab'i haka yasa ta k'arasa shiga kawai ta zauna.d'ukowa yayi saitin kunnenta yace"y'ar lukuta idan kika fasamun laptop sai dai mijinki ya biyani kayata"ya Kuma juya tamkar bashine yayi maganar ba.dan d'agawa tayi ta zaro laptop din ta daura masa bisa cinyarsa,,hannunta yad'an shafi jikinshi yarrr suka ji gaba d'ayansu,amma ko da wasa bai nuna yaji wani abu ba, kallonta yayi yace"kinji dadi kin tab'ani Kuma kinsan saina rama,idan so kikeyi maza su tab'aki to ki komawa mijinki danmu gidan nan ba y'an iska".sake da baki haka Shuzna ta bishi da Kallo ,ji takeyi ae yama gama da ita,kafin tace wani abu motar ta tsaya kawai sai ta saki kuka ,lokacin har Shuhada tayi cikin gida,shima fitowa yayi ya zagayo inda take yace"malama a fito mana daga mota,dan bama tai maka maki zanyi ba gara ki fito da kanki". k'ok'arin fitowa tayi amma k'afarta ta rike sai kawai ta Kuma rushewa da kuka ta rumtse ido sosai tana yarfa hannu tana fad'in"wayyo Allahna,wayyo Nani ,Ummuna k'afana bazan iya fitowa ba Allah"sosai tayi masa kyau ya saki baki yana kallonta ganin zata bude ido yasa yace"Dallah malama rufemu baki Shagwab'a na yara ne ba tsofi jawarawa irinku ba".maganar ta shigeta sosai ,hannu yasa ya kamota kawai sai ta saki murmushi mai wuyar fassaruwa.
Suna shiga parlon tana k'ok'arin kwace hannunta daga rik'on dayayi mata amma sam yaki bata dama.da sauri Umti da Nani sukazo suka kamata suna mata sannu,Umti tace"tun d'azu naketa faman zullimi gashi dai sai da ruwan ya tab'aki,ga Yayanku Aiban can ma yazo tun d'azu yake zaryar nemanki.sai lokacin Aiban ya d'ago yace"Babyn Aiban kije ki canza kaya bana son sanyi ya kamamun ke"dakuwa Umti tayi masa tace"ungo wannan yaushe ka zama marar kunya haka?"sosa k'eya yayi yana dariya,Bayan Nani Shuzna tabi da take cewa"Maza kizo kiyi wanka da ruwan dumi ko zaki daina jin sanyin nan".Ahaad kam bin bayanta yayi da Kallo yadda rigar ta d'ame a jikinta yana kallon yarda hips dinta suke juyawa jin yana neman fad'awa wani yanayi yasa yayi saurin kawar da kanshi suka gaisa da Aiban ya wuce part dinsu,yana shiga ya Samu Muslim yana aekin danna waya,be kulashi ba ya soma zare rigar dake jikin shi,"Wai dan Iskanci mutun ya shigo d'aki amma be iya ko kallon Wanda yake a d'akin ina amfanin bak'in hali wacce ma macace zata iya zama da kai a haka mugu kawai"wani irin duka Ahaad ya kawowa Muslim cikin sauri ya goce ya fice da sauri yana dariya tare da rufo d'akin.kwafa Ahaad yayi ya fad'a toilet.
Lokaci na tafiya,kwanaki suna karewa,mintina na tafiya hakan ne ya faru a rayuwar su Shuzna ,cikinta harya shiga watan haihuwa,zaune take a compound din gidan tayi d'ai d'aya akan tabarma tayi wani irin girman ciki ga k'afarta data kumbure ,yau tunda ta tashi takejin wani irin matsanancin cikin mara saboda dauriya ta shanye ciwan taki fad'awa kowa,Aiban ne gefenta yana yanyanka mata apple tana ci,d'ukar da kanta k'asa tayi tana taunar lips dinta kamar zata huda "ciwanne ko?,tun safe ina lura da ke amma kin wani gardama ki tashi muje asibiti"Aiban ya fad'a yana niyar mik'ewa,isowar Ahaad wurin kenan zai dauki wayar Umti data bari a wajen yana d'ukawa yaji an ruko hannunsa ,batasan ta rike hannun Ahaad ba ta k'wallah k'ara tace"wayyo Allah marana,Yaya zata fashe,ku taimakeni dan Allah".a kidime Aiban yace"Ahaad ka sakata mota bara na kira Nani"be jira ansar Ahaad ba yayi cikin gidan da sauri,shikam kallonta yakeyi yadda ta jike da gumi sai siraran hawaye dakebin kuncinta ga lips dinta data taune sukayi jajir dasu,tayi matuk'ar bashi tausayi da sauri ya sab'eta dukda nauyin da tayi haka ya daure ya sakata mota hakan yayi daidai da fitowar Umti da Nani ,Aiban kasa yin komai yayi dan dole Ahaad yaja motar zuwa asibitin.
Dr Naman ne da Umti ke kanta,Aiban kasa shiga d'akinma yayi,tasha bak'ar wahala Wanda harsun fidda ran zata iya haihuwa da kanta sai kawai ga kan baby ya taho,yana fitowa kuma wani ya biyo baya,sai kuma ga wani,suka saki kuka a tare Alhmdllh kawai Umti ke fad'a.
Bayan minti talatin Umti ta fito ita da wata nurse Ahaad ne kawai a wurin Umti ta saki gud'a tace"yau na zama kaka,kaka Kuma harta y'an ukku,yau bansan wanne irin farin ciki nakeyi ba"ta k'arasa wurin Ahaad tare da daura masa yaro na farko tace"ga Hassan"sannan ta daura na biyu tace"ga Hussain"sai Kuma jikata ta k'arshen mace wato "gambonsu".wani irin Kallo Ahaad yake binsu dashi ganin tsantsar kamarsa da yaran babu abunda suka baro nasa,yayi matuk'ar kidima da ganin wannan kamar,dariya Umti tayi tace"kana kallon kamarku ne ko?,kada ka damu Allah yana iya halitta haka,ina Aiban ne?"kafin ya bata ansa sai ga Nani da Aiban sun iso cike da farin ciki suka k'araso garesa tare da d'aukar yaran suna zumudi dajin dadi,da sauri Nani ta shiga d'akin da aka kai Shuzna ta rungumeta tare da sakin kuka.itama Shuzna kukan ta saki tare da rungume Nani,shigowa Umti tayi ta daura duka yaran akan cinyar Shuzna tace"kibar kukan nan ki kalli abunda kika haifa"a razane take kallon yaran taba kallon Ahaad dake tsaye gabanta.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe
Stylish star
Jorderh majidadi
ππππππππ
*RUHIN FANSA*
ππππππππ
Na
*Maryam ismail Majidadi*
Part 2 ,part 2 ,part 2
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*ππ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Page 21-25
*Wanna page din sadaukarwa ne ga daukacin members na Ruhin fansa Fan,ina matuk'ar jin dadin comments dinku*
Wani tunanin ne yazo mata a zuciya tace me hakan yake nufi?,hakan na nufin Ahaad ne yayi rapping dina?,das das gabanta ya fad'i ,no no sun Kama dashi ne kawai dan yana Yayana bayan wannan Babu wani abu Kuma,Aiban ne ya katse mata tunanin sakamakon shigowarsa yana fad'a fara'arsa cikin sigar tsokana yace"sannu da k'ok'ari uwar y'an ukku,haba mutun dama ya zama rusheshe yana cinye tiyan shinkafa a rana ae da walaki"k'ulli Umti tayi masa a baya yace"washh Allah Umti yanzu fa na girma da dukannan,nifa uban yara ukku ne"dariya dukansu suka saka ya kwashi yaran ya tsura masu ido sosai yana jin soyayyar yaran na ratsa shi ta ko ina,addu'a yayi masu,sannan ya bawa su Shuhada da Muslim da suka shigo yanzu, Shuhada sai surutu takeyi ta rike y'ay'a ita a dole itace mamansu.kwanan Shuzna biyu a asibiti aka sallamesu ,Tasha mamaki da suka koma gida siyayyah jibge ta iske a d'aki d'aya Wai dukna yaran ne,Daddy da Umti sunyi nasu,gana Ahaad da Aiban Muslim ma ba'a barsa a baya ba,Shuzna tayi kukan murna tayi godiya kamar zata cire bakinta bata tab'a zatan yaranta zasu samu soyayyah irin haka ba.
"Kije inji Daddy yana parlo"Shuhada ta fad'a.mikewa Shuzna tayi tare da sako Hijab dinta ta wuce parlon Daddy,anan ta samu Umti da Nani sai Kuma Aiban.har k'asa ta duk'a ta gaishe da Daddy,ya ansa cikin sakin fuska yana rike da Baby d'aya cike da kulawa ya tambayeta lafiyarta sannan ya daura da cewa"kin zab'awa yaran sunan da kikeso ayi masu hud'uba dashi?"sunkuyar da kanta k'asa tayi cikin natsuwa tace"Daddy duk Wanda aka saka masu yayi"murmushi kawai yayi ya juya ga Aiban yace"Baban yara kayi masu hud'uba da sunan da kaga ya dace"sosa Kai Aiban yayi sannan ya matso kusa da Daddy ya dauki hassan yayi masa hud'uba a kunne ya mik'awa Umti shi yace"Sunansa JAFAR zamuna kiransa(Fayyad)",sannan ya k'arb'i Hussain shima yayi masa hud'uba ya mik'awa Nani yace" Sunansa KABIR zamuna kiransa(Fayyam)",sannan ya k'arb'i mace yayi mata hud'uwa ya mik'awa Daddy yace "Allah ya raya Sha'awanatu zamuna kiranta(Faida)"wani irin bugawa gaban Daddy yayi da matuk'ar k'arfi sanadiyar jin sunan Sha'awatu da yayi amma yayi shiru baice komai ba sai faman Allah ya raya suke fad'a,sanarwar gasar da aka sabayi akan computer duk shekara a k'asar India ne akeyi a television dake kunne,masu kud'i daga garuruwa sukan saka kud'ad'e masu matuk'ar yawo domin a bawa wanda yaci,d'agowa Shuzna tayi tana kallon sanarwar hakanan taji tana sonyi ,kallon yanayinta Aiban yayi yace"zakiyi gasar ne?,tunda naga ke baiwarki a computer yake"murmushi tayi ta d'aga kai alamar eh,daga nan Kuma bai sake cewa komai ba.
Yaune suna ansha shagali sosai,sanuwa Daddy ya yanka da raguna Kuma ba wani taro akayi ba kasancewar ba gida bane Nigeria sai dai abokan Umti ne da suka zo yi mata murna,ba laifi Shuzna ta samu kyaututtuka ita da yaranta,sunsha gayu sunsha hotuna ,anyi komai cikin aminci da jin dadi.sai dai muce Allah ya raya mana Fayyad ,Fayyam da Kuma Faida.
Bari mu lek'a gida Nigeria.
Kishingid'e Mama take a jikin kujera tana kallon Fadila dake zaune da k'atoton ciki a gabanta sai ruzgar kuka takeyi tace"Ae Mama duk laifinki ne,kece kika gayawa Yaya Ahaad ,gashi ya hana a zubar ga dukan tsiya da yayimun wata nawa ina jinya,ki duba kiga duk yarda na fige na lalace"."ohni Khadija naga abunda ya isheni a gaskiya Fadila na gaji da wannan iskancin surutun naki,ni meye had'ina da ke,bancin Kabir daya haifo mani bala'i aeda tuni na koreki daga gidannan ciki Kuma saikin haifa,ko da ubanki kike yawa a ka"Mama ta fad'a tana hararen Fadila,sai Kuma kawai ta fashe da kuka tace"nan nan aka kashemun jikata na rasa gano gaskiya gara ma mutuwar y'an uwanta naga gawar amma ita kamar diyar Baby ace ba'a ganta ba,bazan tab'a yafewa Wanda yasa naci amanar da Jafaru ya barmun ba".wani irin ihu Fadila ta saki ta dafe ciki tana "wayyo Allah Mama mutuwa zanyi cikina,wayyo Allah na Mummy na)da gudu Mummy ta shigo d'akin tana rike Fadila ganin nak'uda ce takeyi yasa sukayiwa Dr Jamil waya yazo gidan.cikin