Showing 6001 words to 9000 words out of 16222 words

Chapter 3 - RUHIN FANSA By Maryam Majidadi part 2 -1-1.txt

awa d'aya ta haihu y'arta mace kyakyawa da ita ,gyarasu akayi sannan suka fito sai dai Kuma ba zaka iya gane farin ciki sukeyi ba ko akasin haka,ranar suna yarinya taci Bilkisu suna kiranta(Nasirah),sosai Aliyu yayiwa y'arsa sayayyah dan ya k'arb'i cikin,sai dai daga wurin iyayensa ne keda matsalar.ansha shagali sosai .
Bayan suna da kwana ukku Ahaad ya diro gari,Fadila na hangoshi tayi d'akin Mama da gudu tana ihun ceto tace"Mama na shiga ukku ga Yaya Ahaad nan,wallahi ya dawo dama yace bazai kuma zuwaba harsai na haihu,kuma ae Aliyun ya k'arb'i cikin yarinyar Mama ki taimaka mun"."ae da yake sadda zaki yawan ta zubar dinki na taimaka maki dole a yanzu ma na taimaka maki"Mama ta fad'a ta gutsirar goron dake hannunta.kai tsaye Ahaad d'akin Mama yayi fuskar nan babu alamun annuri ya dawo Ahaad dinsa na asali,zama yayi a chair ba arziki Fadila ta had'iye kukanta tana k'yarma duk'ar da kansa yayi wanda tun d'azu yake barazanar tsarwatsewa wani wawan Kallo yayiwa Fadila yace"Dan uwarki zonan"sai da numfashinta ya dauke na wucin gadi tace"Yaya kayimun rai,ka tausaya mani kodan y'ar dazan raina y'anzu,wallahi Yaya tsautsayi ne".jin maganar Fadila yasa Mummy da Amaan harda Abba shigowa part din Maman,zama Abba yayi yace"Babana lafiya kuwa?".kasa magana Ahaad yayi ya daura kansa saman cinyar Abba kawai yana sauke ajiyar zuciya."to wallahi kaji da iskancinka Sulaiman,Dan nazaka dakarmun y'aba,cikin shege aeba kanta farau ba,kafin tayi ae wata ta fara lokacin da Najma tayi ae bata fuskanci tsangwama irin haka ba,rubuce yake a kaddararta dama zata haifi Nasirah bata hanyar aure bane". murmushi Amaan yayi yace"Mummy ae ita Najma abun soce shiyasa da taje tayo karuwancin t...."kasa k'ara magana Amaan yayi sakamakon wasu gigitattun maruka da Ahaad ya wankesa dasu,kafin ya idasa dawowa daidai Ahaad ya Kuma shakareshi cikin kausashiyar murya yace"don't u ever say something bad against her,cos i will not tolerate it,Najma ta haihu ne da aure,kuma cikin jikinta nawane,nine wanda yayi rapping dinta,kaga yarana ba shegu bane,Kuma Najma tana nan da ranta bata mutuba kuma ta haihu cikin aminci",sosai idanuwan Amaan suka firfito ko motsin kirki ya kasayi ,kuka Mama ta saka tace"kuna kallowannan bayahuden zai kashemun jika da zuciyarsa irinta arna".da k'yar Mummy ta k'arbe Amaan daga hannun Ahaad, Amaan kam numfashi ya soma daukewa ya rarumi kwalbar ruwan sanyi ya soma kwankwad'a yana maida numfashi.cikin sigar rikidewa Mummy ta kalli Ahaad tace"yaushe ka fara shaye shaye ban sani ba?,yaushe ma ka keb'e da Najmar balle har kayi mata ciki,ina ka ganta kasan tana raye?".dafe kansa yayi alamar gajiyawa yace"ki tambayi wancan makirar yarinyar da yanzu zanwa bugun mutuwa sannan zaki gane".hannu Fadila ta daura a Kai tace "na shiga ukku Yaya,ka rufamun asiri".murmushin takaici Ahaad yayi yace"Alhmdlh Fadila aeni godiya ya kamata nayi maki,duk tsananin kiyayyarku da Najma gashi harta haifaman yan ukku,kinga hanyace kika sharemun tana dawo da auren dake tsakaninmu Kuma ta zauna cikinku,kinci arzikin taimakon da kika yimun da wancan yarinyar da kika haifa wallahi da yanzu wani labarin akeyi ba wannan ba"juyawa yayi zai wuce da gudu Mummy ta cakumo wuyan rigarsa tace"kayi hauka ne?,wallahi indai ina raye jinin Sha'awa bai isa ya kusanto inda nake ba,duk ranar daka maida aurenka da wannan yarinyar a ranar zan tsine maka na Kuma sallamaka gareta,Najma ta mutu karya kakeyi wata ka gani kamar ita"tamkar Mummy ta zare haka takeyin surutai sai da Abba ya kamata yayi d'aki da ita.Fadila kam y'arta ta sab'a tayi d'aki da gudu ta danna Key,dariya Mama ta saka tare da sakin gud'a tace"tace Najma gadon arziki yarinya mai nasara a rayuwa kainuwa dashen Allah,duk lokacin da akaso aga bayanshi sai ki dawo da nasarorinki,tabbas ke jinin Jafaruce sai yau na k'ara tabbarwa.
Ahaad kam yana shiga d'aki ya sakawa k'ofar key ya daura kansa bisa gado saijin hawaye nabin gefan fuskarsa yayi.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi Mana kyakyawan karshe
Stylish star
JORDERH MAJIDADI


πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*RUHIN FANSA*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Na
*Maryam ismail Majidadi*


Part 2 ,part 2 ,part 2


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*_________________________________*


Page 26-30


Birnin indiya


Kamar yarda Shuzna ta nuna ra'ayin ta akan gasar haka Daddy da Aiban suka shiga suka fita tare da saya mata form din suka yi mata komai da ake buk'ata.lokacin da Aiban ya kawo mata takardun ba k'aramin farin ciki tayi ba tayi masu godiya kamar ta ari baki Nani ma ta tayata.
A kwana a tashi ba wahala wurin Allah inda rayuwa ke canzawa,ya Kama yaune su Shuzna suke gama wanka,Kuma tun washe garin suna da Ahaad yabar India bai sake waiwayarta ba,hakan yayi daidai da Kuma washe gari zasu gabatarwa da wannan gasar data shiga,tuni an samowa su Fayyad mai aeki sunyi tana kula dasu sunyi wayau sosai.Shuzna kam ta mayar da hankalinta ga bitar gasar da zatayi.
Next day.
Fitowa tayi sanye cikin shigar farin wando sai top bak'a ta tattare gashin kanta ta saka shoe toms bak'ak'e,sai tashin kamshi takeyi,kallonta Umti tayi tare da sakar mata murmushi tace"kinyi kyau y'ata,amma hakan zaki fita?".kallon jikinta tayi tayi murmushin itama ta koma kusa da Umti ta zauna tace"Umti wannan shine shigar dana saba da ita,hasalima inba da wannan cikin ba bana saka kaya irin namu na hausawa,amma Umti kada kiji komai insha Allah zanci gaba da kare mutuncina kamar a da"shafa gefen fuskarta Umti tayi tace"amma y'ata yanzu kefa uwace".k'asa Shuzna tayi da kanta sannan tace"Umti zama uwa bashi zaisa na canza burikan rayuwata ba,ko Kuma na fasa bin hakkina a wurin azzaluman can ba,na rayu ne cikin burin d'aukar Fansa duk da ba hakan yana nufin nima na zalincesu ba,sai dai kuma bazan tab'a iya yafe masu ba"."Allah ya bada sa'a kije idan kin dawo zan fad'a maki abunda baki tambayeni ba,zan gaya maki dalilin baki fuskar nan da nayi"fitowar Aiban yasa batace komai ba ta tashi suka wuce,tunda suka fito take kallon garin yana matuk'ar burgeta,addu'a kawai takeyi a ranta da neman nasarar abunda zatayi ,holl din cike yake tun a hanyar k'arasowa wurin zaka gane ana babban tarone na k'asashe.wurin da aka tanadarwa wad'anda zasuyi gasar taje ta zauna mutun 10 ne kacal a wurin,bayan bayanai aka soma fara gasar Shuzna itace ta 6 dan haka ta shiga wurin canza kaya ta saka rigarta mai tambatin tutar Nigeria da Kuma number dinta a jiki,ko wacce daga cikinsu wurin computer din da aka tanada ta nufa,kallon abun Shuzna takeyi kud'i ne aka saka wurare daban daban tare da matakan tsaro na na'u'rori duk wanda yayi nasarar had'esu a account d'aya cikin awanni biyar ta shine Wanda yazo na d'aya a gasar,umarnin farawa aka basu dan haka Shuzna tayi Bismillah tare da fara sarrafa computer din ta yadda take ganin zata fi Mata sauki.Aiban ma addu'a kawai yakeyi mata,cikin ikon Allah Shuzna tana ta sarrafa computer bataga wani wahala akan aekin ba amma saiya kasance kai k'warone akanta ita dama ta kasance hakan tun tasowarta babu na'u'rar da bata iya shiga ta lalata ko Kuma tayi abunda take so ta fito,ko da akaje hutun rabin lokaci ita bata bar wurin ba ,dan bata da wani malami Wanda zai k'ara bata haske akan abun.cikin awa hud'u cib ta samu nasarar had'e kud'in a babban account na k'ungiyar sunkuyar da kai tayi tare da fadin "Alhmdllh "sannan ta mik'e,ta mik'a sauran takardun dake wurinta,ba k'aramin mamaki mahukuntan wurin sukayi ba Wai a awa hud'u ta gama wannan aekin,zuwa awa biyar din kowa ya fito daga.sannan kowa ya wuce gida zuwa gobe zasu fad'i sakamako a babban taron da suke shiryawa sannan Kuma su bada kyaututtukan da suka tanada,tana dawowa Kuma ta iske takardun makarantarta Wanda har registration an gama masu ita zata karanci Computer ita Kuma Shuhada Law kowa gidan da fatan alkhairi suke bin Shuzna da mata addu'ar Allah yasa taci gasar,yaran Nani ta kawo mata tace "duk yau kinbar yara da madara kawai yanzu saiki basu abincinsu".turo baki tayi tace"Nani ni dan Allah ki barsu ,na gaji yanzu fa"ta k'are maganar tana shagwab'e fuska ."a'a baza'ayi hakan ba,maza kije ki watsa ruwa ki fito ki karb'i yaran ki dubasu".mik'ewa tayi ta wuce hanyar d'akinsu ji tayi ta bige da mutun ta yo baya tare da fadin"washhh"kallonta yayi sama da k'asa yace"daga Ina kike haka ?"murgud'a d'an k'aramin bakinta tayi tace"inda ka aekeni".zaro ido yayi ya mik'a hannu zai tamk'ota ta shige d'aki da gudu tana masa gwalo.k'wafa yayi sannan ya sauko k'asa,kai tsaye wurin Nani ya k'arasa ya d'auki Fayyam dake ta neman fara kuka,d'agashi yayi yace"no baby boy,meyasa zakayi kuka?"kamar yaji me yace yakoyi shiru yana kallon Ahaad,shikam Ahaad kallon da yakeyiwa yaran na ganin yadda suke k'ara rikidewa ne suna komawa shi yakeyi,sosai ya rungume yaron a jikinshi yana k'arajin soyayyarsu a ranshi.Shuzna kam tana gama wanka ta saka k'aramar riga kawai tayi kwanciyarta ta soma lumshe ido alamun bacci.jin ta dade bata fitoba Nani ta fara fad'a"Allah yarinyar nan taurin kanta ke niyar fara aeki akan yaran nan,ace duk lokacin da akace ki bawa yara mama sai anyi rigima dake,ita aeba haka aka reneta ba,shin me madara zata k'ara yaran nan dashi?".mik'ewa Ahaad yayi yace"Nani bani yaran dolenta ta basu abincinsu kuwa"Fayyad ya dauka mai renonsu ta dauko Faida suka nufi d'akin,be lura da ita ba,hakan yasa ya daurasu saman bed sannan ya juyo ya karb'i Faida,yana juyowa idanuwansa suka sauka akan Shuzna wacce tayi d'ai d'aya a bed iskan AC yana ratsata rigarta ba wani kaurine da ita ba musassaman wurin breast din, idanuwansa suka sauka akan santaleliyar cinyarta fara tas sai shek'i takeyi,idonsa yakai a sauran jikinta ji yayi ya fara k'yarma da sauri ya tauna lips dinsa kamar zai huda, breast dinta yake Kallo Wanda suke tsaye g'yam kamar zasu huda rigai har sawun nipples dinta yana gani ,ganin tana motse motse yasa yayi k'ok'arin daidaita kansa,cikin kausashiyar murya yace"ke,ke"juyowa Shuzna tayi tana binsa da Kallo da sauri ta mike tace"malan me kakeyi a d'akina?"ganin yayi shiru yana kallonta yasa ta kalli jikinta,ihu take da niyar yi da sauri ya rufe mata bakinta da hannunsa,wani irin yarr sukaji su duka biyun,basarwa yayi ya rankwafo daidai saitin fuskarta yace"ke ki rufe mana wannan b'areran bakin nak'i mai Kama da k'ofar tukunya mumuna kawai,meye kike wani neman Hijab?,ni ae banga komai a jikinki da zaki boyeba,shi kanshi mijinki na tausaya masa daya auri kwaila,inma rasa abun Kallo sai bsjawara kwantan wani?Ina saurayi sabon jini?".duk da maganar ta matuk'ar shiga Shuzna haka ta daure tare da ture hannunsa a bakinta tace"Dallah malan daina tab'ani da wannan mugun turaren naka mai saka mutane amai,Allah sai ya rik'a sakawa kanayin wari"ta k'arashe maganar tare da shiga toilet ta wanko bakinta.mutuwar tsaye Ahaad yayi sai Kuma ya saki murmushi yace"kina nan yarda kike,yarana na kawo a basu Nono "wani kallon banza tayi masa tace"hmmm to sannu da k'ok'ari nikam barci zanyi na gaji bana da lokacin wasu yara anan"ta juya da niyar hayewa bed fizgota yayi ta fad'o a kirjinshi sai da ta tsorata da ganin fuskarshi danya koma Ahaad dinshi na asali yace"kada kiyi wasa dani Najma inba haka ba ranki zaiyi matuk'ar b'aci,wallahi ko ki basu ko Kuma ni da kaina na basu",tasan sarai zai iya,a zuciyarta tace kardai ace ya ganeni,a fili Kuma tace"ni wallahi ba y'ar iska bace bare ka tab'amun jiki,Kuma ban bada..."bata k'arasa maganar ba tayi saurin d'aukar Faida ta zaro breast din ta saka a bakinta ganin Ahaad yayo kanta, murmushi yayi yana jinjina k'arfin hali irin na Najma,Faida na kamawa Shuzna ta rumtse ido ta saki siririyar k'ara cikin Shagwab'ar da bata San tayi ba tace"wallahi Yaya da zafi,ni bana iyawa duka ukku fa"ya k'are maganar hawaye na gangarowa akan fuskarta,taci gaba da cewa"ni karka k'ara cemun wata ko Najma,ni ba sunana kenan ba"murmushi kawai yayi ya fita daga d'akin.
Washe gari da la'asar suka shirya dan zuwa wajen karb'ar sakamako,duka gidan sukayi Mota biyu suka tafi,Shuzna ansha kwalliya cikin gown purple colour sosai ta matuk'ar yi Mata kyau ga net data yafa a sakan rigar bayan kanta ya sha gyara.
Tunda aka fara jawabi babu abunda Ahaad yakeyi sai kallon Shuzna tayi makukar yi masa kyau musassaman da take rike da yaran nata tana sakar masu murmushi,jin an ambaci sunanta yasa ta d'ago a matuk'ar mamaki kowa ita yake kallo yayinda yayinda camerori da dama suke ta faman daukarta hoto,jinjina kai tayi tace"Alhmdllh ya Allah,yau nice nazo ta d'aya a wannan gasar ta k'arashen duniya,a matsayina na y'ar Nigeria"mik'awa Umti yaran tayi ta mik'e tana tafiya kwanin ban Sha'awa ga kowa ta hau step ta k'arasa inda zata k'arb'i lambar yabon tata,wasu hawayen farin ciki ne suka zubo mata,ta soma d'aga abun tana d'aga hannunta,sai wata y'ar China tazo ta biyu sai y'ar nan k'asar India tazo ta ukku,anan take aka bata ATM da komai na account din da aka tanadarwa wacce tazo na d'aya zunzurutun kud'i ne a ciki Wanda anan Nigeria zasu kai kimanin milyan D'ari ukku da makullin Mantions(manyan gidaje)guda biyu d'aya anan indiya sai d'aya a America ga dank'areriyar motar hawa,sai masu tsaronta har mutum hudu ,sai kuma wad'anda suka bata kyauta na mamakin tana y'an Nigeria taci wannan gasa nan fa companoni da dama suka fara kawo mata hari tun a wurin,amma taki sauraran kowa a lokacin,a kai tsaye aka fara haskata a gidajen television da social media kota ina hotunan Shuzna ke yawo ,anyi mata karramawa sosai harda shugaban k'asar Nigeria sai da ya bata kyauta ,tayi hotuna da y'an uwanta Wanda kowa murna yake tayata da fatan alkhairi,a hankali ta taka zuwa gaban Aiban dake tafa mata hannu ,hawaye nabin fuskarta zatayi magana yayi mata alama da tayi shiru yace"ki godewa Allah,ni kawai d'an aeke ne"da haka aka tashi taron suka dawo gida kowa murna fal a ranshi, Shuhada kam ae bakinta baya rufuwa itace ke ansa ma Shuzna murna ma.a gajiye Shuzna take dan haka key ta sakawa d'akinta ta fara farar bacci abunta.
*Sai muce ni da Ruhin Fansa Fan muna taya uwarsu Fayyad murna ,Allah ya k'ara arzik'i mai amfani*
"Ki shirya kije meeting din gobe,nayi masu alk'awari zakije,kinga Kuma gobe zaki fara zuwa scul"cewar Daddy dake kallon Shuzna.
Lallai Daddy ya wuce ya roka wani abu a wurinta,tun bayan wannan gasar take b'oyewa daga duk wasu taruruka amma yau kam tunda Daddy ya rok'a tabbas zataje,kanta a k'asa tace"to Daddy insha Allah zanyi k'ok'arin zuwa".
Washe gari tunda wuri ta shirya cikin suit bak'a rigar ciki fara tayi matuk'ar kyau hills ta saka suka bak'ak'e sannan ta d'auki hand bang jelar gashin kanta ta tattare ta daure ta fito rike da key din motarta,kai tsaye wurin Umti ta nufa ta gaisheta sannan ta gaishe da Nani tare dasu Muslim kowa ya ansa a tsaitsaye tasha tea ta sumbaci yaranta ta fita da sauri ganin lokacin ya tafi,babban wurin taron ta nufa,driver na Jan motar da take ciki,sai motar bayanta masu tsaronta su hud'u ,tayi parking inda aka tanada sannan ta wuce ciki,kowa ya taru ita kad'ai ake jira cikin takun k'asaita ta shiga wurin gabanta yayi mugun fad'uwa ganin Ahaad a wurin ,kauda idonta tayi ta wuce inda aka tanadar mata ta zauna ,suka fara gabatar da taron,bata tab'a tunanin Ahaad yana kasuwanci ba sai yau.duka taron ya gudana yarda ake so sai bai wuce kowa dake kawo mata hari akan taje tayi aeki a company dinsu ba,duka ta fad'a masu makaranta takeyi yanzu gaskiya Kuma ita bata sha'awar yin aeki amma zata saka hannun jarinta a wani company na America sai d'aya anan india sai d'aya a istanbul.kuma tace idan suna buk'atar wani abun na b'angaren computer din zatazo ta tai maka,dan ita data gama karatu k'asarta Nigeria zata koma,ba yarda suka iya a dole suka yarda da hakan sannan aka tashi kowa yana k'ara tayata murna,da sauri masu tsaronta suka k'araso tare da sakata tsakiya ta wuce abunta,tana tunanin ashe Ahaad babba ne haka a kasuwanci yana da hannuwan jari a campanoni amma ita bata da wani labari Ashe shiyasa baya zama Kuma ayyuka keyi masa yawa ga aekin soji Kuma yana fama.
Lokaci mai tayi baya jira inya wuce ya wuce kenan a kwana a tashi yau gashi Najma ta kammala Digree dinta akan Computer science ta fito da sakamako mai kyau tayi matuk'ar farin ciki sosai, a lokacin yaranta na da shekara 3 ,ga kasuwancinta ta ko ina nasara take samu dukiya sai habb'aka takeyi ta kwanta Naira.abunda ke matuk'ar bama Shuzna mamaki shine Fayyam ,ko kad'an baya jin magana baya da tsoro ga d'an banzan wayau da k'iriniya,ga zuciya baya d'agawa kowa Koda wasa Babu mai iya tank'warashi itama wani lokacin sai tayi da gaske,baya son hayaniya ko magana saika shekara kanayi sai ya ga dama yake maida maka ansa,a tak'aice dai Babu abunda ya baro daga halin Ahaad kamar shine aka sake daukowa aka ajiye yana yaro.a lokacinne ta shiga neman aekin soji bata sha wahala ba ta samu kuwa Navy dan haka ta wuce training na tsawan wata shidda cikin ikon Allah tayi ta gama ta zama cikakkiyar soja Kuma suka dauketa da Digree dinta dan sunan da tayi yasa bata wani wahala ba ta fito a matsayin Captain.bayan samun horon soji da tayi,abubuwa da yawa sun faru a lokacin.
*Note zakuga nan page din yawanci labarin yazo a gaggauce to ina so in shiga cikin aenahin labarin ne,ina so na gama book din kafin azumi,na gode da soyayyarku gareni*


Allah ka gafartawa iyayenmu kayi manakyakyawan karshe
Stylish star
Jorderh majidadi
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*RUHIN FANSA*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Na
*Maryam ismail Majidadi*


Part 2 ,part 2 ,part 2


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*_________________________________*


Page 31-35


Tafiya takeyi cikin nutsuwa sanye take da uniform na kakin soji tayi matuk'ar kyau a cikinsu,gashin kanta a nannade ta rike cap din a hannu ba zaka tab'a cewa wai Shuzna tayi aure ba ,bare Kuma kace ta haihi su Faida,babban wurin taron ta doso da d'an gudu gudunta ta shigo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login