Showing 21001 words to 22311 words out of 22311 words
Chapter 8 - ABU BILAL Document Complete Book (Maryam Isma'il Majidadi ).txt
ya kasa ƙwaƙwaran motsi a wurin da masifar ƙarfi ya rungumi Bilal wanda idanuwansa suke buɗe akan fuskar Abu bilal ,wasu hawaye ne suka zubowa Bilal kafin a hankali idanuwansa suka rufe ruf,Daddyma tsaye ya tsaya cak Aunty Aysha kam numfashinta ke niyar ɗauƙewa ta saki ƙara.a hankali Abu bilal ya soma ɗaga rinanun idanuwansa wanda i zuwa yanzu baya fahimtar komai miyan bakinsa ya ƙafe,kamar a mafarki haka yaga Halima kamar an jefota daga bene ta nufo ƙasa itama,wani irin ƙarfij hali yazo masa yayi saurin miƙewa ya tarota ta faɗo akan hannayensa,tana kuma sandarewa alamar ta some.da gudu Daddy ya karaso yana janyeta daga jikin Abu bilal yana jefa masa wani kallo mai wuyar fassaruwa.shikan kamar marar lakka haka ya faɗi a gaban Bilal,kuka yake son yi amma sam yaƙi zo masa ji yayi kansa na jujjuyawa kamar juwa na katantanwa da shi,da gudu Amma ta karaso tana janye Bilal daga jikinsa tana sakin kuka mai cin rai tana faɗin"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un "a guje Faruq ya karaso wurin yana ansar Bilal daga hannun Amma yayi ɗakinsa dashi dan basa taimakon gaggawa,dishi dishi haka Abu bilal ke gani ko kaɗan ya kasa furta komai sai bin jinin Bilal dake malale a wurin yake da kallo kamar wani dolo,da ƙyar ya iya tattaro sauran yawun dake bakinsa masu masifar ɗaci ya haɗiye da ƙyar yana lumshe idanuwansa yasa hannuwa ya shafi fuskarsa.a rikice Faruq ke duba Bilal kasancewar yana da kayan aiki a gida amma sam Bilal yaƙi ko da motsawa a nan kuma ya tabbatar da cewa Bilal ya mutu,in da ya ajiyeshi kam gaba ɗaya wurin ya ɓaci da jiki,ji yayi kafafunsa sunyi sanyi kamar ba zasu iya ɗaukarsa ba,jan zani yayi ya lulluɓe gawar Bilal yana cewa"Allah ya karɓi baƙuncinka Bilal".kafin jiki a sanyaye ya fito parlo,tsai tsaye ya gansu Aunty Aysha sai kuka takeyi kamar zata shiɗe ,Amma ma kukan takeyi Daddy ne zaune a chair yasa Halima a gaba sai kallonta yake wanda har lokacin bata farfaɗo ba,kallonsa ya mayar ga Abu bilal dake tsaye a jikin bango ya lumshe idanuwansa yana kallon sama ,jijiyoyin kansa sun fito radau raɗau kamar an zana su kallo ɗaya zaki masa kiga tsantsar tashin hankali ƙarara a tattare dashi.cikin rashin ƙwarim gwaiwa Faruq ya ƙarasa gabansa yana dafa kafaɗarsa.a hankali ya buɗe idanuwansa yana kallon fuskar Faruq dake nuna tsantsar karaya lokaci ɗaya,idonsa ya mayar ga ash ɗin wandonsa wanda duk jinin Bilal ya ɓata,jan hannunsa kawai Faruq yayi zuwa cikin ɗakin da Gawar Bilal take a rufe,har gaban gadon Faruq ya kaisa yana bubbuga kafaɗunsa.wani irin tsinkewa gabansa yayi zuciyarsa ta harba da masifar ƙarfi hannu na ƙyarma yasa ya yaye zanin da aka rufe gawar Bilal da ita.
ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA ƘYAƘYAWAN ƘARSHE
2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 18
Baya Sudais yayi saurin yi kamar zai faɗi tarosa Faruq yayi ,kasa cewa komai yayi gaba ɗaya ya koma batun-butumi zamewa yayi daga jikin Faruq ya zauna a chair tare da dafe kansa da duka hannu biyu,a daidai lokacin ne kuma Halima ta farka daga mugun mafarkin da takeyi tana raba ido,ƙoƙari takeyi ta tuna abunda ya faru amma ta kasa,ganin su Amma na kuka yasa ta yunƙura da ƙyar tana kuma kallonsu,safko ƙafanta tayi tana binsu da kallo kafin ta hango Faruq a ɗaki,miƙewa tayi kai tsaye ta nufi ɗakin jiki ba ƙwari,kamar marar gaskiya haka ta ƙarasa shiga ɗakin.saurin runtse ido tayi tana jin zuciyarta kamar zata fasa ƙirjinta ta fito saboda ganin gawar Bilal da tayi ,mayar da kallonta tayi ga Abu bilal dake duƙe har lokacin gabansa ta duƙa tare da ɗaura hannuwanta a kan jikin shi,cikin dishewar murya tace"Yaya talk to me,is'n't you talking".ɗagowa yayi yana kallonta hawayen dake maƙale a idanuwansa suna safkowa akan fuskarshi,ba ƙaramin tsorata tayi ganin hawaye a idon Abu bilal,idasa zama kawai tayi tana fitar da numfashi a hankali..lokaci ɗaya mutuwar Bilal ta zagaye ko ina kasancewar yaro ne na mutane ga fara'a .miƙewa Abu bilal yayi yana barin ɗakin da Gawan Bilal take,da Dattiya yaci karo a gate da Mama uwani da Karima ,kuka wewe haka Dattiya yakeyi yana sharar majina yana ganin Abu bilal ya kuma rushewa da wani sabon kuka yace"wallahi wannan yarinyan ta cucemu,Allah sai ya saka mana,dole yanzu mu wuce da ita chazi ofis idan na yarda Allah ya tsinan,meye wani Halima ?,a'a kaini raba ni dole ta biya Dilalu".ta gefansu Abu bilal ya raɓa ya wuce karima ta bisa da kallo hawaye na safkowa idonta ganin yarda lokaci ɗaya ya gama fita a hayyacin shi.ciki suka ƙarasa wani irin ƙwalalo ido Dattiya yayi yace"kul ba ruwana,meye wani gidan Alhaji Abu,wanda dasa hannunsa aka kore ni ina galantiyo a titi,tona tabbata da gangan ƴarsa ta kashe wannan yaro Dilalu,alqur'an hukuma ce zata rabamu,ni ba ruwana".kallonsa duk mutanan ɗakin suke yi a haka su Mamy suka ƙaraso harda Abba babu wanda yake komai har aka gama shirya Bilal .raba ido kawai Halima takeyi ta makure jikin bango .a haka aka shigo aka ɗauki Bilal zuwa waje dan yiwa gawansa sallah.babu wanda yaga fitar Halima sai dai aka jiyo muryarta da ƙarfin gaske tana kiran"Yaya Aliyuuu".daga duƙen da yake yayi saurin miƙewa ganin yarda ta fito babu ko hijab bare hula,tana hangosa tayi kansa da gudu tare da shaƙareshi tace"Yaya kace su dawo mana da Bilal ɗinmu Allah be mutu ba,kana kallo zasu tafi maka da ɗanka"kuka ya ƙwace mata ta kasa ƙarasa abunda take son faɗa,sosai ya kamata ya riƙe amma ya kasa cewa komai,gaba ɗaya ya nemi kalamai a bakinsa ya rasa .Lamis ne ya ƙaraso yana janyota luuu ta tafi ta sume a jikin Abu bilal,miƙawa Lamis ita yayi yana saurin juyawa ganin Abba da Daddy sunyo in da suke.haka Lamis ya ɗauketa ya wuce da ita cikin gida kafin ya fito aka sallaci Bilal aka tafi dashi maƙwancinsa(Allah kayi mana kyakyawan ƙarshe).kowa ya watse a wurin sai Abu bilal dake duƙe a gaban kabarin,wasu hawaye masu ɗumi suka zubo masa yana taɓa kabarin cikin cushewan murya yace"Allah ya jikanka Bilal,ka tafi ka barni,bana da wani farin ciki ko sauran amfani a duniya bilal haka na rasa Rumana kaima gashi yau na rasaka,hasbunallahu wani'imal wakeel".dafa kafaɗunsa Lamis yayi yana ɗagosa kasa kasa cewa komai yayi sai hannunsa da yaja,bin bayansu Faruq yayi shima he's restless a haka suka dawo gida.a cike unguwan take ta ko ina da maza manya da yara harda mata ko wannensu hannunshi ɗauke da muggan makakai kowa da abunda yake faɗa.da ƙyar suka kutsa zuwa gaban gate ɗin gidan Daddy.cikin rashin fahimta Faruq ya zaro ido yace"ban gane me kuke nufi ba".a fusace ɗaya daga cikin mazan yace"abunda kaji an faɗa dai,dole a fito mana da Halima muma mu kasheta mu rama abunda take yi mana,dama itace ta kashe Junaid ta kuma kashe Zahra ƴar gidan saneta jiya da dare ta kashe Habu da Lawali daga sun ganta tana bakin kango ita da wasu la'annanun irinta yanzu kuma sai ace ta kashe Bilal yaro bawan Allah ,wallahi mun gaji da shiru ana cutar damu".sakin hannun Abu bilal Lamis yayi da sauri ya shige cikin gidan kafin su lura.a dabarbarce yace"Amma ina Halima" Amma da suke tsaitsaye suna jin bala'in da ake waje ta nuna masa Halima da aka kwantar kan chair har lokacin bata farfaɗo ba,be jira cewarsu ba ya sunkuceta ya fito parlon rufa masa baya sukayi da gudu ya fice ta gate ɗin baya ya fice da Halima daga gidan.wata nannauyar ajiyar zuciya Amma ta sauke ganin sai da aka fita da Halima sannan mazan nan suka samu karfin buɗe gate ɗin gidan suka shigo cikin compound ɗin,sai kuma ga ƴan sanda da sojoji sun iso wurin ,take wurin ya hargitse sai da aka yi halbi sama sannan aka samu rangwame aka kora maza a waje