Showing 6001 words to 9000 words out of 22311 words
Chapter 3 - ABU BILAL Document Complete Book (Maryam Isma'il Majidadi ).txt
ta da faɗin"kaga uwar mugai,kaga Hajiya Jamila mata ga Alhaji Abubakar amarya shalele,angulu bata jewar banza,yau kuma da wacce akazo?,me aka ƙunso mana?".murmushi Hajiya Mama ta saki tace "wallahi talatu kinsan kan tsiya"ta ƙare maganar tana muskutawa da gyara zama sosai ,sannan taci gaba da cewa "nifa na gama yanke hukunci,yarda ban taɓa haihuwa a gidan nan ba,bana kuma iya bawa mutanan nan Lamis wallahi,shi kaɗai Allah ya bani wannan dalilin yasa na gama tunanina tsab na yanke shawarar basu ƴar mijina Halimatu".wata muguwar dariya Hajiya Talatu ta saki tace"gaskiya kin ƙware a fannin mugunta,kina ganin Alhaji Abubakar bazai gigice ba idan ya rasa Halimatu?,kifa tuna yayi tsawon shekaru be samu haihuwa ba sai daga baya ya samu Halima kuma ke shaida ce lokacin da yazo neman aurenki sai da ya baki tabbacin in dai kika so Halima to babu abunda bazai gagare sa yayi maki ba in dai a duniyar nan ne".tsuka Hajiya Mama taja tace"to sai meye daga wannan?,ni meya ruwana in ma mutuwa xaiyi ya mutu a raba gado a bani wannan uwar dukiyar daya tara in kwashi kasona in yi gaba,ko da Halimatu ranshi ce sai dai yayi haƙuri dan na gama yanke shawara ita zan bada,kuma ni kinsan basan shegiyar yarinyar nan nake ba mai kama da aljannu,ko kaɗan ita da uwarta bana ƙaunar ganinsu bare kuma naji tausayin su,bayan na gama da ita zan juyo takan uwar ne ae itama ".dariya sosai suka saka kafin Hajiya Talatu tace"hakan yayi,kuma wannan itace hanya mafi sauƙi da zaki kawar da maƙiyanki ba tare da kowa ya sani ba,yanzu idan dare yayi sai ki sanar kawai"da haka sukayi sallama kowa da abunda yake saƙawa a ranshi.tunda suka tashi tahfeez babu wanda yasan dawowanta kai tsaye ɗakinta ta shiga tare da faɗawa akan bed tare da lumshe idanuwanta dake niyyar canza launi,zanen surarshi kawai take gani tana mata yawo da yarda bakinsa ke motsawa yana magana,wani irin ƙayataccen murmushi ta saki tana kuma sauke tagwayen ajiyar zuciya tana jin yarda zuciyarta ke bugawa da tsananin tunaninsa tun daga jiya zuwa yau bata da sukuni sai faman tunanin Abu bilal,ganin duhun magriba ya taho yasa ta miƙe ta shiga toilet sai lokacin ta cire Unifoam tayi wanka kafin ta ɗauro alwala ta fito,cikin sauri ta shirya cikin riga da siket na material kafin ta kabbara sallah tunda ta gama sallahn bata tashi ba sai da akayi sallan isha sannan ta miƙe tana tattara kayan da tayi sallah kafin ta wuce gaban mirrow dan gyara jikinta.."wai ni kan ina Halima?,tun ɗazu banji alamun shigowarta gidan nan ba bare kuma motsinta"Hajiya Mama take tambaya.nisawa Amma tayi tace"ina jin shigowarta kuwa kinsan ƴar taki halinta sai ita wani lokacin shiyasa nima na shareta".gyara zama Faruq yayi yace"wayyo Ammanmu mun tuba ae da sai ki duba mana ita".ya ƙare maganar yana langwaɓe kai kamar zaiyi kuka.jinjina kai Amma tayi tace"Lallai ma Umar tunda an gaya maka nima bani da aikin yi ne ,tayi ta gama zata fito ta same mu ne".murmushi ya saki wanda ya ƙara fito da ainahin kyawun shi.Umar faruq irin mazan nan ne masu tsayi da kuma kaurin jiki sai dai ba sosai can ba,fari ne tas yayin da fuskarsa ke ɗauke da daradaran fararan idanuwa ga bakinshi gwanin kyau red,yana da saje da kuma gemu da gashin baki ga gashin kanshi baƙi sidiƙ kamar na larabawa.Ɗaga kanshi yayi yana dubanta tana tahowa cikin natsuwa tallabar kumatunsa yayi duka biyu yana kafeta da idanuwa ko kibtawa baya son yi.kai tsaye itama kusa dashi tazo ta zauna tana cewa"Yaya lafiya".taɓe baki yayi sannan yace"hala yau gidan lefi akayi maki kenan?".turo ɗan karamin bakinta tayi kafin tace"ko ɗaya fitan ne bana ji".dariya Hajiya Mama tayi tace"banga lefinki ba ƴar gado,kinga duk yau Daddynki yana waje can bukka shima haka ya faɗa mana".da sauri ta miƙe tana yin hanyar waje tana faɗin"ashe Daddy yana gidan shine ko a sanar da ni".miƙewa Amma tayi tana yin hanyar kitchen tana cewa"aifa shikenan,shima Daddyn ya gama sukuni ae".miƙewa Faruq yayi ya rufa mata baya.kai tsaye gate ɗin gidan ta buɗe babu kowa a wajen shiru sai hasken fitulin da suka ƙawata unguwar fita tayi tare da rufe gidan tana ƙoƙarin shiga ɗayan gate ɗin dake jikin nasu in da nan ne wurin shaƙatawar Daddy kuma suke kiransa bukka saboda gaba ɗaya wurin rufin bukka ne ƴar yayi wurin ya ƙawatu matuƙa.ko kaɗan bata kallon gabanta take tafiyarta burinta kawai taga Daddy ji tayi ta faɗa wa abu.cikin wani irin masifar tsoro da zaro ido taɗanyi baya tana niyar kurma ihu.saurin saka hannunsa yayi ya rufe mata baki yana kuma dallah mata harara cikin tsawa yace"ki rufe mun baki a wajen".wani irin ruɗewa ta kuma yi ko kaɗan bata ɗauki muryarsa ba saboda tsananin tsoron da take ciki tuni hawaye sun soma zarya akan kumatunta ta soma kyarma.kallo ɗaya yayi mata ya ganeta ras tsaki yaja tare da murɗe mata kunne yace"ke saurareni kona faffala maki mari".carab kunnuwanta kamar a mafarki suka amsa sautin daddan muryarsa dib dib haka ƙirjinta ya buga da masifar ƙarfi,a hankali ta soma buɗe daradaran idanuwanta wanda suka soma sauya launi tana ƙarewa fuskarsa kallo.wani irin haɗe fuska yayi yace"nifa bansan kallo".kunyace ta kamata tayi ƙasa da kanta yayinda murmushi ke suɓuce mata wanda batayi niya ba.cikin sanyin murya tace"Ayyah Hamma ka bani tsoro ".matsawa yayi daga kusa da ita yayi wucewarsa da sauri ta juyo tana bin bayansa da kallo .daidai nan Faruq ya ƙaraso tsareta yayi da idon tuhuma shima yana bin bayan Abu bilal da kallo kafin yace"waye shi?".taɓe baki tayi tare da buɗe hannuwa alamar bata sani ba tace"na bigeshi ne kawai".jinjina kai yayi kafin yayi gaba tabi bayansa a nan suka samu Daddy kishin kiɗe yana karatun jarida.kai tsaye matsawa tayi kusa dashi ta lafe a jikinsa tana tunanin me ya kawo Abu bilal unguwarsu.kallonta Daddy yayi ganin tayi shiru yasa ya shafo kanta yace"Ammina kina lafiya dai ko?".gyaɗa kai tayi alamar eh,sai wurin 9 suka koma gida shima dan gobe monday yasan Halima zataje school.da tunanin Abu bilal bacci ya ɗauketa.Ɓangaren Abu bilal kuwa yana shiga gida ya samu duka ƴan gidan zaune a tabarma.da sauri Karima ta miƙe tana masa sannu da zuwa beko kalli in da take ba ya ansa da "lafiya"zaiyi wucewarsa.Dattiya dake kwance ya ɗago yace"yanzu Sude sai dai kazo ka wuceni ko gaisuwar arxiƙi babu?",tsakani da Allah baka kyauta mun ba,ni mema na haɗa da kai banda tsoron Allah,nan nan Uwani ta gama kwashe maka karama amma na murje ido ina yayyafim ruwan bala'i"wani irin zabura Mama Uwani tayi tace"wallahi Dattiya kaji tsoron Allah ka canza Hali,ina ce kaine ka fara maganar Aliyun".wiƙi wiƙi da ido haka Dattiya yayi sai kuma yaja gefen babbar riga yana matsar ƙwallah tare da faɗin"shi dai ai Allah yana gani,kuma ba azalimin kowa bane,waye wani Sude can Allah na tuba bare da girmana na zauna ina gulmarshi".ihun da Karima ta saki ne yasa su duka miƙewa kowa yana raba ido a guje tayi ɗaki tana danna kuba,Mama Uwani ma tayi ɗakinta da gudu,kafin Dattiya yayi aure tuni Rambo ya iso kusa dashi yana niyar cabkar ƙafarsa wani irin tsalle yayi ya kama katanga ya afka gidan Malan Audu ya faɗa a bisa tuƙwanan ruwan labara yana ihu iya ƙarfinsa,Abu bilal kam ko a jikinsa ya buɗe ɗakinsa ya shigewarsa.a guje Malan Audu ya fito yana salati tare da kama Dattiya yana miƙar dashi tsaye yana cewa"kai kuwa lafiya ?".fizge rigarsa yayi daga hannun Malan Audu yace"da lafiya ka ganni haka?,wancan mugun yaron ne ya sako mana alkaba'i a gida,amma ka barni da Sude nasan tsiyar dazan ƙullah mashi,Allah zaiga tsiya zaiga Dattiya ma ba daga baya ba mun daɗe a duniya ana damawa damu.Malan Audu da yake aminin Dattiya ne komai suke ƙullawa tare suke yi ya bushe da dariya yace"kai kake raga masa dama,da gida na yake aeda tuni wani labarin akeyi ba wannan ba,haka kawai yaro ya zauna a gari yana cutar mu?".jinjina kai Labara tayi tace"wallahi kudai kiyayi kanku,bakin rijiya ba dai wurin gaɗan makaho bane,Aliyu Sudais dai ba daga baya ba duka zai iya daku".wani irin hayayyaƙo mata da sukayi yasa tayi saurin shigewa ɗaki tana sharesu.Dare ya raba tsakiya misalin ƙarfe 2:30am daidai agogo ta nuna a lokacin ne kuma na hango Hajiya mama lulluɓe cikin shigar jan kaya da baƙi tayi wani iri babu kyan kallo wani baƙin kasko ne a hannunta a haka ta haɗa wuta a ɗakinta tana ƴan sirkullenta,wani ƙaton mutun mai kama da siffar da babu kyan kallo ya bayyana yana wani irin ɓaɓɓaka dariya yana cewa"lokacin sadaukarwarki yayi,dole ne kiyi sadaukarwa dole ne ki bada jini ,dole ne ki bada rai Jamila".cikin rashin tsoro da kuma ƙwarewa a harkan ta kwashe da dariyan itama cikin rashin wani tunani tace"na bada Halimatus sadiya ƴar mijina,yarinya mafi soyu akab ahalinmu".wani irin dariya ya saki hayaƙi yana fitowa daga bakinsa yana faɗin"zaɓi mai ƙyau,dodo zaiyi alfahari dake Jamila ci gaba da ɗaukaka ya samu rayuwarki,kin bada sabon jini"da ƙarfi ya soma ƙwala kiran Halimatus sadiya,Halimatus sadiya,Halimatus sadiya"sai da ya faɗa haka har sau ukku sannan ya ɓace ɓat tare da duk wani abun da Hajiya Mama ta haɗa a wurin.wani irin firgigit Halima ta miƙe tsaye yayinda idanuwanta ke a rufe babu alamar ta farka daga baccin da takeyi ɓat ta ɓace daga dakin babu ita babu alamunta .
ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
VOTE
COMMENTS
SHARE
[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*_______________________
______________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
FREE PAGES
PAGE 5
Zagaye wurin yake da mutane iri iri kowa irin shigarsu ɗaya watau ɓaƙi da ja,wutace keci a tsakiyar babban filin da suke zagaye dashi kowa da abunda yakeyi ,wani ƙaton mutun ne zaune ba kyan gani fuskar nan murtuƙe babu alamun annuri a tattare da ita ya riƙe wata ƙatuwar sanda mai zanan maciji.a daidai tsakiyar mutanan wanda ƙaton mutumin da ya ɗauko Halima ya bayyana,haka itama Haliman ta bayyana har lokacin idanuwanta a rufe suke alamar tana bacci,nuna ta yayi da wannan sandar ta hannunsa tuni ta faɗi akan gwaiwowinta tana layi kamar wacce tasha wani abu.wata iriyar dariya suka fashe da ita,yayin da wata mata mai suna Dosun ta taho riƙe da ƙwarya cikinta ɗauke da wani baƙin ruwa kai tsaye gaban Halima tazo ta ɗago kanta ta saka mata ƙwaryar a baki tsab ta ɗure mata fiye da rabin ruwan kuma ta shanye sauran kuma ta wanko mata tun daga kanta har ƙafafunta.wata irin miƙa Halima tayi tuni xufa ya fara keto mata ,a hankali ta soma buɗe dara-daran idanuwanta wanda suka soma riƙiɗewa ,cikin rashin kuzari ta soma kallon in da take tana kuma jin ihu kala kala a wurin,a kan fuskar wannan ƙaton mutumin ta sauke idanuwanta da sauri tayi baya tana furta"innalillahi wa'inna ialaihir raju'un".sosai muryarta ta shiga kunnuwansa ya rufe ido da ƙarfi ya kuma miƙe zumbur.Halima batayi aune ba taji sirinji a cikin damtsen hannunta ana jan jininta wani irin zafi da daɗaɗin azaban allurar ya shigeta lokaci ɗaya,runtse ido tayi hawaye yana kawo mata ta miƙe tsaye da sauri tana furta"ke lafiya".ko kallonta Dosun bata yi ba tayi gaba da jinin Halima data ɗauka.raba ido Halima ta fara tana kuma karanto duk wata addu'a data zo bakinta ganin wannan mutumin na doso in da take tsaye,kuma sai lokacin ta buɗe idanuwanta da kyau tana ƙarewa in da take tsaye da kallo ba ƙaramin tsoro ya shigeta ba.zagayeta Oga Sam yakeyi kamar zai cinyeta ɗanya haka yake zuro harshe.cikin muryar kuka tace"dan Allah kada ka cutar da ni,kaji tsoron Allah,ni ban sanku ba,in lefi nayi maku dan Allah kuyi haƙuri".wata uwar dariya suka saki gaba ɗayansu wanda ke iya gane abunda take faɗa.cikin hausa marar ɗaɗi da kuma murya marar ɗaɗin ji Oga sam yace"kin damemu da magana a nan wajen".wani wuƙa mai sheƙi da kaifi taga ya bayyana a hannunsa ya ɗaga da niyar caka mata.wani irin ƙwalalo ido tayi ta soma karanta ayatul kursiyyu da duka iya ƙarfinta da sautin muryarta.tuni hannunsa ya soma rawa yana ƙarewa kyakyawan fuskarta kallo wanda a yanzu ta riƙiɗe ta koma ja saboda tsananin tashin hankalin data tsinci kanta a ciki.Ɗan jim yayi kafin yaja baya xuwa wani ɗaki cikin sauri yawancin mutanan dake wurin suka rufa masa baya.ganin duk wanda ake buƙata ya shigo yasa ya fara magana yace"wannan yarinyar xai mana wahala mu iya kasheta da sauƙi,kuma tabbas idan muka takura akan hakan xata mana ɓannar da shekaru da dama aka mana irinta ko kuma in ce ta xarce wacce aka mana ma,wanan dalilin yasa na yanke shawarar mexai hana itama mu janyota a ƙungiyar nan,kafin idan ta gama mana amfani a lokacin babu Allah a bakinta sai mu kasheta kuma daga yanzu lokaci zuwa lokaci xata kasance cikin tsananin azaba da tsoratarta wannan shine hukuncin da xamu mata na kasa kasheta da mukayi a yanzu".babu wanda yaja da maganar tasa lokaci ɗaya dukkansu suka haɗa hannuwa suna karanta wani abu marar ɗadi da yin mubaya'a akan hukuncin da ogan nasu ya yanke.yarda sautin muryarsu ke fita haka hajijiya ke juyar da Halima kanta na matuƙar sarawa da masifar ƙarfi,lokaci ɗaya cikinta ya wani murɗa ta zube a wurin a kakkafe tana kyarmar sanyi wani irin azaba ne ke ziyartarta yayin da ta gara rolling a cikin ƙasar wurin kamar wacce take zagaye wurin.wani irin kukan wahala ta saki lokacin da take jin saukar wani ruwa a jikinta kamar ana yayyafa mata wuta,ga masifar wari,haka tana ji tana gani suka kuma ɗura mata wanan ruwan cikin nishin wahala ta sulale wurin wani wahalallan bacci nayin gaba da ita.nunata Oga Sam yayi da wannan sandar ta hannunshi tuni ta ɓace bat kamar ba'a taɓa kawota wurin ba.dukansu suka fashe da tsananin dariyan mugunta.a cikin daren kuma Talatu ta kirawo Hajiya Mama ta zayyane mata abunda ya faru da kuma hukuncin da Oga Sam ya yanke,a razane ta miƙe zaune tace"ina ce dai bata san wanda ya kawota wurin ba?".dariya Talatu tayi tace"kwantar da hankali ina zata samu damar sani bayan ciwan azaba daya sakata gaba,ae ina mai tabbatar maki ko ni da naje wurin bazata taɓa ganeni ba bare kuma ke".wata sanyayyar ajiyar zuciya Hajiya Mama ta sauke tace"wallahi har naji sanyi,ai ni ƙara ma aita gara mun ƴar iskar ta fitini kowa ta zama anno ba kafin tabar duniya,anjima kizo zaki rakani kan dutse can bicci insa a ƙara ingizowa shegiya abunda xai mun maganinta dan wallahi ni nafi kishi da ita akan uwarta ma".dariya sosai suka saka kafin suka yi sallama da rabuwa akan cewa da azahar zasu je bicci.tun da wuri Daddy yayi kari suka fita office shi da Faruq ko ganin Little be tsaya yi ba saboda kiran daya samu na gaggawa.kallon agogo Amma tayi a lokacin ne kuma agogo ta buga ƙarfe 8:00 daidai na safe,sallamar Iro Driver ta katse mata tunaninta ya matso ya rinsina a gabanta ya gaisheta cike da girmamawa ta ansa kafin yace"Hajiya Babban ,Ammin masu gida yau baxata je makaranta bane?".miƙewa tayi tace"nima yanzu xan shiga na dubota naga shirun yayi yawa ka jirani kaɗan".ta ƙare maganar tana nufan part ɗinta.kai tsaye ɗakin Halima ta tura.hangota tayi lulleɓe akan bed sallama tayi ta shiga ɗakin gefan bed din ta zauna tana yaye duvet ɗin da tayi rufa dashi,daga ita sai ƴar ƙaramar riga kallo ɗaya Amma tayi mata ta gane kwata kwata baccin baya yi mata daɗi ga wata wahalalliyar ajiyar zuciya da take saukewa lokaci zuwa lokaci,idonta ta mayar akan jijiyar kanta dake halbawa da ƙarfi gasu kuma sun fito ruɗu-ruɗu kamar wa'anda aka xana.hannunta na rawa takai akan dokin wuyanta da sauri ta janye jin yayi matuƙar zafi.bubbugata tayi tana cewa"Sadiya,Sadiya".wata irin miƙa Halima ta saki kafin lokaci ɗaya ta wara dara-daran idanuwanta wanda suka kaɗa suka zama jajir,brown ɗin ciki kuma ya juye ya koma baƙi-ƙirin.da ƙarfi Amma ta rufe idonta tana cewa"Hasbunallahu wani'imal wakil".sannan ta buɗe idonta cike da firgici tace"Sadiya meke damunki haka?,kinga idonki kuwa?,ko kinyi kuka ne?,amma kuma ko kuka baya riƙiɗar da idon ki haka,baki da lafiya ne?".a ruɗe Amma duka ke jero mata wanan tambayoyi,ɗago ido Halima tayi tana kallon Amma wanda a lokacin kuma tsab idonta ya koma fari ƙal da brown ɗinshi sai dai ƙallin hawaye dake kwance tab a idon ji tayi baƙinta yayi masifar nauyi ta kasa furta abunda ke ranta sai kawai ta tsinci kanta da cewa"Amma zazzaɓi nake kuma nasha Drugs".cike da al-ajabi Amma kebin idon Halima da kallo can dai tace"to Allah ya sawaƙe ki samu ki tashi ki watsa ruwa sai ko tea ne kishi sai ki ƙara shan maganin".da to kawai ta ansa kafin Amma ta fita taja mata ƙofar ɗakin.zumbur ta miƙe zaune,red haka eyes ball ɗinta yayi kamar wanda ya kawo danja kuma ya ɗauke glass cup ɗin data kallah ya faɗo daga table ya fashe a wurin.saurin runtse ido tayi kafin idonta ya dawo daidai sannan ta miƙe ta shiga toilet ji tayi jikinta wasai kamar ba ita ta tashi tana ciwan kai ba,wanka tayi tayo alwala dan har lokacin batayi sallan asuba ba,da ƙyar tayi sallan wacce babu natsuwa a cikinta sannan ta saka riga da siket na atamfa kasa murxa komai tayi sai turaren data fesa ta ɗaura ɗan kwalinta ta faɗa kan bed take wani baccin ya kuma shureta wanda take yinshi cike da mafarkai iri iri mararsa daɗi.
ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE.
VOTE
COMMENTS
SHARE
DAN GIRMAN ALLAH IDAN KIN KARANTA KIMUN SHARING
[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*_______________________
______________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
`Start``` ```patronizing``` ```ABU BILAL``` luvly ```fans
Ta hanyar wannan account din 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
FREE PAGES
PAGE 8
A hankali ta tura Gidan ta shiga babu kowa