Showing 3001 words to 6000 words out of 22311 words

Chapter 2 - ABU BILAL Document Complete Book (Maryam Isma'il Majidadi ).txt

sakashi mota ya rufe,har motar ta ɓace Bilal na ɗaga masa hannu.juyawa kawai yayi ya koma cikin gidan,kai tsaye bedroom ya shige ya faɗa saman bed tare da rumtse idanuwansa abubuwa da yawa suna dawo masa a kai.


ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE.
VOTE
COMMENTS
SHARE
[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇


```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```


*_______________________
______________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


FREE PAGES
PAGE 3


Ko kaɗan a daren Abu bilal kasa runtsawa yayi gaba ɗaya tunaninsa da komai nasa ya gama birkicewa,ganin abun bamai ƙarewa bane yasa ya tashi ya ɗauro alwala ya soma sallah,wannan yana ɗaya daga cikin nagartan halayansa duk tsanani be manta da sallah ba da kuma azumin alhamis da litinin ,haka zalika yaransa ko me sukeyi basa bari lokacin sallah ya wuce su.sai bayan yayi sallahn asuba ya samu bacci mai nauyi ya ɗauke shi akan sallayar.Tun sassafe Karima ta fito tsakar gidan ta soma share-share(Karima ƴar mama uwani ce).bayan ta gama ta tattaro wanke wanke tana wanke wa,kamar yarda ta saba duk kullun tana gamawa ta ɗaurawa Mama uwani girkin wainan da takeyi na siyarsa,a hankali gidan ya soma tara mutane masu siyan waina,hayaniyarsu ce ta tashi Abu bilal daga bacci wanda dama shi duk irin nauyin baccin da yakeyi motsi kaɗan kan iya tashin shi,wani siririn tsaki ya saki saboda ya tsani wannan sa'an ta Mama Uwani babu abunda suka rasa amma ko kaɗan ta kasa haƙura da wannan sana'ar,zura jallabiya yayi ya fito fuskarnan murtuke sai ɗacin rai yakeyi saurin duƙar da kai Karima tayi ganin irin mugun kallon da yake jefarta dashi,da sauri ta miƙe tayi baya,ji kakeyi gidan yayi tsit gaba ɗaya masu siyan wainan sunyi shiru a tunaninsu yabar gidan tun da sukaga su Jagwado basa ƙofar gida.wiƙi wiƙi da ido Datti yayi sana baya baya yana faman boye rigar dake jikinshi dan rigar Abu bilal ɗince an mashi shanya jiya ya ɗauke yace"Allah ya soni dama Uwani tace in ɗauka in gwada muga ko zaiyi mun kyau,banni dai ban taɓa satar maka kaya ba,ah tau Allah na tuba me akayi akayi wani kayan Sude can bare shi Sude ɗin".wani irin mugun kallo Abu bilal ya jefesa dashi kafin ya halbar da ƙatuwar robar da Karima ta gama zuba ruwa ciki,tuni su Jagwado suka shigo a guje suka kora masu siyan waina,ƙafa yasa ya halbar da ƙullun wainan.da sauri Mama uwani ta miƙe tace"Amma Dattiya kaji tsoron Allah ni nasan kama ɗauki kayanshi bare nace kasa ko xai maka kyau?".ganin da gaske Abu Bilal ƴan ɓannar yake ji sai ɓarin kaya yake yi yasa ta dauke roban kuɗinta tayi ɗaki a guje tana danna kuba.Karime dake rakuɓe ya dakawa tsawar da yasa ta soma sakin ƙara da ƙarfin gaske tace"Yaya Aliyu na tuba wallahi bazan sake fita nayi dare ba".wani kyakyawan mari ya sakar mata wanda yayi sanadiyar dauke jinta da ganinta na mintoci kafin da ƙyar ta fizgo baki da niyar yin ihu ,suman tsaye tayi lokacin da Rambo(karen Abu bilal)yayo kanta yana sinsinanta,a guje Jagwado yazo ya shiga tsakaninsu ya riƙe Rambo yace"Allah ya huci zuciyar mai gida,hakan bazata sake faruwa ba insha Allahu".da kausashiyar murya ya kalleta yace"kin san sauran ai".ya wuce ɗaki yana hararar Dattiya dake laɓe bakin kofa yana niyar sakin fitsari a wando.yana shiga ɗakin towel ya ɗauka ya wuce toilet yin wanka.minti 40 yayi ya gama shiryawa tsab cikin ƙananan kaya kamar kullun yau kam harda p-cap ya murza a kansa sai tashin masifar ƙamshi yakeyi duka kayan jikinsa dark blue ne dama Abu bilal ba daga baya ba wurin saka takalmi sau ciki,sosai ya fito ɗan gaye dashi yana kuma ɗaukar hankali.jin ƙamshin turarensa ya fara tunkaro waje yasa Karima yin saurin ɗauraye robar dake hannunta tayi saurin lafewa bayan kitchen tana raba idanu,wani irin taji lokacin da taga ya fito,ƙura masa ido tayi kamar zata zazzago idanuwanta.tsaye yayi bakin ɗakinshi babu kowa a tsakar gidan kuma ta gyara ko ina tsab.ƙwafa yayi yace"zan kwakwale idanuwanki masu kama dana mayu".da sauri Karima tayi saurin yin ƙasa da kanta tana jin kamar zuciyarta zata fasa ƙirjinta ta fito dan masifar tsoro,tasan ko be ganta ba yana gane idanuwa a kansa,kai tsaye waje ya fita in da ya iske yaransa a wurin miƙewa sukayi suna musabaha dashi kafin ya zauna kan kujera tare dayin ɗaya kan ɗaya ya kuma lumshe idanuwansa.Aguje Halima ta fito tana saka Ahlari a jakar dake rataye a kafaɗanta saurin riƙeta Amma tayi tace"Little ae baki makara ba bare kuma kiyi mani wayau ki fita baki karya ba".wani irin kwaɓe fuska tayi kamar zata saki kuka tace "wallahi Amma basan karin nan nake ba,ki barni dan Allah".zaro ido Hajiya Mama tayi tace"haba Sadiya babbar budurwa Tahfeez fa zakije ina amfanin fita baki ci abinci ba,yanzu tau bara na haɗa maki a lunch box".kyawawan idanuwanta ta lumshe kafin ta waresu tace"to Mama".cike da tsananin soyayyah Faruq ya kalleta yace"ƴan mata yau ni zan ajiyeki a school gaskiya".raurau tayi da ido kafin ta zagaya da sauri wurin Daddy ta saƙalo hannuwanta akan wuyanshi ta kwantar da kanta a kafaɗanshi cikin turo baki tace"Daddyna ka gaya masa ni nafi son zuwa Tahfeez a ƙafa,ƙwaɗayin ladan nake yi".murmushi Daddy yayi ya shafo kan ƴar tasa yace"dandai kince lada Ammina amma ko ni basan fitanki a ƙafa nake yi ba,kinsan yanzu duniyan ta lalace".juya idanuwa tayi kamar mai tunanin wani abu can tace"to Daddy kuyi mani addu'a zanje lafiya na dawo lafiya da yardar Allah".murmushi Hajiya Mama tayi tace"insha Allah kuwa,zoki wuce kada kiyi latti kinji".karɓar box ɗin tayi cike da ladabi ta dan durƙusa tace"na gode Mamana"kafin ta wuce tace"sai anjimanku kafin in dawo yau ayimun abun daɗi".ta fita tana kwashe hijabinta sama tana gyara riƙon box ɗinta.sake baki Amma tayi tace"naga ranar da Sadiya zata girma,kwatakwata yarinyar can bata da wayau sai shirme,kuji yarda ta fita tana yaye hijabi,duk ta wani sakalce a gari".murmushi Daddy yayi yace"ni dai a barmun Ammina tayi abunda take so,komai lokaci ne insha Allah zata daina data ƙara girma".cikin natsuwa take tafiya tana kallon littafin dake hannunta tana gyara haddanta,hankalinta kwance tana tafiya harta ƙaraso ƙofar gidan su Khadija,a daidai soron gidan ta samu Khadija tsaye da alamu fitowarta kenan itama da shiga irin ta Sadiya,washe baki Halima tayi tace"to ki fito muje dan ni nan ba tsayawa zanyi ba".murmushi Khadija tayi tace"a lallai yau dan an fito da wuri ba ae dole kice haka,ni wuce muje".a haka suka jero suna tafiya.yauma Halima ce side din da su Abu bilal suke zaune.ganin unguwar ƙwalam ba kowa yasa Khadija zaro ido shaf ta manta da yaune lahadin ƙarshen wata kuma yaune yaran Abu bilal ke gyara unguwa kuma babu wanda ya isa ya fito bare ya biyo ta hanyan.tsayawa sukayi da sauri ganin su Jagwado sun tsaya a gabansu,ras ras haka gaban Khadija ya bada sauti yayin da Halima kam ko a jikinta dan tsab ta gane Jagwado shine wanda ya watsa mata ruwan kwata a jiki.littafin dake hannunta ta rufe ta kwashe Hijab dinta ta saka littafin a jakka,cikin rawar baki Khadija tace"dan Allah kuyi haƙuri wallahi na manta shiyasa na janyota muka biyo ta nan hanyar"gaba ɗayansu juyowa sukayi suna ƙarewa Halima kallo wanda ko kaɗan bata san me sukeyi ba gaba ɗaya ta zuba kyawawan idanuwan ta ƙure Abu bilal da ido ko kiftawa bata yi.idanuwansa a lumshe kamar ko yaushe cikin kausasshiyar murya yace"bar kallona"ko kaɗan taƙi dainawa saima lumshe ido da tayi lokacin da raji daddaɗar sautin muryarsa ta sauka a dodon kunnenta.wata uwar tsawa Jagwado ya daka mata wacce tasa ta juyo da azabar ƙarfi cikin hassala itama tace"dallah malam kabar mun tsawa tun da kai ba uban.."kasa ƙarasa maganar tayi ganin Abu bilal tsaye a gabanta yana jefarta da mugun fusataccen kallo.har ƙasa Khadija ta duƙa tace"Abu bilal dan girman Allah kayi haƙuri baƙuwace anan,insha Allah ba zata sake kallonka ba ko yiwa yaranka rashin kunya"cikin sauri Khadija ta janyo Hijab ɗin Halima tace"ki basu haƙuri".sakin baki Halima tayi kafin tace"tabɗi,wallahi bazan bashi ba,ko ba shine ba jiya ya watsa mun ruwan kwa.."saurin saka hannu tayi ta rufe bakinta ta kuma fashe da kuka saboda ɗallin da Abu bilal yayi mata a baki fuska ɗaure yace"uwar rashin kunya".ƙasa tayi da kai tana rusa ihu tare da bubbuga ƙafafuwanta tanayin baya baya tana cewa"Allah sai na gayawa Daddy,dama kaima mugune irin wancan"ta ƙare maganar tana nuna Jagwado da hannu.wani uban haushi ne ya turnuƙe zuciyar Abu bilal cikin cool voice yace"bara na maki duka sai ki kawo kaka ba Daddy ba".wani irin zaro ido tayi zuciyarta na bugawa da ƙarfi ta yarda box din hannunta ta fasa wata gigitacciyar ƙara wanda sai da Abu bilal ya rufe kunnuwansa ya kuma rumtse ido da ƙarfi,sannan Halima ta sheƙa a guje har tana ture shi.ƙwafa yayi yana kallon gudun da takeyi wanda taƙi biyu xaiyi ya kamata ya juyo yacewa Khadija"bar nan".har ƙyarmar jiki takeyi ta miƙe zata bar wurin a tsawace Jagwado yace"your box".kwashe box ɗin tayi itama ta runtuma a guje tana godewa Allah daya sa basu faɗa tarkon Abu bilal ba.a hanya ta samu Sadiya,tana ganinta ta ƙalƙale da dariya harda riƙe ciki .wani uban harara Khadija ta jefa mata tace"kici gaba tabbas wata rana bazaki dara ba in dai akan Abu bilal ne,dan baki san waye shi ba shiyasa sakarcinki yake sawa kike neman cutar da rayuwarki a banza,ina mai tabbatar maki kuma Mugun da kika kirashi tabbas zai maki aikin mugunta".wani irin lumshe ido Halima tayi tace"wow nice name Abu bilal"sai kuma ta saki ƙayataccen murmushi.tsaki Khadija taja ta wuce warta cikin islamiyya har lokacin gabanta be daina dakan ukku ukku ba.


ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE.
VOTE
COMMENTS
SHARE
[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇


```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```


*_______________________
______________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


FREE PAGES
PAGE 7




```Start``` ```patronizing``` ```ABU BILAL``` luvly ```fans


Ta hanyar wannan account din 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.


Lumshe ido Halimatu tayi kamar mai bacci sai kuma ta ware idanuwanta akan fuskar Khadija tace"ni bance maki am in luv with him ba,just dai i want to be with him that's all".Dafe kai Khadija tayi tace"lallai kam kice tashin hankali na dunfaromu kuwa,wannan mutumin kina tunani yana da feelings akan wani abu wai soyayyah?,to bari kiji Abu bilal besan meye tausayi ko soyayyah ba,a duk duniyar nan ina ga yaronsa da yayarsa kawai yake tausayi yake kuma ɗagawa,ina tunanin idan kika fahimci waye Abu bilal kece mace ta farko da zaki fara nisanta kanki dashi".wani irin faɗuwa gaban Halimatu yayi sai kawai ta share tace"ashema yana da feelings tunda har yana iya aure ya haifi yaro".ƙwafa Khadija tayi tace"ina dai faɗa maki idan ma son shi kika fara to kiyi gaggawan cirewa dan a duniya babu wanda ya tsana sama da mutun yace yana son shi".fari da ido Halima tayi tace"what ever".suna a haka Faruq yayi ƙwanƙwasa ƙofan jin tace"yes come in "yasa yace"Faruq ne".dariya khadija tayi tace"eh Yaya ka shigo".tura ƙofan ɗakin yayi ya shiga bakinsa da sallama kai tsaye gaban Sadiya ya duƙa yace"Ammina sannu,how is your body"ƙasa tayi da kanta tace"Alhmdllh".kallonta yayi kafin yace"ina kike jin pain ".lumshe ido tayi tace"no where,dama fever ne".gyaɗa kai yayi kafin ya miƙa mata Drugs ɗin hannunshi yace"kisha yanzu and at the night kuma".a hankali ta furta thank u.murmushi yayi kafin ya juyo yace"Khadija ya gida da Ummi?".sakin baki tayi tana dariya tace"haba Yaya Faruq ni da ka manta ko ina existing ma a room ɗin nan,saboda ƴar rigima ba lafiya".murmushi ya saki yace"ba haka bane,kinsan dai Ammin tawa uwar raki ce ae".murmushin itama tayi tace"haka ne kam,su Ummi suna lafiya,ai kwana biyu baka leƙa ba".shafa kansa yayi zuwa gemunsa yace"when i'm less busy zan shigo na gaishe ta"daga haka ya miƙe ya fita yana janyo masu ƙofan.nannauyar ajiyar zuciya Khadija ta sauke tace"ke ga namiji daya ansa sunansa namiji mai nagarta amma ki wani maƙalewa wani".cikin rashin fahimtar in da zancen nata ya dosa tace"who's that".harara Khadija ta zabga mata tace "zaki cemun baki san Yaya Faruq yana sonki bane?".a bazata tambayar yazo mata ta wani ƙwalalo ido tace"haba mana is just your imagination he's my Yaya fa,mu duka Amma ne fa ta rainemu".Dariya zancenta yaso bawa Khadija tace"ai naga dukanku ita ta haifesu kuma babu aure a tsakaninku"."kinga Khadija i can never imagine dating Yaya Faruq,please let's call up the chapter".Halima ta faɗa.
Shiru Khadija tayi bata kuma cewa komai ba ta miƙe tsaye tana cewa"malama tashi ki raka ni".miƙewa Halima tayi tana janyo long hijab ɗinta mai hannu ta saka tace "muje".a jere suka fito a babban parlo suka samu Daddy da Amma suna kallon news.Har ƙasa Khadija ta duƙa ta gaishe da Daddy shima cikin sakin fuska ya ansa yana saka mata albarka 10k ya bata yace ta gaishe da su Ummi.langwaɓar da kai Halima tayi tace"let me escort her".jinjina kai Daddy yayi yace"a kula da hanya".da to suka ansa kafin tayiwa Amma sallama ta fito,a jere suka fita daga gidan.har sun soma tafiya daidai ƙofar gidan Aunty Aysha Halima taci burki tare da kallon Khadija tace"ki rakani nan mana,2days ban shiga wurin Aunty Aysha ba".kallonta Khadija tayi tace"amma baxamu daɗe ba gaskiya bana son magriba yamun a hanya".ta ƙare maganar suna tura ƙofan gate ɗin gidan.da gate man suka fara gaisawa da yake yasan Halima ya barsu suka wuce ciki,babu lefi shima gidan yana da girma ,suka tura main entarance na main parlo bakinsu ɗauke da sallama.tsaye yake ya juya baya yana zuba ruwa a mug,sanye yake da ƙananan kaya kamar kullun yayi sagging trouser ɗinsa har kana iya hango farin boxer ɗin dake jikinsa,duk yarda sukeyin sallaman hakan besa ya juyo ba sai da Aunty Aysha ta fito daga kitchen tace"kai dai Aliyu naga ranar da zaka bar wannan mishkilancin naka ace sallama ma anayi ba zaka iya buɗe baki ka ansa ba".juyowa yayi yana kafeta da ido bece komai ba nan idonsa ya safka akan Halima da yake janyo hijab ɗinta daga jikin door,murmushi Aunty Aysha ta saki tace"haba Halima ai nayi fushi gaskiya,yaushe rabonki da gidan nan saboda Allah,ko jiya kina tahfeez na leƙa na gaishe dasu Amma".da fara'arta itama ta ƙaraso cikin parlon tana cewa"wallahi Aunty school ne baya bari".ta ƙarashe maganan suna zama karab idanuwanta suka sarƙe cikin na Abu bilal wanda yake kai Mug ɗin ruwan sanyi bakinsa wata uwar harara ya afka mata ,da sauri tayi ƙasa da kanta tana cewa"Aunty ina su Nahnah?".juyawa tayi tace "ae kinsan da yake mun ƙara yawa gidan na tabbata Bilal da Khalifa sun janye mun ƴar auta suna baya ana hawa keke".Sai lokacin Khadija taga Abu bilal zaro ido tayi tana addu'ar Allah yasa kada Halima ta ganshi.miƙewa Aunty Aysha tayi tace"bara a kawo maku ruwa".ruwa da lemu ta ɗauro a ƙaramin tray ta kawo masu tare dasu Bilal dake biye da ita.da gudu Bilal yazo ya faɗa jikin Halima yace"la Aunty ni kika zo nema a gidan mu?,kinga Abbana taso muje ki gaishe shi".ya ƙare maganar yana jan hannun Halima dake kallon fuskarshi da murmushi sai a lokacin ne taga tsantsar kamar Bilal da Abu Bilal."ka santa ne"Aunty Aysha ta tambaya.Nahnah dake lafe jikin Halima tace"eh Momy ita ce Auntyn da yake baki labari ta tahfeez".juyowa tayi tana kallon Abu Bilal tace"Aliyu yauga Auntyn Bilal ka gani sai ku gaisa".wani irin haɗe fuska yayi yana kallon Aunty Aysha data tsare shi da ido.cikin ƙasa da kai Halima tace"ina wuni".tana kuma maimaita sunan Aliyu a ranta.yana tafiya yace"lafiya" .yayi hanyar waje wani irin haushi ya turnuƙe zuciyar Khadija kawai tace"to zamu wuce"."da wuri haka kuma".Aunty Aysha ta faɗa.miƙewa Halima tayi tace"dama rakiya zan mata na biyo,insha Allah zan shigo ai".itama Aunty Ayshan miƙewa tayi tana jan hannun Bilal daya maƙalewa Halima tana cewa"to Allah ya kaimu,sai kin shigo".da ƙyar ta janye Bilal daga wurinta sannan suka fita Khadija sai masifa takeyi dan khadija badai faɗa ba.banza Halima ta mata har suka rabu kafin ta dawo gida zuciyarta cike da tambayoyi iri iri.Ɓangaren Hajiya Mama kam duƙe suke a gaban wani ƙaton mutumi baƙi ƙirin dashi sai mazurai yake yi cikin murya marar daɗin saurara yace"me kike so ayiwa yarinyar?".nisawa Hajiya Mama tayi tace"boka ina so a turawa yarinyar baƙaƙen aljannun da zasu hanata zama lafiya,wanda zasu rikita mata rayuwa wani lokacin ma ayi tunanin mayyah ce ko kuma ta haukace,so nakeyi idan suka tashi a kamota can dawa,kuma duk wanda ya kusanceta da sunan so ko tausayinta to ya mutu ya zama kuma ace ita ake tunanin tana kisan".jinjina kai Bokan yayi yace" zaki biya million 1,aikinki an gama da batun shi yanzu haka suna niyyar shiga jikinta,sai dai duk ƙarshen wata xaki basu jinin baƙaƙen dabbobi wannan dalilin ne zaisa duk tsanani su kasance tare da ita".wata irin murmushi ya suɓucewa Hajiya Mama tana jin damuwanta yazo ƙarshe ta buɗe jakkarta ta kwaso kuɗin ta jibgesu gaban Bokan sannan ta tashi suka bar kan dutsen ita da Hajiya talatu.daidai Halima zata shiga gida taji wani irin masifar sanyi na ratsa duka sassan jikinta ga tsigar jikinta data mimmiƙe gaba ɗaya,lokaci ɗaya kuma taji ta daina jin sanyi .gate ɗin gidansu ta buɗe ta shige.


ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
VOTE
COMMETS
SHARE
DAN ALLAH IDAN KIN KARANTA KIMUN SHARING..
[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇


```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```


*_______________________
______________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
FREE PAGES
PAGE 4


Zagaye ɗaki Hajiya mama takeyi tana faman ture ɗaurin ɗankwalin da tayi na shadda,ciza hannu tayi tana zancen zuci da kuma tunanin maganarsu ta jiya tana kuma zancen zuci,lokaci ɗaya tayi na'am da abunda zuciyarta ta saƙa mata,waya ta ɗakko tare da danna wa lambar aminiyarta kira bugu ɗaya ta ɗaga bakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login