Showing 18001 words to 21000 words out of 22311 words
Chapter 7 - ABU BILAL Document Complete Book (Maryam Isma'il Majidadi ).txt
ƙasar waje,bamu so rabuwa da juna ba saboda zamana da Ahalin Hajiya Maryam yana mun daɗi mun zama tamkar wanda muka fito ciki ɗaya,gadan gadan tafiya ta kama saboda shaƙuwar dake tsakanin su Khaleem da Ahmad yasa suka roƙemu damu bar masu Ahmad har Allah ya dawo damu lafiya,tabbas na firgita dajin wannan magana ganin shi kaɗai Allah ya bani amma Hajiya maryam tafi ƙarfin komai a wurina a nan take na mallaka mata Ahmad kuma muka tafi muka bar mata shi,sai dai ta waya mu gaisa.shekarar Ahmad huɗu su Khaleem kuma 6 daga lokacin ne kuma mumunar ƙaddara ta fara faɗawa a wannan family mai cike da soyayyar juna da aminci da zaman lafiya,kuma har lokacin bamu dawo ba ko ziyara bamu taɓa zuwa ba,Hajiya Maryam ta kirani tana gayamun cewa Alhaji Ahmad zaiyi aure,ni kaina na shiga ruɗu amma haka na daure ban nuna mata ba ina bata baki da haƙuri wata biyu aka yi auren Alhaji Ahmad da wata wai Hajiya Jamila wanda harta gama zamanta a gidan ban taɓa ganin ko da hoton ta ba.a lokacin kuma komai ya daidaita tsakanin Rumana da Aliyu yana matuƙar son matarsa yana kuma riritata baya son abunda zai taɓa mashi ita.bayan wata biyar da Auren Hajiya Jamila komai ya canza a gidan,Alhaji Ahmad bayajin maganar kowa sai tata,kuma sai abunda tayi a gidan be isa ya tsallaka koda kara ta gindaya ba,kuma ta shiga ta fita ta raba shi da Aliyu sai da yakai ko da kallo Alhaji Ahmad baya son ganin Aliyu bare kuma ya raɓesa,hakan ya dasa muguwar gaba tsakanin Aliyu da Hajiya Jamila wanda ita hassada da ƙyashi yasa bata son Aliyu kullun burinta bai wuce taga ya faɗi ba,haka naita bawa Hajiya Maryam Hakuri dan bana so tabar gidan uban ƴaƴanta,a kuma lokacin ne Rumana ta kamu da wani matsanan cin ciwo ta koma kamar mahaukaciya ta zaune,sai dai a kullun idan ciwon ya tashi a ɗaɗɗaureta da sarƙa a kuma rufeta a ɗaki,dan xataita yagar fatar jikinta ne tana kuma neman illata kanta,wannan al-amari ba karamin girgiza wannan ahalin yayi ba,anyi magani anyi har an gaji,wanan abun kuma shine farkon fara tarwatsa rayuwar Aliyu duk yabi ya susuce ya lallace baya bacci be da kwanciyar hankali saboda ciwan Rumana,har lokacin shekararsu goma sha biyu da aure amma ko ɓari Rumana bata taɓa yi ba,kuma duk ciwanta besa Aliyu ya rabu da ita ba ko kuma ya ƙara aure,haka yake xama ya bata abinci tana t dukansa tana yakushinsa amma be fasa kula da ita ba,gaba ɗaya ma ya tattara yabar zuwa aiki sai kula da Rumana.a wannan lokacin ne kuma Hajiya jamila da Aliyu sukayi wani gagarumin faɗa saboda ya kamata tana zuba magani a abincin Rumana,ya shiga tashin hankali wanda yakai har ya mari Hajiya Jamila ita kuma tayi amfani da wannn daman tayi masa alƙawarin zai biya marin daya mata ko ta wacce hanya".shiru Amma tayi tana share hawayen daya ƙi tsayawa a idonta tana kallon Halima tace"a cikin wannan yanayin kuma na haifeki kikaci sunan Ammin Faruq wanda itama a lokacin ne ta rasu riƙon Faruq ya dawo hannuna aka dangin mahaifinsa suka kai mana shi har Amerika,a wannan yanayin ne Aliyu ya fita dasu Ahmad ,a yarda yace ya barsu a mota kafin ya dawo ya samu babu Khaleel ,khaleem da kuma Ahmad,yayi ruɗewa iya ruɗewa in da a wurin suka bashi tabbacin wata mata ce tazo ta tafi da yaran,yacce suka kwatanta masa surarta lokaci ɗaya zuciyarsa tayi na'am da Hajiya Jamila ce,gida ya dawo yana tuhumarta ita kuma tace bata san anyi ba don duk ranar be fita ba,a kuma cikin ɗakinsa aka tsinci kayan su Khaleem ɗuk jini da wasu irin abubuwa da suke bada tabbacin Aliyu ya faɗa kungiyar asiri ne,sosai hankalin kowa ya tashi da ƙyar Abba ya kira Daddy yake gaya mana mutuwar su Khaleem da kuma Ahmad,ya girgiza sosai amma sai ya ɓoyemun yaƙi sanar da ni case ɗin dake faruwa kuma ya hanani yin waya da kowa.sam Aliyu ya birkice yaƙi ansar laifinsa ya kuma ɗauki alƙawarin ɗaukar mataki akan Hajiya Jamila ,a wannan lokacin kuma wani tashin hankalin ya doso kai in da Abba da kanshi ya kama Hajiya Jamila tana ihu a ɗaki ga Aliyu kwance kwance a ɗakin akan gadonta yayin da take fitar da jini tana ihun Aliyu yayi mata faɗe".wani irin miƙewa Halima tayi da sauri tace"be yiwuwa,wannan ba gaskiya bane,Yaya Aliyu bazai taɓa aikata haka ba ".ta ƙare maganar hawaye na zubowa a idonta.girgiza kai Amma tayi ta kasa tsayar da hawayenta tace"Ayyah Halima ki daina saurin yanke hukunci haka,mahaifiyar data haifesa ita da kanta ta bada shedan Aliyu yayiwa Hajiya Jamila fyaɗe".daskarewa a wurin Halima tayi ga tsananin tsoro daya bayyana ƙarara a idonta da ƙyar ta haɗiyi wayu mai masifar ɗaci cikin rawan murya tace"yaya za'ayi uwar data duƙa ta haifi ɗanta wanda tafi kowa yarda da ɗanta ta bada wannan ƙazamar shaidan ga ɗan data haifa da cikinta,anya Mamy itace mahaifiyar Yaya Sudais kuwa?".
ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAMYAWAN ƘARSHE
2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 16
Kallonta kawai Amma tayi tace"wannan kuma ko waye ya kallah yasan gaskiya,kuma da bata tabbatar da hakan ba da bata bada shaida ba".wasu hawayen ne suka kawo idon Halima ta kasa cewa komai kafin Amma taci gaba da cewa"a lokacin ne Abba ya kira Daddynki yana sanar masa da baƙin ganin da yayi"haka Daddynki ya kwasa ya tafi gidan amma ba abunda ya canza dan Abba yayi matuƙar fushi a nan ne yake faɗin ya rabu da Aliyu har abada kuma ya ciresa daga cikin ƴaƴansa ko da mutuwa yayi kada Aliyu yazo kan gawarsa kuma duk abunda yasan ya masa toya tattaro ya dawo masa dashi".ko kaɗan Daddy be nuna beji daɗi ba dan shima ya yarda ɗari bisa ɗari Aliyu ya aikata hakan saboda lura da shaidu da kuma yarda Hajiya Maryam ta bada shaida da kanta akan ɗanta,shima cikin fushi ya yayiwa Aliyu faɗa da wulaƙanci sosai ya kuma yi ala wadai da irin halin da Aliyu ya canza kuma a nan ne ya yarda Aliyu ya shiga ƙungiyar Asiri,shima yace bashi ba Aliyu kuma bazai yafe masa ran ɗansa daya salwantar ba,a takaice dai haka suka kori Aliyu da matarsa Rumana wacce take cikin halin ciwo,Allah kadai yasan yarda suka rayu bayan shekaru kuma akaji labarin Rumana ta samu ciki kuma a lokacin Aliyu yana zaune da Dattiya tsohon mai gadin da Hajiya Jamila tasa aka kora ,yanzu kuma bazan iya ce maki ga in da Dattiya yake ba,a wata majiyar wai Hajiya Jamila ta tari Aliyu ta faɗa masa lallai yayi hankali da kansa wannan duk yana daga cikin sakamakon marin daya yi mata ne kuma ya jira abunda zai faru na gaba,bayan ta dawo ne kuma Abba ya saketa duk wani asirin data masa ya warware,.a lokacin Daddynki yaso ya ganta yaji meya haɗa su amma sam Abba ya hana yace ba amfani kawai ya barta shi bazai iya ci gaba da zama da ita bane,wannan takaicin sakin yasa ranar da Rumana ta haihu ko tashi daga in da take bata yi ba Hajiya Jamila ta shigo ta kasheta har lahira ga yaro jariri kuma,a nan ne kuma Aliyu ya kamu da ciwon zuciya mai tsanani saboda tsaban rikicewan da yayi ,daga wannan lokacin kuma babu wanda ya kuma jin labarin Hajiya Jamila har gobe kam,amma kuma Aliyu yana da ƙudirun nemanta a ko wanne yanayi ko da hakan zai zama abu na ƙarshe da zai aikata a rayuwarsa,mu kuma tun daga wannan lokacin alaƙar mu taja baya zan iya ce maki rabon dana ga wani cikinsu harna manta,Ammi kinji iya abunda na sani a rayuwar Aliyu,sanin gaskiyar wannan al-amari kuma sai Allah sai kuma wanda yayi fatanmu dai Allah ya bayyana gaskiya kowa ya gane matsayarsa".kuka sosai Halima ta fashe dashi gaba ɗaya ta gama rikicewa,idanuwanta sunyi jajir tace"Amma har raina ban yarda Yaya Aliyu zai iya haka ba,duk iya halinsa na fahimci yana da kirki ga addini sai dai ban musa shaye-shayen da yake ba shima wannan kuma na ɗauka duk ƙunci ne yasa ya faɗa wannan harkar amma ki yarda yana da zuciya mai kyau".murmushin da yafi kuka ciwo Amma tayi tace"nasan waye Aliyu ,kuma Aliyu a da babban malami ne yana da matuƙar ilimi na boko dana addini,fatanmu dai muyita yi masa addu'a har Allah ya bayyanar da gaskiya".kasa cewa komai Halima tayi ta miƙe ta fito tana share hawayen dake kuma zubo mata.tsayawa Faruq yayi yana ɓata fuska yana kallon yarda idonta ya canza launi alamun taci kuka sosai,langwaɓar da kai yayi yace"meyasa kike son wahalar da kanki haka?,dan Allah kiji tausayinmu Ammina,ki sani kece farin cikinmu a gidan nan,kuma kinsan yawan ɓacin ranki abunda zai iya janyowa".murmushin ƙarfin hali tayi tana cewa"na daina Yayana".murmushinsa mai kyau yayi kafin ya jata suka zauna yana mata fira har yaga taɗan sake tana dariya kafin ya tafi ya barta..
Ɗuƙe take ta rasa abunda ke mata daɗi yau kimanin kwana biyar kenan bata saka Abu bilal a ido ba bare kuma taji daga garesa kusan kullun sai ta shiga gidan Aunty Aysha amma bata ganinsa kuma kota tambayeta itama sai tace kwana biyu bata ganshi ba.miƙewa tayi tana jan Hijab ɗinta ta leƙo parlo ganin babu kowa yasa ta fita da sauri a gate kam babu wanda ya tareta ta fice daga gidan,gidan Aunty Aysha ta shiga da sauri ta ƙarasa ciki tana kallon motar Abu bilal a parking lot ,har tuntuɓe takeyi wurin saurin ta shiga,cak ta tsaya tana ƙare masa kallo wanda shi ɗinma ita yake kallo kamar yau ya soma ganinta,gani tayi yayi rama sosai da alama yana cikin damuwa.ƙasa tayi da kanta,sai lokacin shima ɗauke idonsa daga kallonta ya wuce kan chair ya zauna beko kulata ba,cikin parlon ta dawo daidai gabansa ta tsaya cikin rawar murya hawaye na kawowa idonta tace"Yaya ina ka tafi na daina ganinka?".banxa yayi mata ko kallonta beyi ba bare kuma tasa ran zai bata ansa,zama tayi a gabansa tana tanƙwashe ƙafafunta tace"dan Allah ka gaya mun Yaya".wani irin ɗaure fuska yayi kamar an saukar masa da mutuwa yace"i'm not your Yaya".wani irin haushi ya kama Khadija da shigowanta parlon kenan ta kalli Halima tace"malama tashi muje gida dallah"ko kallonta Halima batayi ba saima saurin miƙewa da tayi ganin Abu bilal yabi hanyar fita cikin ɗaga sauti tace"i know who you are".cak ya tsaya tare da lumshe idanuwansa da suka fara sauya launi ya juyo yana kallon Halima yace"then what?,everything you hear about me just believe it babu wanda bani nayi ba,duka ba zargi bane sai kuma me kike so ki sani bayan wannan?".wani irin kuka mai cin rai Halima ta saki da matuƙar ƙarfi ya runtse idonsa danji yayi sautin kukanta har cikin ƙwaƙwawalwar kansa ya rasa wanne irin yanayi ne yake ji a kanta a lokutan nan,cikin muryar kuka tace"wallahi bazan taɓa yarda ba,tabbas akwai wani abu a ƙasa ba zaka taɓa aikata irin haka ba".wani tsaki yaja afin ya tureta daga gabansa ya wuce abunsa.a nan wurin ta duƙe tana sakin wani kukan da gudu Bilal ya iso wurinta ya duƙa tare da tallabar fuskarta yace"Aunty,ki daina kukan bana so,ki daina zance wa Abba ya daina maki faɗa ina sanki kinji,duk wanda nake so Abbana yana sanshi ".sosai ta riƙe Bilal a jikinta amma ta kasa cewa komai bare ta tsaida hawayen idonta,hannu yasa yana goge mata hawayen fuskarta yana nuna mata alamun tayi dariya,murmushi ta ƙirƙira tana ƙoƙarin miƙewa.Khadija kam ta cika tayi faful a wurin ƙiris take jira ta fashe,jan hannun Halima tayi fuuu suka fice Bilal na binsu da kallo.ta baya Abu bilal ya hango fitarsu wani iska mai zafi ya furzar ya kuma duƙar da kansa yana sauraron bugun zuciyarsa.har cikin bedroom Khadija taja Halima kafin ta sakar mata hannu tace"watau bakiji kashedin Daddy ba kenan?,Halima me kika gani ga Ɗan daba da kika maƙale masa har kina zubar da girmanki da hawayenki a gabansa?,meye ya shiga kanki ne?".wani kallo take bin Khadija dashi kafin tace"kada ki sake ce masa Ɗan daba,nace bana so,ko daban yake yi aike be maki ba".sakin baki Khadija tayi tana kallonta kafin tace"koma me zakice karesa da kikeyi be isa yasa a daina masa wannan kallon ba tunda ya aikata,kuma ki sani bazan taɓa baki goyon bayan kiso Sudais ba har abada".tsuka Halima taja kafin tace"dama ban roƙa ba"ta ƙare maganar tana buɗe ƙofa ta fice daga ɗakin bin bayanta Khadija tayi a daidai ƙofa suka ci karo da Lamis,wani irin faɗuwa gaban Halima yayi ta koma da baya tanayin ƙasa da kai.
ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 17
Dedicated this page to Balkis Adam Bello
Khadija kam da wani irin kallo tabi Lamis mai wuyar fassaruwa,murmushi yayi yana cewa"sarkin ɓoyo yau kin fito kenan".cewar Lamis,kasa cewa komai Halima tayi kafin Khadija tace"ai kwanan nan Yaya sauyi kala-kala ma ka ganshi".harara Halima ta bita dashi kafin tayi ƙasa da kai tace"ina yini Yaya Lamis",da lafiya lau ya ansa yace"muje kuga wani abu".be jira cewarsu ba yayi gaba suka bisa baya a chair ya zauna yana ɗauko wani ƙaramin box ya miƙawa Halima sannan ya ciro agogo mai kyau ya miƙawa Khadija yace"ga naki ƙawarmu,bansan zamu haɗu ba aeda kema an maki naki na daban"murmushi kawai tayi tace"na gode kwarai Yaya hakanma ae yayi".baki Halima ta turo kafin tace"thanks".kallonta kawai yayi kafin ya janye kallonsa daga gareta.miƙewa Khadija tayi tace"muje ki rakani tau".murguɗa baki Halima tayi yace"wallahi baza ni ba".sakin baki Khadija tayi,murmushi kawai Lamis yayi yace"muje na ajiyeki ƙawarmu".dariya tayi tana cewa"kinga na samu rakiyan da yafi naki".gwalo kawai tayi mata ta wuce ɗakinta,a haka suka fita a motar Lamis,tunda suka tafi babu mai cewa komai can Lamis yayi breaking silent ɗin da yace"Khadijatau ya kike da ƙawar taki?",ɗan murmushi tayi tace"Yaya ina lafiya,Halima sarkin rigima ma tana lafiya".kansa ya shafa yana cewa"bari ta jiki nikan in ce bansan anyi bama".dariyan itama tayi tana faɗin "tuba nake" a haka har suka ƙarasa gidan su Khadija,10k ya bata amma da ƙyar ya samu ta ƙarɓa sannan ya juya ya tafi abunsa....shiru yake yana shafa kansa yayinda idanuwansa suke lumshe a hankali ya ware su wanda harsun canza launi ,iska ya furzar yana cewa"wai me yake damuna yanzu?",ina so na ganta".ya faɗa yana miƙewa tsaye key ɗin motarsa ya ɗauka yana fita yayinda zuciyarsa ke masifar azazzalarta da masifan son Halima tabbas yasan son Halima ya shammaceshi yayi masa mugun kamu shi kansa bazai iya faɗin taya hakan ya faru ba,burinsa kawai ya kasance da ita,duk wani motsin da zaiyi sai ta faɗo masa a rai,ɗaura kansa yayi akan sitiyari cikin sanyin murya yace"sonki yana azabtar da ni Halimana".tuno rigimarta yayi lokaci ɗaya ya saki ƙayataccen murmushi ya kuma dannawa motan shi key ya nufi unguwar su Halima.a waje yayi parking daidai ƙofar gidan Aunty Aysha kafin ya fito zai shiga gidan kamar kullun sanye yake da wando jeans ash colour sai t-shirt black colour mai dogon hannu sosai yayi matuƙar kyau sai fitar da sihirtaccen ƙamshi yake yi ga tsadaddiyan agogon gucci ɗaure a tsintsiyar hannunsa,cover's black ne a ƙafarsa sai sheƙi sukeyi ,a hankali ya tura ƙofar gidan Aunty Aysha ya shiga sai da yaje ƙofan parlo sannan yayi sallama da gudu Khalifa ya rugo ya rungumesa yana cewa"oyoyo Uncle".ɗaga yaron yayi sama yana shafa kansa kafin yace"ina Bilal?".ɗan shiru yayi kafin yace"yaje gano aunty Halima ,kuma Umma bata sani ba yace kada na gaya".lumshe idanuwansa yayi lokaci ɗaya yaji zuciyarasa ta buga da ƙarfi ga wani irin tsinkewan zuciya lokaci ɗaya,dafe kansa yayi da yaji ya matuƙar sara mashi yayi saurin sauke Khalifa ya juya zai fito da sauri,riƙesa Aunty Ayaha tayi tace"Sudais lafiya kuwa?" shiru yayi kafin yace"Bilal,zan kira sa".be jira cewarta ba ya fice da sauri,hijab ta saka itama ta bi bayansa dan kwata kwata bata yarda da yanayinsa ba tasan dole akwai abunda ke damunsa.zaune Halima take akan bene sai jujjuya kai takeyi tana jin ansa kuwwar ihun da kuma maganar da ake gaya mata,Bilal kam yana ta tsaye gabanta yana riƙe da hannunta yana jijigawa yana cewa"Aunty ki buɗe idonki don Allah,nifa ke nazo gani ko Umma bata sani ba"ya karashe maganar kamar zaiyi kuka.a hankali ta soma buɗe dara-daran idanuwanta da suka kaɗa sukayi jajir kamar gauta lokaci ɗaya suka juye,zumbur ta miƙe tana rufe kunnanta da ƙarfi ga wani irin rikitaccen ihun data saki,raɗau haka Abu bilal yaji dodon kunnansa ya ɗaukar masa ihun Halima wani irin bugawa ƙirjinsa ya kuma yi ya tura gate ɗin gidan da sauri ya shigo ,Daddy,Amma da fitowarsu kenan dan jin ihun Halima yasa Daddy saurin ɗaga hannu yana cewa"ka sani hukuma ce zata fita da kai a gidan nan Aliyu,tabbas yau sai kayi dana sanin da baka taɓa yi ba a rayuwanka".ko kaɗan Abu bilal be gane abunda Daddy yake faɗa burinsa kawai yakai ga in da su Halima suke dan ya gama gane meke faruwa da wata irin murya da azabar ƙarfi ya furta"Bilal,Bilal".juyowa Bilal yayi yana ɗagawa Abu bilal hannu yana cewa"Abbana,ina sanka sosai,da fatan kazo man da Chocolate,Aunty Halima ma zata sha tunda ina santa zan sammata ko Abu bilal?".runtse ido da ƙarfi Abu bilal yayi yana cewa"no,no Hale..ee...ma,kada kimun haka".a kuma daidai lokacin ne Halima ta saki ihu tana saka hannu ta bangazo Bilal daga kan bene da azabar ƙarfi.da wani irin zafin nama Abu bilal ya ture Daddy dake gabansa yana cewa"a'a".ya ruga wajen a guje,sai dai kash kafin ya ƙarasa Bilal ya kai ƙasa idanuwansa a buɗe yana kallon Abu bilal ga hannunsa ya ɗaya yana miƙawa mahaifin nasa,shima Abu bilal ɗin hannu ya miƙa da niyar kamo na Bilal amma hannun Bilal ya riga nasa zuwa ƙasa,akan gwaiwowinsa ya faɗa yana kallon yarda jini ke malala daga cikin kan Bilal wanda ya fashe,daskarewa yayi a wurin wata irin kyarma na kwace masa