Showing 15001 words to 18000 words out of 22311 words

Chapter 6 - ABU BILAL Document Complete Book (Maryam Isma'il Majidadi ).txt

jini wasu kuma wani irin bakin ruwa me yauƙi,kamar a film haka yake ganin giccin mutane a wurin ƙwafa yayi ya kuma ambaton sunan Allah yace"Haleemah"shiru ba'a ansa ba sai ɓaɓɓakewa da mugun dariyan da akayi,sama ya ɗaga kansa yana hango Halima acan saman ƙaton bishiyan kuka,duk tayi wani hiri hiri ta gama sauyawa da halitta,addu'a ya riƙayi yana tofawa a saman kamar an jefota haka ta faɗo kafin ta iso ƙasa yayi saurin saka hannuwansa ya tareta ta faɗo a ƙirjinsa,wani irin bangajesa tayi ta tsaya tsaye akan manyan ƴan yatsunta na ƙafa tana wani irin gurnani.kallon ikon Allah yakeyi kafin ya fizgota ya matse mata babban yatsanta na hannun dama ,cikin wani irin sauti tace"ka sakeni,ka sakeni nace".ta wani juyo tana ƙwalalo masa muggan idanuwanta da suka fito kamar ƙwan fitila."ku fita daga jikinta,idan ba haka ba kuma zan ƙonaku yanzun nan,kuma ina gargaɗinku da kada ku cutar da wani itama ku barta ta huta haka".wata irin dariya Halima ta saki tana cewa"bazamu iya barin jikinta ba ".murza hannun nata yayi da ƙarfi aiko ta saki ƙara tana tafiya luuu zata faɗa akan ƙayoyin dake wurin.saurin tarbota yayi kafin ya rungumota kamar baby ya fito da ita daga cikin kangon.wani irin ajiyar zuciya Faruq da Lamis suka sauke a tare suna kuma mayar da kallonsu ga jikinta da yayi duƙu-duƙu gashin kanta duk a baje gaba ɗaya ta sauya launi.shikam Abu bilal ko kallonsu beyi ba ya fara tafiya suka rufa masa baya.har cikin gidan ya shiga da ita a parlo ya tsaya yana shimfiɗar da ita akan carpet.wata uwar ƙara Hajiya Mama ta saki tana cewa"Daddy ku fito ku gani,Daddy Amma".kusan a tare Amma da Daddy suka fito , da gudu Hajiya Mama tayi ɗaki dan a matuƙar tsorace take,da sauri Abu bilal ya ɗago yana bin bayan Hajiya Mama da kallo saboda jin muryarta a kunnensa,sai dai be samu ganin fuskanta ba.Aysha dake rakuɓe tana kuka ita ta taso da sauri Mamanta ma na take mata baya.ƙarasowa cikin parlon Daddy yayi yana maida kallonsa ga Abu bilal wanda ya ɗago daga duƙen da yake,kallo sukeyiwa juna ido cikin ido kafin cikin rawar murya Daddy yace"Aliyu kaine?,meya kawo ka gidana?".cikin kausasshiyar murya yana haɗa yatsunsa suna ƙara yace"get out of my hause wannan karon ya zama karo na ƙarshe da ƙafarka zata kuma shigowa gidana balle harka ɗauki kazamin hannunka ka ɗaurashi akan ƴata".da sauri Amma ta shiga gaban Daddy tace"haba Abubakar kai baka ganin irin taimakon da yayi mana?,ko last time shine wanda ya dawo da ita gida data faɗi a school,kome yayi maka ya kamata kayi haƙuri".wani tsaki Daddy yaja cikin ɗaga murya yace"wai ke baki gane shi bane?,it's Aliyu yaron Alhaji Ahmad ,why can't you look at his face very well Amina ".juyowa Amma tayi tsoro ya nuna ƙarara a fuskarta tabbas ranar firgici da tsoro ya hanata kallon fuskar Aliyu da kyau haka yauma sai da Daddy ya nusar da ita kafin ta ganeshi rabon data saka shi ido tun tana da tsohon cikin Halima 17years kenan.bakinta na rawa tace"Sudais".ƙasa Sudais yayi da kai don tun ranar daya zo gidan na farko ya gane Amma sai dai ganin bata ganeshi ba yasa ya share kawai,kuma yasan Aunty Aysha bata san Amma ba sakamakon ba'a gidansu ta tashi ba ko da tayi aure a london take zaune sai tsakanin nan ne ta dawo Nigeria da zama.cikin kausasshiyar murya Daddy yace"dama ashe shine wanda ya taɓa zuwa mun gida kuma baki gayamun ba,Aliyu idan ka kuma shigo mun gida hukuma ce zata rabani da kai and i mean it wallahi".cikin dakiya Aliyu yace"to Allah ya bada iko Daddy,babu wani abun da zai firgita ni tunda har a baya na rayu" .cikin muryar kuka Amma tace"please you people should stop that,komai ya faru ya faru ne a ta dalilin kuskure,kuma kai Daddy kasan an cuci Aliyu da yawa ko don taimakon da yakewa ƴarka bazaisa ku tausaya masa ba"."karki sake min irin wannan maganan,mashayin ,ɗan daban,wanda ya keta haƙƙin Allah,ya aikata saɓo mafi muni wanda ko a zamanin dabbibu banga ana haka ba".runtse ido Aliyu yayi da ƙarfi kafin ya waresu harsun soma canza launi dan tsananin ɓacin rai kasa furta komai yayi ya juya zai fita,ji yayi an riƙo hannunsa,tsaye ya tsaya cak ba tare daya juyo ba yaji sautin muryarta tana cewa"Yaya Sudais" wata uwar tsawa Daddy ya daka mata wanda tunda take a rayuwarta be taɓa mata tsawa irin haka ba.jikinta na ƙyarma tayi sauri ta lafe bayan Lamis dake kusa da ita."kada na kuma ganin kin danganta kanki da Aliyu,har abada babu ke babu shi,idan kuma kika saɓa zakiga irin abunda zai faru da ni da ke a gidan nan Halima".girgiza kai Abu bilal yayi ransa a matuƙar ɓace ya fice daga parlon dan har ji yakeyi bashi gani.hawayen dake zubowa idonta ta goge tana maimaita sunan da Daddy ya kirata dashi wanda tasan a iya rayuwarta xata iya ƙirga sau nawa Daddy ya kirata da Halima.kama hannunta Faruq yayi kai tsaye ya wuce da ita bedroom ɗinta yana lallashinta akan kada ta ɓata ranta baya so kanta yayi ciwo.binsu Amma tayi a ɗakin kafin ta kama Halima zuwa toilet ita da kanta tanwanke mata kai ta wanke ƴarta tas ganin babu wani kuzarin kirki a jikinta,kallonta takeyi yarda tayi masifar rama duk ta zabge a zaman kwana biyu kawai,doguwan riga marar nauyi red ta bata ta saka kafin ta gyara mata kanta.Faruq ne yayi sallama ya shigo ɗakin da mug ɗin tea mai kauri ya zauna yana bata tea ɗin a baki,ganin haka Amma ta wuce part ɗinta tana tuna rayuwar baya data wuce.sai da ta shanye tea ɗin kafin ya bata farfesun ƴan ciki da yaji kayan yaji sai da ya tabbatar ta ƙoshi kafin ya taimaka mata ta kwanta yayi mata addu'a ya shafa mata sannan ya rufeta da duvet ya fita.ikon Allah ne kawai ya mayar da Abu bilal gida ko kaɗan be kula karaɗin Dattiya ba ya faɗa ɗaki ya saka key yana ji zuciyarsa kamar ta fasa ƙirjinsa ta fito saboda tsananin xafin da take masa,naushi ya kaiwa bango ya soma ɓarar da duk abunda yazo gabansa yana fitar da wani nishi marar daɗin ji.a guje Karima tazo ƙofar ɗakin tana bugawa da ƙarfi cikin muryar kuka take cewa"Yaya dan Allah kayi haƙuri ka buɗe,yaya kada ka illata kanka,dan Allah ka buɗe".ta ƙare maganar tana jijjiga door ɗin ɗakin.ganin bashi da niyar buɗewa yasa da gudu tayi waje babu ko hijab a jikinta cikin sa'a kam taci karo da Jagwado wanda zuwansa kenan cikin kuka tace"Abu bilal ne,Abu bilal ne".be jira jin me zata ce ba ya tureta yayi cikin gidan da gudu.itama ta rufa masa baya ganin ɗakin a kulle yasa ya fito da key's ɗinsa ya buɗe ɗakin dan shi kaɗai keda key ɗin ɗakin Abu bilal.a daidai lokacin ne kuma Abu bilal ya dafe kansa da ƙarfi yana ganin ɗakin na jujjuyawa dashi ya tafi luuu zai faɗi,da matuƙar ƙarfi Karima tayi tsalle cikin ɗakin ya faɗo a jikinta suka faɗi tare .lokacin da Jagwado ya ɗagoshi a sume yake .


ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE.


2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 12
Kamar ana mintsininta haka takeji a baccin a matuƙar razane ta farka daga bacin babu kowa a parlon dama bacci ne yaɗan ɗauketa kai tsaye hanyar waje tayi,babu kowa a farfajiyar alamun duka maza masu aikin gidan sun wuce masallaci don yin sallar la'asar gate ta ɓuɗe tana ci gaba da tafiya.fitowarsa kenan daga gidan Aunty Aysha sauri yakeyi ya tafi masallaci dan shigowarsa unguwar kenan da ido ya bita ganin ko shoe babu a ƙafarta balle kuma hijab wanda tunda ya santa be taɓa ganinta ko da veil a waje ba sai hijab saɓanin rana daya da dare ya ganta ta fito a haka.taɓe baki yayi duk da yana da yaƙinin ba ita bace ba yayi wucewarsa masallaci gudun kada ya rasa jam'i.minti 10 da faruwan hakan ya fito daga masallaci gaya mutane tsaye a ƙofar gidan su Halima,shafa kai Faruq yayi yace"tabbas da kowa ya tafi sallah ta fito,abun tashin hankalin ma ba'asan ina ta nufa ba".ta gefansu ya raɓa ya wuce ko kallonsu beyi ba.da gudu Khalifa ya shiga gida yana cewa"Ummi,Ummi Yaya Halima ta ɓata ba'a ganta ba".dungure masa kai tayi tace"liar,ka dai san ba kyau ƙarya"."wallahi Ummi da gaske nake ga Uncle Faruq can a waje ma".kallonta ta mayar ga Abu bilal dake shigowa gidan hankalinsa kwance tace"Aliyu wai da gaske ne".tsura mata idanuwa yayi yace"what"."wai Halima ta ɓace"ta ƙarashe maganar tana ajiye bucket ɗin sock's na yara data wanke.taɓe baki yayi yace"i think so".kafin ya kuma magana ta zare hijab ɗinta dake ajiye a parlo data gama sallah tayi waje hankalinta a matuƙar tashe dasu Faruq ta fara cin karo cikin tashin hankali tace"Faruq anga Haliman?,ina taje? yanzu khalifa ke gayamun".kasa magana yayi sai dai Lamis yace"a'a of to now ba wanda yasan in da take ma"."innalillahi wa'inna ilaihir raju'un "ta faɗa tana shihewa gidansu Halima a tsaitsaye ta samu su Amma wanda tsantsar tashin hankli ya gama bayyana a jikin Amma.nisawa Imam yayi yace"tabbas ba zata wuce cikin wani wurin ba a kusa da gida ,iskan jikinta ne suka fitar da ita ,kada ku damu insha Allah data dawo daidai zata dawo gida".zufa Daddy ya goge yana cewa"hasbunallahu wani'imal wakeel,Allah ka tsare mun ƴata a duk in da take"gaba ɗaya ya gama rikicewa duk addu'ar data zo bakinsa ita kawai yake yi kafin ya taso ya dawo gida a ƙofar gida ya zauna shi da su Faruq suna jiran tsammani.Junaid matashin yaro kuma yaron maƙwabcinsu yazo da sauri gaban Daddy ya duƙa yace"Daddy ga Halima a kangon can".be ƙarasa rufe baki ba dukansu suka miƙe tsaye suna hango tsohon kangon da yake nuna masu wanda tsawon shekaru babu wanda yake gigin zuwa wurin duk shuko kin kuka ne wurin da abubuwa iri iri.kai tsaye wurin suka nufa kowa da abunda yake ayyanawa a ranshi.Halima kam kwance take a cikin kangon sai juye-juye takeyi kamar macijiya gaba ɗaya duk ta jiwa kanta ciwo ga azabar ciwo dake cinta.Oga sam ne ke zagayeta yana yayyafa mata baƙin ruwa mai masifar wari.jin ruwan takeyi tamkar zubar wuta a jikinta gaba ɗaya ta banban ƙare ta gama sauya launi duka jikinta a juye yake yayin da idanuwanta suka koma kamar garwashin wuta .tsaitsaye sukayi ƙofar kangon jin irin ihun dake fitowa daga ciki da sauri Junaid,Lamis da Faruq suka kutsa kai cikin kangon Junaid ne ya fara ƙarasawa ya ɗagota carab idonsu ya haɗu ido cikin ido,bismillah Lamis yayi ya ɗagata tsaye yana janyota waje tana tirjewa babu abunda take kallo sai fuskar Junaid hannu tasa da ƙarfi ta ingije Junaid yayi baya xai faɗi Faruq yayi saurin taro shi"yace what's that?,saboda ya taimaketa tana mace kun kawota wurin ƙazantar nan?".ko kula Faruq bata yi ba suna fitowa waje ta langwaɓe alamar ta sume,akan idon Abu bilal Lamis ya ɗakkota .wani irin tsuka yaja yana buga ƙofa da ƙarfi,saurin kallonsa Aunty Aysha tayi wanda isowarta ƙofar kenan cikin zafin zuciya yace"waye shi daya ɗaukota?".riƙe baki tayi tana ƙare masa kallo tsantsar kishi ta gani ƙarara a idonsa sharewa tayi tace"kana da damuwa da wannan ne,ina kana ganinta ta wuce ae,yanzu ake faɗa wai ka ganta,shine baka tsayar da ita ba?".taɓe baki yayi yace"did i send her?".wani haushi ne ya kama zuciyar Aunty Aysha kamar ta fashe da ihu haka ta ture Abu bilal ta wuce ciki dan tun ɗazu Abban Khalifa ya dawo.da Hajiya Mama Lamis ya fara cin karo.wani irin kwalalo ido tayi tace"Lamis ka haukace ne?"daburburcewa tayi ta kasa komai tana tunanin abunda zaije ya dawo.a saman carpet ya shimfiɗar da Halima ya soma cicire mata ƙayoyin da gashinta ya kwaso,sosai sukayiwa Junaid godiya kafin ya tafi gida.kusan awa ɗaya tana wanan baccin kafin ta miƙe tana faɗin Junaid da iya ƙarfinta riƙeta sosai Faruq yayi ya soma tofa mata addu'o'i kafin ta fara natsuwa.kamar saukar aradu haka suke yin mutuwar Junaid a cikin unguwar.kafin sallar magrib tuni ko ina ya ɗauka cewar Junaid ya mutu.tsurawa Hannuwanta ido tayi tana tuna mafarkin da tayi wai tana shaƙare Junaid wani wahalallan kuka ta saki tana rungume Amma da ƙarfi ,itama Amman riƙeta tayi cikin muryar kuka Halima tace"Amamana na kashe shi,wallahi ni na kashe shi,me yasa ya taimake ni?,me yasa yazo kusa da ni?".ta ƙare maganar kuka na ƙwace mata,saurin rife mata baki Amma tayi tace"kada na ƙara jin irin wannan,bake kika kashe shi ba kiyi masa addu'a dama lokacinsa ne yayi kinji".kuuuu haka cikin Hajiya Mama ya juya ga zufa dake karyo mata fizgar hannun Lamis tayi ta wuce bedroom ɗinta dashi tare da danna key cikin hassala tace"shin wai ni ko dai Amina(Amma) ta haifa mun kai ne,ita Haliman ƙanwar uwarka ce nace?,ka duba halin da ake ciki kowa ya gagara ɗaukota sai kai sallamamme,na rasa ina hankalinka da tunaninka suka tafi Lamis,kai baka ganin duk wanda yaje da niyar taimaka mata sai ta kashe shi?".tsurawa Hajiya Mama ido yayi cike da alamomin tambaya ya ɗaure da ƙyar yace"in dai zan mutu akan taimakon Halima a shirye nake na bada rayuwata ta,kuma ba ita ta kashe Junaid ba kwanansa ne kawai suka ƙare,idan bamu taimake ta ba waye xai taimaketa a wannan halin".hannu Hajiya Mama ta ɗaura saman kai ta sauke tace"yauni maga abunda ya isheni ni jamila,to bari kaji lai kaɗai na mallaka ban kuma shirya rasaka ba".murmushin takaici yayi yace"in dai baki cutar da Ɗan kowa ba toki kwantar da hankalinki babu abunda xai samu Muhammad Lamis"."ban gane wannan tambayar ba Lamis?,kana xargine akan condition ɗin Halima".shafo gemonsa yayi yace"a'a wai magana nayi kawai".rasa abun cewa tayi kafin ta nuna masa hanya tace"maza ka tafi gida wallahi idan na safko parlo na sameka ranka zaiyi matuƙar ɓaci Muhammad,zan saɓa maka ".shiru yayi kafin yace"to sai anjima",ya fice daga gidan.Faruq kam yana parlon Amma yana ta kallon Halima dake xaune taci kuka harta gaji har muryarta ta fara disashewa i zuwa yanzu kam wani mugun tsoron wani ya kusance tako ya taimake takeyi ta gama firgita da duk abunda ta gani a mafarki ta to tabbas tana buɗe ido dashi zata fara cin karo,hawaye ne suka kawo idonta ga zuciyarta tana bugawa da ƙarfi,hannu tasa tana janye eye glasses ɗinta tana share hawayen idonta."kiyi hakuri,bana son kukan nan"shine abunda Faruq ya faɗa.girgiza kai tayi tace"kowa in yi haƙuri yake faɗa mun,tabbas baku san abunda nakeji a zuciyata bane,baku san me yake faruwa bane shiyasa har kuke da bakin bani hakuri"."duk tsanani yana tare da sauki Ammina kiyi hakuri komai xaizo da sauki,kuma hakuri shi yake kawo nasara".


ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 15
Nisawa Amma tayi tace"Sudais ya kasance yaro mafi soyuwa a wurin mahaifansa watau Alhaji Ahmad da Hajiya Maryam yaransu huɗu Aysha itace babba sai Aliyu sai kuma ƙannensa ƴan biyu watau Khaleel da Khaleem,Alhaji Ahmad kuwa ya kasance Aminin Mahaifinki tun yarinta suke tare kuma shima babban ɗan kasuwa,yaso Aliyu ya biyosa shima yayi kasuwanci sai dai Aliyu tunda ya tafi waje karatun Architecture ya daɗe bai dawo ba a kuma can ne ya samu aiki,yayin da ni ban taɓa ganin ƴarsu Aysha ba tunda aka haifeta Hajiya Maryam ta bawa ƙanwarta marigayiya Hajiya Aysha ita,a can ta girma a can kuma tayi aure,Aliyu ya taso cikin gata da soyayyah da kulawa sai dai ya kasance mishkiline na gaske wanda ko iyayensa sai sunyi da gaske yake iya buɗa baki yayi magana,wannan son da suke masa yasa suka lallaɓashi ya dawo gida nan Nageria in da aka buɗe masa Company ɗinsa yana harkar zane zane,a kuma lokacin ne Hajiya Maryam ta haifi yaranta ƴan biyu maza watau Khaleel da Khaleem yara masu matuƙar kama da juna kuma ya zamana duk duniya babu abunda Aliyu yake so sama da Khaleel da Khaleem duk in da zaije yana tare dasu kowa ya sanshi yasan twins ɗinsa rainonsu gaba ɗaya shi yayi".nisawa Amma tayi ta kurɓi ruwa dake kusa da ita sannan taci gaba da cewa"a kuma daidai wannan lokacin ne Hajiya Maryam ta buƙaci da Aliyu yayi aure,hankalinsa yayi matuƙar tashi saboda shi bashi ma kula ƴan mata bare kuma yace ga wacce yake so,kasancewar kusancin iyayenku maza yasa ni da Hajiya Maryam muka zama aminai komai a tare mukeyi sai dai ni matsalar dake damuna a lokacin shine da na samu ciki sai ya ɓare sai bayan su Khaleem sunyi wayau aka samu cikin dana samu ya tsaya har yakai matakin haihuwa,ina dab da zan haihu kuma Hajiya Maryam tazo mun da shawaran tana so taga Aliyu yayi aure tunda ita Aysha ta daɗe dayin aure,sai dai uwar riƙonta ta rasu kuma tabar ƴarta mace mai suna RUMANA rumana kyakyawa ce ajin farko son kowa ƙin wanda ya rasa gata da haƙuri da kuma kawaici hakan yasa na bawa Hajiya Maryam shawarar mexai hana su haɗa auren Rumana da Aliyu,sosai tayi na'am da shawarar tace kuma xata turomun Aliyu tunda taga ɗan gida na ne sai na masa bayani,hakan akayi tunda na masa magana bai musa ba haka ya yarda akayi auren duk da ba Son Rumana yakeyi ba a lokacin.bayan aurensu da Sati ɗaya kuma na haifi ɗana namiji lafiyayye yaci suna Ahmad watau sunan Abban Aliyu kenan".zaro ido Halima tayi tana kallon Amma kafin cikin rawar murya tace"shine wanda naga pic ɗinsa ɗakin Daddy na tambaya waye aka cemun na ajiye kawai?".gyaɗa mata kai Amma tayi tace"eh shine,kuma yayanki uwa ɗaya uba ɗaya"."Amma meyasa kuka ɓoye mun?,kuma yana ina?".girgixa kai Amma tayi tana ƙoƙarin mayar da hawayenta tace"saboda faɗan hakan yana tada wani tsohon ciwo da kuma mumunan tabo ga dukkan ahalin guda biyu".shiru Halima tayi amma ta kasa fahimtar me Amma ke nufi da hakan.ci gaba Amma tayi da cewa"bayan na gama wankan Ahmad mahaifinki ya samu wata kwangila da zaiyi shekaru a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login