Showing 171001 words to 174000 words out of 177664 words

Chapter 58 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete by Garkuwa .txt

06 Dec 2024

7790

tagama watsawa Ishaq wani matsiyacin kallo.


Murmushi Saifuddeen yayi tare da sanya hannu ya shafo yawun bakinta dake bisa kan yan yatsunshi harshensa yasanya yaɗan lashi saliva ɗin, lumshe idanunsa yayi tare da sauƙe wani irin ajiyar zuciya, tunowa da magananta nacewa da tayi da tasha yawunsa gwara tasha tom-tom, yasanyashi sake sakin wani shak'iyin murmushi, cikin zuciyarsa yace.
"Am so sorry Zaleeha wannan al'ƙawarina ne insha Allah saina shayar dake duk wani abun dazai fito daga jikina, dazaran na aureki ba iya yawuna ba ma kaɗai harta spe... ɗinama saina shayardake."


Dubansa yakai ga Ishaq wanda ke zaune shima murmushi ne ɗauke akan fuskarsa, don kuwa shima zuwa yanzu abubuwan Zaleeha da ƙawayenta sun soma bashi dariya, wani zubin kuwa idan Zaleeha tafaɗi wata maganar tsantsar yarintarta kawae yake gani.
Zuciyarsu wasai batare da wani ƙunci ba haka suka baro gidan su Zaleehan.


Zaleeha kuwa koda suka bar BQ ɗin kai tsaye ɓangaren Mama suka nufa, afalon Mama Balkeesu ta zauna yayinda Zaleeha kuwa ta wuce ɗakinta kai tsaye ranta na bala'in tafasa, tarasa maiyasa bayajin haushi ko ciwon duk wata magana da zata faɗa masa.
Sosai al'amuransa ke bata takaici, duk da cewa shiɗin kurmane yakamata ace ae yana da zafin zuciya irin na kurame amma wani abu da ta lura dashi shine, shi kamar dutse yake ko bugunsa zakayi to sai kashirya kakuma saka duka ƙarfinka.
Hmmm Zaleeha taka a sannu zuciyar irinsu Saifuddeen bata tankwaruwa in ta hatsalo kada ki k'ureshi, wani sashi na zuciyarta ke rad'a mata a hatsale tace zaiko ci ƙaniyarsa a wurina. Ta fad'i kamar tana mgna da wani.


Balkeesuce ta kalli Mama wanda take zaune akan kujera 1 sitter fuskarnan tata aɗaure take tamau, ɗigon fara'a babu akanta.
Cikin iyayi da kisisina haɗi da zallan munafurci irin na Balkeesu ta gyara zama, tare da fuskantar Mama murya kamar wacce zatayi kuka tace.
"Yanzu Mama haka zamu zubawa Zaleeha idanu takasance kullum cikin kuka? amatsayina na ƙawarta sam bazanso cutuwarta ba, dan Allah Mama kiƙara sa baki akan maganar Saifuddeen ɗinnan wallahi Zaleeha bata sonshi, hasali ma babu wanda Zaleeha ta tsana sama dashi, Zaleeha kyakkyawace son kowa ƙin wanda yarasa, ni aganina tauye haƙƙine idan har aka haɗata zama da nakasashshe, wanda bashi da banbanci da dutse."


Cikin tsananin baƙin ciki da takaici Mama ta watsawa Balkeesu jajayen idanunta, duk yanda kowa a duniya yakai ga ƙin son auren Zaleeha da wannan musakin to abayanta yake, domin ko tunowa da batun auren tayi saitaji wani abu kamar jiri na ƙoƙarin kada ita.
Wani abu daya tsaya amaƙoshinta ta haɗiya, ranta adagule cikin cushewar murya tace.
"Da ace zanbuɗe miki zuciyata ki gani Balkeesu da tuni kinsha mamaki, duk yanda wani yakai ga tsanar auren Zaleeha da wannan banzan musakin ninafishi, duk da cewa ban taɓa ganinsa ba amma tsanar danayi mishi babu wani wanda na taɓa yiwa irinta!." Mama taƙare maganan cikin ƙunan zuciya.
Ɗan jim tayi tare dayin ƙwafa, abayyane tace.
"Badai dani suke wasan ba, Insha Allahu zasusha ruwan mamaki, in -dai-da-raina da lafiyata bazan taɓa bari ƴata Zaleeha dana haifa acikina ta auri wannan shashashan nakasashshen ba, bazan taɓa bari wannan banzan auren da suke shirin ƙullawa ya tabbata ba, Ni nan nayi al'ƙawari ƴata Zaleeha ba zata taɓa auren MUSAKI ba!!.".
Murya akausashe Mama taƙare maganan domin kuwa ji take kamar zatayi aman wuta don bala'i, alwashi ne bazata taɓa bari Zaleeha ta auri Matsiyacin gurgu kuma mayataccen kurma ba, tayi al'ƙawarin saita tashi hankalin kowa dake gidan, sannan kuma sai takau da duk wani zaman lafiya dake cikin gidan matuƙar akaƙi bin zaɓinta.
Cikin jin daɗin kalaman Mama Balkeesu ta saki wani ɓoyayyen killer smile, tabbas so take Mama ta jajirce wajen ganin Zaleeha bata auri Nagartaccen Namiji kamar Saifuddeen ba, tasan cewa Saifuddeen nakasashshene, amma sam ita bata hango nakasartasa, don kuwa babu wata nakasa da ta nuna ajikinsa, hasalima ita bata taɓa ganin wani nagartaccen Namiji kamar Saifuddeen ɗin ba, tahango abubuwa da yawa dangane da Saifuddeen ɗin wanda maza da yawa basu dashi, irin Saifuddeen sune mazan da suka fi ƙaranci aduniya, haka kuma irin sa mata da yawa ke fata da burin samu matsayin abokin rayuwa. Kullum haushinta d'aya kada Zaleeha ta rigata aure, kuma kada ta fita samun miji na nunawa sa'a shiyasa ta dage ta raba Manager da son Zaleeha tana ta son cusa kanta gareshi, dan Raveel dai ya nuna mata baya tare da ita, A wani sashi na ranta kuwa dadi takeji dan in zaliha ta auri nakasasshe ta samu abin nunawa mutane tawayarsa.
Miƙewa tsaye tayi yayinda ta nufi ɗakin Zaleeha.


Zaleeha kuwa tana shiga cikin ɗakinta, kai tsaye kan lallausan gadonta ta faɗa, cikin tsananin baƙin ciki da takaici haɗi da tsanar Saifuddeen tashiga rera kuka, tayaya zai fuskanci cewa ta tsanesa? mai yasa bazai gane irin tarin tsanar da tayi masa ba ya rabu da ita? meyasa shi baida zuciya? ta tsanesa tsana irin ta wuce misali, sam batason duk wani abu da ya shafesa, ganin fuskarsa na sawa tanajin kamar takashe kanta, meyasa har yanzu kowa ya kasa fahimtar irin raɗaɗi da kuma zafin da takeji? meyasa kowa yakasa sanin zafin ƙiyayya irin wanda takeji, mutum ɗaya takeso aduniya shi ɗaya za kuma taci gaba da so, har iya ƙarshen rayuwarta, batajin zata so wani koda kuwa kwatan kwacin rabin yanda takeson wanda yakasance mai taimako agareta, abu ɗaya tasani shine, ko duka mutanen duniya zasu taru suyi mata kallon mahaukaciya akan son da takeyi masa to bazata taɓa fasawa ba, koda kowa zai yi mata kallon shashasha, tayarda zata amince za kuma ta jure matuƙar akan soyyayarsa ne, tariga tasa aranta cewa komai wahala komai daɗi, komai kusa komai nesa zata bada kai da ƙarfinta wajen zaman jiransa, sau dayawa zuciyarta na gaya mata cewa watarana zaizo gareta, ta kuma aminta da hakan, saboda haka tasa aranta cewa, har abada bazata taɓa daina so da ƙaunarsa ba.


Balkeesu ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, ganin Zaleeha kwance na kuka, yasanyata taɓe baki, cikin ranta tace.
"Bakiyi komai bama Zaleeha, sai alokacin da idanunki suka buɗe ki ka gane cewa kinrasa nagartaccen namiji kamarsa, daga wannan lokacin zakiyi kuka irin wanda ake ƙiransa da sunan kuka bawannan sharan fage ba, wanda ni kuwa dama hakan shine burina."
Afili kuwa ƙarasawa gaban gadon tayi tare da zama abaki bakin gadon, cikin son zuga tasanya hannu ta dafa kafaɗan Zaleeahan, cikin ƙoƙarin ɓoye manufarta tace.
"Kuka baya maganin damuwa Zaleeha, sam kuka bai kamaceki ba ba kuka yakamata ace kinyi ba."
Afusace Zaleeha ta tashi zaune, fuska caɓa-caɓa da hawaye tace.
"Bakuka yakamata nayi ba? dariya kenan kikeso nayi mai gado? okay nagane saboda ke bakisan zafin ƙiyayya dana soyayya ba ko shiyasa zakice haka, da ace kinsan yanda nakejin zafi a zuciyata wallahi da ke ce zaki fara cewa naƙara sautin kukana tayanda gaba ɗaya Nigeria zasu jiyoni bama iyaka Gombe kaɗai ba, Natsaneshi Mai gado, Natsaneshi, banason koda ganin fuskarsa, aurensa dai-dai yake da tarwatsewan zuciya da rayuwata gaba ɗaya, da ace na buɗi idona naganni matsayin matarsa gwara ace na wayi gari bana numfashi.!"


Wani irin ƙatuwar ajiyar zuciya Balkeesu ta sauƙe, tabbas haƙanta gaf yake da cimma ruwa, saidai kuma har yanzu bata hango irin zazzafar tsanar da takeson Zaleeha tayiwa Saifuddeen ba, haƙiƙa komai na Zaleeha na bayyanar da tsanar Saifuddeen saidai ita har yanzu akwai abun da bata gamsu dashi ba.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
"Bance kiyi dariya ba Zaleeha, ni ƙawarkice maison duk wani abun da kikeso, saboda haka burina shine ki samu wanda kikeso, kishare hawayenki Zaleeha, saikin cire tsoro haɗi da kunya kin fuskanci kowa sannanne zaki samu cikar burinki, saikin dage kin kuma ɗaga hankalin kowa dake gidannan, sannan zasu fuskanci cewa babu soyayyar Saifuddeen aranki."


Ɗago jajayen idanunta wanda suke cike da ƙwalla tayi ta kalli Balkeesu, murmushi Balkeesu tayi tare da dafa shoulder ɗinta, cikin son tarwatsa nutsuwar Zaleehan tace.
"Nasan kin fahimci abunda nake nufi, dole ne ki tashi tsaye wajen ganin kin samawa kanki ƴanci, wani irin kallo kike tunanin mutane zasuyi miki aduk sanda sukaji cewa da kyawunki da komai kin kashe ƙuruciyarki wajen auren nakasashshe? ki dubeki Zaleeha, kyau, ilimi, diri, hutu, wayewa, aji, sanin darajar kai, duk fa kin mallakesu, babu wani ɗa namiji da zaki gifta ta gaban idanunsa matuƙar ya amsa sunansa namiji ace baiji komai game da ke ba, sam bakiyi kama da matar nakasashshe ba, zama da nakasashshe kuwa agareki tamkar tarwatsa rayuwarki ne!."
Ɗan tsagaitawa da maganan tayi tare da miƙewa tsaye, duban Zaleeha tayi da kyau, tare da sakin wani ɗan guntun murmushi, ahankali tashiga takawa harta ƙarasa jikin ƙofar fita daga ɗakin, juyowa tayi still fake smile ne ɗauke akan fuskarta, cikin son tausasa zance tace. "Nabarki lafiya ƙawata, ina fata zakiyi tunani me kyau akan maganata, idan kuma kin amince nakasashshen kurma yazamanto ango agareki am fine, mudai always zamu tayaki murna." Tana kaiwa nan azancennata ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fice, tana sakin wani dariya mai ɗauke da tsananin mugunta.
Lumshe idanu Zaleeha tayi saiga wasu sabin hawaye shaaaa sun kwaranyo daga cikin idanunta, wani zafi-zafi ɗaci-ɗaci haka takeji acikin maƙoshinta, cikin ɗaya daga cikin trow pillows ɗin dake watse bisa kan gadon ta jawo ɗaya, tare dayin hugging ɗinsa a ƙirjinta, kanta ta jingina da saman gadon tare da sake sakin wani sabon kuka, sosai shawaran Balkeesu yasamu mazauni acikin zuciyarta, don ta ƙudurta aranta cewa daga yau babu wani wanda zai ƙara bacci cikin daɗin rai acikin gidan, saita ɗaga hankalin kowa, bazata nutsa ba kuwa harsai taga ta samu abunda takeso...


Ɓangaren su Saifuddeen kuwa daga gidan su Zaleeha kai tsaye wani babban Cafe dake cikin unguwar federal lowcost suka nufa, wanda ananne suka narka kuɗi don buga musu ƙawataccen katin auren nasu wanda yanzu kwana biyar ne kacal ya rage, koda sukaje tuni suka samu an gama kammala musu komai, nanfa suka amsa, daganan gidansu Ishaq suka wuce, domin kuwa musamman Ummu'n Ishaq taturowa Saifuddeen ɗin saƙon text message akan cewar tayi masa tuwon semovita miyar moringa (zogale) sanin cewa yana matuƙar son miyar, koda sukaje gidansu Ishaq ɗin nan sukaci abinci suka ƙoshi, domin kuwa harda wani irin daddaɗan coconut drinks da kuma zoɓo Ummun ta haɗa musu, anan gidansu Ishaq ɗin Ahmad da Salisu da Jabeer sukatarar dasu, suka karɓi kusan rabin katin, daga gidansu Ishaq ɗin kaitsaye Ahamd wajen ƴan uwa da abokan arziki ya nufa inda yadinga raba musu katin auren nan kowa yake cika da murna da kuma fatan al'khairi.
***


Ƙarfe 6 dai-dai jirgin Azman Air Land ya sauƙa ababban airport ɗin dake cikin garin Gombe, wato Gombe International Airport, mutanene da dama cike a airport ɗin, dagani kowa da wanda yazo tarba, can nesa kaɗan na hango wasu matasan samari wanda aƙalla zasu kai su 10 sunyi gungu guda, gabaki ɗayansu hankalinsu naga ƙofar fita daga cikin jirgin.
Sannu ahankali mutane keta sauƙowa daga cikin jirgin, shine wanda yayi kusan na ƙarshen fitowa.
Cikin isa, izzza, haɗi da zallan iskanci da kuma tsageranci, haka yake sauƙowa daga kan matattakalan jirgin, kallo ɗaya zakayi masa kafuskanci cewa riƙaƙƙen ɗan iskane irin wanda babu wanda ya isa sashi babu kuma wanda ya isa hanashi, ko daga nesa ka hangosa saiya baka tsoro balle kuma ka kai gayin face to face dashi, *Dalla* kenan, riƙaƙƙen ɗan iskan da ya riƙa a iskanci, sannan kuma sunansa ya buwayi ko ina na cikin gombe, babban tashin hankalin ko wacce ƴa mace shine wani ya ambato mata sunan Dalla, musamman ga waƴanda suka sansa, sam baya ragawa mace wajen yi mata Dalla-Dalla da virginity ɗinta.
Cikin yanayinsa dake nuna nutsewarsa acikin daba yaƙarasa sauƙowa daga kan matakalan jirgin.
Da wani irin ihu haɗi da shewa yaransa sukayo kansa, cikin tsananin jin daɗin ganinsa da kuma murnar samun lafiyansa, suka shiga yi masa ƙirari da yi masa take irin nasu, take kan Dalla ya ƙara huruwa har takai ha yanajin kansa kamar wani sarki, nan yasoma ɗaga kai yana hura hanci, cikin nuna isa da halinsa wanda sama da shekara ɗaya yakasa sanjawa ya dubi yaran nasa, hannayensa ya zura acikin aljihun wandonsa, tare da ɗage kansa sama, cikin murya da yanayin magana irin tasu ta riƙaƙƙun ƴan daba yace.
"Allah yayi dawowana yau, bayan nashafe sama da shekara ɗaya ina jinya a k'asar Jermany, Wallahi Na rantse da sarkin dake busan numfashi, babu wani mahaluƙi aduniya daya isa ya hanani yiwa yarinyar da a sanadinta na haɗu da lalurar da takaini.shafe sama da shekara ina jinyan kaina Dalla dalla, ni Dalla al'ƙawari naɗaukarwa kaina cewa duk inda tashiga tafita saina nemota, zan banƙarata kamar kaza, sannan zanyi mata dalla-dalla irin wanda ban taɓayiwa wata mace ba, zan keta mata haddi irin ketawar cin zarafi, sannan zanyi watsi da duk wani mutumcinta, wallahi saina yaga rigar budurcinta na tarwatsa shi tayanda bazata ƙara numfashi ba bare takai ga yin motsi, idan kuwa har hakan bata kasance ba Ni Dalla ban haifu acikin uwata da ubana ta hanyar sunna ba, sannan kuma al'ƙawarine akanta zan fara gwada lafiyar dana shafe tsawon lokuta ina nema!!!."


Ihu haɗi da kirari yaran nasa suka yi masa, haka suka cigaba da masa kirari suna ƙara fasa masa kai, shikuwa Dalla tuni kansa ya ƙara girma, ayanzu burinsa ɗayane a duniya shine ya damƙi tsinaniyar yarinyar nan da sanadinta ya fita daga sahun mazaje tsawon wasu lokuta, haka suka cika mota shida yaransa ƴan daba, kaitsaye babban gidan na Dalla wanda acanne yake hutawa idan yazo suka nufa, inda nan cikin unguwar shango estate gidan yake.

***
Ummi ce zaune akan makeken gadonta, yayinda gaba ɗaya hankalinta sam baya jikinta, sosai tayi nisa cikin tunani, zuwa yanzu kwata-kwata takasa jure rauni, damuwa, fargaba, haɗi da tsoron dake kwance cikin ranta, sam kwana biyunnan bata tare da nutsuwarta, wani irin tsoro haɗi da fargaba suke cika zuciyarta, har yakai ga ko bacci take fargaban baya barinta, sosai al'amarin auren na Saifuddeen ke mugun ɗaga mata hankali, kwata kwata bata da nutsuwa akan maganan auren, musamman yanda labarin irin tsanar da Zaleeha keyiwa Saifuddeen dayazo kunnenta, ko acikin ƴaƴanta son da takeyiwa Saifuddeen daban yake, har acikin jininta takejin soyayyar ɗan nata, sam koda wasa bata ƙaunar abun da zai cutar mata da Saifuddeen ɗinta, haka ko kaɗan batajin son wanda bayason Saifuddeen ɗinta, sosai takejjn tsoron abun da zaije yazo idan Saifuddeen ɗin ya auri Zaleeha, daga gefe guda kuwa tsananin tausayin Saifuddeen ɗin ne kullum ke ƙara cika zuciyarta, musamman yanda ta lura da irin sonda Saifuddeen ɗin keyiwa Zaleehan kamar ransa, aduk sanda ta so tunkarar Saifuddeen da maganar son fasa auren nasa da Zaleeha, takansamu kanta cikin rashin ƙarfin guiwa domin kuwa da ta kallesa zata hango tsantsar soyayyar da yakewa Zaleehan kwance acikin idanunsa, wannan shine abun da yake karya garkuwanta ako da yaushe, ɗan numfasawa Ummin tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, a hankali tace.
"Lallai yanzun kam bazan iya jurewa ba, dan dole zan aiwatar da abun dake zuciyata, sam bazan taɓa yarda in zuba idanu inga Saifuddeen yakai kansa inda za'a halakar min dashi ba, shiɗin garkuwa ne agaremu, muna tsananin buƙatarsa, daga ini har ƴan uwa da abokansa bazamu taɓa son abun da zai cutar dashi ba, saboda haka na gama yanke shawara tabbas zan ƙira Baffa Ali da Malam Ashiru kamar yanda sukaje suka nemawa Saifuddeen ɗin auren Zaleeha, to ayanzu ma zasu koma suce Saifuddeen ɗin ya janye, saboda kwata kwata babu wani alfano wajen auren matar da bata sonsa, babu komai cikinsa sai, danasani, baƙin ciki, da kuma tashin hankali, sam kuma bana fatan Saifuddeen ɗinna yaji koda ɗaya daga cikin waƴannan ne, burinna shine yayi aure yaji daɗi, ya kuma samu kwanciyar hankali, da nutsuwa, sam bana fatan akasin ɗaya daga cikinsu ya samesa, saboda haka na aminta da shawaran da zuciyarta ta yanke min, dole ne za'a fasa auren Saifuddeen da Zaleeha." ta k'arishe maganar tare da kwanciya.


Hayatuddeen da abokansa kuwa, tuni suke ta murnar bikin, inda suka shirya partyn da zasuyi a bikin nasu na musamman, tuni Hayatuddeen ya watsa hotunan katin auren ashafinsa na Instagram da kuma WhatsApp status ɗinsa, tuni Ameena ta haukace masa da tayi tozali da invitation card ɗin, nan tafara kuka yayinda zuciyarta tacika da kishi haɗi da raɗaɗin auren na Saifuddeen da zaiyi, wasa-wasa fa Ameena harda kwanciya zazzaɓi.
Asma'u ma sosai tayi takaici domin bata da wani buri daya wuce kasancewarta da Saifuddeen, ita kanta batasan soyayyarsa tashigeta sosai ba saida taga katin na aurensa da Zaleeha kuma dai hakan baisa ta sauya k'udirinta ba.




Ɓangaren Zaleeha kuwa tun jiya da ta sa kanta aɗaki ta kulle bata ƙara ko leƙowa ba, gaba ɗaya haka ta wuni cikin ɗaki, zuciyarta cike da ƙunci, haɗi da takaici, tuni tagama shirya duk wani plant ɗinta na yanda zata fitowa da ƴan gidannasu sabon tsarin takunta, na yanda zata rufe idanunta ta shumfuɗa taɓaran ƙin auren Saifuddeen da ake ƙoƙarin laƙaba mata. Hakanan ta-tashi yau da son zuwa gidan yayarta Maryam, don haka tun safe ta kammala shirye shiryenta, wanka tayi inda ta shirya kanta cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga navy blue colour mai kyaun gaske, sosai rigan tabi shape ɗin jikinta ta ƙafe, yayinda adon stones ɗin rigarta keta shinning yana ɗauke ido, parking dogon gashinta tayi atsakiyar kanta, kana tayi rolling ɗan maidaidaicin vail ɗin rigan akanta, wanda ya sauƙo har zuwa kan ƙirjinta, wani ɗan maidaidaicin hand bag ɗinta shima me kalar navy ta riƙe ahannunta tare da ɗaukan wayoyinta, ƙiran iphone da kuma samsung, wani navy blue toms masu kyau da taushin gaske ta sanya aƙafafunta, wanka tayiwa jikinta da daddaɗan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login