Showing 168001 words to 171000 words out of 177664 words

Chapter 57 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete by Garkuwa .txt

06 Dec 2024

7785

mgna."
Dam-dam zuciyar Hayatuddeen ya bada wasu tagwayen tarnaki mai cike da fargaba cikin zargin kai anya kuwa wannan bada Hammanshi take ba, cikin tsananin fargaba baki na rawa yace.
"Uhmmm me sunan shi ne!?."
cikin tarin tsanar tsuna taja wani dogon tsaki tare da mik'ewa kana tace.
"Wai Saifuddeen n!!!."
da sauri Zakariyya ya mik'e tsaye tare da cewa.
"Hamma Saifuddeen.
Shi kuwa Hayatuddeen cikin k'arfi ya fizgo hannunta tare da zaro idanunshi da sukayi jazir tuni hawaye na shatata a kumatunshi har kan gemunshi cikin rawan murya yace.
"K'arya ne wallahi Hamma na ba nakasasshe bane, domin nakasarsa bata zame mishi kasawa ba,
Ke da kike zagin nakasarsa kinada tabbacin naki lafiyar ne, da har kike inkarin ke da lafiyarki, to wlh yanzu kika fara kuka ko zaki mutu sai kin zama matar kurma kuma gurgun nan,
D'an uwane shine jigon rayuwar ahlinmu."
Sai kuma ya sake mata hannu ya koma ya zauna, Zakariyya ma tuni hawaye yake zubdawa, dan sai yanzu ya gane ashe Hamma Saifuddeen ne wanda yayarshi Zaleeha keta ƙi.
hakama Ziyada hawaye take zubdawa,
Hajja Inna kuwa cikin mmki tace.
"Hayatu, ashe ma Saifuddeen kyakkyawa ne ta samu har take rigima.
Wlh ni ban saniba."
Cikin zubda kwalla shima Hayatuddeen yace.
"Wlh Hajja Inna nima sai yanzu na gane data kira sunanshi da yanayin nakasarsa kuma,
na tuna ance min sunan matar da aka bashi Zaleeha ne."
ita kam Zaleeha juyawa tayi ta fita jin ƙaninta Zakariyya na cewa.
"Wlh nima ban san akan Hamma Saifuddeen bane take wannan haukan da ko inda take bazanma kallaba."


Hajja Inna ce ta katsesu da cewa.
"Ai kuwa ko mutuwa zatayi sai ta aureshi."
Sai ta kuma kalli Hayatuddeen cikin rarrashi tace.
"Kayi haƙuri kaji ko Hayatu, dan Allah kada ka gayawa Umminku da yayunka wannan batun in sha Allah Zaleeha zata tanƙwaru."
Kai ya gyaɗa mata alamar to,
sai ya kuma Kalli Zakariyya tare da cewa.
"Dama nazo nefa muje gidansu Imran muyi batun dinner ɗin da za'ayi a bikin ne, ina son mu tsara fita ta musamman a wurin," cikin bada ƙarfin guiwa Zakariyya yace.
"To muje, danko abu namune maganin a kwaɓemu."


Daga nan suka tafi gidansu Imran ƙanin ishaq.


Ita kuwa Zaleeha abu ya cakuɗe mata komai ya birkice mata,
Yanzu ba mai bin ta kanta ta lura Aunty Lubna da Zakariyya basu damu da dmuwar tata ba


Haka yasa dole ta ƙudurci son haɗuwa dashi ido da ido ayita ta ƙare.


A lissafi dai yau saura kwana biyar ne auren.
ganin har danginsu na Dukku sun fara zuwane ya ƙara tayar mata da hankalin.
Gashi haka nan take jin kamar ana ingzata da zugata kan tayi wani mummunan abu.
Shiyasa yau tunda safe taketa tura mishi text akan yazo gidansu zasuyi mgna mai mahimmanci ganin har yamma ba amsa ne yasa ta kira Ishaq bayan ta tuttura mishi saƙo dan Allah ya amsa kiranta,
Yana d'agawa cikin rawan murya alamun zata fara kuka tace.
"Dan Allah Malam Ishaq na rok'eka da manzon rahma kace yazo gidanmu inada mgna dashi."
cikin danne dariyarshi da sai yanzu kalamanta na wai sun ce mata irin larrarshi basa iya aure dariyar ya ɗan danne kana yace.
"Yaushe kike son yazo?."
Da sauri tace .
"Dan Allah yazo yau. Ban san in da zan sameshi ba da naje na sameshi."
wani munafukin murmushi ishaq yayi sannan yace.
"Ki duba hanyarshi zuwa bayan sallan isha."
Da sauri tace to kana ta katse kiran,
a take ta kira Bilkisu dan tasan itace zata tayata ci musu zarafi ta yadda sai sun tsani kawunansu ma, aiko Bilkisu najin shirin Zaleeha tace gata nan zuwa.


Bayan sallan isha, Saifuddeen ne zaune bisa wheelchair ɗin shi kalar ruwan toka mai azabar kyau da sheƙi, a zahiri yadda yake caccanza sutura da ɗaukan wanka to hakama mota da wheelchair ɗinshi suma masu kyau da tsada ajin forko yake hawa hakama huluna da takalma,
Sanye yake cikin wani d'anyen yadin voyel mai kalar shud'in sararin samaniya, sai kuma ratsin fari fari tamkar gajumare,
an ƙyanƙyasawa rigar aiki da surfani mai ruwan garai-garai,
hannun rigar guntu ne masu zagayen zaren garai-garai d'in daga bakinsu, hannun yayi cib damatsan hannunsa da suke farare k'al-k'al masu yalwar gargasa mai tsawo da shek'in bak'i mai d'aukar hankalin duk wanda ya gansu sun zauna cib,
hular damanga ya kafa a kanshi irin kafin nan da ake cewa baruwanka da duniya bi ma'ana ya d'an tura hular tayi baya,
hular farace sai ratsin shud'in zare, sajen nan nashi ya kwanta lib-lib a kyakkyawar fuskarshi mai suturce da farar fata da kan sura jajayen labbansa sai Sheƙi sukeyi a cikin zagayen gashin bakinsa.
hakama takalmanshi farare ne k'al sai layi biyu da akaja mai kalar shuɗin daga samansu,
sai wani zazzafan agogon fata na Gucci mai kalar garai da manna a tsintsiyar hannunshi na dama,
sai farin ring ɗin azurfa dake ɗauke da ɗigon diamond a tsakiyarshi daketa wal-wal,
wayarshi samfarin iPhone daya zura cikin al'jihun gaban rigarsa, wanda kana iya ganin kusan rabin wayar ma a sarari.
Hayatuddeen ne ya lumshe ido tare da ƙara zuƙan numfashi dan shaƙan ƙamshin turaren Hamman nashi.
Ummi kuwa ido ta zuba mishi cikin yin hamdala da godiya wa ubangijinta da azurtata da wannan kyakkyawan matashi a matsayin ɗanta.
Murmushi yayi tare da mishi fatan a dawo lfy bayan ya mata alamun zai fita.
Hayatuddeen kuwa har bakin mota ya rakashi inda suka samu Ishaq da Sule direba suna jiran fitowarshi.
Mota suka shiga sannan suka nufi New G.R.A.


Suna isa cikin gidan kuwa sukayi kicibis da Ya Aminu shi yayi musu jagora har cikin parlourn BQ kana yaje ya turo Zaleeha wacce,
take tare da bilkeesu.
kusan a tare suka fito yana gabansu.
suna bayanshi suna tafe zuƙatansu fal farin cikin zasuci zarafinsu


A harabar wajen suka samu Ya Aminun da Ishaq suna mgna da alamun mai mahimmanci ce.


Suna shiga cikin parlour'n. Zaleeha tayi wani irin taku me tattare da izza ta isa gabanshi kujerar dake gefenshi ta zauna tare da ɗaura ƙafanta ɗaya kan ɗaya, a hankali take karkaɗa ƙafafun nata cikin tsaurin ido ta ɗago fuska tare da harba mishi ida nunta cikin nashi idanun.
A hankali ya muskuta ya gyara zamanshi tare da sarƙe manyan idanunshi cikin nata idanun, kana yayi wani irin makirin murmushi tare da ɗaga mata girarshi ɗaya, alamun.
"Baby ya dai ya akayi ne?."
Wani irin yam taji tsikar jikinta duka na amsawa, hatta gashin kanta saida taji ya amsa,
wani irin azabebben kwarjini fuskarshi tayi mata tsoronshi da shakkarshi suka cika mata idanu.
A gigice ta janye ƙwayar idanunta daga nasa, tare da rumtse idanun Nata, jiki na rawa murya a sarƙafe cikin zato da yaƙinin wannan ba mutun bane tace.
"WA innahu Sulaiman...!".






Yau dai ba editing


By
*GARKUWAR FULANI*
8/22/20, 5:15 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*NAKASA BAKASAWA BACE*


*PAGE 31*


~End of part one~


*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*




🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




*WANNAN SHAFI GABA ƊAYANSHI NAKANE KYAUTA NA BAKA SHI Babana ALIYU IBRAHIM WAMMABI, inayi maka fatan al'khairi a rayuwarka Allah ya kauda mugun ido da mugun kunne daga kanka rabbi ya Al'barkaci rayuwarka yasa ka zamo al'waladdussaliha ga iyayenka. Allah dai ya raya mana mai sunan babana ka rage mishi rawan kai, ke kuma Zaleeha in na sake jin kin cewa babana A cici kazar birni nidake bibbiyu..*


_Fatan al'khairi ga WambaiFamly_


"Innahu Sulaimanu wa'innahu bismillahirrahamanirrahim!."
Tafaɗa ƙasa-ƙasa tana me watsa masa harara da manyan fararen idanunta, yayinda kuma idanun nata suke fallatsa tsantsar tsoron dake wanzuwa daga zuciyarta zuwa jikinta.
Wani irin ƙawataccen murmushine ya bayyana akan fuskar Saifuddeen, sosai maganan nata ya bashi dariya, wato ma matsayin Aljani ta ɗaukeshi?.
Sake jawo wheelchair ɗinsa yayi ya ƙaraso gaf da ita, wani irin killer smile ne ɗauke akan fuskarsa, ƙasa yayi da kyawawan idanunsa masu matuƙar kyau sannu ahankali yake ƙarewa kekyawar surarta kallo, jin yamatso kusa da ita ne yasanyata ɗago da kanta da nufin tasake watsa masa wata hararan, amman sai tayi maza tayi ƙasa da kanta dan kwarjininshi yi yawaita gareta, ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba cikin son ƙuntata ransa tace.
"Amma dai kasan cewa bana son ka aureni, nafaɗa maka ni bazanyi aureba, aduniya babu wani abinda na tsana kamar ayi min mgnar aure, meyasa bazaka gane hakan ba? kada fa ka taɓa tunanin cewa wai aurena zai sama maka farin ciki, wallahi bazan taɓa bari kasamu farin ciki a dalilina ba, zama dani tamkar kana kusanto da ajalinna zuwa gareni ne, wallahi idan ka bari aka ɗaura aurena aka kaini gidanka zan mutu!."
Taƙare maganar murya na rawa, domin kuwa wani irin tuƙuƙin baƙinciki ne, takejin na game gaba ɗaya zuciarta da jikinta.
Sam ko sau ɗaya munanan kalaman nata basu shiga kansa ba dan shi yasa a ranshi bata da abinda zatayi mishi ta b'ata mishi rai, kana har yanzu killer smile ɗin dake kwance akan fuskarsa na nan bai kau ba, komai tayi sai yayi gmagar zuci cewa.
"Uhumm kinci bashi, zaki biya, dan ni ba-bawan gidanku bane da xakiyi ta soka min baƙaƙen mganganu son ranki."
a fili kuwa yanda ƙananan laɓɓanta ke motsawa ya ɗan zubawa ido a fakaic, jiyake kamar ya jawota jikinsa ya bata wani irin professional kissing, lumshe idanunsa yayi tare da ɗan jingina bayansa da jikin kujeransa, hannunsa ya ɗaura adai dai saitin zuciyarsa wacce ke beating da sauri-sauri, ɗan buɗe idanunsa yayi tare da watsa mata su, idanunsu ne suka sarƙe ajikin na juna da sauri tayi ƙasa da kanta, domin sam bata iya jure ganin idanun nan nasa masu birkita mata lissafi, wani irin malolon baƙinciki ne ya zo ya tsaya mata amaƙoshinta, sosai tafito daniyar cin zarafinsu, tayanda gaba koda kuɗi akace suyi zancenta bazasuyi ba, amma kuma sai gashi ganinsa yasanya tanemi wutar bala'in dake cinta arai ta rasa, tarasa shi wani irin mutum ne, mai tsananin kwarjini da haiba mai firgita zuk'atan magautanshi.
Zuwa yanzu kam tagama gamsuwa da cewa shiɗin al'janine, idan ba aljani bane to kuwa maye ne!.
Kallon-kallo sukayi ita da Balkeesu, cikin salon ƙarin zuga Balkeesu tasaki wani ɗan iskan murmushi mai ɗauke da ma'anoni kala-kala, cikin yanayi na gatse haɗi da muzantawa, tace.
"Musakan angwayenmu ina wuni ku!."
Kafun ma sukai ga cewa komai tayi saurin cewa.
"Au ashema na manta cewa ginannen taɓon angon namu dutse ne, bayaji baya tashi gani kawai yake iyawa." Taƙare maganan cikin nishaɗi da son ƙufular da Ishaq, domin atunaninta shi Saifuddeen bajinta yake ba, itakuwa dama tunda idanunta ya sauƙa akan Ishaq takejin wani irin tsanansa acikin ranta, domin acewarta shine wanda yafara kawo Saifuddeen cikin rayuwar Zaleeha.
Shikuwa Saifuddeen duk abun data faɗa yajita sarai domin tun fara maganan nata yake kallonta.
To amman shi ganinta yake kamar akuya aka shafawa jambaki asalima dariya take bashi, sai dai miskilancin ya danne sirrin zuciyarshi ta yadda sam Zaleeha da bilkeesu suka gane me yakeji game da kalamansu.
Wani irin murmushi Ishaq yayi, tare da cije laɓɓansa, tabbas bazaice baiji zafin maganganun da Balkeesun ta faɗa musu ba, saidai kuma shima akwai wani tunanin dake yawo acikin ransa, saboda haka baya tunanin ayanzu zai tanka mata, saidai zai bari nan gaba kaɗan zaisa tagane kurenta itama dan sai ya sata cikin komar nakasassu sai ya ganar da ita *Babu nakasasshe sai kasasshe.*


Rumste idanunta tayi sakamakon wani irin ɗaci da takeji amaƙoshinta, sam batason kallon dayakeyi mata, rai da zuciyarta tafasa suke, ayanzu aduniya bata da wani maƙiyi irinsa arayuwa taso taga zallan tashin hankali da tsoronta a ida Saifuddeen, amman ina Namijin duniya ya nuna mata bata da wani kalamin da zata gaya mishi wanda zai razanashi.
Sosai tayarda da abun da zuciyarta ke gaya mata hakan yasa ta miƙe tsaye, kallonsa tayi sama da ƙasa, kana ayangance ta watsa mishi k'ask'antaccen kallo, cikin yanayi dake nuna tsananin shakkar kwayar idanunshi taɗan ranƙwafo da kanta kusa dashi, cikin son ƙuntata masa tace.
"Sam bakayi kama da namijin aure ba, saboda haka zaifi dacewa kabar cikakkun maza masu lafiya su tinkareni bawai kai nakasashshe ba, baka da abun da zaka bani koda kuwa ka aureni bazaka iya zame min miji ba, kaiba Namiji bane, kai wani halittane dayakasance marar kumfa a saman ruwa dana zauna dakai gwamma na tabbata ba aure tunda dai nasan da aurenka da tabbata ba auren duk d'aya ne."
Sai ta kuma fesar da zazzafan numfashi kana taci gaba da cewa.
"Naji shikenan tunda kanace lallai cewa dolen-dole wai kai saika aureni to daga yau kuma daga yanzu kafara ƙirga kwanakin mutuwarta!, saboda nasan zan dan rashin abinda rai kene zaiyi ajalina!, mai wahalalliyar zuciya!.".
ta k'arishe mgnar tare zare mishi ido wai ita zata bashi tsoro.
Wani mugun kallo ta watsa masa kana ta juya cikin azama zata bar wajen domin kallon fuskarsama yana sata mata ɗimaucewa.
Azafafe Saifuddeen yasanya k'afarshi ya d'an tad'eta, lokaci guda tayi taga-taga tayi su zata faɗo.
Cikin tsananin tsoro da figita ta rumtse idanunta da azaban k'arfi tare rik'e numfashinta kana ta sakin k'ara mai cike da tsoro, dan tasan kan table dake gefenta zata dad'i kuma na glass ne, hannunshi ya mik'a daga zaune ya jawo mayafinta-ta fad'o jikinsa, al'amarin daya girgiza Balkeesu kenan, shikuwa Ishaq dama ba gani yake ba hakan yasanya baisan nenene ya faru ba.


Manyan idanunta ta zaro waje, cikin tsananin takaicin haɗewar da jikinsu yayi waje ɗaya,
a gigice tasoma kiciniyar ƙwace kanta, amma ina ƙarfin musakin da ta raina ya wuce tunaninta, don kuwa riƙo yayi mata bana wasa ba.
Yanayin idanunsa ne suka sauya daga farare zuwa ɗan garai-garai sai k'ank'ancewa da suka d'anyi kad'an, take jijiyoyin jikinsa suka mimmiƙe, yayinda lokaci guda yanayin fuskarsa ya sauya, cikin zaƙuwa haɗi da takaici ta ɗago kanta daniyar auna masa wata mummunar baƙar magana, tuni maganar ta maƙale amaƙoshinta sakamakon yanda jikinta gaba ɗaya yashiga shock, sosai ganin yanayin idanunsa ya tsorata ta, da sauri ta ɗauke idanunta daga garesa, cikin wani sabon fargaba haɗi da ɓacin rai da suka ziyartota ta tasanya hannunta ta bugi chest ɗinsa da ɗan ƙarfi, atunaninta idan yaji zafi dole zai sake ta, saidai amma ko motsi bataga yayi ba, jikintane gaba ɗaya ya ɗauki rawa sakamakon yanda yake ladabtar da ita da wani irin kallonsa da idanunshi masu sata shayinshi da shakkarsa, shikuwa Saifuddeen da gangan ya tsareta da idanunsa, bakomai ya ɓata ransa cikin maganganunta ba kamar cewa da tayi waishi ba namiji bane, hmmm wai harshi Saifuddeen ne za aƙirasa da sunan bacikakken Namiji ba, ahankali yake matso da fuskarsa gab da tata, wanda hakan yasanya gaba ɗaya ta ruɗe, ahankali yake ƙara kusanto da fuskarsa gaf da nata, hartakai takawo numfashinsu ya cakuɗa dana juna, haɗuwar numfashinsu waje ɗaya, baƙaramin bugun zuciya ya haifar musu ba suduka biyun, sosai zuciyar Zaleeha ke bugu kamar zata faso kirjinta tafito, akaron farko dataji wani matsanancin tsoronsa ya shigeta, don kuwa matsowarsa gareta baƙaramin zautar da tunaninta yayi ba, sosai yayi mata wani irin kwarjini a idanunta, sam batasan cewa haɗuwa da kyawunsa yakai har haka ba sai ayau ɗin daya kusanto da fuskarsa gareta, daga gefe kuwa fitinannen ƙamshin turarensa ne yacika hancinta, lokaci guda jikinta yafara fitar da wani irin gumi da kerma da karkarwa, dake nuna tashin hankalin dake bunne cikin zuciyarta.
Haka Saifuddeen ya cigaba da kawo fuskarsa gab da nata, ahankali yake matsowa kamar zai haɗe bakinsu waje ɗaya, tuni Zaleeha ta rumtse idanunta jikinta kuwa rawa yake sosai, ta sadakar aranta cewa wannan musakin na sauƙe bakinsa akan nata, babu makawa saitayi kuka!, Allah ma yasauwaƙe ita Zaleeha tasha yawun shi.
Kawar da fuskarsa yayi zuwa gefen wuyanta, ahankali ya fesa mata wani irin numfashi mai tsananin ɗumi, wanda take yasanya tsikar jikinta mimmiƙewa, hannunsa dake kan waist ɗinta ya janye tare daɗan matsar dakansa baya, jin ya sake ta yasanya ta sauƙe wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, buɗe idanunta wanda suka kaɗa sukai ja saboda tsananin tsoritan da tayi, wani ɗan guntun tsuka taja tare da ƙwace jikinta daga cikin nasa, batare da tunanin komai ba haka Zaleeha ta tattaro yawun bakinta da tunanin zata tofar had'e tsukakkun lips d'inta tayi da niyar zata tofar da yawun.
Sai kuma ta zazzaro idanunta woje tare yarfa hannu jin yadda Saifuddeen yasa yatsunshi biyu ya had'e lips d'inta da yaga tanada niyar yimishi tijarar da bazai lamunta ba,
matse lips d'in nata yayi da k'arfi har saida taji fitsari na son kwabce mata.
Ida nunshi ya jujjuya mata tare da k'ada mata kai kana ya d'an kamo gefen lip d'inshi na k'asa ya d'an ciza alamar.
"Ko mafarki kikayi in kin farka kiyi sadaka."
kana ya sake mata lips d'inta da tuni sunyi jazir,
a tsoroce ta had'iye yawun nata tare da juya da sauri
cikin tsoro da ƙunan da zafin da lips ɗinta keyi tace.
"Ɗan is kawai, Allah ya haneni ranan da zaka ƙara taɓani, mugu! Allah ya isana!!
Kuwa wlh, koda wasa kada ka taɓa tunanin sake haɗa jiki dani, balle har tunaninka yabaka daman kawo bakinka kusa da nawa, wlh dana sha yawun bakinka gwamma ace nasha tom-tom, saboda ko bakomai nasan tom-tom yafi ɗanɗanon yawun bakinka daɗi.
Ganin ya ɗan taɓa masarrafin kekenshine ya nufi gareta, yasa ta juya da gudu-gudu

tafice daga cikin falon kamar wace aka koro
Da sauri Balkeesu tatashi ta rufa mata baya bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login