Showing 159001 words to 162000 words out of 177664 words

Chapter 54 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete by Garkuwa .txt

06 Dec 2024

7832

samun yara masu kama da kai."
sai kuma ta kalleshi ganin ya tsareta da ido haka nan yake jin kalaman nata har cikin zuciyarsa,
to amman wai meyasa ita bata kunyan faɗi mishi wasu abin ne, ita kuwa ganin yayi shiru ya kuma rage girmam idanunshi ne ya sata cewa.
"Ka gaji ko? bacci kakeji ko?, naga idonka yayi limshi, bari in kashe wayar sai da safe."
Tana kaiwa nan ta katse kiran,
shi kuwa Saifudddeen dariya yayi a ranshi yace.
"Sokuwa kawai mai tunanin yara wato kina sona, hmmm ke dai faɗi gsky bani kike wani soba, kinada dai abinda kikeso daga gareni."
daga nan yayi ta aikinshi.
sai kusan ƙarfe ɗaya,
ya sauƙo ya shimfid'a sallaya kana yaje yayi al'wala sannan yazo yayi nafilfilinshi sai d'aya da rabi ya konta.


Washe gari ranar Jummu'a tun da safe su Zaleeha suka dawo,
daga gidan Hajja inna tayi wanka ta wuce Billiri dan hira da nakassusun wancan yankin wanda k'arfe biyar na yammacin ranar jumma'ar ne zata gabatar da shirin, tun randa ta had'u da Saifudden a Jonapwd, bata sake zuwa canba,
kuma tunda ta turawa ishaq text ɗin ban haƙuri bai kulataba itama bata sake bin ta kanshi ba,
shi kuwa Ishaq shida Saifuddeen bakinsu a had'e a cewarshi ita da kanshi zata nemeshi har mazauninshi...


K'arfe uku ta dawo daga billiri kai tsaye gidan radio nasu ta nufa,
a nan tayi sallan la'asar, sannan ta zauna jiran lokacinta,
tana zaune anan Bilkisu ta shigo ita da Manager d'insu tana ganin Zaleeha ta kwashe da dariyar shak'iyanci cikin ingizarwa tace.
"Hajiyar nakasassu ina mutanen naki ne? Koda yake amaryar nakasashen gurgu kurma zance ko."
cikin tsananin takaici Zaleeha ta watsa mata harara tare da cewa.
"A a uwar nakasashe zakice ba amryar nakasashe ba wlh mai gado bana so ki daina had'ani da wannan musakin."
cikin Shek'iyanci bilkisu ta iso gareta tare da cewa.
"Sorry baza k'araba, amman mutanen nakine da abin dariya."
juyawa tayi ta fita tabi bayan Manager ita kuwa Zaleeha Raveel ta kalla wanda yake mik'o mata sweet amsa tayi tare da cewa.
"Ngd."
kai ya gyad'a mata tare da cewa.
"Kada ki sake aibata nakasassu dan duk wanda bai mutuba ba'a gama mishi halittaba.
da kullum haka kike gaya min to meyasa kawai dan nakasasshe yace yana sonki sai ki juye daga Mai kakkyawar alaƙa i zuwa mummunar ɗabi'a, kada ki bari imaninki ya samu rauni."
kai ta gyaɗa mishi sannan ta juya ta nufi ɗakin gabatar da shirin nata ganin lokacinta yayi.


Mama kuwa da Zahira sosai zugar Ruda yayi tasiri a kwanyarsu da yake dama zuciyar ba inganci.


Ƙarfe huɗu dai-dai suka dawo daga doho,
suna shiga gidan kai tsaye side d'in Baba malam suka nupa,
a parlour suka sameshi shida Ya Ahmad da Ya Habu, sai Mamy dake haɗa musu tea a kofuna.
sannu da hanya sukayi musu, fuskarnan kamar zatayi ruwan jini Mama ta amsa musu kana ta gaida Baba malam,
sannan Ahmad da Habu suka gaidata,
Zahira kuma duk ta gaidasu sannan ta wuce cikin gidan tayi shashin maman.
Ita kuwa Mama a hankali ta mik'e ta fita ganin duk basubi ta kantaba,
to wazai kulata yadda taketa harare-harare,
tana fita ta nufi Side d'inta da yake tsab Maryam da Aunty Lubna sun gyarashi jiya da dare.
A parlour ta zauna,
dai-dai lokacin kuma Zahira ta fito daga bedroom d'in Maman a guje,
ganin Maman a parlour yasata tsayuwa cikin rawan jiki da halin fitina tace.
"Mama zo zo zo kiga wani abu a bedroom naki."
tsaki ta d'an ja tare da cewa.
"Menene kike wani zaro idanu haka?."
hannun uwar ta kamo tare da cewa.
"Mama zo ki gani mana an cika miki d'aki da akwatuna dasu buhunan gishiri dasu goro."
ido ta zaro gaba d'aya tare da cewa.
"Akwa tuna kuma to na meye."
cikin hatsabibanci tace.
"To waya sani ko lefen Anty Zaleeha aka kawo."
ai kafin ta rufe bakima Mama ta kutsa kai cikin bedroom ɗin.
wani irin wawan birki taja tare da cewa.
"To wanna kuma daga ina, to ko Abdussalam ne da tace mishi a turo komanshi Zaleeha ta yarda dashi, tuni ya turo ɗin,
sai kuma ta girgiza kai ina sam ba shi bane ai in shine zai gaya mata, shida kuma ɗazu suka gama mgna,
cikin tafasan bala'i tace to waye.
Sai kuma ta dawo parlour da sauri cikin karad'i da kware murya baki d'aya ta fara rabkawa Habu kira.
"Habu! Habu!! Habu!!! Habuuuu!."
da sauri ya iso cikin parlourn a tsorace yace.
"Na'am Mama ganifa nazo."
A hatsale tace.
"To dan ubanka meyasa bazaka amsa da kyau ba."
cikin had'e fuska yace, "Na'am." cikin yamutsa fuska tace.
"Wancan kayan fa na meye ne."
Kai tsaye yace.
"Lefen Zaleeha aka kawo jiya."
cikin ɗaga sauti tace waye kawo lefen?."
A dake yace.
"Wasu mata ne."
zaburowa tayi kanshi tare da cewa.
"Dan ubanka ba wanda suka kawo nake tambaya ba wanda aka kawowa nake nufi."
cikin kauda kai yace.
"Zaleeha aka kawowa."
wani dogon tsaki taja tare da jawo hannunshi tace.
"Kai mahaukacin inane wanne saurayin ne ya aiko lefen."
Cikin dakiya da rashin tsoro yace.
"Saifuddeen."
wani irin zabura tayi tare da buga tsalle tace.
"Inji uban waye ya basu damar kawo banzayen lefen wanna musakin d'an nasu?."
Yana fita yace.
"Inji Baba Malam mana Baban Zaleeha shine ya basu dama."
wani irin kware murya tayi tare da yin sauri ta nufi parlour Baba malam tana shiga parlour tare da masifa murya a hargitse tace.
"Lallai yau za'a sabunta yaƙin duniya....!






*Dan Allah da manzonsa ku dena fitarmin da littafi,*


By
*GARKUWAR FULANI*
8/


*NAKASA BA KASAWA BACE*


*PAGE 30*


NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




"Lallai yau za'a sabunta yaƙin duniya na biyu".
Fuska ta ƙara haɗewa tamkar wacce akayiwa bushara da mummunan al'kaba'in rayuwar duniya.
Ido suka zuba mata baki ɗayansu, tare da maida hankalinsu gareta.
Cikin takaici da tashin hankali tace.
"Meyasa! Meyasa haka ne malam? Ina dalilin kullum sai an sani baƙin ciki kan aurar da ƴaƴana?."
Kauda kanshi yayi daga kallon mummunar fuskarta tare da maida dubanshi ga al'ƙiblah, a hankali yaci gaba da tasbihi da yakeyi.
"Subahallahi, walhamdulillahi, wa la'ilahalillahu, wallahu akhbar."
haka yaketa mai-maitawa tare da motsa yatsun hannunshi na dama, kana yana ɗan karkaɗa ƙafafunshi dake miƙe bisa table ɗin dake gabanshi a hankali a hankali.
idonshi ya rumtse da ƙarfi jin Mama na cewa.
"Wallahi-Wallahi bazan taɓa yarda a zalumunci Zaleeha irin yadda aka zalumci Maryam ba, akan wani dalili zai sa baza'a sakarmin rayuwar yarana ba, suma su auri wanda sukeso sai ayi ta musu cushe da auren dole ina dalili? to Wallahi muddin ina raye, Wallahi bazan taɓa lamunta Zaleeha ta zauna da wannan banzan nakasasshen kurma kuma gurgun, da kuka yayibo zaku liƙa mata ku kashe mata rayuwa ba,
haka kawai dan an iya min kisan mummuƙe, shine za'a nunamin wariyar launin fata, a nuna min ni bare ce to Wallahi ban amince ba!."
Cikin gajiya da ihu da hayagagar da take musu Ya Ahmad ya ɗan tanƙwashe sawunshi tare da cewa.
"Mama ai Zaleeha ita ta kawo shi, zaɓinta ne ita ta amince dashi babu wanda ya mata dole,
itace ta amince tasa ya turo iyayenshi."
Cikin tsawa tace.
"Rufe min baki, kaima ae munafuki ne, ban nemi jin ta bakinka ba, da ubanka nake magana,
karka wani karkace kace zaka meda laifin kan Zaleeha, munafurcin banza kawai."
Rumtse idanu Ya Ahmad yayi, cikin takaicin abinda Mama'n kewa mahaifin nashi yace.
"Allah ya huci zuciyarki."
A hasale tace.
"Wannan karon dai zuciyar tawa ba zata huce ba, Wallahi bazan taɓa lamunta da batun ƴata ta auri musakiba,
dan rainin hankalin yarinya da kyawunta da ƙimarta tanada masoya gabas da yamma kudu da arewa amman a rasa wanda za'a zaɓa mata sai nakasasshe, wulaƙantacce wanda ko magana bayaji!."
Tafaɗa ranta amatuƙar ɓace domin sosai zuciyarta ke tafasa.


Duk ihu da hargowan da takeyi Baba Malam bai sake ɗaga ido ya kalleta ba, sai ma tasbihi da yakeyi ga mahaliccinsa da ya jarabceshi da auran wanna mata mai munanan al'adu.
Mamy kuwa wayarta ta jawo kana ta fara karanta Dua Azkar.
Ganin haka shima Ahmad sai yasa hannu ya ɗauki ɗan madai-daicin Qur'Ani'n dake gefenshi ya buɗe ya fara karatu ahankali cikin suratul. Kahf kasan cewar yammacin Jummu'a ne.


Habu ne ya shigo parlour'n a hankali ya nufi gefen mahaifin nasu ya zauna kusa da ɗan uwan shi Ahmad,
ido ya rumtse da ƙarfi yana mai jin takaicin hali irin na mahaifiyar tashi,
cikin sanyin sauti yace.
"Ya salam! Dan Allah Mama kiyi haƙuri ki bar yin ihun nan, kowa yanayin abinda zai samar mishi lada ke kuma kinzo kina tarawa kanki zunubi kina ɗaga harshenki sama dana mijink..."
Da sauri ya haɗiye rogowar maganar tashi, sakamakon jin Maman ta kai mishi wani uban bugu kan bakinshi.
"Habu kayi asara Wallahi, kai dai ka banunka da baka da kishin mahaifiyarka!." Takuma faɗa a hasale.


Baba Malam ne ya miƙe tsaye, tare da kallon yaran nashi cikin kamala da cikar haiba yace.
"Kuyi al'awala mu tafi masalaci lokacin sallah ya gabato."
Da sauri suka mimmiƙe tare da cewa.
"To."
Haka duk sukaje suka sabunta al'wala kana suka tafi zuwa masallaci.


Mamy ma tuni tayi side ɗinta, inda ta samu Aunty Lubna a parlour tana sawa ƴarta hijabi alamun zatayi salla ne.
"Barka da shigowa Mamy."
cikin nitsuwa da mutuntaka Mamy tace.
"Barka dai Lubna ya gajiyar kitchen? na tafi na barki ke ɗaya da aiki niƙi niƙi ko."
Kai ta rausayar tare da cewa.
"Tun ɗazu na gama ai Mamy aikin ba yawa."
"Masha Allah! Allah Ya saka da al'khairi, ya baki surkai masu miki fiye da abinda kike min."
"Amin Amin" Aunty Lubna ta amsa cikin jin daɗi, kana tayi side ɗin da nanne masauƙinsu duk lokacin da sukazo Gombe dan ita da Mamy tamkar uwa da ƴarta haka suke.


Ita kuwa Mama ta cika tayi tam sai ihu da haushi takeyi ita kaɗai kamar karya.


"Watoma mahaukaciya suka medani? sun watse sun barni wato inyi ta haushi ni ɗaya ko, tam zanyi maganinku, Wallahi gaba ɗaya saikunji aranku cewa inama da ace bakuyi ganganci ƙulla wannan haɗin ba, saina sanya baƙinciki acikin zuciyoyinku, kuma sannan saina saku danasani marar yankewa, badai dani kuke wasan ba, hmmm Wallahi zakusan kun taɓo cikakkiyar ƙaɓila Batangali da surkin bateriya, akan auren nan babu wanda zan ɗagawa ƙafa!!."
Tana gama faɗin haka ta juya fuuuuu kamar kububuwa tafice daga cikin falon na Baba Malam.


Tana shigowa falonta ta soma afkawa Zahira ƙira,
da sauri Zahira ta fito daga cikin ɗakinsu tana cewa.
"Na'am Mama."


A harzuƙe tace.
"Zo zonan mu kwashi ƴan iskan kayayyakin nan mu watsasu waje, Wallahi bazasu kwanar min a ɗaki ba gayyar tsiya!."


Da sauri Zahira tace "To."


Nan suka shiga cikin ɗakin, haka suka dinga ibo akwatunan nan masu kyaun gaske, suna watsasu a tsakiyar farfajiyar gidan,
wai don ma kasancewar Mama ƙaƙƙarfar mace ce shiyasa kab ta iya jidon manyan akwatunan, tanayin waje dasu harda su gishiri da goron bata bari ba, ranta yakai ƙololuwa wajen tafasa, jin kanta take dai-dai da uban kowa, jira take wani yace mata cass tuni zata sullesa tas.


Saida ta gama watsasu a tsakiyar gidan, sannan ta koma cikin ɗakinta tana haki tamkar wacce tayi dambe ta gaji.
Al'wala tayi sannan tazo ta kabbara niyar sallan magriba, wanda tuni lokaci ya ƙure mata, don har an riga da anƙirayi sallan isha.


Zaleeha kuwa daga ma'aikatan nasu gidan kakar tasu ta koma,
don dama kwana uku ta roƙi Baba Malam daya barta tayi, kuma da yake gidan mahaifiyarshi ce sai bai hanata ba.


Kafin ma ta dawo tuni Ziyada ta gama haɗa musu komai na girki,
tuwon ɗanyar shinkafa da miyar kase,
tana ganin haka tace.
"Ziyada ina Zakariyya kuma da tsohuwar nan sukaje, suka barki ke ɗaya a gida?."
Cikin yanayin nutsuwarta irin na Maryam sak tace.
"Sun tafi gidansu abokinshi Hayatuddeen."


Tana warware naɗin gyalen hijabin dake jikinta tace.
"Sun daɗe da tafiya ne?."
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
"Eh tun da akayi sallan la'asar suka tafi."
kai ta jinjina kana ta zaro wayarta ta danna ƙiran number'n Zakariyya.


Shi kuwa Zakariyya lokacin suna parlour'n Ummi shida Hayatuddeen da Raliya, sunata tsiya wa Hajja Inna, ita kuwa Hajja inna
sai surfa musu boris takeyi,
Ummi kuwa sai nan-nan takeyi da hajja Inna dan taji dad'in zuwan kakar abokin autan nata, sosai takejin son tsohuwar a ranta, musamman yadda ta nuna tana masifar son Saifuddeen ɗinta.
Ta tasashi gaba tana yabo harda kukanta tana.
"Allah sarki bawan Allah, yaro kyakkyawa, Allah ya jarabceshi da nakasa,
ganshi kuwa kamar balarabe."
Sai kuma ta juyo ta kalli Ummy tare da cewa.
"Wannan yaron naki abin sone da tausayawa ga ko wanne mutum ɗan Adam me imani, ki godewa Allah daya azurtaki da samunsa a matsayin ɗa,
wasu suna can sun haifi lafi yayyun yara amman sai ki samu yaran munanane kamar kashin dare,
kinga ko gwara miki kyakkyawa fari ƙal nakasasshen."
Hayatuddeen ne yayi dariya sosai tare da cewa.
"Kai tsohuwar nan munana sun boni a wajenki."
Zakariyya ne ya zaro wayarshi dake suwa, wacce take cikin aljihun wondonshi yana cewa.
"Itafa sam bata son mummunan mutum, in taga kyakkyawan mutun kuma wai ji take kamar ta dawo dashi ɗanta."
Dariya sukayi baki ɗaya,
kana shiko Zakariyya ya amsa kiran Zaleeha tare da cewa.
"Hello Adda Zalees ya akayi ne?."
Sai ya kuma yafito Hayatuddeen tare da mishi alamun ga mutuniyarshi fa.
amsar wayar yayi ya kara a kunne tare da cewa.
"Adda Zalees nayi fushi dake muka dawo ko kizo ki duba kyakkyawan hammana da jiki ko."


Murmushi tayi tare da cewa.
"Afwan autan gidansu."
da sauri yace.
"No autan Ummi dai zakice, gidanmu kam ai kwanannan ma Hamma na zai fara ƙenƙesa mana yara sabbin zubi, ƴan yayi kuma kyawawa, irin yaran da Hajja inna ke masifar so."
Ƴar dariya tayi tare da cewa.
"To aku sarkin zance, please ka cewa Zakariyya su biya Abba bakery ya saya min pizza dan Allah."
Da sauri yace.
"To ba matsala karki damu zan bashi abin daɗi ma ya kawo miki, cikin na Hamma na zan ɗiba miki."
Da sauri tace.
"A a ni dai pizza kawai nake so."
Bai kulataba ya katse ƙiran.
sannan ya amshi kular da Raliya ta haɗa musu tsarabar Kai kayan lefen jiya."
Daga nan suka miƙe zasu tafi, har sun kusa fita daga parlour Hajja Inna ta juyo ta kalli Saifuddeen murmushi ya mata, haka itama murmushin tayi mishi sannan ta kalli Ummi cikin halin tsufa tace.
"Kin ga ƴata kada ki yarda ki bari wannan kyakkyawan ɗan naki ya auro miki mummunar surka,
in kuwa kika bari ya auro miki mummunar surka, to shike nan ya ɓata miki wannan kyakkyawar zuriyar taki, dan tabbas dole wata rana sai ta haifo muku mai kama da ita,
dan ni dai anmin na gani, yanzu in kika kalli Zahira zakice ba jinin ahlina bane dan ita kamannin dangin uwarsu tayi yo."
Zakariyya ne ya tura baki tare da cewa.
"Kefa kince baki da goni a duniya sai mai kyau, to sam gigin tsufarki baya gaya miki gsk, ya zaki rinƙa sarata ina ji, aikin kawai."
Dariya sukayi dukansu ganin yadda ta kamo hannun Zakariyya tana cewa.
"A a kada kaji haushi shalelena, ai kai sak da kakanka baban babanka kakeyi, shiyasa kai da Ahmad kuke tsananin kama,
Zaleeha da Ziyada kuwa dani suke kama, bakaga Zaleeha ko gashi irin nawa ta gado ba?."
Janye hannunshi yayi tare da kunna machine ɗinsa, kana ya amshi kular da Hayatuddeen ke miƙo mishi ya saka a cikin ɗan kondon dake gaban machine ɗin.
Sai ya kuma kallon Hayatuddeen dake miƙo mishi 10k kana yace.
"Ga tukuicinmu na jiya."
Dariya Zakariyya yayi tare da cewa.
"Kace abin namu ne babu ƙaranci, ashe ko zamuyi casu a bikinga."
Sosai Ummi ke murmushi dan Zakariyya sak autan tane da shirmensa.
Sosai hajja Inna ta ɗale saman machine ɗin na Zakariyya, kamar ba tsohuwa ba,
da sauri Ummi ta riƙe kai ganin yadda Zakariyya ya figi machine ɗin ya fita a guje.
Hayatuddeen ne ya kece da dariya tare da cewa.
"Hege Zakary namu, wata rana zai ɓarar da hagwaran tsohuwar nan a titi yaseen."
Dariya Raliya tayi tare da cewa.
"Ai harda karya mata ƙafa."
Daƙuwa Ummi tayi musu tare da juyawa tayi cikin gida sannan suma sukabita a baya.


Su kuwa Zakariyya na isa ya miƙawa Zaleeha kular da Hayatuddeen yabasa yayi, dan tuni shi yaci a can yayi haniƙan,
ita kuwa Zaleeha kamar bazata buɗe kularba sai ta kuma buɗe, ganin abinda ke cikine ya sata yin murmushi sannan ta miƙe tsaye, lemon exotic ta ɗauko acikin fridge kana ta dawo ta zauna, haka ta fara cin pepper chicken ɗin dayaji onion, tanaci tana latsa wayarta,
Ziyada kuwa tuni tabi bayan Hajja inna da ta kirata wai tazo ta cire mata sarkan da ta sanya awuyanta, kasancewar idanun tsufa gareta bazata iya cirewa kanta ba.


Ƙarfe tara dai-dai Zaliha Ziyada da Zakariyya dukansu suna zaune parlour'n Hajja ina sunata hirarsu irin ta ƴan uwan juna,
yayinda kakarsu ke tsakiyarsu,
tana kallon kyawawan jikokinta da take matuƙar so arayuwa, dan
duk cikin jikokinta tafi son Ahmad da kuma Zakariyya.
Sam bata shiri da Habu a cewarta wai shi baya dariya.


A can New G.R.A kuwa kasan cewar yau girkin Mamane dan Mamy yau ta ƙare kwana biyunta.


Suna dawowa sallan isha Ahmad da Habu sukayi cikin gida.
Da sauri Habu ya tsaya, cikin mamaki yace.
"Ya Ahmad kalli can."
Da sauri Ahmad ya isa wurin da Habu ke nuna mishi, ganin
kayan lefen Zaleeha ne da aka kawo jiya watse aƙasa, setin gaba ɗaya akwatuna 30 dasu tarkacen gishiri da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login