Showing 162001 words to 165000 words out of 177664 words

Chapter 55 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete by Garkuwa .txt

06 Dec 2024

7788

goro duk an watsosu waje,
cikin tsananin Al'ajabin halin Mama da tsaurin ido irin nata yace.
"Innalillahi! Habu tayani mu kwashesu, tunkan Baba Malam yazo yagani, nasan bazaiji daɗi ba aransa ba."
Da sauri suka fara tattara kayan, sai kuma duk suka tsaya tare dayin shiru, sakamakon jin muryar mahaifinsu ta window parlour'n shi.


"Ku barsu a wurin ko tsinke kada ku ɗaga, ku wuce ku bar wurin."


Shiru sukayi cikin tsananin tarin damuwa dan dagajin muryar Baba malam yana cikin tsananin baƙin ciki, muryarshin ce ta katse musu tunanin da sukeyi.
"Ku bar wurin ko nace!." ya ƙarishe maganar cikin bada umarni irin na fusata.
Da sauri sukace.
"Toh".
sannan suka juya, kowa ya nufi ɗakin mahaifiyarshi.


Gefen Mamy Ahmad ya zauna cikin ƙunan rai yace.
"Please Mamy kije ki bawa Baba malam haƙuri, naga ranshi ya matuƙar ɓaci, kice yayi haƙuri ya barmu mu kwashi kayan, in yaso mushigo dashi nan ɗakinki."


Murmushi Mamy tayi tare da cewa.
"Hmmm Ahmad ai wannan ba hurumi na bane,
ku bar kayan kamar yadda ya umarceku,
Mamanku ta zauna da Malam kusan tsawon shekaru 30 kenan yau, amman har yau bata san waye Malam ba, bata taɓa ƙureshi ba,
amman da dukkan alama yau zata san kaɗan daga cikin halaiyarsa, idan ransa ya ɓaci,
shi acikin ruwan sanyi zai dafata."


Jin haka yasanya Ahmad cewa.
"Hmmm kai Mama tanada matsala Wallahi, mutum duk haƙurinshi sai ta ƙureshi."


"Kaje kaci abinci ka dena zama da yunwa."
Mamy ta umarceshi cikin son kauda zancen, kasancewar bata son tayi mgnar kishiyarta, dan wannan shi ke ɓata alaƙar zuciyar yaro da matar ubanshi.


Ƙarfe tara dai-dai Mama ta shiga parlour'n Baba Malam, tare da yin sallama can ƙasan maƙoshi, ta yadda shi baima jitaba.
A kan kujera ta sameshi zaune ya zubawa TV idanu yana kallon BBC News.
Kan dinning table ta kai dubanta, gani tayi yanda ta ajiye abinci, yana nan ayanda yake, da alama babu wanda ya taɓa ko food flask ɗin bare akai ga ci,
juyowa tayi ta maida kallonta kan fuskarshi da ta ɓoye ɓacin ransa,
ta sani koda bazaici abinciba to tabbas zaisha tea,
dan haka taku uku zuwa biyar ne yakaita gaban dinning area,
cup ta ɗauka sannan ta haɗa mishi tea kamar yadda ta saba,
a hankali tazo ta ajiye mishi cup ɗin a kan table ɗin dake gabanshi, wanda yawanci nan yake miƙe sawunshi idan yana zaune akan kujera.
danne ɓacin ranta tayi dan yanzu so take ta gwada kirsa tunda taga hayagagar bata kamashi,
gefenshi ta zauna tare da cewa.
"Ga tea ɗinka nan nahaɗa ma kada yayi sanyi."
shiru yayi baice ƙala ba, ganin yadda yayi kamar babu wani mahaluƙin dake kusa dashi, yasanya
cikin tsareshi da ido taƙira sunanshi.
"Malam!."
Baima juyo ya kalleta ba bare tayi zaton ko zai amsa mata,
saima kaɗa ƙafafunshi da ya farayi a hankali.
shi kuwa wani irin tafarfasa zuciyarsa keyi,
yadda tazo tayi ta mishi ihu da haushi a kanshi gaban yaranshi da uwar gidanshi, shine ke ƙara ɓata masa rai, sam bata sa hankali da nutsuwa cikin lamuranta.
Kusa dashi ta kuma matsowa tare da cewa.
"Malam magana nake so muyi da kai fa."
Bai bi ta kantaba bare ya saurareta saima ƙara volume ɗin TV da yayi.
Cikin takaicin abin tace.
"Ya kamata muyi magana ta fahimtar juna,
a bani matsayina da damata a matsayina na uwar yarinya,
ni nasan Zaleeha bata son wannan nakasasshen, ta tsaida gwaninta, harma ta bashi daman ya turo komai na aure, tunda dama iyayenshi kam sun zo kuma ka sansu ba baƙin fuska bane,
d'an manya ne gaba da bayansa."


Gum yayi mata tamkar dutse,
ita kuwa sai surutai takeyi uwa aku,
ganin an gama labaran ne ya sashi,
miƙewa tare da kashe TV sannan ya nufi bedroom ɗinsa,
da sauri tabi bayanshi tana Magana, bai kulata ba, haka ya shiga bathroom,
ruwa ya watsa sannan yayi al'wala kana ya fito.
A bakin gado ya sameta tana zaune,
shi kuwa shirin bacci yayi kana yazo ya tsaya gefenta, da hannu ya nuna mata hanyar fita alamun ta fice mishi daga ɗaki,
fuska a tsuke tace.
"Muyi maganar tukun!."
Fuska ya kuma tsukewa wanda saida taji gabanta ya ɗan faɗi, yayinda zuciyarta kuwa ta buga da ƙarfi,
hanyar fita ya kuma nuna mata,
da sauri tace.
"Dan Allah, dan darajar ma'aiki kayi haƙuri ka buɗi baki muyi magana."
Ido ya rumtse dan ya rigada ta haɗashi da Allah.
Itama sanin in dai ta haɗashi da Allah zai saurareta ne ya sata yin hakan.
cikin kaushin murya da haɗe fuska zuciya na tafasa murya a zafafe yace.
"Kije ki kwashi kayan da kika watsar ɗin ki maidasu ɗakinki ki ajiyesu yadda kika samesu."
da sauri tace.
"Dare yayi fa."
A kausashe yace.
"Baza kuma su kwana a waje ba."
Cikin sanyin jiki tace.
"To bari in ƙira Habu yazo ya kwashesu."
A ƙufule yace.
"Waya fito dasu?."
Kai ta juya tare da cewa.
"Ni ce."
Cikin bada umarni yace.
"To kije ki maidasu kizo muyi maganar."
Bata da zaɓi dan ta san kaɗan kenan daga halinshi dole taje a daren ta kwashi kayan,
ta maidasu cikin ɗakinta,
tana gamawa a gajiye ta koma ɗakin nashi, a kwance ta sameshi cikin maida numfashi tace.
"Na maidasu. Ka tashi muyi maganar."
Kai ya jujjuya tare cikar haiba da isa da gidanshi yace.
"Maganar ai na gamata babu wani wanda zan aurawa ɗiyata Zaleeha sai Saifuddeen, kuma babu wani mahaluƙin da ya isa hanani sai ubangijin daya halicceni!."
Yana faɗin haka ya gyara kwanciyarshi tare da rufe ido alamun bacci zaiyi.


Cikin tsananin takaici haɗi da ƙunci tace.
"Ni kuwa Wallahi ƴata bazata auri gurgu kuma kurma ba, ɗiyata bazataje ta zama majinyaciya ina kallo da idona ba, sannan bazan taɓa bari takashe rayuwarta wajen kula da nakasasshe ƙaskantacce ba, Allah ya sauwaƙa ma, ni dai ajinina ban haifawa nakasashshe matar da zai aura ba ehe!!."
Tana gama faɗin haka ta juya ta fita a fusace.
Gyara kwanciya Baba Malam yayi tare da rufe idanunsa, sunayen Allah Kawai yake ambata acikin ransa.
***


Washe gari kuwa Zaleeha daga gidan hajja Inna ma'aikatarsu ta nufa, bayan ta gabatar da shirinta na mushaƙata kai tsaye gidansu kuma ta nufa.


A harabar gidan tayi kiciɓis da ya Ahmad,
cikin shaƙuwarsu ta nufi inda yake, da alamun cewa shima yanzu shigowarsa cikin gidan.
hannunshi ta kamo tare da cewa.
"Ya Ahmad nayi kewarku kwana biyu bana nan ko kuyi cikiyata."
murmushi yayi tare da cewa.
"Muma munyi kewarki, kin san inata shirin tafiyarmu ne,
naso in wuce da Lubna amman Mamy tace wai in bar miki ita."
tsalle tayi cikin jin daɗi tace.
"Yessss! My mamy kai amman ko naji daɗi sosai!!."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ato ai dama amare yan jin daɗine."
Sam bata kawo komai a rantaba da jin furucinsa,
sai sakin hannunshi da tayi lokacin da sukazo dab da ƙofar Mama, cikin alamun gajiya da kuma yunwa dake damunta tace.
"Yauwa Ya Ahmad bari inje inyi wanka sai inzo muyi hira, ka cewa Aunty Lubna ta gasa min abin daɗi yunwa nakeji, please ko roasted fish nema nasamu idan nazo."


"To." Kawai yace tare da juyawa yayi side ɗin Mamy.


Ita kuwa Zaleeha da sallama ta shiga,
da sauri ta kutsa kanta cikin parlour'n, saboda hango Mamanta na zaune fuskar nan a kumbure alamun tsananin fushi,
da sauri ta durƙusa agabanta cikin tsoro tace.
"Lafiya kuwa Mama? Meya sameki? baki da lfy ne?." Duk tayi mata tambayar cikin kulawa, irin wacce ke tsakanin Ƴa da Uwa.


Cikin tsananin takaici Mama ta watsa mata harara tare da cewa.
"Ae naji ke har dariya ma kike ko? yayinda ni kika barni ina nan baƙin ciki da ɓacin ranki zasu haɗu su kasheni!."


Cikin zaro ido haɗi da tsoro tace.


"Na shiga uku Mama me nayi miki?."


A hasale Mama tace.
" kikamin ko kikayiwa kanki."
Sai kuma ta miƙe tsaye tare da watsawa Zaleeha wani irin mugun kallo.
Sannan tayi cikin bedroom ɗinta, wanda idan ba doleba, sam bata son shigarsa, saboda idan taga wannan kayan ji takeyi kamar ta faɗi ta mutu, tsabar baƙincikin dake cika zuciyarta.


Da sauri Zaleeha ta bita,
a gaban Maman ta tsaya, cikin raunin murya tace.
"Mama kiyi haƙuri in na miki laifine ki gaya min Wallahi bazan sakeba!."


Azafafe ta nuna mata tarin akwatunan wanda ita sam bata gansuba sai yanzu cikin kakkausan murya tace.
"Kinyi asara Zaleeha, Wallahi kinyiwa kanki sakiyar da ba ruwa, ki rasa wanda zaki zaɓa duk cikin masoyanki sai wannan banzan nakasasshen da baya ji baya magana, uwa uba kuma baya tafiya, ki zaɓeshi matsayin miji har zaki bashi dama ya turo iyayenshi su kawo tarkacensu harda su sadaki,
wato kin maidani shasha naje inata haushi ashema ban saniba kece kika amince mishi sai ɗazu Habu yake sanar min."
Mama fa bata tsagaita da masifaba bare tasan halin da Zaleeha ke ciki.
sai Zahira ne ta zaro ido da ƙarfi ganin yadda Zaleeha tasa hannu da tsananin ƙarfi ta kama kanta,
yayinda tuni kunnuwanta sun toshe tun lokacin da Mama tace mata an kawo sadakinta kuma wai ga kayan aurenta a gabanta,
sannan wai da yardarta uwa uba kuma wai da wancan ginannen taɓon ne da Allah ya ƙawatashi da kyan sura,
daga nan bata kuma jin zancen Mama ba, sai rumtse idanunta da tayi tare da cilla wani irin gigitaccen ƙara mai tsananin ƙarfi, haɗe da cewa.
"Ƙarya ne banice na turo shiba, bana sonshi! bazanyi aureba Wallahi, bazan zauna da kowaba sai wanda ya taimakeni!!."
Sai ta kuma buɗe idanunta, wanda sukayi jazir ta kalli tarin akwatunan, wani irin gigitaccen ƙara ta saki wanda yasa,
Ahmad, Habu,Aunty Lubna da suka nufo parlour'n maman tun ihunta da sukaji na forko ya sasu shigowa a guje,
suna shiga ita kuwa zaliha ta yanki jiki ta faɗi sumemmiya.


Da sauri Ahmad ya tarota ta faɗa jikinshi,
cikin rawan jiki murya a hargitse yake ɗan jijjigata tare da marin kumatunta yana faɗin.
"Zaleeha! Zaleeha!! Ki tashi Zaleehaaa!!!."
Sai ya kuma kalli Zahira daketa kuka tana cewa.
"Shike nan ta mutu, tace muku bata son auren ba wanda take so ku barta ta jira wanda takeso anƙi gashi yanzu baƙin ciki zai kasheta.
Mama kuwa da sauri ta juya ta nufi falon Baba malam tana shiga tasa kuka tare da cewa.
"Shike nan baƙin ciki zai kashe min ƴata,
in ta mutu ai kowa ya huta sai a kaiwa shashashan musakin gawanta."


Shiru Baba malam yayi sai murmushin da yakeyi, Mamy kuwa da sauri ta miƙe zata nufi side ɗin Maman,
dan da fari da suka jiyo ihun Zaleeha sunyi zaton ko uwarce ke dukanta, shiyasa data yunƙura zata je Baba malam ya dakatar da ita.


A can ɗakin Mama kuwa a kiɗime Lubna ke cewa Ahmad.
"Hubby a sume take fa, ko dai da gaske al'jani ne ya taima keta shine yau zasu baiyana kansu? Hubby mu kaita wurin Baba Malam!." Tafaɗi maganan cikin tsananin ruɗewa.


Yunƙurawa Ahmad yayi da ita a jikinshi, fita yayi da matsanancin sauri ya nufi parlour'n Baba Malam,
a bakin ƙofa sukayi karo da Mamy.
Cikin tsoro da firgitan ganin Zaleeha kamar gawa Mamy tace.
"Malam da gaske Zaleeha ba lfy."
Shi kuwa Ahmad a gaban mahaifin nasu ya direta tare da cewa.
"Baba malam al'janine fa a jikin Zaleeha da gaske danfa kawai taji batun auren ne yasa ta suma."
Habu ne yaja wani dogon tsaki tare da cewa.
"Ya Ahmad meyasa kake yarda wai Zaleeha iska gareta?."
Cikin tsawa yace da Habu.
"To in ban yarda tanada iskaba meya sumar da ita?
please Baba malam ayi mata ruƙiyya ko al'janin zaiyi magana."


Cikin takaici Habu ya juya gaban fridge ɗin dake gefenshi, buɗewa yayi tare da ɗaukan goran bottle water mai ɗan karen sanyi,
kana ya juyo marfin gorar ya murɗa kana ya ziraro da bakin gorar dai-dai saitin fuskar Zaleeha ya fara tsula mata ruwan sanyin.
Wani irin wawan ajiyan zuciya taja, me ɗauke da azaban ƙarfi kana ta fizgo numfashinta da wani zazzafan kuka,
cikin kuka mai cin rai ƙuna da kuma tsananin tsoro take cewa.
"Bana sonshi Ya Ahmad ka gayawa Baba malam wallahi bana sonshi na tsaneshi!."
Sai ta kuma kamo hannun Ya Ahmad ɗinta da tuni ya fara zubda hawaye, cikin kuka taci gaba da cewa.
"Ya Ahmad ka gayawa Baba malam mana,
ka faɗa mishi cewa gurgu nefa haka kuma kurma ne, kace mishi bana sonshi na tsaneshi,
wallahi in aka aura min shi zan mutu wlh ya Ahmad mutuwa zanyi!!!." Taƙare maganar cikin wani irin kukan fitar hayyaci.


Habu ne ya watsa mata wani zazzafan harara tare da cewa.
"To ki mutu mana! In kin mutun sai me? Ko kina zaton mutuwarki zaisa muma mu mutu ne?."
Faɗawa jikin Aunty Lubna dake raɓe agefe tana zubda hawaye tayi, cikin kuka da raunin murya tace.
"Wayyo Allah na Aunty Lubna ki taimaka min ki faɗa musu inada wanda nake so, kice musu wlh bana son musakin can."
Cikin rauni Ahmad ya kalleta murya a tausashe yace.
"To meyasa kika ce mishi kin amince dashi ya turo iyayenshi tunda kin san bakya sonshi?."
cikin kiɗima da gigita tace.
"Wallahi ban faɗaba wlh ƙarya yake min, to shida kurmane ta inama zaiji abinda zance mishi?."
cikin hatsala Habu yace.
"Ba text messages kika tura mishi ba, da wayarki."
Miƙewa tayi a hargitse ta kalli Mahaifinsu da ya zuba musu ido, yana murmushin ganin ƙuruciyar yaran nashi, ba abinda ke sashi murmushi kamar yadda Ahmad yake taya Zaleeha kuka kamar yaro,
yana jin daɗin zafin Habu dan yasan Habu Baban ya Aminu ya gado yayan Baba malam kenan,
cikin kuka Zaleeha tace.
"Wallahi ƙarya yake min ni bani da number shi ma."
Mama ce tayi kaffa tare da jan dogon tsuka.
Habu kuwa falon Mama ya koma,
jim kaɗan sai gashi da wayar Zaleeha riƙe a hannunshi,
cikin takaici ya cire wayar a key dan yasan komai na wayar, hakan kuma tsarinshine dan bincikar woyoyin ƙannenshi yasa su duk yasan komai na wayarsu.
kai tsaye inbox nata ya shiga ai kuwa text biyar ya duba, ana shida sai ga text ɗin gama number shi da Saifuddeen yayi seven da My happiness.
Cikin zafin rai ya nuna mata wayar tare da cewa.
"Meye wannan?".
Ido ta zaro gaba ɗaya, ganin abinda ke rubuce da kuma haƙiƙa ita ta rubuta, kuma ta turawa number da aka sawa suna da my happiness, sai kawai ta miƙe ta koma can gefe nesa da mahaifin nasu ta fara buga tsalle tare da yarfa hannu tare da kurma ihu kana tana cewa.
"Sharri! Sharri!! Sharri!!! Sharrine yayi min wallahi ƙarya ne ni bana sonshi!!!."


Ganin yanda takeyifa yasa Baba malam yin wani murmushi mai kama da dariya.
Saura kuma gaba ɗaya ido suka zuba mata.
Habu kuwa belt ɗin ƙugunshi ya zaro tare da yin kanta.
ai fa tana ganin haka ta juya a guje tayi cikin gidan, shi kuma ya mara mata baya a guje,
radadada kake jinsu a guje.
ganin yadda Habu ya bita yasa Ahmad binsu da gudu hakama Aunty Lubna da Zahira.


Zaleeha kuwa gudu take da iya ƙarfinta dan tasan Habu ba mutunci ne dashi ba. In ya kama duka kamar mara imani.
Kai tsaye ɗakinta ta shiga cikin sa'a ta samu ta maida ƙofar garam ta rufe,
tun kafin ya iso,
ganin haka yayi kwaffa ya juya tare da cewa.
"Yar iska kawai da ki tsaya mana."
Ita kuwa a cikin ɗakin wani irin fitininan nen kuka tasa da iya ƙarfinta, tana kuka da surutai cewa.
Ita dai bata sonshi ta tsaneshi zata mutu in an aura mata shi.
Ahmad kuwa da Lubna rarrashinta sukayi tayi da bata baki amman ina.
ranar haka ta kwana a rufe tana kuka da al'washin ciwa Saifuddeen zarafi.


Mama kuwa sosai taji daɗin abinda Zaleeha tayi,
ta kuma yi niyar yaƙi da wannan auren.


Ƙarfe takwas dai-dai na safiyar ranar asabar Zaleeha fito cikin d'akinta inanun ta a kumbure tayi ja alamu tayi kukan mai yawa.
gefen Mamanta ta zauna cikin sanyi tace.
"Ina kwana Mama".
"Lfy."
ta bata amsa a tak'aice.
kai ta d'an sunkuyar ida nunta cike da hawaye tace.
"Mama wlh k'arya yake min sharri ne, ni bance ina sonshi ba." kai Mama ta gyad'a mata cikin alamun gamsuwa tace.
"To yanzu ya zakiyi?."
cikin k'arifin hali tace.
"Zan yi mgnin abun in sha Allah shida kanshi zai dawo yace ya fasa."
Cikin jin dad'in Mama tace.
"Ke dai ki kafa ki tsare cewa bakya sonshi ni kuwa zan san abinda zanyi a kai."
To tace kana ta kira Zahira tare da cewa.
"Je parlour Baba Malam ki d'auko min wayata".
Juyawa tayi ta nufi bedroom d'in Mama tare da cewa.
"Gashi nan na d'aukoshi tun jiyan ai."
Amsar wayar tayi kana ta koma d'aakinta.
Ita kuwa Mama murmushin jin k'arfin guiwa tayi tare da cewa.
"Bazaki auri gurgu ba kam ko kina sonshi zan hana kuma wlh bazan bari kiyababanki boyayya kan arennamba dole zanyiwa boka bayanin yadda nake son yasa ki bijirewa wannaɓin da BAban naki ya miki, don ko sama zata had'e da k'asa zaki auri Abdussalam dan shine dai-dai dake."
Tana kaiwa nan ta kira wayar Abdussalam yana d'agawa suka gaisa kana tace mishi,
ya had'o komi da komai na aure ya turo iyayenshi Zaleeha ta yarda dashi.


Jin haka yasa Abdussalam jin k'arfin guiwa nanfa yaci gaba da shirya lefenshi dai-dai da matsayinshi.


Ita kuwa Zaleeha konciya tayi kan gadonta sannan ta fara rubuta text kamar haka.


```Kai baka cancanci inyi makasa sallama ba, domin ita sallama ta masu amincine ba mak'aryata azzalumai irinka ba. nace maka bana sonka na tsaneka bazan soka ba har abadan,
dan haka kayi maza ka turo wad'anda ka aiko suka kawo wannan tarkacen suyi maza su zo su kwashe gaiyar dukiyarka```
murmushi tayi lokacin da ta tura text d'in a ganinta ta k'unsa mishi bak'ak'en maganganu.


Saifuddeen kuwa yana zaune bisa kujerar wheelchair d'inshi Amman a dinning table,
Ummi na had'a mishi tea yayinda yake cin soyayyan doya da kwai,
jin wayarshi dake cikin al'jihunshi ta bashi wani alamun sak'o ya shigo kamar bazai duba ba,
sai ya kuma zaro wayar ganin number tane ya sashi yin murmushin mugunta dan yasan,
Kwanan zancen.
ganin yanata murmushi Ummi yin murmushi dan farin cikinsa shine nata.
Raliya kuwa da Hayatuddeen suma murmushin suke tayasu.


Bai bud'e text d'inba saida ya koma side d'inshi sannan ya bud'e ganin abinda ta rubuta ne yasashi yin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login