Showing 15001 words to 18000 words out of 36457 words

Chapter 6 - Deejamah Part 1 Complete Hausa Novel By Fatima Zahra Lawan.txt

kuskura kizomin Babu mijin Aure,sai da Shakeerah tasaka space dinta sannan ta'aje jakanta tataso ta matso har gabansa tace"Baba Ayuba idan nadawo ka koreni gabadaya sandarewa sukayi taja motarta tayi gaba.
Sai Bayan tafiyanta yaketa zage-zage Kan wai Shakeerah ta rainasa,Babu wanda yatanka masa sai abokin haushinsa baba sani.




Sai wajen 6 ta Isa gida gate din fulani tashiga da motarta,fitowa tayi a gajiye ta nufi hanyar part dinsu,sai dai Jin hayaniya a part din fulani yasata juyowa ta nufi hanyar part din.
_I NEED UR COMMENT_








Xahratty ce✍🏽
Lallai Alqalami🖋️Yafi takobi🗡️
💕💕
❤️
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨
( Daukar Fansa )








Story& writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
______✍🏽______








*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah))


*_T.W.A_*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_________________________




Marubuciyar⬇️


_ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_




*DA*


_ _MIJIN ZAHRA_




*Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.*






Bismillahir-rahmanir-raheem.




*Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai*....






Page:1️⃣6️⃣--1️⃣7️⃣






___________A haka rayuwa ke tafiya gaskiya Abba yabar dukiya sosai munsamu,a gefe daya na adana files dinda Abba na ya bani ajiya.


Rayuwa muke mai cike da farin ciki fulani kuwa tazama tamkar wata step mother dita,tanamun Abu irin na da da mahaifi tana bani kulawa,har yau ban taba haduwa da family dinta ko daya, business din Abban mu tasamu wani Mai Amana tadora shi akai muna cemasa Abba kabeer Yana kula da dukiyar mu damu kammu,taso Auren Ammi ta dakatar dashi tunkafin tafiya tayi nisa domin bazata sake aure ba tace,zuciyarta kuwa tace Abba yariga yatafi dashi Babu yanda za'ayi wani yasamu makwafin zama.

Lokacin Exam yazo muka yi jarabawar fita daga secondry,jamb nafara Alhamdulillah nasamu score masu kyau domin nafita da 240 wannan DALILIN yasa fulani tabani gift dinta ba komai tabani ba sai mukullin mota hadaddiya kirar KIA gata derk Ash sosai.
Nayii waec da neco dama A.B.U da KASU da B.U.K nacike.


Koda nagama Suma gaba daya na cinye don haka fulani tasama mun gida a kaduna na sannan aka nema mun add mission a kASU na samu.


To wannan shine cikakken tarihina,yanzu kuwa kusan wasan zai fara diamond ladies.
Su Fauzi sukace haka ne,gaskiya Shakeerah kema Kinga rayuwa Amma tunda duk kanmu zamuje weekend gida mu Bari mudawo sai asan abinyi.


Shakeerah tace"hakane to aini da khadee gari Daya zamu.
Fauzi tace"hakane kuwa na manta ba 'yar bauchi bace da mun jera.
Dariya khadee tayi Tace"Hakane to babe's yanzu sai mun dawo tukuna za'ai solving din matsalolin mu?
Shakeerah tace"Har sai mungama Exam ma domin bazamu hada karatun mu da matsalarsu ba,matsalar fah ba karama bace Dole muna bukatan kwakwalwarmu tayi caji domin muna bukatan temako.
Gabadaya suka hada baki wajen fadin"hakane daimond love Dole mudauki fansa,a dade anayi sai gaskiya.




Sosai suka mai da hankali wajen karatun su,weekend kuwa ya zagayo da yake duk ranar Friday suke tafiya gida sannan paper daya sukayi,shiri suke sosai duk cikiansu.
Sai da suka fara zuwa suka saka Fauzi a motar gombe sannan su sukayi Zaria sai wajen seven suka iso,direct Shakeerah tudun Wada takai khadeee Bayan ta sauketa,ita kuma ta wuce gaskiya.


A dai-dai randar agwaro wani Mai mashin yazo da gudu saura kiris ya buge Shakeerah da Mutane da dama ma,juyowa yayi yafara zage-zage Wai ana ganinshi ba'a kaucemai ba gaba daya ya hada goslow 'yan kasteliyan dake wajen duk sunkasa tabuka komai Wai Dan daba ne kada mutum yayi maganar ya Burma masa wuka.


Cikin bacin Rai Shakeerah tafito daga cikin motar ta,tsiya tafara yimai akan hada gaslow din da yahada,Aiko dama jiran Mai tankasa yake,Nan kuwa yafara duddura ma ta zagi Wanda ko jare bazai ciba.


Ranta ne yagama baci Aiko ta bashi punch a hanci,ihu yasa yakuwa zaro wuka yayo Kant dashi da niyyar cakamata a ciki,aikuwa Allah yabawa Shakeerah sa'a ta samu hannun ta murde har Sai da wukar ta Fadi,sannan ta murde hannun sai da ta balle Tace kassss!
Da yawon mutanen wajen mamamki suke yaza'ayi wannan 'yar ficiciyar yarinyar nan tayi fada da shago?nan kuwa akadinga murna ansamu mai cin ubanshi.
Ihu sosai shago yakeyi Yana Bata hakuri domin kokarin karya dayan hannun takeyi dubanshi tayi cikin fresh voice nd sweet Colin natsuwa tace"Meyasa Mutane Sam basu da tunani ne son zuciya yayi yawa a gari inbanda haka baka da wani isashshen sana'ah,makarantar bayi kuke ba sai dai zaman banza da neman magana agari inbanda haka Meye naka na Tara dubban jama'ah haka ,kaduba Mana,tayi maganar tana nuna masa mutanen wajen.
Muryansa na rawa yace"don Allah kiyimun aikin gafara ki yafemun don Allah.
"Ni daka ganni am simple kanemi gafara da yafiyan wadnda kataba yimawa ne but ni Babu abinda kamun a yanzu,fatana dakai kanemi abin yi ka natsu kasan Allah ya faku.
"Insha Allah nayi Miki alkawarin zan shiryu da yardan Allah to jirani,Shiga motar tayi ta dauko Masa kudi dubu goma casss tace"yaje yayi magani,mutanen wajen kusan Rabi duk sai da tabasu sadakan dubu biyar-biyar sannan taja motar ta tayi gaba.
Wani yadaga murya a cikinsu yace"Yarinyar Alhj Muhammad Adali ne,Aiko nan akkafara yaban mahaifinta akadinga Masa addu'o'i,ita Kuma akadinga sa mata albarka.




A gajiya tayi hon a bangaren su ta Shiga cikin Falon tundaga Nan tafara Jin ana ta hayaniya kamar muryan baba Ayuba taji, jitayi yana cewa"don munafunci irin naki algun guma kin hau dukiyan Dan uwan mu kinyi kane-kane dashi kin dauki fitsararriyar 'yarki kin sakata a makaranta makaranta ko karuwanci? Baba Sani yace"Ayuba bama wannan ba abin da ke bamu mamaki yanda ta maidamu kamar almajiranta idan munason wani Abu sai munzo mun tambayeta,to baki Isa ba banza tsintacciya kawai,tsintacciyar mage,dama ance tsintacciyar mage Bata mage......Cike da bacin Rai Shakeerah ta buga kofan falon duk cikansu suke duban ta Ammi kuwa kuka take ganin Shakeerah yasa cikin Sauri ta goge tears din, Shakeerah tace"ai gwanda tsintacciyar mage Akan wasu masu iyayen domin ku naku matan Babu abinda suka Sani sai duddura muku bakin ciki,na rantse da Allah duk Wanda yasake batawa mahaifiyata Rai sai na ci du........Ammi tace"ke ke ke Shakeerah.
Cikin bacin Rai Shakeerah tace"Ammi don Allah kiyi shiru,har yaushe su baba Sani da baba Ayuba zasu Dena cimmiki Kashi kina shiru?wa billahillazi bazan dauka ba Ni sai na yiwa mutum rashin mutumci.
Saria su baba Ayuba sun San halinta yasajikinsu na rawa suka bar gidan.


Nan Ammi tayiwa Shakeerah ta tas sannan Tace tashirya taje tabawa 'yan uwan babanta hakuri.
Da toh Shakeerah ta'amsa ma Ammi bawai Yana nufin taji ba,sannan tasake bawa Ammin tata hakuri.


Shiryawa tayi cikin wani Riga da wando Pakistan purple nd white gaskiya Sunyi Mata kyau sosai part din fulani taje gaisheta,ta cidda mota a harabar gidan hannunta rike da foodflask ne a hannunta da sallama ta shiga falon wata mata tataras a zaune a zaune mai Kama da Goggoji duk cikansu da fara'a suka dago suna duban Shakeerah,fulani tace"A'ah Shakeerah ur welcome,da Murmushi ta Isa wajen gaida fulani tayi sannan tagaida bakuwar,amsawa tayi face nata dauke da Murmushi aje foodflask tayi tace"fulani ga alalen inji Ammi.


Murmushi tayi tana jawo cooler din ta bude"Wow Masha Allah fulani tafada,ita kanta bakuwar hadiye miyau tayi,duban matar fulani tayi tace"Kinga Shakeerah jikata jikan arziki.
Shakeerah wannan 'yata ce itace ta hudu.
Murmushi Shakeerah tayi tana kallon matar tace"Allah sarki ai Ina ganin ta naga kamar ku,mikewa tayi tashiga kitchen ta dauko mata roban wanke hannu da plates biyu da spoons,duk cikansu suka wanke hannnayen sannan matar tazuba ma fulani abinci itama ta zuba nata.
Shakeerah tace"Fulani n atafi zanje kasuwa.


Fulani tace"Toh Shakeerah Sai kin dawo,fita tayi ta nufi part dinsu.
_I need ur comment_








Xahratty ce✍🏽
Lallai Alqalami 🖋️ Yafi takobi 🗡️
💕💕
❤️
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨
(Daukar Fansa)







Story&writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
_______✍🏽_______




*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tamvarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah))

*T.W.A*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_________________________




Marubuciya:-
_ *A DALILIN 'YAR TSUNTUWA*


_ *MIJIN ZAHRA*

*ND*
*NOW*
*DIAMOND LADIES*
(Daukar Fansa)




*Littafin diamond ladies (Daukar Fansa)na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari 100 na waya ta wannan number 08060719719,sai nayi adding dinsa a group din*




Bismillahir-rahmanir-raheem.


*Da sunan Allah mai rahama mai jin kai....*






_FREE PAGE_




Page:2️⃣2️⃣--2️⃣3️⃣🖊️






__________Mezai hana muhada wannan yarinyar da Jalaludden Aure?duk cikansu suka ce Eah,tadai Hjy Kaltume tana ta kallon su,hjy shamsiyya tajuyo tace"Aunty Kaltume ko a kika gani? Hjy Kaltume tace"hjy shamsiyya idan matanshin ce ita Allah ya Sanya alkhairi.
Hjy shamsiyya ta dubi fulani tace"fulani to kefah? Fulani tace"tun Ranar da na fara ganin ta nayiwa Jalal sha'awar ta a matsayin mata.


Hjy shamsiyya tace"to Alhamdulillah abun kam yayi kyau sai ayi zaman meeting na musamman koh? Gaba dayansu su suka amsa da Eah,cigaba sukayi dacin dambun naman zabin da kunun ayar sai Santi Sukeyi,suma su Alhj kabeer ba'a barsu a Baya ba,domin suma sunci.


Washegari Shakeerah da sassafe da wuri ta nufi kd domin suna da Exam da karfe takwas da Rabi, direct KASU ta wuce,tayi mamaki matuka na ganin su Fauzi,nan sukayi Exam suka fito,nufar capteria sukayi don zuwa susha coffee.


Nan fa aka dasa hirar yaushe rabo,Baya sun sake fitowa Exam suka wuce gida,a lokacin da suka Isa a zahar yayi,don haka suka gabatar da sallar da ke kansu.


Shakeerah taciro musu dambun naman da Ammi ta hada musu,cike da farin ciki suka fara ci Fauzi tace"Wallahi Shiyasa nakeson Ammi domin ita din akwai kula,khadee tace"kedai bari,kunsan matsalar da nake fuskanta kuwa diamond ladies?
Cikin Sauri suka girgiza kai tare da mai da hankalin su kanta khadee taci gaba"Hmmm kannena yaran amaryan Daddy gaba daya anwayi gari sun rasu,biyu a ciki mata ne duk an kwakule musu Ido,dayan na miji ne anyanke masa joyst*ck nasa.


"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un su Shakeerah suka ambata ita da Fauzi,Fauzi tace"gaskiya khadee matsalar ki yakamata a fara warware wa yanzu,domin bai kamata a bar Daddy yana cigaba da wannan aika aikar ba.
Shakeerah tace"haka ne nidai a bangare na matsala daya ne wanda Kuma bazai yuwu ba,duban ta sukayi suna cewa menene matsalar?
A jiyan zuciya Shakeerah ta sauke tace"a cikin mu biyu nida ke fauza sai wata ta auri Daddy,duk cikansu su a firgice suka dube ta,tace"Yes ta haka ne kawai zamu iya cimma burin mu na daukar fansa a wajenshi babu wanda zai iya hakan sai makusan cinshi,wato matar shi,zufa ne yafara kwararo musu.


Yake Shakeerah tayi tace"Diamond ladies ku kwantar da hankalin ku lokaci yayi da zamu fara daukan fansa fa nasake jaddada muku,idan dame mgn Ina saura ransa.


Khadee tace"Shakeerah wannan shawarar ba me yuwuwa bace gaskiya yakamata a canza ta a memi wani.
Duban khadee Shakeerah tayi tace"Yaushe ne akayi rasuwar? Khadee tace"jiya ne Wallahi.
Shakeeerah tace"to Kingani,abinda za'ayi shine insha Allah yazama wajibi wannan week end din muyi shi a gidan Daddy.....duk cikansu su a firgice suke duban ta,bakin Fauzi na rawa ta dubi Shakeerah tace"Shakeerah kada kiman ta Daddyn khadee nada matukar hadari.


Shakeerah tace"yess I know but hakan shine mafita,pls kada kuman ta taken mu mana,mun day alkawarin daukan fansa ga duk wani azzalumi,Muddin bamu cire tsoro a zuka tanmu ba to tabbas Babu yanda za'ai mu cinma buri kanmu,mudai musa Allah Daya a zuciyan mu,kuma Yana tare damu a duk inda muke, duk cikansu suka ce hakane kam.
Mikewa Shakeerah tayi ta nufi dakinta don gyarawa sai dai ko da tashiga taga dakin fesss Banda kamshin turare babu abinda yake,juyowa tayi face data dauke da smile Tace"Wow dakinfa yayi kyau ngd muku sosai diamond ladies domin nasan mutum guda bazata gyaramun daki ba sai guda ta hadaka,suma murmushin suka mai da mata.
Cigaba sukayi da zuwa school, yanzu Exam saura 1week su gama cikin ikon Allah suka shirya Ranar friday ita da Fauzi don tafiya bauchi,da yake duk after 2 weeks suke zuwa week end shiyasa wannan week din nan bazasu gida ba,sun samu damar zuwa bauchi.


A motar Shakeerah suka nufi garin bauchi Cike da kewar khadee,sai dai sunja mata kunne akan fita tinda da komai a gida pls kada tafita ita kadai har sai sun dawo.




Tun 7:00am suka fita Basu Isa ba sai 5:00pm,a gajiye suka Isa gidan Daddy tabbas gidan sa abun kallo ne sai da suka tabbatar da gidan Alhj Sani Bukar Mai Iyali ne sannan suka kutsa kai cikin gidan bakinsu dauke da addu'an shiga gida" _bismillahi walajna wa bismillahir-rahmanir-raheem kharajna wa'alallahi rabba na tawakkal na_,sannan suka shiga yanacan sama yana hangen su,zumbur ya mike don 'yan matan sun Gama tafiya da imanin sa,duk abinda yakeyi Shakeerah na ankare dashi.
Direct dakin Mai gadi suka nufa,tambayar shi sukayi ko yasan part din hjy saddiqa? Amsawa yayi da Eah yasani,ya nuna musu wani part yace gashi can shine nata.
Shakeerah tayi wani makirin Murmushi tace"pls idan Babu damuwa zanso ka hadamu da ita wato Kai Mana iso gareta.
Diddilo idanuwa Mai gadi yayi yace"bayin Allah ai yanzu shekaru kusan goma Kenan da rasuwar hjy saddiqa........." _Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun_ suka fada a tare suna dafe chest Cike da pretending,babu zato babu tsamanni Shakeerah tafara hawayen munafinci,"Kingani Koh Fauzi Shiyasa naso tun kafin motaho mukira ta mom tace bata da number nata sai dai adrees ai gashinan.
Muryan fauzi na rawa tace"mun shiga uku to yau ya zamuyi? Mai gadi yadu besu yace"meke faruwa ne?ko da matsala ne?
Ko kafin su bashi answer Alhj Sani ya kariso Yana tambayar Mai gadi"Mal sale meke faruwa?nan me gadi yake sanar dashi duk yqnda sukayi dasu Shakeerah.
Dawo da dubanshi yayi ga su Shakeerah yace"Ayya 'yan mata sai dai kuyi hakuri,but mushiga ko ruwa ne kusha don na ganku da niki-nikin akwati,tafiya yafara sukuma suka bishi a baya wannan ta kalli wannan,wannan ta kalli wannan a haka duk suka shiga Falon gidan.


Wata kyakkyawan mace suka tarar akan 3sitter tana zaune tasaka tagumi,gyaran murya Alhj Sani yafara cikin Sauri ta dago tana fadin sannu da zuwa Alhj.
Daure face Daddy khadee yayi tamkar Murmushi bai taba wanzu wa a face din sa ba yace"Yauwa pls shiga Daya ciki ki bamu waje,sannan ki dauko ma baki lemu.
Gaishe ta su Shakeerah sukayi face nasu dauke da murmushi,itama mayar musu da murmushin tayi ta shige.

Gaishe shi su Shakeerah sukayi daga nan daddyn khadee yafara tambayar su daga Ina suke,ko su 'yan uwan marigayiyar ce?lokaci daya Shakeerah karyan da zata shirya mai yazo mata a kwakwalwa tafara magana kaman haka"Daddy mu ba 'yan uwan ta bane,wata shekara ne sukayi aikin hajj da mom namu shine fa suka hada kawance tare da zumunci Bayan sun dawo sukayi exchanging din address tayi kwatan cen gidan nan shine fah mom namu tunda ga garin zaria ta turomu don duba mata ita.
Girgiza kai ya shiga yo a hankali,yace"lallai kam ai tun tuni tarasu to gashi dare yayi 'yan mata ya Kenan?
Shakeerah tace"No bb komai yanzu zamuje munemi hotel da safe sai muwuce.
Murmushi yayi yace"A'ah ai ba za'ayi haka ba Muddin muna garin nan ai ba zaku wulakan ta ba 'yan mata yayi maganar Yana lashe harshe kaman tsohon maye yana duban Shakeerah.
Shakeerah tace"Toh Daddy GODIYA muke.
Daddyn khadee yasa hannu a mouth yace"shiiiiiiii babu godiya tsakanim mu,kuma kada kisake cemun Daddy as from today.
"Ok daddy.....bata karisa ba tace"Au Ok tohm bazan sake ba,Murmushi yayi yace"kyawawan 'yan mata dakin ku daya? Cikin Sauri Shakeerah tace"Eah dakin mu daya baban mu daya.
"Ayya anyway Bari nasadaku da daya daga cikin Mata na.


Da toh suka amsa mishi sannan ya mike yatafi.


Ba'a dauki wani dogon lokaci ba,matar da suka tarar a falon still itace ta dawo fuskanta still dauke da Murmushi cikin sanyin murya tace"kutaso muje ciki koh? Mikewa sukayi tare da binta ciki,sosai dakunan nasu ya burge su Zahra wani daki da basu da alamu dakinta ne,nan suka gabatar da sallolin da basuyi ba,suka kimtsa tare da wanka,ko suka fito matar ta dubesu tace"Alhj yace kuje waje Yana jiranku ku tafi, diddilo idanuwa sukayi gaba daya.
Shap shap suka shirya ciikin arnayen wasu dogayen riguna masu tsada wadanda suka gaji da kyau da duwatsu.

Fita sukayi suka sameshi a cikin motar sa yaci babban Riga,tun daga nesa yake sakem musu murmushi har suka kariso,baya duk kansu suka bure domin shiga,daga murya yayi yace"pls Shakeerah dawo nan mana.
Sai da tayi dan jim tare da yatsine face sannan tashiga gaban,hadadden park ya kaisu suka sha ice-cream Banda kallon Shakeerah yake zuciyar sa na raya masa abubuwa da dama akan yarinyar,duk suna ankare da halin da Daddy ya shiga,ta wutsiyar Ido suke ma juna magana itada Fauzi.
Daga nan wani super market yawuce dasu ya siya musu kayan shafa da takalma.
Godiya sosai suka masa,daga nan daukan su yayi suka wuce gida,ledan balango ya siyo hudu da gasassun kaji Suma hudu.
Koda yafaka motar a harabar gidan Fauzi tafara fita,itama Shakeerah ta balle murfin motar don fita,hannunta yariko,cikin Sauri Shakeerah tajuyo jikinta na wani irin shock don tunda take ba'a taba kokarin taba ta haka ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login