Showing 3001 words to 6000 words out of 36457 words
Chapter 2 - Deejamah Part 1 Complete Hausa Novel By Fatima Zahra Lawan.txt
maiso ya turo katin Naira dari#100 katin waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.*
Bismillahir-rahmanir-raheem.
*Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai....*
Page:1️⃣3️⃣--1️⃣4️⃣🖊️
_________Kijina ne yaketa aikin lugude da faduwa tashin hankali ya bayyana a fuskata nace"A'ah Abba karabu dasu Sunaso ayi kure ne Kuma ni banaso na fallasa abin kunyar da yayi namai haka.
Abba yace"koma menene sai anje islamiyar.
La'asar nayi Abba yatasa keyata har office din headmaster sannan aka Kira mal shafi'u,Nan kuwa ta zayyane duk abinda yafaru.
Cikin bacin Rai Abba yace katanan ku zaneta,ko Kuma ni nazaneta da kaina,kukan munafurci na saka Ina fadin wallahi shegemaster ba haka akayi ba(Wai headmaster ne shegemaster) gabadaya saura rena akayi nayi nawa bayanin,nafara da cewa"tunda nashigo islamiyar yake mun maganar 'yan iska Yana cewa yasan mu talakawa ne nazo yayi iskanci Dani zai bani kudi,kullum-kullum haka yake fada da yaga naki yarda ne shine ya tsaneni yayi ta zanana,abin duka da bana duka ba yadau jibgata,shine ranan yatareni a lungun oske Wai zaiyyi iska*ci Dani nikuma na masa haka.
Gabadaya Office din salati Akasa,shikuwa mal shafi'u Banda zufa Babu abinda yake alamun rashin gaskiya, shegemaster yace Ashe Mal shafi'u baka bar wannan banzar halin naka ba?to ni bazan iya ba wallahi wannan Karan Dole kabar islamiyar nan kada ka lalata yara azo ana kuka dani.
Malamai kowa yace gaskiya kam kada wani Abu yafaru ayi kuka da makarantarmu,hakuri Mal shafi'u ke badawa,Ina nan kuwa akabashi red card,Ni kaina sai da yabani tausayi,but a zahiri hakinsa kenan sai dai ni baimun ba,kawai nema ma kaina mafita nayi.
Nan naciga da zuwa islamiya, Aunty Saudah ma tadawo,yanzu tadena zuwa talla ni ke zuwa Ni kadai,wata Rana nayi sha'awar shiga kasuwan tudun Wada don Kai tallah,wata matace na hango tsohuwa da ita tana tafe tana dingisa kafa daka ganta bata cikin wahala sai dai daga gani rigimammiya ce,wani ne ya taho da Sauri ya bangaje ta,Aiko tsohuwar nan ta baje a kasa,babu Wanda yamasa magana nan kuwa yafara magana Yana karkata mouth alamu dai Dan daba ne ku tsofaffin nan 'yan iska ne taya Zaki shigo kasuwar mu wallahi kinci darajar ke tsohuwa ce da nayi Miki bakin aiki,cikin tsiwa na taho na dagata ina cewa sannu kaka,amsawa tayi tanamun godiya.
Zagina yafara Yana cewa Ni ajawon inace don uwata?banza na masa ganin hakan yasa yajiyo gabana ya dauke ni da mari dafe kunci na nayi Cike da azaba don naji zafi sosai kada kumanta a lokacin 12years gareni bansan sanda nayi kukan kura na dauki bucket din pure water Dina ba na buga masa, dai-dai lokacin wani Dan sanda yazo wucewa Aiko ya kariso Yana tambayar neje faruwa?Nan kuwa tsohuwan nan ta zayyane mai komai tana kuka,albarka yasamun sosai sannan yace nakai tsohuwar gida,tab nida bansanta ba daga haduwa taya zansan gidanta,a gaskiya tacema Dan adai-dai tan da ya daukemu take,tayimai kwantancen layin Aiko nan aka kaimu.
Wani dankareren gida mukaje Wanda tunda nake bantaba ganin gida mai kyau da haduwa irin gidan ba don haka nema cikin zumudi nabita gidan,gani nayi ma'aikata kowa na ya duke a kasa Yana kwasan gaisuwa tsoro ne yakamani bansan sanda na diddilo idanuwa waje ba Fadi nake " _innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir-rahmanir-raheem_ yau nakawo kaina mahallaka garin temako,wani falo muka isa babba mai cike da Kayan alatu wallahi kamar ba gidan mutane ba Zama tayi a wani kujeran one sitter tare da dannna wani kararrawa,can sai ga masu aiki sun Kai goma suka taho ajere,kirari suka fara mata tare da zubewa suna kwasan gaisuwa,Murmushi tayi ta dubi daya daga cikinsu tace"Jakadiya!wacce akakira da jakadiyar na kalla babban macece sanna tafi sauran shekaru kayanta daban ne Kuma duk cikansu suna jinsu neat.
Murmushi tayi jakadiyar tare da karisowa tana fadin"gaisuwa nake uwar dakina uwar gida sarautar mata gani gareki fulani.
Murmushi tsohuwan nan takuma tace"Uhm kuntashi hala baku ganni ba? Eah wallahi fulani tunda banganki ba nace yanzu haka kinje zaga gari ne kamar yanda Kika Saba.
Murmushi tayi tace"Aikam nan take Basu labarina tanuna ni sannar ta sanar masu da duk abinda yafaru,duk cikansu kallo na suke Cike da mamaki da yanda nayi fada da Dan daba,Jakadiya tace"Amma fulani meyasa baki Kira waya ba anzo ankoya Masa hankali?
Fulani Tace kada kidamu ko yanzu wannan yarinyar ai tayi gaba Koda zaiyi zai tuna da abinda yafaru,Jakadiya tace haka ne.
Duba na fulani tayi tace 'yammata yaya sunanki? Bata amsa nayi da Maryam Amma anfi kirana da Shakeerah,wow Masha Allah tafada,Cike da mamaki na dago ina kallonta,ba komai yabani mamaki ba illa wow dinda tace nikam da bansan meaning dinshi ba.
Tambayata tayi nabata labarina,nan kuwa na zayya ne mata komai,abubuwa da dama dariya take nan tadubi Jakadiya tace taje tacema Sarkin gida a shirye motoci uku xataje unguwa.
Ba'a dauki lokaci ba muka shirya nidai Ina rungume da bucket din pure water da farantin bread.
Shiga motocin mukayi Wanda najini tamkar nashiga cikin jirgin sama tsaban dadin danaji,a haka nadinga musu kwantace har muka Kai kofar gidan mu,ya wanci 'yan layinmu duk sunfito ganin motoci da manya manya a hankali suka tsaya aka budema fulani murfin motan,nima aka budemun.
Tunda akaga amfito Dani daga cikin motar 'yan unguwar mu sukafara gulma kala-kala.
Fulani ta dubeni tana tambayata gidan mu,nuna mata gidan nayi,jakadiyar ta da kuyangi uku muka shiga sauran kunyangin da dogarai suka tsaya a waje.
Tafe suke da carpet dinsu da Sauri Ammi tatashi ganin antaso keyata gashi daga gani masu kudi ne.
Murmushi ne a fuskan fulani,sannu da zuwa Ammi tafara mata sannan tashiga dasu daki don wajen babu wajen fakewa Rana.
Dakinmu ta kaita,Wanda yake shimfide da wani tsohon dadduma sai dai tsafta yasa yanajinshi fesss.
Carpet Jakadiya tayi kokarin shimfidawa sai fulani ta hanata Zama tayi akasa suka fara gaisawa da Ammi cike da fargaba.
Fulani ta dubeta tace"kece mahaifiyar wannan yarinyar Koh?Ammi cike da fargaba Ammi tace"Eah nice! Da fatan dai bawani lefi tayi ba?
Girgiza Kai Ammi tayi Nan tasanar da ita duk abinda yafaru sannan tace idan Babu damuwa tana son ganin Abba.
Nan Ammi tafita tasamu Dan makota yaje kiransa a wajen bread.
Basu dau wani time ba suka shigo shima da kaganshi kasan Cike da mamaki yake a tsakar gida Ammi ta tareshi tace Abban su yau Shakeerah ta nemo Mana magana.
Shiru Abba yayi tare da sallama ya Shiga,su Jakadiya fulani ta kalla alamun su bamu waje,fita sukayi tsakar gida,nan suka gaisa cikin mutumci da Abba.
Tambayar shi tayi sana'arshi yace mata bread ne,tace to yau yarinyar ku ta temakeni da alamu daga gidan tarbiya tafito tunda har tasan darajar tsoho,ganin haka yasa na biyota don ganin iyayen ta.
A tare suka sauke nannauyan ajiyar zuciya.
Fulani ta cigaba da cewa idan Babu damuwa,zanso in temaka muku da muhalli sannan Kai nabaka jari mai karfi.
Jin kalaman fulani mukayi kamar a mafarki,cikin rawar baki Abba yace Ni...n...I...diin..? Daga Masa kai fulani tayi ai a take anan suka fara godiya saboda tsananin murna.
Nan takira ma'ajinta Mai kula da harkan komai tace masa tanaso a dubo mata gida mai kyau Mai 3 bedrooms,Kuma yazama dakwai komai da komai da ake bukata na muhalli.
Amsa mata yayi da toh,Aiko cikin awa biyu yakirata yace ansamu,tambayar shi tayi a Ina?yace a kwangila.
A lokacin Ammi tagama alqlen gwangwani rai-rai da dakaken yaji tafarnuwa,nan akazuba ma fulani da da kuyanginta da fadawa gaba daya,mukuma ko oho,tsabar yunwa tasa mun manta da yunwa,sosai sukaji dadin alalen.
Shakeerah ta dubi su Fauzi tace"In takaice muku fulani itace dalilin arzikinmu.
Munje munga sabon gidanmu,gaskiya yayi kyau sosai nida Aunty Saudah a daki guda,daki daya na Ammi dake kallon namu sai daya na Abba da yake da kofa ta waje,duka dakuna biyu Italian bed ne,Daya Kuma Royal shine na dakin Abba,dakuna ne manya² Wanda da safayan 1-1 sitter sai na Abba ne da 1-2 sitter da bangaren dining Falon Kuma kujeru ne hadaddu golden saikace glass Sunyi kyau sosai.
Jali tabawa Abba na miliyan Daya sannan ta hadAshi da direban ta suka fara sana'ar sai da motoci.
Nan kuwa 'yan uwan Abba suka sake tsanar sa suna yawon cewa yankan Kai yafara,watarana muna zaune da Ammi shi Abba bayanan sun fita da direban fulani sunje kano dauko wata mota.
Wani yaro ne yayi sallama ya shigo,amsawa nayi na fita tambayata yayi Wai ance Nan ne gidan wai malam muhammadu? Na'amsa da Eah nan ne wake nemanshi? yaron yacemin wasu maza ne su biyu a waje,cema yaron nayi muje nagansu tare muka fita na bude gate din gidan,Cike da mamaki nake dubansu baba Ayuba ne da baba sani,duk yayyen baban mu ne.
Ganina yasasu sakin murmushi gaba dayansu,Nima murmushin naayar musu Ina cewa lahh kune?ku shigo,da to suka amsa ko wanne yana kokarin fara shigowa ganin zasu bangaje ni yasani matsawa suka Shiga,gaba daya bin gidan suke da kallo,wani kolulun bakin ciki baba Ayuba ya hadiye har muka shiga falon,daburcewa sukayi ganin kujerun,Cike da fara'a Ammi ta tarbesu Zama sukayi akan kujerun duk da sunsa ba gani a gidan chairmomin local government,gwanda ma baba sani idan yaso kirki yanayi Zama sukayi,Nikuma nashiga kitchen da kyar na iya bude firij saboda kauyan cina yayi yawa lemu na dauko musu da ruwa na Basu.
Nan baba Ayuba ke tambayar Ammi Abba Tace Aiko bayanan,sun tafi kano,wani takaicine ya lullubesu baba sani kuwa har Yana kwarewa yace kano Kuma?
Baba Ayuba yace oh rayuwa yanzu muhammadu ne da wannan gidan?harda zuwa kano? Idan natuna sanda yake kwasan masai da bola abin mamaki yake bani.
Magana suka gasama Ammi itama Kuma tagani,Murmushi nayi nace wallahi kuwa baba gashi yanzu a dalilin katsalan dan dina muka shiga daukar nan,yaran da ake tsine musu idan ba iyayensu ke tsine musu ba ai abin sai kaga Yana tafiya yanda akeso,yau da hjy 'yar mai goro nanan nasan da zatayi alfahari(wato mahaifiyar Abba) harara baba Ayuba yasakin min yace Mai Hali dai Sam baya canza Hali to yanzu dake nayi magana?Nima hararar na wurga mai nace maganar mahaifina fa kakeyi shiyasa nasa baki.
Kwafa baba sani yayi yace ai yanzu Dole muhammadu yayi aure tunda arziki yasamu kaga ni saina samo Mai bazawara.
Daka tsalle nayi kamar nice za'ama kishiya nace wallahi bazai yuwuba Kuma Abba bazai dauki shawarar na ba,galala suka saki mouth suna kallo na,Ammi tace Shakeerah tashi kiwuce ciki,da toh na amsa mata na mike Suma mikewar sukayi daganan suka fara Dora ashar,inaso in rama saboda jikina har tsuma yake sai dai Ammi ta hanani.
_I need ur comment and sharhi_
Xahratty ce✍🏽
Lallai Alqalami🖋️Yafi takobi 🗡️
💕💕
❤️
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨
( Daukar Fansa )
Story& writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
______✍🏽______
*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah))
*_T.W.A_*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_________________________
Marubuciyar⬇️
_ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_
*DA*
_ _MIJIN ZAHRA_
*Littafin diamond ladies (Daukar fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari biyu#200 katin waya ta wannan number 08060719719,sannan a nemeni ta wannan number 08060719719 sai nayi adding din mutum a group a group din diamond ladies (Daukar fansa),Wanda suka biya kadai zan zira a ciki......kushiga daga ciki don Jin labari Mai darasi,nishadi,tausayi,fadakarwa,ilimantarwa da jarumta.Nagode.*
Bismillahi-rahmanir-raheem.
*Da sunan Allah Mai rahama mai jin kai*
Page:7️⃣&8️⃣🖊️
__________Bayan sunje lectures Sai wajen karfe shida suka dawo,sai da suka wuje restaurant sukaci abinci sannan sannan sukayo take away din Chip's sukayo gida.
Sallah suka gabatar Cike da gajiya suke,sannan bayan sallah isha'i khadee ta cigaba da Basu labarin a baya.
"Bayan rasuwar Aunty sakina gaba daya 'yan gidanmu sun gama tsorata da al'amarin,haka Kuma 'yan Unguwa har takai ba'ason hulda dasu Ummina.
Aunty Nana kuwa jikinta yariga ya gama sanyi tasan cewa yanzu itace next.
A kwana a tashi Babu wuya har shekaru suka shude da watanni babu Wanda aka sake kashewa a gidanmu,kwatsam inada 13years lokacin Ina j s s 2 aka wayi gari an tsinci gawar ya Anas Wanda yakebin Aunty sakina innalillahi wa Inna ilaihirrajiun a lokacin hauka ne kawai hajy saddiqa batayi ba,ganin haka yasa Ummina ta shirya wata ranar laraba Babu kowa a gidanmu domin Daddy da hjy sameera wajen aikinsu daya,itakuwa hajy saddiqa tatafi gidansu sha'ani.
Shiryawa Ummina tayi ta hada Kayan Aunty Nana gaba daya tasa driver ya daukemu ya kaimu tasha, daganan motar maidugri muka hau wajen yayar Ummina da bata taba haihuwa.
Already tasan da zuwan mu,don haka munsamu tarba mai kyau,Bayan munvi abinci munhuta Ummina tayima yayarta bayanin abinda ke faruwa,itama tabata goyon baya hundred percent,sannan Ummina tace to ga amanar Aunty Nana nan tabata ita Amana.
Tayi farin ciki mara misaltuwa saboda macece Mai hakuri da son yara,uwa uba ga addini da dukiya,mijinta ma yayi farin ciki duk da bada izini Daddy aka kawo Aunty Nana ba.
Washegari suka shirya da Ummina da yayarta sukaje hospital aka juya mata mahaifa bazata sake daukar ciki ba,domin ummina tace"ita tana zargin Daddy ke kashe masu yara.
Kwanan mu daya muka dawo duk da nida Aunty Nana munyi kukan rabuwa da juna sai dai hakan shine mafita.
Koda muka dawo gida Daddy da Hjy sameera Basu dawo ba sai hjy saddiqa,nan Ummina ta sanar da ita abinda ke faruwa,itama tayi farin ciki sosai Kuma ta bata goyon baya.
Wata Rana hjy saddiqa tafara ciwo Wanda anyi magani abin kaman gaba yakeyi,Ashe Daddy ne yafara amfani da ita ta baya,shine fah tsutsotsi suketa cinye mata wajen,hatta kashi Bata iyayi sai dai wajen yayi ta zubar da jini,dalilin sanin ummina kuwa ita da kanta hjy saddiqa ke sanar da Ummina, gaba daya ta rame taui bakinkiri babu kyan gani.
Duk mutuwar da akeyi ba'a taba wanda ya girgiza ummina ba sai na wanna Karan,domin Allah yayiwa hjy saddiqa rasuwa,a dalilin homosex da Daddy yayi da ita,sai dai abin takaici likitoci sun boye,shida kanshi yamata sittura aka kaita.
Sajida tadawo hannun Ummina da Zama, nida ita sai muka koma kamar twins,ummi dalilin ta dena fita ita kadai saidamu,sanna ta dena aikemmu ko Ina hatta wajen Daddy,wannan dalilin ne yasa Daddy suka fara tsiya da Ummina,sanna yace saita nemo Aunty Nana duk inda ta kaita, Ummina tace bazata nemo taba.
Wannan dalilin yasa Daddy ya tsani Ummina sannan hatta abinci yadena bamu,da kula damu,hatta ni saboda tsanar da nanuna Ina Mai karara.
Ummina ta Kira ya mashkur ta sanar dashi abinda ke faruwa,yaso daukar mataki,Amma Ummina tana tsoron kada mutumci na Daddy ya zube.
A sirrince Daddy ya siyama Ummina gida a garin Zaria.
Wani dare Ya mashkur yaturo wani abokinshi ya daukemu muka gudu,komai bamu dauka ba hatta kayan sawarmu,bayan komawarmu da wata biyu aka daura Auren ya mashkur cikin jimamin rashin ganin Ummina da yaranta,ko taron biki 'yan bauchi da dangin Ummina basuyi ba saboda jimami,Daddy na kuwa hankalinshi ya tashi na rashin ganinmu.
A halin yanzu Daddy yakara aure da matansa ta haifi yara biyar,Amma yanzu saura uku biyu sun rasu,a shirye nake yanzu Dan daukar fansa da hukunta Daddy na da temakon ki Shakeerah,domin nasan Babu mai temako na sai ke, mahaifina babban mai lefi ne.
To wannan shine labari na.
Cike da tausayi duk cikansu fauzi da shakeera ke duban khadee, Shakeerah tace"Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun tunda nakejin labari bantabajin irin labari irin wannan ba,tabbas Sai an hukunta shi,ke da duk Wanda keda hannu a wannan annobar hatta munafikin likitan Daddyn ki.
Fauzi tace"Tabbas wannan yacika azzalumi Allah yasaka muku,insha allahu sai yayi mummmunar karshe,ki yahakuri mahaifinki ne,Amma meyasa kikace mun ke 'yar bauchi ce?
Khadee ta share tears din da suka zubo Mata tace"Eah Mana ni bauchi nasani garinmu,bakiji labarin bNe?
Fauzi tace"ok naganae sorry kinji kada kidamu kinji?
Khadee tace"kada kidamu am ok.
Shakeerah tace"to ya maganar sajida ita tana wane skul ne yanzu?
Khadee tace"tana A.B.U teaching hospital ne yanzu tana karantar dental.
Shakeerah tace"Allah sarki ummi taga iftila'i,to maganar Aunty Nana fah?
Khadee tace"tayi aure yanzu haka tana kasar Argentina ta auri wani dan jarida.
Shakeerah tace"Allah sarki rayuwar duniya duk babu dadi,idan kana ganin damuwar ka idan kaga na wani sai jikin ka yayi sanyi.
Fauzi tace"Allah sarki ni kuwa sai na dunga ganin kamar tawa damuwar tafi ta kowa.
Shakeerah ta buga tagumi tace"Fauzi muna sauraranki.
Fauzi ta cigaba dafari dai,
"Sunana Fauziyya Aleeyu ni haifaffiyar garin gombe ce,mahaifina mutum ne mai rufin asiri dai-dai gwargwado gaskiya mu ba masu kudi bane,mahaifiyata wacce nike cema Inna mu uku ta haifa nice babba Sai kannena su biyu duka Mata,sana'ar mahaifiyata sai da manja da man gyada Kuma Alhamdulillah Yana rufa Mana asiri,shikuwa mahaifina icce yake siyarwa,a haka Allah ya rufa musu asiri suka samu a makaranta.
Kishiyar Inna ta muna kiranta da baba ladi tanada yara hudu duka mata,tunda muka taso muka cidda baba ladi itace ke mulkar gidan mu sai abinda tace ayi akeyi,da yake Inna macece mai hakuri Sam magana ba yadameta bane,a hankali nataso da bakin jini a gidanmu har a wajen Inna ta wanda narasa dalili,ana cewa babu Wanda yakai mahaifiya son 'yayanta,Amma Banda tawa mahaifiyar domin kuwa a cikin wahala na taso,mutum Daya ne zuwa biyu nake raba naji dadi,mahaifina da yayata 'yar-'yan baba ladi itace babbar 'yarta.
Sune kawai kesani bakin ciki abubuwa da dama idan Inna ta tayimun Zama nake na tambayeta anya ita ta haifeni?
Tunda nataso bantaba Jin dadin uwa ba,itace kyara hantara,lokuta da dama nasha kwana bansa abinci a bakina ba,inda Allah yake temako na wajen kanne na nake kwata nace wallahi Muddin bazanci ba Suma ba zasu ciba,saboda inada bakina to abubuwa da dama su suke temakona,a cikin kannena akwai khadeeja wacce muke cema dijee,yarinya ce mai natsuwa jinimmu ya hadu sosai,hadasiyya itace ke bina sai dai ko kadan bamu ga maciji,itace 'ya mafi soyuwa a zuciyar Inna saboda ita ta amince da talla,muko nida hadasiyya da babbar yayarmu munason karatu ,sai dai