Showing 21001 words to 24000 words out of 98640 words

Chapter 8 - A RUBUCE TA KE PART 2 COMPLETED huguma 2023 .txt

din komai fes bisa tsari,saika dauka watanni aka dauka ba'a gyarashi ba.


Baki ta tabe ta fice abinta,yau daga kitchen din har Parlor din babu inda zata sama hannu,itama tasan dadin jikinta,kawai dai tanayin komai ne don samun walwala da nutsuwarsa,tunda ta fuskanci babu abinda ke daga masa hankali a rayuwa irin qazanta,amma tunda bai gani itama ba zata dinga wahalar da rayuwarta ba,zata barsu shida hafsat din tasa.


Tana isowa falon sukaci karo da mimi


"Ina kwana anty?"


"Oyoyo mimin daddy,kin tashi lafiya?"


"Lafiya lau anty,yau duka baki fito ba"


"Banajin dadi ne,ungo wannan ki kaima mommynki kice kudin cefane ne inji ni" ta hada dukka kudin da abbas din ya bata ta sanyashi a hannun mimi,sai da taga ta shiga dakin sannan ta fice abinta harabar gidan.


Kai tsaye boys quaters ta nufa wajen maari matar baba mai gadi,sosai taji dadin ganinta kuwa,don bata taba zuwan mata ba,ko yaushe widad din tafi ganewa zamanta daki tayi kallo ko chart,ta marabceta sosai suka fara dan taba hira,tun widad din bata sake ba har ta saki jikinta suka shiga hira sosai,kasancewar hajiyan bata nan,babu wani aiki cikin gidan haka suka wuni tare.


Maari din saita tuna mata da latifanta,cikin awanni kadan ta gane tana da kirki matuqa da jan mutum ajiki,har tafi tsohuwar me aikin hajiyan data dinga tayata kwana sanda abbas yake tafiya bauchi ba tare da ita ba.


Tayi musu faten tsakin masara da yasha gyada da yakuwa,batayi zaton zata iya ci ba,sai gashi taci sosai sunata hira,kirkin widad da yadda take girmama kowa cikin rashin nuna qyama ya sanya maari ma taji ta shiga ranta,ba kamar hafsat din ba,dake dagawa izgilanci da wulaqanta na qasa da ita.


Hafsat na tsaka da barci taji mimi na qwala mata kira saman kanta,da qyar ta bude idonta tana jan mugun tsaki,kafin daga bisani kuma ta buda hancinta sosai saboda warin bayan gida da take jiyowa,dole ta wartsake ta miqe sosai ta zauna tana duban mimi


"Ban hanaki idan ina bacci ki dinga tashina ba don ubanki?" Kebe fuska yarinyar tayi kamar zata saki kuka


"Ai ban tasheki ba harma su nawwara sukayi kashi,yanzunma anty ce tace na kawo miki kudin cefane"


"Kudin cefane kuma?"ta tambayeta da mamaki,saita jinjina kai,ta miqa mata hannu ta saka mata kudin,ta waresu tana irgawa.


To me yarinyar take nufi?,nufinta ta ajjiye girki kenan saboda abinda ya faru jiya?,aiko ba zata sabu ba,ita dinma ai ba jaka bace da zata zauna tayita girka musu suna ci.*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02




Page 10




Kamar ta bawa mimi kudin ta maida mata,sai taga kada tayi asara,ta bata kudin kuma tazo batayi musu girkin ba,don haka sai ta ajjiye kudin tanata qananun mitoci.


Tun tana saka ran ganin widad din ta shigo sashen har ta fidda rai,don yamma ta riga tayi,ga yunwa suna ji ita da yaran,dole ta shiga kitchen ta dora dafa dukan shinkafa.


Tana kitchen din tana fama ga magrib ya kawo jiki widad ta dawo,dakinta ta wuce kai tsaye,bata bi ta kan jagulallen parlor din nasu ba,tana mamakin yadda suke iya hargitsa guri har haka suci gaba da zama a cikinsu abinsu hankali kwance.


Ta taho da sauran faten tsakin daxu,da zafinsa don a wani warmer mai kyau da hajiya ta bawa maari yake a ajjiye,saita hada ruwa me zafi ta cire kayanta ta shiga toilet tayi wanka ta gasa jikinta sosai,ta dawo ta zura wata armless riga da iya tsahonta gwiwa,ta wadata jikinta da turare,ta sake jona humidifier sannan ta dawo tana laluben hijabin da zatayi sallar dashi wanda zai saukar mata har qasa.


Sosai yau ya hado yunwa da kuma gajiya a jikinsa,ya tabbatar zai samu dukkan wani hutu da kulawa hadi da kwanciyar hankali daga gurinta,wannan yasa ya hada dukkan yunwarsa ta yinin ranar,bai wani tsaya yaci cikakken abinci ba,don yasan zai tarar da irin taste din da yake muradi,har fiye ma da yadda yakeso.


Ajiyar zuciya ya sauke sanda ya kashe motar tasa,ya waiwaya baya ya dauko ledar fruit din da ya siyo da chocolate nasu mimi ya fito,ya kashe motar sannan ya nufi cikin gidan.


Tun kafin ya qaraso ya fara buda hancinsa yana tsammatar samuwa sassanyan qamshin nan dake masa maraba a duk sanda girkinta ya shiga,saidai babu shi ba alamarsa,duk da haka yaci gaba da takawa cikin hope da kuma karsashi.


Sosai mamaki ya cikashi sanda ya yaye labulen falon ya sameshi a tarwatse,komai yana zaune zaman kansa,sai su mimi dake ta hada hada da kayan ciye ciye na leda irin wanda yake siyowa ya jibge musu,ko ina tarkacen kayan ledojin da tsinken sweet ne,dukansu suka watsar da abinda yake hannunsu suka nufoshi suna rige rigen qarasowa,ya tsugunna ya tarbesu gaba daya.


Miqewa yayi yana dauke da nawwara mimi na hannunsa,yaji motsi a kitchen,don haka zuciyarsa ta bashi widad ce,sai ya wuce kitchen din dasu kanshi tsaye yana amsa tarin tambayoyinsu da suketa damunshi dasu.


Tun bai gama shiga kitchen din ba idanu da hancinsa suka gaya masa ba widad bace,hafsat ce sanye da doguwar rigar wani material ruwan qwaiduwar qwai,sulbinsa ya sanya dinkin da aka masa a wasu sassan ya zazzame yayi zare zare,tana goye da yusra daketa mutsu mutsun son a sauko da ita,ya qarasa yana amsar yarinyar,ta sauke masa ita tana masa sannu da zuwa muryar a cunkushe.


"Ina antyn nasu?"


"Tana dakinta mana" hafsat ta amsa adan fusace tana juya dafadukan data fara kamawa


"Lafiyarta qalau?" Juyowa tayi kamar ta banka masa harara,amma kwarjinin nashi idanuwan sun shallake nata


"Aiba wannan ya kamata ka fara tambaya ba,kamata yayi ace ka tambayi wanda ya bamu abinci wunin yau,ta shige daki saboda ta samu daurin gindi tayi kwanciyar ta wuni guda ta barmu da yunwa ni da yara" sam hankalinsa bashi akan maganarta, zuciyarsa da tunaninsa sun karkata kan sanin lafiyarta da abinda ya hanata fitowa wunin yau,sai ya juya yana sabe da yusra ya fice a kitchen din.


Ana fara knocking ta gane shine,ta riga ta saba da komai nasa,hatta takun takalminsa ya banbanta dana kowa,tana kuma iya banbancewa,ranta yadan quntata,itakam ko son ganinsa batason yi,space take da buqata, batason takura,to amma batason tayi wani abu na rashin girmamawa a gareshi gaban yaransa,dole ta ajjiye qaramar hular da take qoqarin sanyawa sassalkar sumarta daketa sheqi saboda yadda tayi oiling dinta da mai,tana tura baki da shagwababbiyar fuskarta ta isa qofar ta bude masa,sai taja ta tsaya daga bakin qofar,kamar wadda aka zo gayawa saqo take jira a gama gaya mata a fita ta kulle qofarta.


Tun daga kwanyarsa har zuwa tafin qafarsa wani abu ya tsarga masa,yadda batasaka brassiere ba amma hakan bai hana na shanunta tsaiwa kyam suna nuna kansu ba,lafiyayyun cinyoyinta sun fita sosai ta cikin tsingilalliyar rigar,yadda ta turo bakinta gaba kuma ya qarasa kunnashi,soft pink lips dinta daketa sheqin lip gloss,sai yaji kamar ya jata cikin jikinsa ya kama bakin ya tsotse,amma yusra na kafadarsa,tilas ya daure,ya qarasa gefan gadon ya zauna ya dora yarinyar saman cinyarsa


"Sannu da zuwa" shuru ya ratsa maimakon ya amsa mata,ya tsareta da ido yana jin yadda kallonta kawai yake saukar masa da kasala


"Banda na shigo na nemeki bakisan ma na dawo ba kenan?"


"To me zanzo nayi maka?,bayan maganar matarka kawai kake ji" ta fadi haka cikin ranta,amma a fili saita sake tura baki gaba tana yamutsa girarta hadi da sarqafe yatsunta waje daya tana ballaqasu


"Zonan" ya fada a tausashe yana nuna mata kujerar madubin dake gabansa,ta kalli wajen sannan ta kalleshi,ko yaushe girma da kimarsa ke sakata ta kasa masa musu ko wasu dabi'u da basu kamata ba,ta sauke hannuwanta ta dawo inda ya nuna matan ta zauna,wannan karon idanunta cikin nasa tanason jin abinda zai gaya mata kuma.


Rage kaifin nasa idanun yayi kadan daga kanta sannan ya magantu


"Ya akayi gidan ya zamana yau duk a hargitse,infact ma yau girkinki ne amma baki fito kwata kwata ba,ko yanzun ma antynki ce cikin kitchen din" wani haushi ya kamata,aiki?.....a nan tafi kauri kenan, idanunta ta lumshe kadan tana daukesu daga kansa,abinda ya sake fusgarsa da wani madaukakin shauqi zuwa gareta,duk da ba tayi bane don ta burgeshi ko kuma da wata manufa


"Gida a hargitse?,ina cewa mummyn mimi tana cikin gidan,amfanin zaman mutum biyu kenan,idan dayan ya gaza ko ya gajiya sai dayan ya tallafa masa.......girki kuma ni na daina girki,na bar mata komai da komai harda kwanana" mamakin widad din sosai ya kamshi,yadda tayi maganar ya tabbatar da gamewar hankali a jikinta,don tana maganar ne with seriousness in her sound,baibi takan maganarta ta farko ba,maganarta ta qarshe tafi fusgar hankalinsa tare da tabashi,don abune da bayajin ko sama da qasa zata hadu zai amince da hakan


"Kin daina girki?,meye dalili?,da kuma izinin wa kika dauki wannan matakin?" Sake tura bakinta gaba tayi sosai tana hade fuska,ta kuma kaucewa dubansa


"Saboda gidan da mijin duka nata ne,so komai da yake cikin gidan yafi cancanta ya zama nata" sai yanzu ya sake gano inda ta dosa,can qasan ransa murmushi ya kubce masa,kishi take da gaske.....ta kuma ji haushin abinda yayi mata kenan fiye da yadda ma shi ya zata,amma bayason ta dore da haka don haka ya miqe yana dora yusra a kafadarsa


"Ki shirya komai kamar yadda kika saba,banason dawo da zance,abinda ya wuce ya wuce" sai ya taka yana ficewa a dakin.


Sam maganarsa bata bawa zuciyarta sassauci ba,saima tunzurata da yayi,bazai iya daukan mataki ba kenan kwata kwata?,indai haka ne itama bataga dalilin da zai sanyata saukowa ba,don haka yana fita sallar magariba ta sakawa dakinta key tayi sallarta ta jirayi isha'i ta bada ita sannan ta haye gado ta nutse cikin duvet hankali kwance.


Sai daya dawo daga masallaci sannan ya zarce dakinta don ya samu ruwan nan nata me wani irin dumi da qamshi don yayi wanka,ruwan da ita kadai tasan yadda take hada masa shi,don koshi ya hada da kansa baya jin dadinsa kamar haka.


A nutse ya tsaya yana knocking a bakin qofar,tana jinsa ta share,saita saka earpiece ma a kunnenta,don haka batasan adadin awannin ko mintunan da ya dauka yana bugun ba.


Sosai ransa ya quntata,don yadda yayi tsaye yana bugun har mimi taji ta fito ya tabbatar tana jinsa,ya kirayi sunanta kusan biyar shuru,dole ya juya dakinsa dakin kuma hafsat,tana zaune a qasa ta tara kayan qazantar yusra tana waresu,ya wuce gaban cupboard dinsa yana rage kayan jikinsa.


Binsa tayi da kallo ta tabe baki,ita da zasu tabbata a haka sai tafi kowa farinciki,duk bugun akan kunnenta akayishi,tana sane tayi bakam


"Ba kwananta bane?,ya na ganka a nan dakin?" Ta jefa masa tambayar da tasan amsarta.


"Na sani,hadamin ruwa zanyi wanka" ya fada muryarsa da wani irin laushi daya bata mata rai,komai na yarinyar tabashi yakeyi,saka masa damuwa yakeyi,duk qoqarinta na kau da hankalinsa amma baya wani tasiri yadda take da buqata,ita sau nawa suna irin wannan sabanin,amma ko a fuska bata taba gani yayi laushi irin haka ba,komai dadewar da zasuyi,sai yanzu akan qaramar yarinya kwana uku kacal amma duka ya canza?.


Da tunani iri daban daban ya shiga wankan,sam ruwan baiyi masa ba,hasalima ya cika zafi da yawa,yaja tsaki ya saki famfo akai,sai kuma yaso salance masa,ya sake jan wani tsakin yana komawa cikin bathtub din ransa duka a jagule.


Koda sukazo cin abinci ma yasa mimi ta bubbuga mata,duk da yadda hafsat ke faman hada rai tana ganin ya girkinta ne batayi ba ita ta zauna tayi kuma saboda gata wai a kirata taci,itama mimin haka ta qaraci bugunta ta haqura ta dawo jiki a sanyaye


"Bata bude ba" sai ya shafa kanta


"Inajin tayi bacci" a yadda yake jinsa koda lafiyayyen girki hafsat din tayi abincin bazai masa dadi a baki ba,bare tafashi kadan hafsat din wadda ta cuccure waje daya,kamar gidan da aka yiwa gorin man girki,bayan komai a wadace yake a store dinsu,zuciyar tata ce dai haka.


Da qyar yayi loma hudu ya ture abincin,ya maida hankalinsa ga news da ake haskowa a channel din al_hadath,duk da a badini fiye da rabin hankalinsa yana kan qofar dakinta,duk bayan mintuna biyu saiya kalli qofar dakin,amma ko motsinta daga ciki baiji ba bare ya sanya ran zata bude ta fito.


Har yaran sukayi bacci hafsat ta debesu takai daki ta dawo tayi masa sallama yana zaune a wajen,sanda sha daya na dare ta buga sai ya tashi yana sake gwada bugun,a lokacin tuni tayi bacci,bugunsa ne ya tasheta,ta sauko a hankali ta wuce toilet abinta,tayi fitsari ta sake alwala ta dawo ta kuma kwanciyarta.


Wannan karon yaji motsinta shigarta bandaki zuwa fitarta,hakan ya nuna masa tana jinsa,bata kuma da niyyar bude masa,ya koma da baya ransa yana baci,ya juya yana nufar dakinsa.


Dadi ya kama hafsat dake labe,saita koma bakin gado ta zauna tana kada qafa a hankali,itakam gaba ta kaita,dole yau ya kwana dakinta,sannu a hankali dai gida yana shirin dawowa hannunta sai yadda ta juyashi, murmushin nasara da farinciki ya kubce mata.[5/10, 2:11 PM] +234 816 811 4418: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02


Page 11




Yana turo qofan dakin ta kalleshi,irin kallon mamakin nan wanda tuni ta shiryama hakan


"A'ah,abban mimi ba kwanana bane" idanunsa ya zube fes akan fuskarta,yana iya hangen wani abu fake behind her face,sai ya lumshe ido kadan ya gyada kai


"I know" sai ya qarasa ya dauki duvet dinsa da pillow ya juya ya fice yana ja mata qofa.


Da kallon mamaki ta bishi,saita miqe ta nufi qofar yana leqensa,saman kujerun parlor din ya shimfidashi ya yada pillow din ya kwanta bayan ya rage hasken qwan falon,ranta yayi mummunar baci,wato ita bai isa ya kwana gurinta ba,saboda kwanan gimbiya ne?,har ta buda qofar zata iskeshi a falon wata zuciyar ta haneta,saita koma da baya ta maida qofar ta rufe.

A wannan daren haka kowa cikinsu ya kwana,kowa da irin abinda ke kai kawo a zuciyarsa.


*******Tun daga ranar suka koma 'yar haka dashi,sai sa'ar gaske yake iya sanyata a qwayar idanunsa,tuni ta ajjiye girkinta dama komai da komai,iyaka ta gyara bedroom dinta da kanta,idan tana da ra'ayin hira ta kira wanda takeso cikin 'yan uwanta,ummunta anty deena ko anty madeena koma mom dinta,ko kuma ta fice wajen maari susha hirarsu,ita kuma dake mata kallon me qaramin ciki tayita mata dafe dafe na abubuwan gargajiya,wanda da gudu widad din ke ci,don wasu abubuwan ma ta manta dasu sam,ummu ke musu lokaci lokaci a gida dama.


Ba wanda ta taba gayawa abinda ke faruwa,don sai taji abun baya ma wani damunta gaba daya,yammaci tana yi dab da zai dawo zata koma dakinta ta kulle.


Yadda hafsat take ganin damuwa qarara tattare da abbas din sai hankalinta yayi mugun dagawa,bata taba zaton baka ya damu da yarinyar ya kuma bata muhimmanci mai yawa cikin rayuwarsa ba irin wannan lokacin,ta auna ta auno......taga kaf zamansu bata taba irin wannan sakarcin ya damu da ita haka ko yabi ta kanta ba,hasalima wani lokacin saidai ta bude qofar ta tarar ya koma wajen aikinsa ya ajjiye mata dan note.


Kishi sosai ya tasata a gaba,ta daina jin dadin gidan gaba daya,ba zata iya jure ganin soyayya da damuwar abbas akan wata diya mace ba a gaban idanunta tana raye ba,sai ya zamana bata da aiki sai mita da qorafi


"Gaba daya qaramar yarinya na neman rikita maka lissafi,totally ka canza abban mimi,ba ita ta zabi haka ba,aiba wansa ya tilastata,saika qyaleta idan ta gaji ta watsar.....banda ma iyayin banza da samun waje,mema akayi mata?" Sai taja qaramin tsaki.


A sannan yana shiryawa ne bayan ya fito a wanka,sanda take wannan maganar ma yanata bulayin neman wankakkiyyar singlet da zaisa duka babu,ya watsar dana hannunsa yana duban idanunta


"Kin gaza ta abubuwa masu yawa,wannan ya sanya dole nayi kewar kebance kanta da tayi daga wajena,abubuwan da kika kasa ita din duka bata daukesu a komai ba.......ki jiqamin singlets dina da hypo zan wanke da kaina,na gaji da siyan sabbin undies,idan kin gama ki gyara parlor zuwa cikin dakin nan,idan Fresheners dinmu ne suka qare ki gayamin,idan na fita zan shigo da wasu,banason na dawo na samu gidan nan a yadda yake" daga haka ya juya yaci gaba da shiryawa.


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login