Showing 3001 words to 6000 words out of 98640 words
Chapter 2 - A RUBUCE TA KE PART 2 COMPLETED huguma 2023 .txt
tace masa gata nan fitowa,ta gama shirinta a nutse,ta dauki duk wani abu da takega ya dace da wanda taga suna dauka suma idan zasu fita din,ita kanta tana jin banbanci da canji a tattare da ita,ta kammala komai a nutse ta fito.
Ko sau daya baiji ya qosa da jiranta ba har ta iso,kasa magana yayi sanda qamshinta ya gaurayeshi,sai ajiyat zuciya mai nauyi daya sauke kawai,suna shiga dakin ya maida qofar ya rufe da wani irin zafin nama,ko ina na jikinsa yana daukan rawa.
Zaucewa ya kusa yi sanda widad din ta miqa masa kanta yadda yakeso,ta kuma hada da bashi gudunmawa,sai kansa gaba daya ya kunce,jikinsa ya dauki rawa tako ina ya fita mata a hayyancinsa.
Bawai shi ba,ko ita din a yau ta gane da banbanci,ta fahimci kuma maganganun su hajiya fanna,bayan komai ya kammala wata kunya ta kamata,yayin da shi kuma ya hanata sakat,bakinsa kuma ya kasa yin shuru,ya dinga zuba sumbatu ya kasa tsuke bakinsa,domin kuwa ta shammace shi fiye da kima,ta kuma kaishi wata duniya da tunda hajiya ta kawoshi sararin duniyar nan bai tana zuwa can din ba,ko sanda yake kidansa yayi rawarsa shi kadai yaya ya qare?,bare yanzu data bashi tallafi ta kuma miqa masa kanta kacokam.
Wannan canji na widad ya tabashi fiye da kima,ya sake kuma cusa wata irin zazzafar soyayyarta a zuciyarsa,ya sake susucewa,har abun yake bawa widad din mamaki,yadda ya dinga cire kudi yana mata siyayya abun sai ya dinga daure mata kai,wanne irin so uncle din nata yake mata haka?.
Ranar da suka fita siyayyar data sake sanya widad sallamawa abbas rayuwarta da jikinta......ta sake yaqini da yadda yake yawan fadin yana sonta,cikin shagon gold ya mallaka mata wata sarqa da farashinta yakai naira dubu dari tara da hamsin.
Kanta ya daure sosai,a wauta da quruciya irin tata tace ba zata karba ba,sai bayan taje dakinsu da ita su hajiya sha'awa suka dinga mata dariya
"Karki qara cewa ba zaki karba ba,tunda ya siya baifi qarfinsa bane,kuma tukuici ne tabbas yake baki,lallai soyayyar da yake miki tana da girma da fadi,saiki sake kula ki kuma tabbatar duk abinda yakeso kina aikatashi sau da qafa,tabbas gaba saikin mallaki abinda yafi haka muddin zaki sallamawa mijinki tare da tsare duk wani abu da yakeso,ki kuma guji wanda bayaso" ta jima a kwance tana tariyo rayuwarta ta baya,da kuma abubuwa da suka faru a yanzu,ko addu'a ce da ummu da mommynta suka yita jaddada mata ta yiwa kanta mijinta da kuma rayuwar aurenta?,ba shakka akwai tasirin addu'ar data dinga yi tuquru,sai gashi tanata ganin abubuwan da ada bata iyasu ba batama san dasu ba.
Ranar da suka qara fita siyayya gefe ta koma kawai tana kallonshi,yadda ya zage yana siyan kayan babies kamar yasan me za'a haifa,har sai data gaji da ganin yadda yake diban kaya kamar baisan ciwon kudinsa ba tayi magana
"Uncle" ta fada a narke
"Baby" ya amsa bayan yabar dukkan abinda yakeyi ya waiwayo yana duban idanunta farare masu haske sosai,wanda suka dan qara girma kadan
"Wai don Allah bakajin kunya?,ciki fa ka yiwa mace" dariyar da bai shiryawa ba ita ta kubce masa,nutsatstsiyar dariya mai wani irin siririn sauti da tasa fararen haqoransa bayyana,sakalci da shirmen quruciya dai a cikin jinin widad qilan yake,sai tayi kaman ta daina sai wataran ta sakankance ta yanko maka wata wautar,kallonta yake kawai yana dariyarsa,yama rasa wacce amsa zai bata.
Turo baki gaba tayi ganin yadda yaketa mata dariyar yana kuma kallonta
"Kaiko a jikinka,ka yiwa mace ciki kuma kana siyan kayan jarirai,bakajin kunya ma mutane su gane". Takowa yayi gaba kadan ya tsaya a gabanta yana kallonta,ko yaushe qara kyau takeyi tana zama wata balarabiya,ba wanda zai kalleta ya yadda ta iya hausa,hakanan babu wanda zai kalleta ya yarda akwai ciki a jikinta
"To ko mutanen duniya zasu fara boye kawunansu ne?" Kai ta daga ta kalleshi don bata gane me yake nufi ba,saiya kashe mata ido daya
"Ai kowa ma ta yadda wannan cikin ya samu ta haka yazo,ciki harda ni dake da......." Da sauri ta rufe masa bakinsa bayan ta danyi dage kadan,saita janye hannunta da sauri
"Kuma me ya kawo wannan maganar?"
"Kece mana" ya amsata yana qunshe dariyarsa
"To naji,amma bakasan fa me za'a haifa ba kake diban kaya"
"Ko meye kika haifa wuud(qauna/soyayya matsananciya) inaso,idan ana haifar rabin mutum ma kika haifamin zan karba hannu bibbiyu" ido ta zaro tana kama haba
"Rabin mutum?,wai?" Yadda tayin ta bashi dariya,sai.ya janyeta cikin hikima sukaci gaba da zaban kayan unisex a tare,ya kuma tura mata option na zabar favourite colors dinta a dabarance,ta zaba din sosai,duk da tanayi tana waiwaye kamar wadda ke aikata wani abu ba dai dai ba.
**************Karfe sha biyu da mintuna na dare motarsu ta tsaya qofar gidansu na bauchi,a sanyaye widad din ta maida bayanta jikin kujera tana kallon gidan,wani mugun tsanar gidan na shigarta sosai,tana jin kamae ta balle murfin motar ta fice ta kama hanyarta,inda zai bata zabi....da salin alin zatace masa ya kaita gidan hajiya ko gidan uncle muhsin,to amma koda ta fada din tasan ba lallai yayi hakan,don zaice mata ne dare yayi,ko baya ga haka ma.....iya kusancin da suka samu a yanzu a tsakaninsu,bata tunanin zai bari tayi nesa dashi.
Shi ya fara fita daga motar yana cewa
"Ina zuwa" saita gyada kai kawai,tana jin yadda qirjinta yake bugawa,tana iya hangensa daga inda suke zaune a motar ita da umar qaninsa daya daukosu,yanata knocking.
Tun yana qwanqwasa a hankali har ya koma bubbugawa da dan tsauri,wasa wasa sai gashi sun kwashe mintuna masu tsaho yana bugawa,amma qofar ko gezau,babu alamun za'a bude musu gidan,har umar dake zaune cikin motar ya miqe ya fita ya soma tayashi bugun.
Tun ransa bai baci ba har ya soma baci,don ba cikin gida ba......muddin dai ba wani abu bane ya samesu ba a irin bugun da yakeyi yasan har maqota sun jishi,sannan ma ba ita daya bace a gidan,idan ita bata ji ba saboda tayi ciki......shi kuma lawal fa dake kusa kusa?(dan dan uwanshi daya dauko sanda zaiyi tafiya).
"Kira number lawal ka hadani dashi" ya fada yana duba agogon hannunsa,umar ya fidda waya ya fara kiransa,amma wayarsa na a kashe,sabanin ta hafsat daketa ringing kuma ba'a daga ba,a handsfree take don haka yaji me computer ta fada, kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai sunji motsi ana tambayar waje,abbas ya tsaya kam yana riqe da qugunsa yana kallon qofar,umar ne ya amsa mata da
"Mune" sai aka fara buda qofar gidan a hankali kamar mai ciwon hannu*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*A RUBUCE TAKE*
(K'addarata)
*Book 02*
Page 03
Sakin qofar tayi tayi gaba,abbas din yabi qofar da kallo sannan ya taka zuwa cikin gidan,ya cimmata sanda take juyawa abinta zuwa ciki,daure da zanin atamfa saman wata kodaddiyar rigar baccinta daya jima yana ganinta jikinta,jin takunsa ya sanyata dan dakatawa kadan ta waiwayo,suka hada ido.
Duk da dare ne da kuma qarancin haske,amma tana iyabhangen yadda taga yayi wani mugun fresh,qamshinsa ya cika wajen,ya mata kyau,amma data tuna a yanzun tare da wa yake sai taji komai ya gushe mata,kishinta ya motsa sosai,wanda tunda umar yazo ya dauki motar da zummar daukosu tahau kan zafinta,ita tunda suke tare dashi bata taba ganin yayi kyau da gogewa irin hakan ba,kuma ba wannan bane ai zuwansa aikin hajji na farko ba
"Me kikeyi mintuna kusan nawa muna tsaye muna bugu?" Ya fada ransa a dan bace
"Bacci ne fa ya daukeni" ta fada murya a cunkushe tana bata rai,sai ya janye idanunsa yana dan jan qaramin tsaki
"Ta yaya zaki kwanta kinsan muna hanya?, at least dai ai kya tsaya kiga shigowata" ya fada yana qoqarin buda gate din gidan da kansa yana yiwa umar maganar ya shigo da motar ciki dare yana qara yi.
Ranta ya sosu,ta tura kayan baki gaba tana jin kamar ta maida masa magana,ason ranta ta shige ciki,amma sai taji tana son tsaiwa taga yarinyar,ta sake tabbatarwa babu cikin da a kullum ta kwanta cikin mafarkinta take ganin kamar tana dashi.
Tana tsaye daga gefan har umar ya shigo da motar ya fakata a parking lot na gidan,ya kasheta sannan widad ta buda murfin motar ta fito tana jin ranta da zuciyarta duka babu dadi.
Rawa qafafun hafsat suka danyi,ta kadu sosai da yadda taga yarinyar ta sake canzawa,sanye take da wata lafiyayyar abaya baqa sidik mai sulbi, balarabiya sakkk!! Haka ta koma,hasken fatarta sai daukan ido yakeyi,ta sake cika sosai,ta zama cikakkiyar mace,kai bazakace widad din da aka mata aure da qananun shekaru bace,duka cikin watannin da basu wuce biyu da tafiyarsu ba irin wannan gagarumin sauyin na babu zato bare tsammani?.
Kasa amsa gaisuwar da take mata tayi,gaba daya a rude take har umar yayi musu sallama ya fice daga gidan bayan abbas ya masa izinin tafiya da motar ya kawo masa ita gobe.
Gajiya gami da tsanar data yiwa gidan ya sake kashe mata jiki,ta kallai abbas
"Uncle bacci nakeji fa" yadda tayi maganar a mugun shagwabe ya taba ran hafsat sosai,saidai a wajen widad din hakan ba komai bane,don kusan a haka yanzun ta saba magana dashi
"Muje sashena,nasan bangarenki akwai qura kam yanzu,dare kuma ya riga yayi bare ki gyara" ya amsa mata a tausashe yana mata wani irin sassanyan kallo da ya riga ya saba yi mata shi,har baisan yana fidda kansa da kansa daga idanunsa ba.
Turqashi!.....me abbas din yake nufi?,taje sashensa ta kwana?,aiko sama da qasa zata hadu ba zata bari hakan ta faru ba,wannan ba komai bane ba face zallar rainin hankali,ta gama fadi tashin gyaran sashen saboda shi sannan yace wata ce zata kwana?,uwa uba ma watansa nawa basa tare,hakan yana nufin zai karbe kwananta na yau ya bawa yarinyar?.
Taku biyu sukayi tasha gabansu,dubansu takeyi kai tsaye
"Ba inda zata ta kwana wallahi,bazan dauki wannan rainin wayon ba" ta fada tana fidda idanunta.
Ido yadan qanqance yana dubanta
"Me kikeyi ne haka?"
"Abinda idonka ya gane maka" kafin abbas din ya sake cewa komai widad ta zame hannunta a hankali ta fara takawa zuwa shiyyar sashenta,shi da hafsat din dukansu suka bita da kallo,sai ya motsa da sauri yabi bayanta,yayin da hafsat ta rakasu da ido qirjinta kamar zai qone saboda zafi da tsananin kishi.
A qofar sassanta tana gwada keys din hannunta ya cimmata
"Me zakiyi a ciki?" Murmushi ta sake masa a nutse
"Zan shiga na kwanta ne uncle dare yana sake yi" ta fada a narke
"Amma ai ba'a gyare yake ba,nace muje part dina ki kwanta a can kafin safiya" a nutse ta girgiza masa kai,fuskarta still da murmushi
"Zan kwanta a nan din uncle,awa nawa ne gari ya waye?,kada ka damu,kana buqatar hutu,kaje ka huta" gaba daya saita gama kwance masa kai,abinda ya kamata ace hafsta dince tayi ita ta gaza sai 'yar cikinta,wani irin qauna da kimar yarinyar ya sake qaruwa a idanunsa,ya santa gwanar tsoro ce,kawai dai tayi hakanne don ta samar masa da kwanciyar hankali da nutsuwa,ya fuskanci wannan din kusan a dabi'arta yake,batason hayaniya sam,sai ya rasa me zaice mata,ya matsa ya karba keys din ya gwada na qofar ya bude sannan ya tura yayi gaba tana biye dashi.
Sosai wajen yayi qura,da kansa ya dinga saka tsintsiya yana kade mata hanya har zuwa bedroom dinta,sai daya tabbatar ta gama komai ta kwanta sannan ya baro sashen.
Runtse idanunta tayi zuciyarta na matsanancin bugu da tsoron dake shigarta kamar zuciyarta zata faso qirjinta ta fito,tana ji har cikin Zuciyarta kamar ana tunkudata ta fice,amma can qasan zuciyarta tana kiran sunan Allah kadan kadan,abinda ya kawo sauqin yanayin da takeji din wanda keta azalzalarta kamar ana gaya mata cikin kunnuwanta.
Bai samu Hafsat din a wajen ba,sai bai wani damu ba,har yanzu Zuciyarsa tana cike da mamakin halayenta, kullum babu sauyi?, sai sake ta'azzara al'amuranta sukeyi?,da wanann tunanin ya isa sassansa.
Ba laifi babu datti hakanan babu qura,yaci gaba da takawa har dakin gadonsa,yana tura kansa,sautin sheshsheqar kukanta yana masa maraba.
Dauke kansa yayi kamar bai ganta ba,baqinciki yana cika masa zuciya,baiga me akayi mata ba da zata zauna a daren daya dawo yana buqatar ya huta ta tusashi da koke koke ba,idan ita bai rufeta da fada ba bazata sashi gaba tana masa kuka ba,sai kawai ya fara rage kayan jikinsa ba tare da yabi ta kanta ba,rabin hankalinsa yana ga widad da yadda yaga taqi sakewa,lallai tsoronta ya dawo,irin tsoron daya ninka na baya,sai wani bangare na zuciyarsa ya bashi ko juna biyun da take dashi ne,qaramin murmushi ya kubce masa sanda ya tuna da ajiyarsa dake jikinta,dai dai sanda muryarta ta ratsa kunnensa cikin sautin kuka
"Da wannan wulaqancin da kakeyimin gwara kacemin ka gaji da zama dani na tafi gid......."
"Hey..... stop it dallah!" Ya katseta da mugun sauri cikin bacin rai yana dubanta,bacin ran data gani a idanunsa sun ninka nata don haka dole tayi shuru tana binsa da kallo
"Banason rainin wayo da wulaqanci cikin daren nan,hutu nake da buqata,idan qorafi ya shigo dake ki tashi ki fita ki bani waje,idan kin fita idan kinga dama ki wuce gidan ban riqe miki qafa ba" sosai.maganar ta daga mata hankali sannan ta bata mata rai,ta sake fashewa da kuka ta miqe tana daukan yusra ta fice a dakin,yaja tsaki yabi bayanta ya kulle qofarsa ya dawo ya wuce bandaki,gaba daya ta gama fita a kansa,fushinta ko kukanta ya daina damunsa sam.
Wannan abun daya faru a daren ya sake tunxura zuciyarta,ta kasa kuma bacci sai data kira ummanta,cikin daren suka qulla abubuwa masu yawa da suke saka ran zasu aiwatar,ko akan widad ko akan abbas din,duk wanda nasararsu ta fada a kansa.
*********Da qyar ta wayi gari da wani irin matsanancin tsoro daya haifar mata da ciwon kai,inda Allah ya taimaketa washegarin saiga su nujood harda hajjaaa sunzo mata,ta samu tadan sake,daga qarshe hajjaa ta tafi tabar mata nujood ta tayata kintsa sashen da sauran gyare gyare,wannan ne ya sanyata tadan warware,saidai komai a darare takeyinsa,koda abune yayi babban faduwa yanzu zata firgita,har nujood ta fahimta ta tambayeta
"Hakanan nakejin haka,nima bansan dalili ba"
"Saikiyita kiran sunan Allah da addu'a"
"Inayi,daqyar nayi bacci jiya"
"Zan karbo miki addu'ar yawan firgita a wajen ya sayyadinmu" da haka suka fada wani zancan,tana ci gaba da addu'a cikin ranta duk sanda taji irin hakan,da haka ta dinga samun sassauci cikin ranta.
Dawowarsu daga saudiyyan sai komai ya sake canzawa,gaba daya hafsat din ta tattara sanya idanunta da komai ta aza akan abbas da widad wadda bata sakata a lissafinta ba kwata kwata,don abinda yake gabanta shi ya dameta,saidai duk wata tijara da abubuwan da zatayi tana jinta daga farfajiyar gidan,ko idan guri ya hadasu,ko daga kai ta kalleta batayi bare akai ga jallin tanka mata,tunda bata taba tararta gaba da gaba ta kama sunanta ba tun sanda abbas din yaja kunnen hafsat,ita a yanzun kawai burinta abbas yace ta shirya su koma kaduna,gaba daya ta tsani garin wani muguwar tsana,duk ranar da ba girkinta bane da qyar take iya bacci saboda wani irin tsoro da yake shigarta,da qyar take hana kanta fita a wasu dararen,saidai ta zauna bakin qofar falo tayita kuka tana jin fita kawai takeson yi.
A WANI DARE karfe sha biyu da rabi na dare,har ya shiga sassansa ya kwanta ya tuna kamar yau din da daddare batasha magungunanta na anti natal ba,ya sauko daga gadon hafsat na gefe tana kwasar baccinta ya fito.
Kamar mutum ya dinga hangowa daga nesa,sai ya sauya yanayin tafiyarsa cikin hikima da dabararsu ta jami'an tsaro,bai wani jima ba ya gane widad dince ke nufar qofa,cikin wani irin zafin nama ya cimmata cikin takun da basu gaza biyar ba,saiji tayi caraf an riqota,ta waiwayo suka hada ido,cikin matuqar kaduwa yace mata
"Ina zaki da daren nan?" Kamar jira takeyi ta fashe da kuka
"Fita nakeson yi,banason gidan nan uncle" mamakinsa ya qaru,to duka me yake kawo haka?,wannan shine karo na biyu daya taba ganinta zata fita din.
A tausashe ya kama hannunta yana son maidata ciki,saita kuma saka kuka
"Don Allah uncle" shuru yayi ya zuba mata ido,yadan lumshe idanunsa hadi da budesu
"Muje ciki magana zamuyi" dole ta sakar masa hannun ya riqeta zuwa ciki.
Bakin gado dukansu suka zauna yana dubanta
"Me yake faruwa?"
"Banason gidan nan" ta amsa masa kanta tsaye tana qwalla
"Me yasa?"
"Tsoro nakeji" shuru ya danyi,ya ciro wayarsa yana son kiran dr,saidai yaga dare yayi,amma duk da haka yanajin ya zama dole ya kirata din.
Bugu daya