Showing 78001 words to 81000 words out of 98640 words
Chapter 27 - A RUBUCE TA KE PART 2 COMPLETED huguma 2023 .txt
a rayuwarsu,ba wanda ya sake tada zance makamancin wannan a tsakaninsu,ta koma masa widad din nan dake rikita duniyarsa,ta sake shigewa rayuwarsa da zafafan sirrikan mallakar zuciyar miji tsaftatacciyar hanya babu boka ba malam,sai addu'a data duqufa da ita haiqan a kowacce sujjadarta akan Allah yaci gaba da mallaka mata abbas din.
Da yake zuciyarta akwai haske da tsarki,sai komai yake zuwa mata yadda takeso,abbas din ya samu a gareta har fiye da yadda ta zata,ta sake gasgata cewa addu'a ba qarya bace,hakanan duk macen data sadaukarwa kanta wa mijinta,tabbas zai zama bawa a gareta ba tare daya ankara da hakan ba.
Samun nutsuwa da kwanciyar hankalin da yayi daga widad yasa yake aiki tuquru cikin garin katsina,aikin da ya sake tamfatsa sunansa,ya kuma sake sanya sunansa a bakunan manyansa,suka kuma ji tabbas hazaqarsa da qoqarinsa sun girmi wannan matsayin da yake kai a yanzu.
Budi sosai ya dinga shigo masa,hatta da kasuwancinsa kamar an qara masa albarka,cikin lokacin ya rasa wanne tukuici ya kamata ya bawa widad din,ba tare da saninta ko shawara da ita ba ya dallo mata sabuwar mota,ya kuma siya wani babban gida daban acan qasan layinsu dake garin bauchi ya ajjiyeshi reserve.
Randa ya danqa mata motar tsananin murna ya sanyata kasa runtsawa,kyau da tsadar motar sai takejin kamae tafi qarfinta kamar ba tata bace
"Madam,azo a kwanta hakanan murnar ya isa,ko kin manta bake kadai bace?,anya bazan fasa wannan kyautar ba?" Da sauri ta qaraso ta haye gadon tana dariya
"Afwan yallabai,suma babies din naka taya ummarsu murna sukeyi" ya saki murmushi ya yaye rigar baccin jikinta yayi kissing cikinta sannan yaja mata duvets ya rufeta.
[5/24, 12:41 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 38
Duk wajen wanda hafsat tasan zata ya yiwa abbas magana ya maidata taje amma abbas yayi biris,yaqi bawa kowa fuska yayi masa zancan hafsat din,suma din kuma suna kunya da nauyin yi masa maganar,saboda kowa yasan irin haquri da wahalar da yasha da ita,a yanzun sai yakejin ya samu wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali da ya jima baiji irinta a rayuwarsa ba.
Duk yadda takai ga bugawa bataga alamun samun nasarar komawarta gidan abbas ba,cikin qasqanci mugun bacin rai da baqinciki mai tsanani ta dauki shawarar da ummanta ta bata
"Tunda yanzun itace ke fada masa yaji,babu wata hanya data rage illa mu wanke qafarmu muje kanon,mu samu kakanta shi kadai nakejin yayi saura da zai gaya masa yaji,karkiyi baqinciki,idan kika samu nasarar dawowarki gidan,wannan karon ko komai nawa da naki zai qare saimun salwantar da ita,ko ta fita daga gidan d qafafunta,koshi ya koreta,ko kuma tabar duniyar gaba daya".
Washegari suka shirya suka nufi kano ita da ummanta,ummu ta ganesu,ta kuma tarbesu kadaran kadaham,basu gaya mata abinda ya kawosu ba amma sun nemi ganin alhaji tsoho,ta sanar masa tayi musu iso ta kuma basu guri.
Yadda ta dinga kuka tana gaya masa qaramin ciki ne a jikinta tana roqon alhaji ya sanya baki ya karyar masa da zuciya,duk da yana sane da komai da yake faruwa,ba kuma wai bayajin ciwo ba,to amma hausawa sunce d'a na kowa ne,kuma har yanzu shi akwai wannan jinin na karamci cikin jikinsa,wannan ya sanya ya tabbatar mata da cewa zata koma dakinta in sha Allah ta riqe yaranta.
Murna kamar ta taka rawa ita da umman nata,ta yamutsa fuska bayan sun fito ta goge sauran ruwan hawayen dake fuskarta
"Yadda kika qasqantar dani kika sanya na nemi alfarma daga wajen iyayenki,na zubda ruwan hawaye na duk ta dalilinki wallahi bazan qyaleki ba" hafsat ta fada cikin cin alwashi da buri.
Sanda alhaji yayi kiran abbas din yana office,yabar dukka aikin dake gabansa ya saurari alhajin.
Yayi mamakin jin ta inda hafsat ta bullo,bazai iya musu da tsohon ba koda wuqa ya dora masa a maqoshi,saidai yasan maganin hafsat,idan tasan wata batasan wata ba,don haka bai musa din ba yace ya karbi komen ya maidata,amma alhajin yayi masa alfarmar sanar da ita cewa,daga rana irin ta yau,duk randa ta sake yunquri ko ta daga masa hankali to a bakin aurenta.
Alhajin baiso yayi wanna furucin ba,to amma kuma mai daki shi yasan inda yake masa yoyo,duk mutumin da ya iya irin wannan hukuncin akan uwargidansa duk da zuri'ar dake tsakaninsu......shi kadai yasan irin abinda yake fuskanta.
Saida alhaji ya nemi magabatan hafsa sukayi magana ta waya,ya kuma shaida musu sharadin abbas sannan yace musu ya maidata.
"Alhmdlh,Allah ya qara girma,ya saka maka da alkhairi yasa a gama lafiya" kawunta da ya cire hannunsa daga lamarin saboda baqincikin hafsat da uwarta ya fada,yanason 'ya'yan yan uwansa,amma hafsat ta fita zakka ko a cikin marasa mutuncin gidan,dukka qoqarin da yakewa rayuwarta yana yine kawai don girman zatin Allah da kuma hakkin zumunta.
A washegari ta tattara kayanta ta koma gidan,gidan da har ta debe haso da tsammani daga zamanta a cikinsa.
Ranar data koma ta tsammaci zai maido mata dasu mimi,saidai har washegari shuru,washegarin ma data saka rai shima dai shuru,haka ta wuni gidan ita daya kamar mayya,zuwa dare ta kasa haquri,ta daga waya ta kirashi.
Dai dai sanda suke zaune a falonshi shida widad da tsohon cikinta da take gab da shiga watan haihuwarta,tana saman kujera yana zaune a qasa,ya dora qafafunta saman cinyarsa yana matsa mata saboda yadda suke yawan kumburar mata,iya girman cikin kawai ya isa ya gaya maka cewa lallai twince dinne da gaske,labari yake bata kan gagarumin promotion din da yake sanya rai za'a yi masa koda wanne lokaci,muqamin CP wato commissioner of police,saidai akwai masu so da yawa,amma yana fatan indai zai zame masa rayuwarsa data iyalinsa alkhairi Allah ya tabbatar masa.
A yanzun widad din itace abokiyar shawararsa da baya iya boye mata kowanne sirri nasa,duk abinda ya taso masa zai zaunar da ita yayi shawara da ita,Allah ya hore mata wani irin kaifin qwaqwalwa da basirar da muddin ta bashi shawara yana ganin haskenta.
"Waye yake kira?" Ya tambayeta saboda tafi kusa da wayar,ta kalli screen na wayar sannan ta amsa masa tana miqa masa wayar
"Mummyn mimi ce" qaramin tsakin da baisan ya fito ba yaja
"Ki daga kice mata hutawa nakeyi" kai ta girgiza
"A'ah fa,ba ruwana,kayi mata dai bayani"
"Bazanyi ba,ke nace ki daga,idan kuma ba zaki daga ba ki gayamin kanki tsaye"
"Allah ya baka haquri" ta fada tana girgiza kai,sannan ta daga wayar takai kunnenta
Cikin kwantar da murya da kuma laushi tayi sallama ta dora da
"Daddyn Mimi yanzu ba yafiya tsakanina da kai kenan"
"Sorry,yana hutawa ne yanzun haka,saidai ki sake kira anjima" wata ashar ce ta tasowa hafsat din amma ta haqura ta danneta, zuciyarta kamar zata fito ta bakinta,saboda tsabar wulaqanci ita zai bawa wata ta daga mata waya?,a duniya yanzu cikin wadanda ta tsana babu sama da widad,sai taja mugun tsaki ta dauke wayar daga kunnenta,saidai ashe widad din ta rigata gimtse kiran.
Safa da marwa kawai ta dinga yi a falon,da qyar ta taushi zuciyarta da dare ta sake kiransa amma bata sameshi bama kwata kwata,haka ta kwana biyar cikin gidan,ga kayan amfaninta duka sunyi qasa,sai takejin gidan gaba daya ya sauya mata tunda ba haka ta saba rayuwa a cikinsa ba.
Tasan yaran suna gidan yaaya bara'atu,koda ta kira tace don Allah tasa a kawo mata su sai tace
"Babansu yace zai kirani ya gayan duk sanda za'a kaisu din" kan bala'in ubancan,ita da yaranta ma sai an shata mata layin sanda zata gansu?,me abbas ke nufi da ita ne?,anya zata iya jura kuwa?.
"Dole ki jure muddin kinason zama cikin gidan" haka anty ummee tace da ita,haka taci gaba da hadiyar baqinciki,cikin lokaci kadan ta fara rama.
Sai da tayi sati uku da dawowa sannan umar ya shigo mata da kayan abinci zallarsu,bata ga alamun nama kifi fruits ko drinks da ya saba hadawa dasu ba,babu kuma kudin da yake dora mata akai,wannan karon ta kasa daurewa ta kirashi
"Iya abinda zan iya kenan,idan zaki zauna ki zauna,idan ba zaki zauna ba qofa a bude take" amsar da ya bata kenan ya kashe wayarsa.
Tana kuka sosai ta kira anty ummee tana gaya mata,don ta kasa samun ummanta
"Ke kin cika gajen haquri,tunda bada yunwa ya barki ba saikiyi haquri ai" ta fada a mugun gajiye,saboda itama yanzun ta kanta takeyi,nata ballin kissar ya fara tashi,miji da sauran danginsa sun fara ramfota.
Cikin aljannar kare abbas din ya sakata,dukkan wani abu da bai zama dole a addini ba ya janye mata shi,kudi da yake bata na kashewa da qari da yake mata da sauran wasu kayan alatu da basu zama tabbas ba gaba daya ya janye,yanason ya gani shin da gaske ta rusuna?,saidai a yadda ta fara rawa da kiraye kiraye zuciyarsa ta gaya masa
"Mai hali fa baya fasa halinsa".
Sai da tayi wata guda da komawa sannan ya shirya zuwa bauchi,wannan karon da widad din za'a je,abinda ta manta rabonta dashi,ta jima sosai rabonta da bauchin,gaba daya ma garin ya fita a ranta tun wancan lokacin,yanzun ma tsaowar bikin nujood ne zai kaita garin,don dole taje tayi kara duk da nauyin da tayi,abun kuma yazo dai dai da saukar 'yar yaaya bara'atu.
Ya zame mata dabi'a,a duk sanda zaiyi tafiya bata qasa a gwiwa ita ka shirya masa komai,koda weekend din kuwa zaije bauchi,duk dadai ya jima rabonsa da bauchin,tun bayan kammala bincikensa da sallamar hafsat da yayi.
Koda ta gama da qyar ta iya miqewa da taimakonsa hannunta riqe da bayanta tana cije lebe
"Anya madam,kodai triples ne computer bai gano dayan ba?" Ya fada cikin sigar tsokana yana boye dariyarsa,harara ta balla masa
"Ta ina zasu fito?,yallabai ka barni ma naji da wadan nan guda biyun,bansan ina zaka kai son yara ba"
"Yaya ai rahama ne,banqi kowacce shekara na dauki sabon baby cikin gidan nan ba" kukan shagwaba ta sake masa tana yarfa hannu,tayi tayi qafa ta taku takai gareshi ya rufeshi da duka kamar yadda ranta keso amma ta kasa,wannan ya sake hasalata ta sakar masa kuka sosai.
Shi da affan suka dinga mata dariya,duk da yaran baisan me akewa dariyar ba amma ya taya babansa,sai daga bisani daya fuskanci da gaske take sannan ya aje affan din yana cewa
"Baka kyauta ba affan,kawo hannun taho ki rabu dashi" data samu kanta tana isowa kuwa abbas din ranqwasa saman kansa,ya dafe wajen yana shafawa a hankali,sai tasa hannu ta tureshi gaba daya yayi baya ya fadi.
Motarsa ya ajjiye ya dauki tata motar,a ciki suka tsara tafiya bauchin dama,tunda already yana da wata motar a gida,idan sunje sai ya bata abarta tayi ziyarce ziyarce itama.
Tunda suka idar da sallar asuba basu koma ba,sun gama shiri tsaf sai suka dauki hanya,sammakon da sukayi ya basu damar isa da wuri,taso ta masa magana kan ya sauketa a gidan uncle muhsin amma sai tayi Shuru gudun ta zama mai yawan qorafi,tasan dai yana sane da sharadin raba musu muhalli.
Sun shiga layin sai taga yana fakawa qofar wani gidan na daban,tabi gidan da kallo,yakai girman nasu gidan,a tsare yake kamar dai nasun,ya fita ya bude qofar sannan ya tura gate din,ya dawo cikin motar ya jata zuwa ciki.
A parking lot ya tsaya ya kashe motar ya waiwaya yana kallon widad din,ya sakar mata murmushi sannan ya fita a motar,ya zagayo side din da take zaune ya bude mata sannan yace
"Welcome to your new home" kallonsa tayi da alamun son qarin bayani,sai ya dage mata dukka girarsa
"Eh ga naki gidan.....kin dauka mance?,ni na isa nayi saken mantawa da sharadin abba?,ban shirya rasaki bafa kwata kwata koda kuwa da wasa" yayi furucin yana miqa mata hannunsa,saita dora nata akai murmushi yana qwace mata,ya taimaka mata fita a motar,ya fidda affan ya aza a kafadarsa suka wuce cikin gidan.[5/25, 2:37 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 39
Duk da kayanta ne na wancan gidan nasu amma gidan yayi bala'in burgeta,komai ya tsaru,an kuma shirya mata shi dai dai da ra'ayinta da kuma yadda takeson gida ya kasance,ta dinga satar kallon abbas tana mamakin yadda ya karanci komai nata,me takeso,meye bataso,walwala da damuwarta,sai taji zuciyarta ta karaya,ta samu kanta da addu'ar kada Allah ya kawo abinda zai sake rabasu ko ya saka shakka ko rudani a tsakaninsu har qarewar numfashinsu.
Widad din mutum ce mai matuqar qoqari,a tsaye take kan hidimar gidanta,duk da komai a gyare yake amma sai da tayi goge goge,ta kuma samar musu da abinci duk da akwai taimakon abbas din yana kama mata,sannan suka sake wanka gaba dayansu suka shirya don wucewa gidan saukar yaaya bara'atu.
Yana riqe da hannunta suka shiga motar tata
"Inajin aminatu zanje na roqa abarmiki,wannan aikin yana miki yawa" dadi sosai ya kamata,ta murmusa tana cewa
"Amma da ka kyautamin qwarai,inason yarinyar,tana da hankali,amma kuma ranka ya dade,naga kaman baka da ra'ayin daukan mai aiki" kallonta yayi sannan yayi murmushi
"Wayon tsiya gareki,nasan me kikeso kice,na farko amintu ai bame aiki bace,qaramin qarfi garesu,daukotan zai zama kamar taimako,kamar yadda tasa aka dauko lawan yaso ya zame mana wani abu daban,na biyu kuma ina da tabbacin ko ire iren aminatu dubu zan cika miki gidanki dasu,ba zaki bari kowacce tayi hidimar mijinki ba,ba kuma zaki sakar musu hidimar gidanki gaba daya sai yadda sukaso suyi ba,munsan aminatu muna da tabbaci akan tarbiyyarta,ba zata batamin yara ba,kuma na tabbatar baki da sakaci da zaki kasa sanya ido a kanta,ko yaya motsinta ya canza nasan in sha Allah zaki kula,zaki kuma tsawatar" shuru tayi tana dan gyada kai,komai yayi wato yana sane,yana kuma da hujja akai
"To Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" ya fada cikin nuna kulawa.
Sai da ya ajjiyeta a qofar gidan sannan ya miqa mata key dinta yana jifanta da wani kallo,saika dauka sabon saurayi da budurwa ne
"Drivernki ya gama aikinsa ranki ya dade" dariya ta tsuntsire da ita
"Godiya nake,zan ninka maka salary dinka"
"Da kuwa kin kyautawa dan marayan Allah" ta girgiza kai tausayinsa yana dan tabata
"Allah ya jiqansu ya kyauta makwancinsu ya kyauta namu zuwan"
"Ameen ya Allah,Allah yayi albarka" ta amsa da ameen ya fita a motar yana gaya mata zai qarasa gidan suraj da yake basu da nisa,idan sun shiga wata sabgar yasan zata iya maida kanta gida,idan kuma ya dawo da wuri sai ya maidata
"Koka maidani dawowa zakayi,kasan dai kwanan waye ai" harara ya balla mata,tayi kamar bata gani ba ta wuce ciki tana qunshe dariya tana riqe da hannun affan da ya fara koyon tafiya,wannan yasa ta dinga takawa a hankali cikin kula da takatsantsan.
Tun daga qofar gidan jama'a ne,ta dinga gaisawa da mutane sunayi mata sannu saboda ganin yadda tayi nauyi sosai da uban ciki a gaba,yan mata matan suka daukar mata affan din suka kutsa cikin gidan dashi ita kuma ta tsaya tana ci gaba da gaisawa da mutane.
Hafsat din na tsakar gida anata rabon tuwon sauka,gaba daya ba cikin sukuninta take ba ganin yadda su mimi suka shiga sabgarsu cikin mutane,ko ta kanta basayi,yaran sunyi fes dasu sunyi haske sunyi qiba
"La la la,da gani babu tambaya wannan yaron sir abbas ne" wata qanwar mijin yaaya bara'atu ta fada bayan an shigo da affan ciki
"Tubarkalla ma sha Allah,yaro ya debo ruwa biyu,miqomin shi na ganshi" ta miqa hannu tana karbar affan dake fidda qamshi cikin navy blue din jeans da shirt dinsa.
Sosai maganar taja hankalin hafsat,gabanta ya fadi ta waiwaya tana kallon yaron dake da yawan fara'a,abinda ya qara masa farinjini kenan,saita dauke kanta wani abu yana tsaya mata a wuya,shi da babansa sukazo lo shi kadai?, indai kuwa shi da babansa ne lallai abun abbas qara ta'azzara yakeyi,har yazo bauchi amma bata da mutuncin da zai gaya mata yazo din?.
Bata gama wanann taraddadin ba widad ta danno kai,kamar kunna fitila