Showing 75001 words to 78000 words out of 98640 words
Chapter 26 - A RUBUCE TA KE PART 2 COMPLETED huguma 2023 .txt
yana magana da ita
"Ina hannun police,sun kamani ne akan batun maman affan, wallahi bakiga mugun dukan da nakesha a hannunsu ba,yanzu haka basusan da wannan wayar a hannuna ba,sun gama dukana sun fita su hutane na kiraki,don Allah kizo kiyi beli na,ki fitar dani daga wannan masifar da kika jefani a ciki". Wata hajijiya ce ta kwasheta ta jefar,dama da gaske ne kenan?,ashe dai zancen bai mutu ba?,wannan wacce irin masifa ce,tana zaton komai ya lafa,tana zaton ta samu nasara ashe qura tana baya
"Idan na sake nazo wannan wajen lawan na zama nama na tabbatar,ka jirani zan nemi abban mimi na gaya masa qarya da gaskiya,zaiyi magana kosu waye na tabbatar zaka fito" saita yanke kiran tabar lawan da waya a hannu cikin matuqar mamakin yadda takeso ta barshi shi kadai a masifar,bayan ita ya yiwa aikin.
Sanda taketa yunqurin kiran wayar abbas din a kashe take,dai dai sanda ya kashe wayarsa bayan widad ta yaba masa maganar data masa zafi matuqa,tayita kira a jere amma amsar daya ce,haka ta fito wajen baqinta tana rarraba idanu,fuskarta a yamutse,gumi yana tsattsafo mata ta kowacce kafa ta jikinta
"Don Allah ina zuwa" ta fada tana yin waje da hanzari zani a hannu kamar zata ci da baka ta fara kiran wayar habiba tana dosar sassan abbas da nufin fakewa a can tayi wayar,don can dinne bata da haufi dashi,tana da tabbacin babu kowa a ciki bare tayi shakka ko taji dar dar din wani zai iya jinta.
Koda ta bude sashen abban din sai data tabbatar ta qule har cikin bedroom dinsa,tsabar hankalinta a tashe yake bata ma yi tunanin yadda akayi qofar bedroom din yake a bude ba,burinta kawai ta isa dakin habiba kuma ta daga wayarta.
Sama sama ya dinga jin magana yana tsaye gaban madubin bandakin yana kallon fuskarsa,ya matsawa kansa da tambaya da kuma tunanin son sanin yadda akayi ya yankewa widad wannan hukuncin,ya akayi ya aminta da zancan hafsat,a irin baiwa da Allah yayi masa,a irin matsayi da yake dashi da rank a wajen aiki?, tabbas wannan babbar jarrabawa ce,kuma qaddara ce mai girma,wadda ya godewa Allah da ya taqaita masa komai,bai jarrabeshi da sakin widad ba.
Sautin muryar hafsat da ya fara ji yasa ya tako a hankali zuwa gaban qofar,har ya sanya hannu zai bude qofar sai ya fasa,kalamanta cikin rudani da tashin hankali suka fara shiga kunnuwansa
"Ina cikin tashin hankali habiba,komai yana iya faruwa dani,wannan maganar dai bata mutu ba yadda malam yace,yanzu haka lawan yana hannun 'yan sanda ba,na tabbatar zuwa yanzu indai sun gama bincikarsa to asirina ya gama tonuwa,don ba lallai ya iya iurewa dukansu wallahi sunana zai fadi,ki taimakamin habiba a sake danne maganar nan,dama hankalina tun ranar da sukayi maganar zuwa kotu ba'a kwance yake ba,ko baccin kirki bana iyayi wallahi,idan har abbas yaji maganar nan bani da sauran dabara kuma sai abinda y........" Gaba daya ya rasa karsashi da qwarin gwiwar tsaiwa yaji qarshen maganganunta,hankalinsa yayi mummunar tashi,bayan sharri makirci da qazafi harda bin malamai hafsat din ta hada dashi?,a yaushe?,kuma yana me?,sai kawai ya buda qofar da wani irin qarfi,qarar qofar taja hankalin hafsat har sauran maganar ta maqale mata a maqoshi.
Batasan wanne yanayi ta shiga ba,suma tayi a tsaye ko mutuwa tayi ta dawo?,itadai ta bude idanunta taga abbas a gaban mudubi riqe da biro yana rubutu,ta dinga qoqarin zaqulo kalamai daga qasan maqoshinta amma kalma daya ta gaza fita daga bakinta,har ya kammala rubutun ya iso inda take ya ajjiye takardar a gefanta
"Daraja daya zuwa biyu kawai zakici yau a hannuna,na farko iyayen widad tun sunan zallar tauhidinsu,sun miqa ki kotun ubangiji wadda babu wata kotu a gaba da ita,babu wani adalin alqali da yakai ubangiji iya hukunci,to kije ni dasu suka mun barki da wannan,na biyu kuma kinci darajar mimi nawwara da yusra,banason na fito na qara ganin fuskarki cikin dakin nan,idan kuma baki yarda ba......" Sai ya murza yatsunsa kawai ya gewayeta ya fice ya barta a wajen a tsugunne.
Dukka hannuwanta ta saka ta kama kanta da kyau ta riqe,sai kuma ta saki kuka mai qarfi kamar wata zautacciya
"Haba abbas......daddyn ya zakayimin haka?,ko meye nayi nayi ne saboda kai" sake rushewa tayi da kuka,tana jin abun tamkar a mafarki,yau ita abbas ya saka?,abinda bai taba giftawa ba tsahon zamansu sai a yanzu?,a dalilin wata?,wai shin saki nawa ma yayi mata?,sai ta zabura ta dauko takardar ta warware jikinta yana rawa kamar wadda zazzabi ya yiwa mugun kamu.
Saki biyu ta gani a rubuce fes,ta saki takardar tana sake rushewa da kuka,duk da ta samu sassauci ganin akwai sauran igiya daya da tayi saura, saita miqe da sassarfa ta fita daga dakin nasa ta doshi sashenta.
Wayam ta tarar babu kowa,ba yaran babu baqinta,ta shiga nemansu kamar zautacciya lungu da saqo na gidan amma babu su,a bakin gate shazali ya gaya mata yaga mai gida ya fita shi da yaran duka a mota,batasan sadda ta sulale a wajen ba ta sake fashewa da kuka,tsoro ya kama shazali ganin yadda take sheqa kuka yau a gabansa,gashi babu damar ya tambayeta ko kuma ya bata haquri saboda yasan cin mutunci irin nata,haka ya koma gefe yana satar kallonta,har ta gama me isarta taja qafafunta tayi cikin gida bayan tayi futu futu da jikinta a wajen.
Baifi minti talatin ba sai gata da jakarta tana janta,ta buda motarta ta jefa jakar ta shige itama,ta dannewa shazali wani mugun hon,tuni ya durfafi gate din ya bude mata da hanzari gudun kada ta huce haushinta a kansa.
Gidan yaaya bara'atu yakai yaran wadda ta cika da mamakin ganinsa,diyarta budurwa ta kira ta dauki yaran,tace ta hada musu abinci,tuni sukabi bayan mariya ta zuba musu abincin suka sake abinsu sunaci,don dama yunwa ce fal cikinsu,tunda tun rana rabonta da basu abinci,tana ta business dinta,sai kuma wannan tashin hankalin yazo ya ratso na kama lawan,hatta da yusra abinci taci sosai,suna gama ci ba dadewa dukkansu bacci ya kwashesu a wajen.
A can falo kuwa Shuru yaaya bara'atu tayi kamar ruwa ya cita,jikinta gaba daya ya gama mutuwa murus,tausayi da kuma namijin qoqarin da abbas yayi na zama da ita har tsahon wadan nan shekarun duka sun gama kasheta,gidan abbas dama duka ba wajen zuwansu bane,don babu fuska daga wajen hafsat din,wannan yasa da yawan dangi suka janye jiki saidai idan an hadu a gaisa,wannan ya sanya da yawa basusan wanne hali yake ciki ba,sai idan taso kawo qorafinta a kansa ta hada qarya da gaskiya ta fada saboda ta bawa kanta kariya.
"Inason yaran suci gaba da zama a wajenki kafin na gama settling komai"
"Ko har abada zakace ka barminsu ina maraba da haka" ta fada tana girgiza kai zuciyarta tana karaya,tausayin yaran na sake kamata.
Murmushi kawai ya saki,yana son yaransa sosai,bayajin zai iya kyautarsu.
Daren ranar daga hafsat har ummanta babu wanda ya runtsa,sun raba dare suna jajanta abun,don basu taba zaton zai iya sakinta ba,sun masa mugun qullin da tun aurensa da hafsat din sukayi wannan shirin,tsohon shiri ne da ita kanta hafsat din ta manta anyishi,saboda a sannan zuciyarta najin zata iya zama da abbas ba tare da anji kansu ba,zata kuma iya sauke duk wani hakki nasa,tayi abinda yakeso tabar wanda bayaso,don sanda umman ke mata albishir din anyi abun ma ita bata wani daukeshi da muhimmanci ba.
[5/23, 10:14 PM] +234 803 416 2581: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 37
Tun bakwai na safe ya gama shirin barin bauchi ya wuce katsina,sai daya tabbatar yabar gidan hannun umar,yace ya kula da kowanne sashe na gidan,idan ya gama ya rufe gidan,ya kaiwa yaaya bara'atu key din,sannan ya dauki dukka wani abu me muhimmanci ya zuba a motarsa ya fice a gidan.
Gidan yaaya bara'atun ya fara isa,tasa aka kawo masa breakfast ya taba sama sama,don shi yanzu kowanne abinci kallon hadarin kaji yake masa indai ba abincin widad ba,bayan ta sallami mai gidanta dake sammakon fita tazo suka zauna,a sannan su mimi na tare dashi,yaran duka babu wata damuwa a tattare dasu,ita mimi ma nata murnar
"Daddy har anyi kana wanka munci abinci,daddy aiba yanzu zamu koma gida ba ko?" Sai ya gyada kai yana shafa kanta,tausayin yaran kawai yake damunsa,banda mutuwa babu abinda zai raba uwa da danta,amma da yake Allah ya jarabcesu da shashashar uwa bata wani shiga jikinsu da zasu damu can da ita ba,kawai yana baqincikin su girma su tuhumeshi da rashin samar musu da uwa ta gari,saidai yayi imanin Allah bazai taba tozartar dashi ba,tunda yayi dukkan iya bakin qoqarinsa bisa kyautatawa hafsat din zato ya zabeta a matsayin uwar 'ya'yansa.
Duk da yaaya bara'atu tana dojewa amma bai bar mata wahalar yaran ta sisin kwabo ba,komai sai daya ajjiye musu kama daga na islamiyya har zuwa na boko,sannan ya bada wasu kudaden yace a canza musu suturar sanyawa,saboda ya lura da yadda kaf kayansu suka qarasa macewa,harda tsadaddun laces din da ya dinka musu,wanda ko shekara basu rufa ba,don shi baya jiran sai wani lokaci na daban zaiyiwa iyalinsa dinki,kusan ko yaushe cikin yi musu suttura yake.
A nan ne tace ba zata karba sisinsa ba, dole ya maida kudin dinkinsu,ya mata sallama ya wuce.
Tunaninsa a hanya kaf ya qare kan yadda zai doshi widad da yadda zai hukuntata,don ya gaji da maganar da take yaba masa a fakaice,yanaji a jikinsa muddin taci gaba da haka wataran za'a wayi gari ya samu matsalar hawan jini ko zuciyarsa ta tabu,ta shiga rayuwarsa da yawa,a yanzun kuma ta sake kutsawa nisan inda baiyi zato ba,wannana abun da ya faru sai sake qara mata kima da daraja a idanunsa,ya sake qaunar iyayenta tare da ganin zallar dattakonsu.
Tun tana bagarar da batunsa daga ranta har tadan soma jin damuwar rashin jin wayarsa da kuma dawowarsa,amma hakanan dai taci gaba da daurewar tana yakicewa.
Ko a yau data tashi duk jikinta babu kuzari sosai,ta gama komanta da wuri wajejen azahar,saita zauna shuru,sai kallo da kuma duba littafi zuwa waya da ta dinga yi,affan baya nan,wata maqociyarta ta daukeshi tun azahar din,babbar macace,dukka yaranta sun girma,shi yasa suke da son qananun yara.
Karfe uku da kusan minti talatin da tara ya sauka a cikin gidan,ya sanya motarsa cikin parking lot ya kasheta,ya fito yana yiwa yaron gidan magana ya bude booth na motar ya fidda tsarabar da yayo a hanya ya aje masa qofar falon sannan ya wuce.
Knocking yayi,ta dauke fuskarta daga kan littafin dake hannunta,sai ta aje littafin ta miqe a zatonta affan aka dawo dashi,tana gyara wuyan rigar wata bubu ta net da aka yiwa shafin wani irin yadi me kyau daga qasanta,rigar tayi mata kyau sosai,saboda ko ina na jikinta ya a cike yake,babu wani rami loko ko lobawa sai inda yake dama a halittar diya mace haka yake,fatarta lumui lumui,wiyanta ta saka wani ziririn zaren sarqa me qyalli da ya ake qawata wuyan nata,ta riga data saba,ya kuma zame mata jiki,ko yaushe a haka zaka sameta fes tana fidda qamshinta me laushi.
A nutse ta bude qofar,ta buda siraran labbanta zatayi magana sai maganar tata ta maqale,yana tsaye gaban qofar falon hannunsa harde a qirjinsa,idanunsu suka gauraya waje daya,sai wani abu ya tsarga ma kowannensu,wani abu ya tasowa widad mai matuqar qarfi da tasiri.
Ashe dai qarya ne idan kace ka daina son mutum?,ashe dai qarya ne kace baka damu da masoyinka ba saboda wani sabani ko bacin rai,saita juya da hanzari zuwa ciki,batason ta bada kanta.
Baice mata komai ba ya dauki kayan duka ya shiga dasu ciki,ya maida qofar ya rufe,ya tsaya tsakiyar falon yana sauke ajiyar zuciya hancinsa yana zuqar lallausan qamshin da yake bayarwa,qirjinsa yana masa wani irin wasai,duk uban nauyin nan da yakeji cikin qirjinsa a yanzu babu shi,yana jin kamar ya sauke wani uban dutse daya danne masa zuciya.
Ya wuwwulga idanunsa bata cikin falon,yasan ba zata wuce bedroom dinta ba,don haka ya wuce kai tsaye.
Gaban madubi ta wuce kai tsaye, tayi tsaye kawai tana kallon fuskarta da qirjinta dake motsawa saboda bugun da zuciyarta ke mata,ta lumshe ido tana tuhumar kanta akan yadda take samun sauyi akan abbas din,duk wani alwashinta yana sulalewa yana yin nasa waje.
Sam bataji shigowarsa ba,sai sautin muryarsa daga bayanta
"Me bakin tsiwa,ina tsiwar taki ta tafi?,kin iya gasama mutum magana ko?,ki barshi da ciwon zuciya kiqi nemansa" ya fada yana kafeta da ido,gami da hukuntata da kallon nan nasa,haka kawai batasan ya akayi ta juye masa kalar shagwabarta data saba ba,saita tura baki gaba taja baya tana qara kusancin dake tsakaninsu
"Qarya nayi?,ai banyi qarya ba k......." Kasa qarasawa tayi saboda yadda taku biyu kacal ya hade ratar dake tsakaninsu,yaci gaba da ritsata da kaifaffen kallon nan nasa
"Uhmmm......qarasa mana" ya fada yana matsota.
Ta hangi fitintinu bama fitina ba fal idanunsa,ta kuma tabbatar yau idan ya kamata zata ji jiki da kyau,don haka ta kulle bakinta taqi tanka masa,saidai duk da hakan bai fasa matsota ba,har ya danga da bangon dakin
"Tunda kinji tsoro zan qarasa cire wannan rashin kunyar taki,kin dauka ni age mate dinki ne ko?" Kai ya shiga girgiza masa,saidai kafin tace wani abu yakai mata cafka,yayi mata wata wawuyar runguma har yana takure abinda ke kwance a cikinta,baiyi wata waya ba ya hade bakinsu waje daya,ya fara aika mata da wani zazzafan kiss,wanda ko sau daya ya gaza dauke bakinsa daga cikin nata.
Cikin mintunan da ba masu yawa ba ya zare mata dukka wata laka ta jikinta,ya cire dukkan wani zafin rai taurin kai da kuma qwafar data yi masa,cikin qalilan din mintuna ya zautata,ya jefata wata duniya wadda ta mantar da ita wacece ita,ta sukurkuce gaba daya,ta kuma miqa masa kanta,irin miqawar da bata tashi gane cewa ta tafka abun kunya ba sai bayan da komai ya kammala,tana kwance a qirjinsa tana kukan da dai dai yake da nade tabarmar kunya.
Tabbas taji jiki a hannunsa,ta kuma biya dukkan bashin soyayya da kewa da suka cima juna,yana maqale da ita tsam a jikinsa yana aikin lallashinta,hannunsa daya kan sumarta yana shafawa a hankali,zuciyarsa fes,nutsuwa tana saukar masa
"Ka daina tabamin kai,bayan tunda na dawo baka nema komai a gurina ba,har dai kaje bauchi ka gama bincikenka" ta fada cikin kukan shagwaba tana turo baki gaba.
Don dole dariya ta kubce masa,ya rungumeta da kyau jikinsa
"Am sorry madam,bansan a matse kike ba ai....."kuka ta fashe masa dashi,ta dunqule hannunta tana dan dukan qirjinsa
"To na daina,na fasa fada,nine a matse" ya fada yana kare dukan da take kai masa da hannayensa shima.
Sai da ya tsagaita dariyar sannan ya sake gyara mata kwanciya sosai a jikinsa,ya kira sunanta cikin sautin muryar data sanyata daga kai ta kalleshi
"Banqi neman komai a wajenki da gangan kodon saboda wata mafita ba,a lokacin kina cikin zafi da radadin abinda na aikata miki,na tabbatar idan na nemi wani abu a wajenki a sannan,abinda zaizo kanki shine jikinki kawai nakeso,ban fara sonki saboda jikinki ba ke shaida ce akan hakan,kuma bazan fara saboda hakan ba in sha Allah,koda baki da komai tattare da ke banajin zan daina sonki har gaban abada" sosai kalamansa suka kashe mata jiki,tayi shuru tana saurarensa,tana kuma sake gasgata zancan nujood da tace mata,abinda uncle abbas yayi din tabbas ba halinsa bane,tafi gasgata asiri ne yake dawainiya dashi,a lokacin tace mata hafsat,saidai ita din har yau bata kawota cikin ranta ba.
Sake kiran sunanta yayi bayan ya hade hannayensu guri guda cikin wani irin taushi da sanyi,sai data sake shigewa jikinsa da kyau saboda yadda sautin muryar yaratsa kowacce gaba ta jikinta
"Don girman Allah ki yafemin,yafiya irin ta har abada,banason ki sake tuna wani abu makamancin wannan ya taba faruwa a rayuwar aurenmu" Abbas ya cancanci yafiyarta,koba komai uban danta ne wanda ta haifa da wanda zata haifa ma a gaba,ba zata taba mancewa kuma da yadda ya tsayawa rayuwarta ba,ya dauki wautarta da shirmenta,ya raineta har ta zama abun kallo ga kowa ba
"Na yafe maka har abada" wani farinciki yaji yana ratsa zuciyarsa,har baisan adadin godiyar daya dinga jera mata ba.
Cikin kwanakin komai ya wuce ya kuma zama tarihi