Showing 21001 words to 21725 words out of 21725 words
Chapter 8 - ZARGE Book Free Hausa Novels by Zahra Royal & Salma Ahmed Isa.txt
matashin da ta kira da Fu'ad ya tada motar ya soma ƙoƙarin barin wurin, sai da yavkusa barin layin kafin ya ankara da wani book da ƙanwar tasa ta manta a kotar. Murmushi ya yi kawai yana girgiza kai, kafin ya dawo baya, wannan karon har cikin makarantar ya shiga. Ya fito daga motarsa riƙe da littafin nata, ya nufi faculty of Law, inda ya san cewa a can ƙanwar tasa take.
Tun daga nesa ya hango wata budurwa sanye da abaya blue, tashin farko zuciyarsa ta raya masa cewar ƙanwarsa Umaima ce. Dan haka ya soma ƙwala mata ƙira yana nufar inda take, amma ba ya juyo ba har sai da ya isa kusa da ita, ua saka hannunsa ya riƙo damtsen hannunta, ya juyo da ita yana faɗin.
"Ke wai ba ki ji ne ina ta ƙwala miki..."
Bai kai ga ƙarasa furtawa ba saboda wani lamari da ya faru unexpected.
FALAK POV.
Kasancewar yau Khamis yace mata ba ya gari yasa ta shirya ta tafi Makaranta, ba wai dan tana so ba sai dan ya zame mata dole. Kuma tun da ɗazu Hajiya ke faɗa mata cewar Faisal zai dawo ta hango kamawar watan tashin hankalinta na shirin kamawa. Domin idan yana nan dole ta rage wasu abubuwan, sannan dole ta yi wasu da ba ta yi a baya.
Tsabar murɗɗaɗen halinta yasa ba ta da ƙawa ko kaɗan, ba a makarantar ba ba a gida ba. Ita kaɗai take tafiya a cikin makarantar, tayin da ta nufi Library, dan ba ma ta jin za ta iya attending class ɗin. Kamar daga sama ta ji an riƙo damtsen hannunta hannunta, sannan aka juyo da ita, ɓacin ran rainin hankalin da ta ga ana shirin mata yasa ba ma ta tsaya ta ji abin da mutumin ke faɗa ba, ta rufe idonta ta ɗaga hannunta ta shararawa matashin marin da yasa ya ɗauke wuta.
"How dare you touch me this way?"
Ta furta idanuwanta zare a kansa, ba ta duba girmansa ba, ba ta duna kamalarsa ba, ba ta duba kimarsa ba ta zage ta ci mutuncinsa yadda taso. Shi ko Fu'ad kuncinsa kawai ya dafe yana kallon yarinyar da ya san ba ta kai Umaima ƙanwarsa a haife ba, amma gata tsaye a gabansa tana ci masa mutunci, tasa jama'a na ta kallonsu.
"Ke! Falak! Kar ki sake furta wata mummunar kalma a kan yayana! Dan Wallahi idan har kika sake ni ma sai na mareki!"
Umaima da ta ga abin da ya faru ta faɗa, tana isowa wurin, wani irin kallo Falak ta yi wa Umaiman dake sanye da abaya blue, kusan shigen wadda ke jikinta.
"Shi yayan naki ba shi da ɗa'a ne? Ko gyatuma ba ta koya muku a gida ba? Ya kamata ace kin ba shi labari cewar babu wani ƙazamin saurayi da ya isa ya yi gigin taɓa Falak..."
"Ke har kin isa!..."
Umaima ta faɗa tana ɗaga hannunta za ta mari Falak, amma sai Fu'ad ya riƙe hannun nata.
"Ya isa Umaima! Tana da gaskiya, kin mance book ɗinki ne a car, shi ne na zo zan baki, da na ganta da farko na ɗauka cewar ke ce, shi yasa na riƙe hannunta a bisa rashin sani, dan Allah ki yi haƙuri!"
Ya ƙarashe yana kallon Falak dake binsu da kallon sama da ƙasa. Wani dogon tsaki ta ja, sannan ta juya ta barsu tsaye a wurin ana ta kallonsu.
"Ka yi haƙuri Ya Fu'ad! Kowa ya san halin Falak kan ba ta da mutunci!"
Cewar Umaima tana duba gefen fuskarsa da ya yi ja, alamun a nan ya sha marin, abinka da farin mutum. Fu'ad bai amsata ba, saboda bayan Falak kawai ya bi da kallo, sakamakon wani abu da ya karanto a cikin idonta, wani abu! Wani abu! Tabbas wani abu!.
_____________
_Hello!_
_Free pages sun ƙare daga nan oo... Domin ci gaba da karanta wannan book ɗin za ku biya ₦500 kacal_
_Humm! Akwai gwarama fa!_
_A ganinku wani hali Amira da Zahra za su kasance a ciki?_
_Wani hali Yabintu ke ciki?_
_Sannan ga Falak ga kuma Fu'ad_
_Ga Maryam ga Faisal!_
_Me kuke ganin Faisal zai yi a kan Maryam, Mama, Bilkis da Falak idan jar asiri ya tonu... Domin ku sani, ƙarya fure take ba ta 'ya'ya._
_Ina mai tabbatar muku fa har yanzu ba mu yi komai ha a tafiyar nan_
Domin biyan kuɗin book ɗin za ku tura kuɗin ta:
5487270431
Salma Isah
Monie point
Sai ku tura shaidar biyanku ta 0813 047 9973.
Zahra Royal Star 🌝
Salma Ahmad Isah ✍️