Showing 12001 words to 15000 words out of 21725 words
Chapter 5 - ZARGE Book Free Hausa Novels by Zahra Royal & Salma Ahmed Isa.txt
da yake kusa da desk za ki ga wani book mai suna 'The Inner Child' ki ɗauka ki bawa Maryam"
Cike da takaici Falak ta cije leɓenta na ƙasa, dan ta san da gangan Maryam ɗin ta aikata mata haka. In dai kuwa haka ne yanzu za ta gasa mata maganar da za ta hana mata sukuni.
"Shikenan yanzu zan je na ɗauko mata... Yaushe za ka dawo ne Yaya?"
Abin ka da ɗan uwa, sai ta samu kanta da tambayarsa hakan, duk da ta san ba lalle ta yi gwaninta ba, dan wata ƙil ma gwasaleta zai yi, kuma sai ya yi abin da take hasashen.
"Ban sani ba"
Kawai yace a dake, dan haka ita ma ba ta sake cewa komai ba ta aje wayar tana kallonta, duk da bai katse ƙiran ba, shi a rayuwarsa ba a yanke masa ƙira, ko da kuwa kai ka ƙira shi ba shi ya ƙiraka ba, saboda a wasu lokutan ya kan manta abin da zai ce, sai bayan wasu mintoci kuma zai tuna, sai ka ga ya faɗa maka, wani lokacin kuma maganar ta ƙare, amma saboda isa da gadara ba ka isa ka kashe masa waya ba sai in shi ya kashe. Har bayan shuɗewar wasu sakkani, kafin Falak ta ga ƙiran ya katse, a bayyane ta ja tsaki, sannan ta ɓoye kwalaban da ta fito da su, ta ɗauki wayarta ta kuma fita.
Ɗakin Bilkis ta shiga, ta ɗauki keys ɗin, sannan ta sauƙo ƙasa tana bin Mama da Maryam dake hira da kalll, dan zuwa lokacin Hajiya ba ta falon, wani ɗan iskan kallo ta wurgawa Maryam, kafin ta yi ƙwafa ta fice daga falon. Part ɗin Faisal dake gidan ta shiga, sannan kamar yanda yace mata haka ta yi, har ta samu book ɗin. Lokacin da ta fito take kulle part ɗin nasa ta ji muryar Maryam a bayanta.
"Yauwwa Sister, kin ɗauko mini?"
Ta juyo tana kallonta.
"Ga shi na ɗauko ƙuda sarkin naci!"
Ta faɗa tana danƙa mata book ɗin a hannunta, a karo na uku Maryam ta shaƙa, dan tun da ta zo Falak ke mata abubuwan da ba su mata daɗi.
"Kar ki damu sister, yayanki ya kusa zama nawa"
Falak ta yi murmushi mai sauti tana harɗe hannayenta a ƙirji.
"Idan ma bacci kike to ki farka! Domin jelar raƙumi ta yi nesa da ƙasa Maryam, kuma ko da girgiza kurna ta fi magarya, dan haka Ya Faisal ya fi ƙarfinki, na san kina ganin kamar kalamaina a matsayin shashanci ko wauta. Duk ki cire wannan, batu ne na gaskiya nake miki, Faisal ba zai taɓa aurenki ba"
Maryam ta yi murmushi tana juya book ɗin dake hannunta.
"Zan so ace na ga yanda za ki yi ranar da na mallaki yayanki a tafin hannuna!"
Falak ta yi taku biyu zuwa gabanta, sannan ta ɗaga hannunta dake riƙe da wayarta ta dafa kafaɗarta.
"Wannan ranar ba za ta zo ba Habibty 'yar wahala"
Tana gama gasa mata maganar ta janye hannunta daga kan kafaɗarta, sannan ta raɓata ta wuce tana karkaɗe hannunta da ya taɓa Maryam ɗin, kamar wadda ta ɗauki buhu mai datti. Haka Maryam ta bi bayanta da kallo a kufule, tana hasaso kalar abubuwan da za ta yi wa Falak bayan ta shigo gidan a matsayin batar Faisal.
YABINTU POV.
Gaba ɗaya ƙawayenta ne suke zazzaune a ɗakinsu, yayin da suke hirar tafiyar da za ta yi, duk da wasu daga cikinsu su ma za su je gida.
"Ni fa ji nake kamar na biki mu tafi Zamfara tare!"
Cewar Khadija... Yabintu ta wurga mata hararar wasa.
"Kamar da gaske, ke ɗin da tsoro ya cika miki ciki kika kasa zuwa last time da muka yi za mu tafi da ke?"
"A'a ni fa ban ga laifinta ba! Yo ai ko ni ba zan iya zuwa yankinku a halin da ƙasar nan take ciki ba"
Faɗin wata daga cikin friends ɗin nasu.
"Kai duk fa wannan abubuwan da kuke ji ana yi bakinsu ƙauyuka... Ba su shiga cikin gari"
Cewar Yabintu.
"To ai ka fin a isa garin dole sai an ratsa ta ƙauyen ko?"
Cewar wata tana taɓe baki.
"Wallahi duk kallonku nake, kawai dan abin bai zama muku dole ba ne shi yasa!"
"Ke da ya zamewa dole sai ki je... Mu dai Allah ya yaye mana"
Yabintu ta yi dariya kawai.
"Amma dai da Umar za a je ya yi rakiya?"
Faɗin Laura a sigar tsokana.
"Ai shi ba rago ba ne kamar su o'o, tun da shi da 'yan uwansa suka tashi tun daga Abuja har zuwa Zamfara suka je naiman aurena!"
Gaba ɗaya su shida suka sheƙe da dariya.
"Oh Yabintu da Umar soyayya kamar ba za a rabuba! Mu dai Allah ya kaimu lokacin bikin nan mu cashe!"
Faɗin Khadija tana ɗaura ɗankawalin kanta da ya since, Yabintu ta yi murmushin jin daɗi.
"Amin"
Ta amsa tare da sauran... Su da kansu suka tayata shirya kayanta, domin zuwa gobe za ta bi jirgi zuwa Sokoto, daga nan kuma za ta hau mota ta kaita cikin Gusau. Sai da aka gama shirya kayan kuma aka dawo aka ci gaba da hirar da rabinta ya fi karkata a kan karatunsu da suke daf da gamawa.
Salma Ahmad Isah ✍️
Zahra Royal Star 🌝
_________________
ZARGE littafin kuɗi ne, domin more naku sai ku biya ₦500 to.
5487270431
Salma Isah
Monie point
Sai ku tura shaidar biyanku ta 0813 047 9973
*ZARGE*
BY
ZAHRA ROYAL STAR
&
SALMA AHMAD ISAH
Page 06
*Channels Television station, Abazie Ifeanyi Close, Guzape, Abuja.*
BILAL POV.
Zaune yake a office ɗinsa yana wasu rubuce-rubuce, sosai ya maida hankali kan rubutun da yake, lokacin da ya ɗiga aya ya miƙa hannunsa na dama ya ɗauko wata takarda, kamin ya fara wani rubutu a kanta, shigowar Aliyu office ɗin ce ta sa ya dakatar da rubutun da yake, na tattara wasu bayanai game da binciken da yake son farawa.
Kuma kallo ɗaya ya masa ya sake maida hankalinsa kan rubutun da yake. Aliyu dake kallonsa tunda ya shigo ganin yadda aiki ya sha masa kai, yasa shi zama kawai.
Ƙara kallonsa Bilal ya yi, ganin yadda ya yi shuru ya sa Bilal ture tarin takardun dak gabansa, kamin ya ɗan murza goshinsa yana runtse idonsa, kamin ya ware hannunsa ya d'auki wata takarda yana ta kallonsa, jin shirun ya yi yawa yasa shi ya fara magana.
"Me ya faru ne na ganka a haka?".
Ya tambaya ba tare da ya kalle shi ba, A hankali Aliyu ya aje masa fallan jaridar da ya shigo da shi a kan table ɗinsa. Bilal ya bi takardar da kallo, kuma kafin ya kai ga karanta abin da ke rubuce a jiki Aliyu yace.
"An kama shugaban ƙungiyar GKL hukuma tace za su gudanar bincike a kansa da ƙungiyarsa"
Bilal ya sa hannu ya ɗauki jaridar, sannan ya bi hoto haɗe da rubutun dake jiki, ya miƙe tsaye yana ci gaba da kallon jaridar.
"Ban sani ba ai, saboda tun da na tashi yau wani aiki ya sha min kai... Alhamdulillah".
Ya faɗa muryarsa ɗauke da murnar yin nasara, ya koma ya zauna yayin da Aliyu ke murmushi.
"Ɗazu Victor ke sanar min cewa wai ka ɗauki hutun sati guda... Yanzu kuma wani sabon aikin za ka yi?"
Bilal ya aje jaridar da yake ta riƙe da ita, sannan ba tare da jin komai a ranaa ba yace.
"Bincike a kan 'yan bindigar cikin daji! Waɗan da suka addabi mahaifata da maƙotanmu!"
Ido waje Aliyu yake kallonsa, ya tabbatar Bilal ba zai bar aiki ba sai ya jawowa kansa da ma su gabaki ɗaya mutuwa.
"Lallai ka d'auko bincike mai tsananin had'ari tare da rikitarwa, domin kuwa shi ma wannan akwai sa hannun wasu hafaffu da mai a ƙasa, me yasa wai kai ba ka da aiki sai binciko abubuwa maau haɗari irin waɗannan?".
Bilal ya yi murmushin gefen baki.
"Kawai addu'a za ka min, ku sai ku tsaya a matsayarku, amma ni dai na sa a raina cewar sai na binciko duk wata badaƙalar da ake a ban ƙasa... Zuwa gobe zan wucw Zamfara".
Bilal bai tanka masa a kan maganarsa ya farko ba, domin ya san maganarsa ba ta isa ta sa Bilal ya fasa abin da ya yi niyya ba... Tun da har yace zai yi to zai yi, dan haka ya tsallake wannan maganar yace.
"Za a je duba Mama ke nan?"
"Eh ka san na kwana biyu ban je ba, kuma idan na je can zan fi samun wasu bayanai daga wurin mutane"
"Gaskiya kam, to Allah ya tsare, ya kaika lafiya, a miƙawa Mama saƙon gaisuwata, sai mun yi waya".
"Yeah, amin thank you".
Daga haka Aliyu ya tashi ya fita ya bar shi zaune yana nazarin ta inda zai fara aikin da ya ɗauko.
*Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja, Nigeria.*
YABINTU POV.
Zaune take a cikin motar Umar, isowarsu ke nan filin jirgin, kuma dalilin da ya sa ba ta fito ba wai sallama suke, kuma lokacin tashin jirgin da saura, dan wajejan awa ɗaya sauya.
Kallon Umar ta yi, ganin yadda yake kallonta kamar zai cinyeta, murmushi ta saki tana ɗan gyara zamanta a cikin motar ta ce.
"Ya da wannan kallo kuma? Sai kace wacce ba za ta dawo ba?".
Umar ya sauƙe ajiyar zuciya, yana ɗan shafa sumar kansa kamin ya ce.
"Ji nake kamar kar ki tafi ne, kuma sai da muka zo filin jirgin na fara jin hakan".
Wani murmushin Yabintu ta saki tana cewa "Uhum kamar fa yau ne za ka ga na dawo, ai hutun ba mai yawa bane, it's just 1 to 2 weeks... And whenever you missed me you can give me a touch abi?".
Ba ta san sanda ya kamo hannunta ba, sai ji ta yi yana murza shi kaɗan-kaɗan, haka kawai yake jin kamar idan ta tafi za su rabu ne har abada... Tun da Yabintu take da shi bai tab'a gigin koda tab'a d'an yatsanta ba, shi ya sa take kallonsa cike da tsananin mamakinsa.
"Hayati na ga jikinka ya yi sanyi, ka daina damuwa please lafiya lau zan dawo inshaallah". Cewar Yabintu ganin duk jikinsa ya yi sanyi.
Lumshe idonsa ya yi, kafin ya buɗe ya shiga binta da wani kallo wadda bai tab'a mata irinsa ba, muryarsa a sanyaye ya ce.
"Na sani ba dad'ewa za ki yi ba, amma wallahi haka kawai nake ji kamar a fasa tafiyar nan taki".
A hankali ta d'an murza hannunsa dake cikin nata tana kallon cikin kwaryar idonsa.
"Ba na so ina ganin damuwa a kan fuskar nan taka fa please, ni da zan tafi a jirgi, kuma insha Allahu 'kalau zan dawo ka ji?".
Daga haka ta yi saurin janye hannunta daga cikin nasa, a hankali tasa hannunta na dama ta murɗa murfin motar ta fita, shi ma fitar ya yi yana kallon terminal, ya zagoyi inda take, suka fara tafiya, a ƙofar Terminal suka rabu, suna ta waving ma juna hannu kamar kar su rabu. Daga ƙarshe ma dai tace masa ya zo su ɗan zauna a ciki kafin lokacin tashin jirginsu, bai ƙi ba, domin har ga Allah shi ma bai gaji da ganinta ba.
A kan wasu kujeru suka zauna, Yabintu sai baza idonta take, domin hatta ita kanta zuciyarta ba ta mata daɗi. Suna zaune a wurin wayar Umar ta yi ƙara. A hankali ya zaro wayar ganin mai kiran nasa yasa shi ɗauka da sauri.
"Okay ga ni nan zuwa yanzu insha Allah".
Abin da ya ce ke nan bayan ya gama sauraron abin da na wayar yace. Kallonsa Yabintu ta yi ganin yadda ya tashi da sauri yasa ta ce "Me ya faru?".
"Wai Umma ce taƙi shan magani, tace dole sai na zo na ba ta da kaina, na san duk salon kar ta sha maganin ne, saboda na san ba son maganin take ba, ga shi jikin nata sai a hankali har yanzu. I'm so sorry cuz I have to leave before you leave"
Yabintu ta saki murmushi, sannan ta miƙe tsaye tana kallonsa.
"Haba ba komai, ka je kawai, tun da kai ka kawo ni har airport".
Murmushi ya sakar mata yana ƙara jin ƙaunarta har cikin ransa, sai da ya furta mata i love you kamin ya bar wajan.
Yana niyyar saka key ya tayar da motarsa domin tafiya kawai kamar an ce ya waiga ya hango wata jakar Yabintu da ta manta ta, hannu ya miƙa ya ɗauko jakar, ya fito dai-dai da wayarsa na sake ringing. Yana fitowa daga motar su kai k'aro da wani, tsabar saurin da Umar yake bai ma lura da shi ba. D'agowa ya yi domin bawa wanda ya bige haƙuri, sai idonsa ya gane masa wani tsohon friend ɗinsa Bilal B. Liman.
Murmushi kowanne d'auke a kan fuskarsa Umar ya ce "Ah-ah B. Liman?".
Bilal ya gyara zaman hular dara dake kansa yana murmushin ganin tsohon abokinsa.
"Na'am Faruk Yola"
Dariya suka yi, sannan suka yi musabihi.
"Ya na ganka a nan? Ko aikin jaridar ne ya kawoka?"
Bilal ya girgiza kansa.
"Ko kaɗan, ganin gida zan je?"
Umar ya yi dariya.
"Sai ka ce wata mace... Za a leƙa Zamfara ke nan?"
"Wallahi da yake na d'an kwana biyu ban je ba".
Umar zai sake magana ya sake jin k'arar wayarsa, da sauri Umar ya kalli Bilal ya ce.
"Ohhh sorry friend dan Allah ga wannan jakar ka bawa Yabintu, wallahi sauri nake Umma ba lafiya, za ka ganta zaune wajan waiting chairs, ba mu gaisa sosai ba, Allah ya tsare hanya Kuma".
Yana damƙa masa Umar ɗin ya yi saurin buɗe motarsa ya shiga, ko damar tambayar wace ce Yabintun ma bai ba shi ba, domin shi bai san wacece budurwar Umar ɗin ba.
Bilal ya bi abin da ya basa da kallo. Shi ya za'ai ya gane ta, tunda ba wani saninta ya yi ba, koda yake ya yi masa uzuri da alama jikin Umman nasu ne ya sake tashi, kuma Mahaifiya ai ba abar wasa ba ce, shi ya sa Umar d'in duk ya bi ya rud'e, "Uwa mai dad'i."
Cewar Bilal a zuciyarsa. Murmushi ya saki sanda ya fara tafiya yana nufar inda waiting chairs ɗin.
Dai-dai lokacin da ya iso wurin, aka fara wata sanarwa cewa jirgin da zai tashi k'arfe 9AM, wadda zai tashi daga Abuja zuwa Sokoto an soke tashinsa sakamakon wasu 'yan dalilai da ba su bayyana ba, suka kuma ƙara da bawa fasinjojinsu haƙuri game da wannan tangarɗar da aka samu.
Hankali a tashe Yabintu ta mik'e, sai kuma ta saki wani dogon tsaki, a dai-dai lokacin, a wannan wurin, zuciyarta ta ƙissima mata wani abu da ya zama sanadiyyat faruwar ƙaddararta ta rayuwa. Tunanin take kan ba za ta iya jira sai zuwa gobe ba, ta riga ta yanke cewar yau a kan gadon ɗakinta na Gusau za ta kwana, dan haka gara ta hau motar Kaduna daga Abuja, idan an sauƙeta a Kaduna kuma sai ta hau motar Gusau.
Duk da da ba haka tsarin yake ba, idan ta hau jirgi zai sauƙesu ne a Sokoto, daga nan kuma za ta hau kota zuwa Gummi, daga Gummi kuma za ta hau motar Gusau.
Mutane da yawa sun ji haushin tsaida masu tafiya da akai, wasu kuma sun bada uzurin ko jirgin ne akwai matsala ko kuma sun dai hango wani abun ne.
Shi ko Bilal dake tsaye kusa da Yabintu bai ji wani abu ba, Allahn da ya yi hau shi ya yi gobe, kuma goben ma kamar yau take... Tsayawa da ya yi sauraron sanarwar ya mantat da shi saƙon da aka ba shi, juyowar da zai yi suka kusan cin karo da Yabintu da ta ɗauki bags ɗinta.
Kuma hakan ya sa ya tune da saƙon da aka ba shi, sai ya dubeta yayin da ita ma shi take kallo.
"Oh sorry Pleas"
Bilal ya girgiza kansa alamun ba komai, kafin yace.
"please ko ke ce Yabintu girlfriend d'in Umar?".
Da ɗan mamaki Yabintu ta ƙara kallonsa, dan ba ta sansa ba, shi ina ya santa? Sai kawai ta samu kanta da d'aga masa kai kawai.
Murmushi ya saki yana mik'a mata jakarta dake hannunsa yana cewa "Ga wannan Umar ne ya bada ya ce a baki, kin manta tata ne a cikin mota, yana sauri, shi ya sa ya bani na baki. Kuma gashi an samu matsalar tashin jirginmu".
Murmushi ta d'an sakar masa, jin wajan Umar ya santa ta amsa tana godiya ta ƙara da. "Eh amma ni ba zan iya jira har sai gobe ba, yau zan wuce gaskiya".
"Ohh amma baki tsoron hanya?... Saboda akwai hatsari sosai fa".
"Ba wani abu da yardar Ubangiji lafiya lau zan isa".
D'aga k'afad'arsa ya yi kamin ya bata bata waje yana mata fatan sauƙa lafiya, lokacin da ya fito faga terminal ya shiga motarsa sai ya ƙira mahaifiyarsa ya sanar mata da cewa an soke tashin jirginsu, sai zuwa gobe zai zo.
A lokacin kuma Yabintu ta fito daga terminal da kayanta, ta tare taxi wadda za ta kaita tashar motar da za ta hau ta Kaduna... A kan idonsa ta shiga taxi ɗin, kuma har taxi ɗin ta bar wurin bai gama wayar ba, sai da ya gama sannan, ya sauk'e numfashi, yana jin kamar bai yi dai-dai ba, da ya bar ta ta tafi, kuma ya san motar haya za ta hau, mi ya sa bai hanata ba? Ko ma ya bita su tafi tare, haka kawai yake jin kamar bai kyauta ba.
*Ƙauyen Gyaza, Kankia Local Government, Katsina State, Nigeria.*
*12:44 na rana.*
ZAHRA POV.
A hankali Zahra ke matsama Hajiya kakarsu k'afarta.
Amira kuma na zaune kusa da Hajiyar tana cin kwaɗon rama da aka musu, duk sun zagaye Hajiya suna mata hira. Hatta Mummy na kusa da Hajiyar suna ta lallaɓata, domin yanda suke son tsohuwar sosai. Shi ko Daddy yana can wurin 'yan uwa, abin ka da mutan ƙauye, akwai son sada zumunci.
"Wash! ke ki bi min k'afa a hankali fa, ja'ira karki k'arasa ni".
Hajiya ta k'are maganar cike da wasa da zolaya. Turo baki Zahra ta yi tana cewa.
"Haba Hajja? yanzu ai sai kisa amin dariya, ina malamar asibiti guda?"
Ai kuwa dariyar Amira ta kece da ita, tana cewa "Yo da ma ke mai yima Hajiya gwaninta ai saiya shirya, ke ce da gulma wai sai kin mata tausa, na san hakan sai ta faru ai, shi ya sa ban ma yi gigin cewa zan yi mata ba". Ta ƙarasa tana cusa rama a bakinta.
Hajiya dake dariya a hankali ta jawo Zahra jikinta tana cewa "Ke rabu da ita dan Allah, wasa nake miki fa, ci