Showing 9001 words to 12000 words out of 21725 words
Chapter 4 - ZARGE Book Free Hausa Novels by Zahra Royal & Salma Ahmed Isa.txt
bayan sandwich ɗin, domin bayan tarin gajiya da ayyukan da suka shige masa ba ya jin yana da lokacin zama ya girka wani abin mai nauyi.
Fitowa ya yi daga kitchen hannunsa riƙe da plate mai ɗauke da yankan sandwich biyu da kuma mug mai ɗauke da tean da ya haɗa. Lokacin da ya ratso ta falon da babu hasken komai cikinsa sai na Tv ya yanke shawarar zama a falon domin ya ci sandwich ɗin a nan. Sanda ya zauna ya janyo center table ya aje mug tare da plate ɗin da yake riƙe da su a kan table ɗin.
Sannan ya ɗauki remote control ya sauya channel daga StarPlus zuwa Channels Tv, domin yana so ya ga ko za a saka rahoton da ya kawo bayan yin cecekuce tsakaninsa da shugansu na wurin aiki, duk da sun tsaida magana kan za a fitar da rahoton tunaninsa bai gama yarda kan za a saka ɗin ba, gara ya gani da idonsa.
Remote control ɗin ya aje, lokacin da ya ga har an yi nisa a rahoton ƙarfe tara na dare da ake haskawa, ya ɗauki mug ɗinsa ya kai baki ya yi sipping tea ɗin dake ciki kaɗan, hankalinsa gaba ɗaya yana kan Tvn, rahoton da yake ta tuƙuburin gani shi ne na ƙarshe a cikin rahotannin da aka gabatar, sai dai duk da haka ya yi farin cikin ganin labarin, domin babu abin da aka rage na daga wanda ya kawo.
Sai da aka gama haska labaran bai ci ko rabin sandwich ɗin da ya haɗa ba, duk kuwa da muguwar yunwar da ya kwaso daga wurin aiki. Sai da aka gama ɗin ne ma kafin ya samu sukunin cinyewa, ya ɗauke kayan ya kai kitchen, bai fito ba sai da ya wanke duk abubuwan da ya ɓata. Lokacin da ya fito daga kitchen ɗin wayarsa dake gurzawa a kan sofa ta ja hankalinsa.
Ko da ya ɗauki wayar har ƙiran ya katse, a nan ya ga 3 missed call daga Aliyu, kasancewar wayar a vibration mode take yasa ƙaran wayar bai fito ba. Murmushi kawai ya yi, ganin ƙiran Aliyu ya sake shigowa wayar a karo na huɗu, kuma ya san me yasa yake ta jera masa wannan ƙiran kamar wanda yake binsa bashi.
"Yane?"
Kawai yace yana ɗaga wayar.
"To! Buri ya cika, an haska labarai kuma an bada rahoto, yanzu sai mu koma gefe mu ga abin da zai wakana!"
Wani murmushi mai kyau Bilal ya yi yana shafa kwantaccen gashin sajensa, kafin yace.
"Inshaallah komai zai tafi kamar yanda muke fata, ko hukuma da gwamnati ba su ɗauki mataki ba wannan rahoton ya isa ya wayar da kan al'umma game da illar tura yaransu mata ƙasashen waje zuwa aikatau! Kuma ka ga ko ta nan ma mun yi nasara!"
Ya ji alamar Aliyu ya gyaɗa kansa, kuma ƙasa-ƙasa yake jiyowa muryar tilon yaron Aliyun yana wasa.
"Ina madam da Boy?"
"Suna lafiya gwauro!"
Bilal ya yi dariya yana zaunawa a kan sofa.
"Ka yi ka bar ni! Komai lokaci ne, kuma na Allah ne, mu ma inda rai da rabo namu na nan tafe"
"Allah ya nuna mana..."
Wayar tasu ba ta tsawaita ba ta ƙare, saboda ƙiran Adebisi wata abokiyar aikinsu da ya shigo ya kori na Aliyu.
"Yanzu na gama kallon labaran da aka haska yau! Gaskiya ka yi na mijin ƙoƙari B. Liman!"
Faɗin Adebisi cike da farin cikin abin da abokin aikin nata ya yi. Bilal ya shafa kansa yana faɗin.
"Ƙoƙarin ba nawa ne ni kaɗai ba, har da ke Ade, domin ke ma kin taimaka da taki gudunmawar!"
Ade ta yi dariya.
"Komai zan maka zai zama kamar na yi wa kaina ne B. Liman!"
Ta kuma ƙiran sunansa da ta saba ƙiransa da shi, wato B. Liman, cikakken sunansa kuma Bilal Bashir Liman, ana taƙaitawa ne da B. Liman ɗin kawai dan ya fi sauƙin faɗa ko a baki.
"Zuwa yaushe za ki dawo?"
Ya tambaya, dan yanzu haka ita Adebisi tana garin Enugu.
"Nan da sati mai zuwa zan dawo"
"Ki kawo min tsarabar doya"
Shi kansa da ya yi batun sai da ya yi dariya, ballantana kuma ita da ya shaidawa.
"Wa zai girka maka doyan idan na kawo? Ko Mama za ka kaiwa?"
Ya girgiza kansa yana taɓe baki.
"Ni zan ci abata!"
"To zan kawo maka, kar ka damu"
"To na gode, ni zan sauƙa a kan layi!"
"Okay bye"
Ya aje wayar a gefensa, sannan ya ɗaga kansa yana shafa sumar kansa, sabon aikinsa da ya saka a gaba yana yawo cikin tunaninsa.
*Sabon Titin kwaɗo, Katsina state...*
Mummy ta aje flask biyun da take riƙe da su a kan center table, kafin ta waiga ta kalli Daddy dake operating wayarsa.
"Ga abincin nan"
Ta idasa maganar tana zama kusa da shi, kafin ta ɗauki plate ta shiga zuba masa abincin, har sai da yace ya isa, ya aje wayar hannunsa sannan ya karɓi plate ɗin ya soma cin abincin.
"Su Zahra sun kwanta ne?"
Daddy ya cillowa Mummy tambayar, yayin da take zuba masa drink a cikin cup. A hankali Mummy ta aje cup ɗin da ta zuba masa drink ɗin next to plate ɗin abincinsa.
"Ba lalle ba, ita Zahra ɗazu ta dawo daga Aldusar Park, kuma na san a gajiye take, yanzu haka ba za ta kasa baccin ba, ita dai idon screen ina da tabbacin ba ta yi baccin ba"
Abba ya yi dariya jin sunan da ta ƙira Amira da shi.
"To ko zuwa gobe da safe ne ki sanar da su, zuwa gobe su shirya, tun da Saturday ce na san Zahra ba ta da class, za mu je Gyaza mu duba Hajiya!"
Mummy ta yi murmushi tana shafa cinyarta.
"Ai ba sai gobe ba, yanzu ya kamata na gaya musu, domin su shirya tun yanzu, duk da na san ba kwana za mu yi ba kamar yanda muka saba!"
Daddy yana taunar abinci ya jinjina mata kai.
ZAHRA POV.
Yayin da Amira ke soyewa tana ƙonewa da Mahmud saurayinta a waya ita kuwa duk ƙauri ne ya cika mata hanci. Tana kwance a kan gadonta, ta kunna kallo a system ɗin Amira tana kallon wani indian series. Duk da a gajiye take daɗin Film ɗin ya hanata kwanta da wuri, don so take ta gama kallon wannan episode ɗin sai ta kwanta, saboda yau Kulsum da A. Sani wato Aisha Sani ƙawarsu sun bata wahala kamar me, dan bayan Aldusar Parks and Zoo da suka yi niyyar zuwa tun farko har Maryam Park suka ja ta.
Sai da ta yi nadamar binsu zuwa wannan yawon, kuma tsabar tijara duka da uniform suka fita, kowa ya gansu ya ga ɗalibai. Rabi da rabi hankalinta na kan wayar da Amira ke yi da Mahmud, wadda ke kwance tana wani juyi, alamun wayar tana kai mata har ka, ta wani kashe murya kamar ba ita ba. Ita har mamakin kalaman da Amiran ke amfani da su a wayar take, dan ita kam ji take ba za ta iya ba. A wani ɓangaren kuma zuciyarta ce ke raya mata cewar anjima kaɗan za ta shukawa Mahmud tsiya, domin Amira ba a abin arziƙi da ita, ko sun shirya to fa sai ta yi abin da zai sa su ɓata.
Har episode ɗin ya ƙara Amira ba ta gama wayar ba, da yake ta gaji sai ta rufe system ɗin, ta ɗorata a kan side drawern da ta raba gadonta da na Amira. Sannan ta ɗaga bargonta ta rufa a kan ƙafafunta, ta lalubo hula ta saka a kanta, sannan ta shiga yin addu'o'in bacci da na kariya.
"Ya Amira mu kwana lafiya"
Ta faɗa tana shirin kwanciya, shigowar Mummy ɗakin ce ta katse abubuwa biyu lokaci guda, kwanciyar Zahra da kuma wayar da Amira ke yi da Mahmud.
"Au! Har yanzu ba ku kwanta ba ke nan?"
Mummy ta tambaya tana binsu da kallo.
"Yanzu dai zan kwanta... Ya Amira kuma waya take"
"In ji wa? Ni ma kwanciyar zan yi ai!"
Cewar Amira tana harar Zahra, alamun dake nuna ke ke ba a rufin asiri da ke?. Mummy ta yi murmushi, kafin ta furta musu wasu kalmomi da za su zama sanadiyayyar rabuwarsu da juna na har abada.
"To! Daddynku yace ku shirya, zuwa gobe za mu tafi wurin Hajiya a Gyaza!"
Zahra ce ta fara zumbur ta tashi zaune tana kallon Mummy.
"Dan Allah Mummy?"
"Da ina muku wasa ne?... Sai da safe"
Ta ƙarashe tana rufe ƙofar, dan da ma ba ta gama shigowa cikin ɗakin gaba ɗaya ba. Zahra da Amira suka dubi juna, cike da farin cikin batun tafiyarsu Gyaza, domin gaba ɗayansu babu wanda bai son zuwa Gyaza, wato mahaifar Daddynsu, inda 'yan uwansa da mahaifiyarsa suke zaune... Dalilin son zuwansu Gyaza shi ne, ana nuna musu gata sosai, duk sanda za su je suna ganin gata a wurin 'yan uwan ubansu...
Kakarsu ma haka na matuƙar ji da su, duk da tun da yanzu lamuran tsaro suka ɓaci idan sun je ba sa kwana a can, zuwa suke su yini su dawo cikin garin Katsina. A cikin daren suka tashi suka fara shirya kayan da za su saka gobe idan za su tafi, kai kace zuwa za su su yi wata a can. Kuma tun a cikin daren Amira ta faɗawa Mahmud batun tafiyarsu zuwa Gyaza... Wata tafiya da za su yi nadamar yinta, a lokacin da nadamar ba za ta amfanesu da komai ba.
Salma Ahmad Isah ✍️
Zahra Royal Star 🌝
_________________
ZARGE littafin kuɗi ne, domin more naku sai ku biya ₦500 to.
5487270431
Salma Isah
Monie point
Sai ku tura shaidar biyanku ta 0813 047 9973
*ZARGE*
BY
ZAHRA ROYAL STAR
&
SALMA AHMAD ISAH
Page 05
*Unguwar Samaru, Gusau, Zamfara state, Nigeria.*
*08:22 na dare.*
FALAK POV.
Zaune take a falo, hannunta na dama riƙe da smoothie jar, yayin da take juya straw ɗin dake ciki a hankali da hannunta na hagu... Jin takun mutum ta wurin stairs bai sa ta kalli wurin ba, dan kowa ya yi wa Falak shaidar shariya da rashin kunya, wai kuma hakan ma ko kaso biyar cikin ɗari na halin ɗan uwanta Faisal ba ta ɗauka ba...
"A dawo lafiya Bilkis, dan Allah ki kula, ki duƙufa ki yi karatu sosai!"
Muryar Mama da ta ji ce ma tasa ta samu arziƙin kallon wurin da suke tsaye ita da Bilkis, ta sha dogon Hijab har ƙasa, domin da ma ita ba ta da shigar da ta wuce dogon Hijabi, a wasu lokutan ma idan za su fita tare da Falak sai tace ba za ta je da ita ba, don ita ba za ta bita da dogon Hijabi kamar matar takaba ba...
"Inshaallah Mama"
Faɗin Bilkis kanta a ƙasa, sai da Mama ta gama mata nasiha, sannan tace mata ta tafi, ta gaban Falak ta zo ta wuce tana mata sai da safe, wani ɗan iskan kallo Falak ta bita da shi, wanda yasa lokaci guda Bilkis ta kama kanta, sannan ta fita daga falon da sauri.
"Falak! Kallo ake ne?"
Mama ta tambaya yayin da take zaunawa a kan settee, Falak na zuƙar smoothie ɗin dake cikin jar ɗin hannunta ta kalli Mama, kafin ta ciro straw ɗin daga bakinta tana murmushi.
"Umm kallo nake"
"Ke ba za ki yi karatun ba?"
"Wani karatu kuma Alaji?"
Ta furta ba tare da ta damu da zancen karatun ba, domin a yanzu ba shi ne a gabanta ba, a duniya idan tana da maƙiyi to bai wuce karatu da makaranta ba, shi yasa a wasu lokutan take haura sati ba tare da ta leƙa makarantar ba, duk kuwa da yanda Kawunsu Alhaji Sammani wanda ya ci gaba da kula da kasuwancin mahaifinsu bayan rasuwarsa yake kashe mata kuɗi sosai a kan makarantarta.
A wani ɓangaren ma za ta iya cewa damuwar karatu ce ta saka ta fara shaye-shaye, ba wai dan ba ta gane karatun ba, haka kawai take jin cewa ta tsani makaranta da duk wani abu da ya shafeta, a lokacin da tace ba za ta ci gaba da zuwa makaranta ba Hajiya ta balbaleta da faɗa, har ta kai ga tace idan ba ta maida hankali kan karatunta ba sai ta tsine mata, kuma daga lokacin ta fara shaye-shaye.
"Ba exams za ku fara ba?"
Ta ɗan kalli Mama kaɗan, kafin ta girgiza kanta.
"Na sani, amma ni ba yanzu zan fara nawa karatun ba..."
"Sai zuwa yaushe ke nan? Uwar malalata"
Muryar Hajiya ta katse mata hanzari, dubanta ya kai kan Hajiyar dake tsaye jikin banister.
"Ai in dai ba za ki maida hankali a kan karatunki ba mun yi ta samun matsala da ke"
Ita dai ba tace komai ba, jar ɗin hannunta kawai ta aje a kan center table, Hajiya ta ƙaraso cikin falon, lokacin da Mama ke faɗin.
"Haba Hajiya? Ai ba haka za ki riƙa mata ba! Cikin lallami za ki na mata nasiha, ki kuma nuna mata hanyar da kike son ta bi"
"Humm! Maman yara ke nan! Yanzu Falak ba ta yi hankalin da za ta yi wa wani faɗa ba? Da wannan girman nata zan wani zaunar da ita ina lallaɓata?"
Ita dai Falak ƙala ba tace musu ba, dan idan ta faɗa ɗin ran Hajiya ne zai ɓaci nan take, kuma za ta iya yin kanta da faɗa, wata ƙila ma ta bugeta, yawan faɗan Hajiya yasa gaba ɗaya ba su yi wata shaƙuwa da ita ba, kullum cikin tsare gida take, babu wani lokacin samun kusanci irin na 'ya da uwarta a tsakaninsu, ita kuma ba ƙawa gareta ba ballantana idan damuwa ta mata yawa ta samu wani da za su tattauna da shi domin samun mafita...
Shi ko Faisal kar ma ta soma tunkararsa da batun shawara ko wani abu, mutumin da sai su yi wata ba su ga farin haƙorinsa ba, saboda sam shi dariya ba ta dame shi ba, kullum fuskar nan a ɗaure tamau, kamar haddarin da ya so zubar da ruwa, wasa na wa da ƙaninsa ma ba ya haɗata da shi, ballantana har ta kai su ga hira, kuma shi in zai yi magana umarni yake bayarwa, ka ƙi bi kuma jikinka ya gaya maka.
"Ina Bilkis ne? Ban ji motsinta ba"
Faɗin Hajiya, Mama ta yi murmushin jin daɗi.
"Ta tafi makaranta, tace yau a hostel za ta kwana saboda suna da exams gobe, so tana so ta yi karatu sosai..."
Hajiya ta wurgawa Falak dake latsa wayarta harara.
"Kin ji fa? Yarinyar kirki, wadda ba ta sa shashanci a gaba ba, ita karatun ne kawai a gabanta..."
"Ai ita ma Falak ɗin tana karatun Hajiya, kawai dai sai san barka"
"Ina fa..."
Ƙofar falo da aka ƙwanƙwasa yasa hirar tasu dakatawa.
"Falak tashi ki duba waye"
Falak ta aje wayar hannunta, sannan ta nufi ƙofar ta buɗe, tana arba da wanda yake bayan ƙofar ta ja tsaki a fili tana ɗauke kai.
"Falak waye?"
Hajiya ta tambaya tana zaune daga cikin falo.
"Sirikarki ta gobe ce"
Ta faɗi maganar cikin shaguɓe, tare da buɗe ƙofar gaba ɗaya, Maryam budurwar Faisal kuma ƙanwar Mama ciki ɗaya ta bayyana ga su Hajiya. Lokaci guda Hajiya ta washe baki tana miƙewa tsaye.
"Maryam? Ke ce tafe?"
Maryam dake tsaye a bakin ƙofa ta shiga ciki, yayin da Falak ke binta da wani kallon rashin kunya, duk da ta lura sai ta ɓoye, da yake ita ma 'yar bariki ce sai ta matsa kusa da ita za ta rungumeta tana faɗin.
"Ohhh my little sister..."
Dakatawa ta yi, lokacin da Falak ta ɗaga mata hannu alamun ta dakata.
"Ja jikinki a nawa!..."
Kawai tace, sannan ta juya ta ɗauki wayarta ta yi sama, shi ma wannan Maryam ta shaƙa, amma ganin Hajiya da Mama yayarta yasa duk ta shanye komai, ta nufi wurin Hajiya tana gaisheta kamar ta Allah. Hajiya ko kamar ta saka zani ta goyata, dan ita kanta ba ta ce ga dalilin da ya sa take son Maryam ba, kuma soyayyar da take mata ce tasa lokacin da ta nuna cewa tana son Faisal Hajiyar ta yi Uwa ta yi makarɓiya ta tilasta Faisal amincewa da soyayyar Maryam, duk kuwa da shi ɗin ba ya sonta.
"Amma dai a nan za ki kwana ko?"
Cewar Hajiya lokacin da ta kawowa Maryam drink. Maryam ta yi sipping drink ɗin, kafin tace.
"A'a, yanzu ma zan koma, mun yi magana da Major ne a kan wani book da na daɗe ina naima, yace mini shi kuma yana da shi, shi yasa na zo karɓa"
Hajiya ta kama baki tana 'yar dariya.
"Ikon Allah! Ai kuwa kin ga bai barwa kowa keyn ɗakinsa sai Bilkis, ita kuma yanzun nan ta fita!"
Kamar da gaske Maryam ta ɓata fuska cikin rashin jin daɗi.
"Oh oh, amma ban ji daɗi ba Wallahi"
"Ah haba Maryam? Kar ki ji ba daɗi mana, bari na saka Falak ta zo ta duba miki"
"Za ta yarda kuwa? Kin san halin Falak fa?"
Hajiya ta ja tsaki.
"Ita ta haifi kanta?"
"A'a Hajiya, amma bari dai na ƙira wanda zai iya sakata ko da ranta bai so ba"
Ta ƙarashe tana latsa wayarta, a cikin contact list ta naimo lambar 'Heart beat' sannan ta aika masa ƙira.
Falak na shiga ɗakinta ta kwanta a kan gado, damuwar Hajiya da abin da mata duk sun bi sun hanata bacci... Da ta ga ba za ta iya ba sai ta tashi zaune, sannan ta sauka daga kan gadonta ta sunkuya a ƙasan gadon, ta miƙa hannunta ta janyo wata jaka dake ƙasan gadon, ta fito da wasu kwalaban kayan maye guda biyu, ta mayar jakar ƙasan gadon, sannan ta zauna a kan gado, ta buɗe kwalba ɗaya tana shirin ɗurawa cikinta wayarta ta dakatar da ita... Tsaki ta ja, sannan ta rufe kwalbar tana miƙa hannunta saitin wayar, ganin sunan 'MR. BEAST' ya fito ɓaro-ɓaro a kan screen yasa ta zaro ido. Ta yi saurin aje kwalbar, ta goge bakinta, har da su kimtsa kanta kamar wadda ya ƙira videocall.
"Assalamu alaikum! Ya Faisal ina yini"
Ta faɗa a salihance, domin ko kusa ba ta son abin da zai haɗata faɗa da Faisal, dan sai ta gwammaci barin zaman gidansu gaba ɗaya a kan Faisal ya yi fushi da ita. Daga cikin wayar, wata murya mai kauri, wadda ta ƙunshi zallar kamewa da kwarjini ta fito ta doki dodon kunnenta.
"Da ban wuni ba za ki jini haka? Kina ina?"
Falak ta juya idonta, a ranta kuwa faɗi take. _"Masifaffe"_
"Ina zan je a lokaci irin wannan? Ai ina gida?"
"Ok! Maryam ta zo, ki je ɗakin Bilkis ki ɗauko keys ɗin ɗakina, ki je ki buɗe, a cikin wannan shelf ɗin